← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 47

Sashe 38

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta warware mayafi da tayi kallabi dashi ta yafa a kanta ta fita, yana jingine da motarsa ta tsaya a gefensa tace, "Sannu da zuwa ranka ya d'ad'e ka shammaceni sai dai kuma na ji dadin ganinka." Babu yabo babu fallasa yace, "Ina Little Aliyu da Muhammad?" Ta ce, "Suna makaranta."

Ji tayi yace, "Miye a tsakaninki da Aliyu?"

Saida gabanta ya yanke ya fad'i amma ta dake, tambaya ce wacce bata tab'a zatonta daga gareshi ba. Tace, "Aliyu babana, ya tsaya min a lokacin da Hisham ya gujeni. Yayi min gata a rayuwa. Na daukeshi kamar uba mahaifi."

Ashraim ya dubeta da mamaki sai kuma yace, "Kina nufin wannan shine kadai abun da yake a tsakaninku."

Hafsat ta samu kanta gyad'a kai duk da tasan k'arya ne, Ashraim ya girgiza kai yace, "Hafsat na so a ce kin fad'a min gaskiya. Angel, a rayuwata na tsani k'arya da wasa da hankali." Ya kunna recording na wayar da nada na video call dinta da Aliyu. "Hafsat na soki a shekarun baya kuma har yanzu ina sonki saidai na lura ba tani kikeyi ba, a kullum idan nayi maki maganar aure sai ki ce in dakata. Hafsat zuciyarki tana wajen Aliyu don haka na hakura dake, ina maki fatan alheri a rayuwa."

Tana kiran sunanshi yayi banza da ita, ya shige motarsa ya wuce, tunda ranar bai k'ara kiranta ba idan ta kirashi bata samu, tayi kuka har ta gode Allah, wannan shine abun da Jalila take guje mata, she brought it upon herself, ta janyo wa kanta da kanta, ta kori wanda yake shirye da aurenta, akan wanda mahaifiyarsa tace ko bayan ranta ya aureta bata yafe ba. Tayi matuk'ar nadama abun da ta aikata wanda hausawa suke kira da 'Sakin na hannu kamun na dawa'

*****

Kwana biyu Aliyu ya lura da ta daina mashi maganar Ashraim yana son ya tambayeta amma yana tsoron kada abun da yake zargi ya zama gaskiya, dukkanin samarin Hafsat shine sanadin rabuwarta dasu, shine sanadin da ya saka har yanzu ba tayi aure ba.

Aliyu ya tsareta da idanu yace, "Ina Ashraim?" A karo na biyu tayi k'ok'arin kawar da hirar saidai kallon da yayi mata ne ya saka ta bashi amsa, "Na rabu dashi." Tace a takaice.

Aliyu ya murtuke fuska yace, "Mi yasa kika rabu dashi?" Kanta tsaye tace, "Saboda Aliyu nike so kuma ya fahimci hakan, ya gaji da yawo da hankali da nike mashi. Bugu da kari yayi min tambaya akan abun da yake a tsakaninmu sai na zab'i da inyi mashi k'arya. Saidai kash abun da ban sani ba shine yana hujoji akan soyayya dake a tsakaninmu."

Tausayinta ya kamashi yace, "Hafsat mi yasa kikayi haka? Ummana bata sonki, na sani idan nayi magana wa Alhajinmu zai bari in aureki saidai Hafsat kin sha wahala a rayuwa, kin hadu da kalubale masu yawa, ina guje maki da kiyayyar uwar miji ba."

Hafsat ta fashe da kuka tace, "Amma Aliyu ina sonka." Aliyu ya ware idanu sannan yace, "Yau kuma a Aliyu nike." Ta share hawayen dake fuskarta tace, "Tun da kana so ka rabu dani ne na daina cewa Yaa Aliyu, Aliyu zan ce."

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 17

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*

*ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY*

*WE CREATED ALL KIND OF GRAPHICS SUCH AS: FLYER, LOGO, BANNER, INVITATION AND MORE*

*WE SELLS SHADDA, ATAMFA, SHOES AND BAGS, MATERIALS, VEILS, UNDERWEAR, HIJABS AND KITCHEN UTENSILS*
*CALL 09160588758 CHAT 09017040402*

*Kina Buk'atar Flyer, Logo, Banner, Invitation Card Da Sauran Ayyuka Da Suka Shafi Graphics Design, Kina Son Aiki Mai Kyawu Akan Farashi Mai Rahusa, ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY Shine Amsarki.. A ZARAH GRAPHICS DESIGN AND GALLERY Zaki Samu Tsala-tsala Da Galla-gallan Shaddoji, Atamfofi, Takalma, Jikkuna, Material, Under wears, Veils, Hijabs Da Kayan Kitchen, Kayansu Suna Da Sauki Da Rahusa, Ku Kira 09160588758 Ko Kuma Kuyi Magana Ta WhatsApp 09017040402 Domin Gwangwaje Kanku Da Kayansu Masu Sauki Da Rahusa.*

Jin shiru ta zare wayar daga kunnanta tana mai kai kallonta akan majigin wayar, tsinke kiran yayi, ta fashe da kuka tana mai tausayawa kanta akan abun da ta aikata ta yi sanadin tafiyar Ashraim akan Aliyu, wanda ba ta da tabbacin samun sa, ta yi sakin na hannu kamun na dawa, ta yi sanadin tafiyar wanda ya ke sonta a dalilin wanda ba ta da tabbacin samu.

Tun daga ranar ba su k'ara waya ba, idan ta kira numbarsa ba ta samu, ta shiga damuwa sosai, ta rame, ba ta iya cin abincin kirki sai dai ta tsakura kadan ta bar ragowa. Har Umma ta lura ta tusata a gaba tana tambayarta abun da ya ke faruwa, ta share hawayen da su ke zubo mata ta ce, "Ashraim ya tambayi abun da ya ke tsakanina da Aliyu na yi mashi k'arya, a tunanina bai fahimci komai ba, ashe har hujja a yana da ita, ya ce ya tsani k'arya, ya ce ya hakura da ni. A ranar da mu ka yi waya da Aliyu na sanar da shi, tun daga ranar bai k'ara samun numbarsa ba." Ta dakata da magana tana mai fashewa da kuka sannan ta ce, "Umma na yi babban kuskure na kori wanda ya ke shirye da aurena akan wanda mahaifiyarsa ba ta kaunata."

Umma ta jinjina kai, ta yi shiru na wani lokaci kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce, "Allah ya zab'a mako abun da ya fi zama alheri a gare ki duniya da lahira."

Hafsat ta amsa da, "Amin." Hawaye suna zubowa daga idanunta, da sauri ta goge hawayen a dalilin shigowa da yaran su ka yi, mikewa ta yi ta haye bene ta shiga dakinta, durkushewa ta yi a kasa ta fashe da kuka idanunta akan hoton Aliyu da ke manne akan bangon dakin. Kira ya shigo wayarta kamar ba za ta duba ba sai kuma ta mika hannu ta janyo wayar ta duba, Aliyu ne, ta amsa ta yi shiru tana mai sheshshekar kuka.

Daga daya bangaren muryarsa kamar wanda ya tashi daga barci ya ce, "Koda kin kira numbata ba ki samu ba karki damu kanki, zan yi tafiya da zarar na dawo zan aureki. Hafsat ni Aliyu zan aureki, wannan alkawari ne da na yi maki." Ya tsinke kiran ba tare da ya ba ta damar da za ta yi magana ba.

Tun daga ranar ta fara kirgar kwanaki, kwanaki suka koma watanni har aka yi wata shidda, ta kasa hakuri ta kira numbar k'anwarsa Mufida. "Tun da yaya Aliyu ya ce min zaiyi tafiya watanni shidda kenan ban k'ara samun numbarsa ba."

Mufida ta fashe da kuka, hankalin Hafsat ya tashi tana tambayarta abun da ya faru. Tana kuka ta ce, "Ya dawo daga tafiya Italy watanni biyu da suka wuce, a ranar da ya dawo yazo gida akan hanyarsa ta zuwa gidansa ya yi hatsari ya shiga doguwar suma, yana a coma na tsayin watanni hudu."

Hannunta ya fara rawa, wayar ta sub'uce daga hannunta kanta ya yi mata doom. Ta zube a kasa daga nan ba ta sake sanin inda kanta ya ke ba sai dai farkawa ta yi ta tsinci kanta kwance akan gadon asibiti da karin ruwa akan hannunta. K'arar ruwa da ta ji a bandaki dake a ward din ya tabbatar mata da Umma tana a ciki. Ta yi hanzarin zare karin ruwan daga hannunta ta duro daga saman gadon ta fita. Sai dai fitowa Umma ta yi ta ga wayam.

Hafsat ta taka a kafa har bakin titi ta tsayar da kekenapep ya sauketa a asibitin. "Ina kudina?" Ya tambaya ganin tana neman tafiya. Ta girgiza kai ta ce, "Babu kudi a wajena." Ya fito zai yi mata tijara, matar dake a ciki ta dakatar dashi, "Ba ka ga halin da take a ciki ba." Ya juya a fusace ya ce, "Za ki biya mata ne? Na ga ba ta sanar da ni ba ta da kudi ba har saida na sauketa, muguwa kawai."

Hafsat ta yi murmushi mai ciwo, tashin hankali ne ya saka ta manta da babu kudi a hannunta. Matar ta ce, "Da ina da kudi da na biya mata." Hafsat ta yi murmushi ta ce, "Er uwa na gode..." Da sauri ya katseta, "Idan kunnenki baiji daidai ba torh cewa ta yi ba ta da kudi da ta biya maki." Hafsat ta jinjina kai ta ce, "Na ji abun da ta ce da kyau, ina ce akan kudinka ne torh zan biya." Ta juyawa matar ta ce, "Please er uwa ki ara min wayarki." Matar ta fiddo wayar daga jikka ta mik'a mata, ta amsa ta dauko application tayi logging ta mik'awa matar ta ce, "Ki saka account numbarki?" Da mamaki matar take kallonta sai kuma ta amsa ta saka, a take Hafsat ta tura mata dubu dari biyar 500k.

Matar ta ware idanu ta ce, "Dubu dari biyar ne." Hafsat ta murmusa ta ce, "Ki gode Allah da ya ciyar da ke, kyakyatawan halinki na tausayi da son taimako ne ya janyo maki." Ta juyawa mai kekenapep wanda jikinsa yayi sanyi, "Nawa ne kudinka?" Ta tambaya. Ya ce, "Dari biyar." Ta juyawa matar ta ce, "Ki bashi dari biyar daidai kudinsa." Ya washe baki ya ce, "Hajjaju." Jin ta tura dubu dari biyar wa matar amma shi ta ce a ba shi naira dari biyar, ta gane nufinsa ta girgiza kai ta ce, "Duk da ka gani ina a cikin damuwa amma sai ka zab'i ka ci min mutunci har kana kirana da muguwa. Damuwa da tashin hankali ne ya sakani mantawa na hau kekenka babu kudi a jikina, ka zama mai taimakon wanda ya ke da buk'atar taimako, maganar kudi daidai kudinka zata baka." Tana gama fad'ar haka ta juya ta shiga cikin asibitin.
Chapter 38 · 0% Book details