← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 47

Sashe 44

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su ka yi sallama kowace ta wuce wajen motarta, Hafsat ta manta ta dauki hanyar asibiti har sai da ta yi parking motarta a wajen ajiye motoci sannan ta ankara. Ta yi reverse ta ja motar ta wuce gida, haka ta wuni sukuku ta rasa abun da yake mata dadi, ta saba da kasancewa a tare da shi tana kulawa da shi.

Bayan sallar Asr ta kai mata abinci, da dare su ka je tare da Umma. Batuul ta mike tare da baiwa Umma kujerar da ta ke a zaune, "Ina wuni?"

"Lafiya lau. Ya mai jiki?"

"Da sauki."

"Allah ya k'ara sauki."

"Amin."

"Sannu da k'ok'ari kinji, Allah ya saka maku da alheri."

"Amin."

Kwana biyu Batuul ta yi tana kwana a wajensa Hafsat ta amsa itama ta yi kwana biyu, Hafsat tana shiga damuwa sosai a dukkanin lokacin da kwananta ya k'are, idan son ranta ta kasance a koda yaushe a tare da shi tana mashi hidima, ya yi mata halarci a rayuwa, dukkanin abun da ta yi mashi ba ta fad'i ba, ba ta tab'a ji ta gaji da jinyarsa ba sai dai karsashi da ta ke samu a dukkanin lokacin da ta ke kula da shi.

*******

Tana zaune tayi tagumi ya fara motsi da hannuwansa ba, ba ta lura ba har saida ya ware idanunsa a kanta ya kama hannunta yana murzawa a hankali ya ce, "Miye yake damun MATAR ALIYU?"

Da sauri ta maida dubanta a kansa tana ware idanu jin muryarsa, ya yi mata murmushi ya ce, "MATAR ALIYU mi yake damunki? Ki kwantar da hankalinki zan cigaba da rokonta har sai ta yarda da aurenmu."

Ta yi murmushi tana maida hannunta akan hannunsa ta ce, "Aure kuma? Da ma ana aure biyu ne? Wannan da take a gabanka MATAR ALIYU ce, MATARSHI TA BIYU." Ya ware idanu ya ce, "Ban gane ba." Ta ce, "Lokacin da baka farka ba aka d'aura auren." Da sauri yace, "Na ji wasu abubuwan sai dai yana min ne kamar a mafarki. Umma fa? Ta yarda?" Ta yi murmurshi ta ce, "Mamata kenan ta kaina, yadda take kulawa da ni ina jin sai ka yi da gaske domin tuni na kwace fadarka a wajenta." Ya fad'ad'a fuskarsa da murmurshi ya ce, "Alhamdulillah." The more yake murza hannunta the more hannun yake k'ara mashi taushi (Torh hajiya ki ce ki kula da jikinki kafin ki fara complain ba ya ba ki kulawa ki fara tambayar kan ki; Shin kina kula da tsaftar jikin ki? Shin kina kula da gyaran jiki? Haba sister ki kwana ukku ba ki yi wanka ba, bakin ki yana wari, hammata tana wari, turare kuwa daga biki sai suna a hakan ki ke tunanin za ki samu kulawa yadda ta dace. Kamar yadda na ce ki kula da tsaftar jikinki da ta gidan ki, kalolin girki daban-daban, kin ce ke kullum shinkafa da tuwo zaki rink'a girka mashi ay dole wata rana ya je wani wajen ya siya, kowa yana son canji, mun san akwai rashi amma wata koda shinkafa da wake ta girka sai kin ji ta yi daban, abun duk karatu da lissafi, kina iya asusu domin ki tara ki ware rana daya ki yi mashi girki mai kyau. Wata idan ta yi wa mijinta wata maganar sai kin ji kamar ki yi ihu; imagine ya yi mata matsa tsawa and she will be like kaga kada ka k'ara min tsawa or yoh miye nayi maka da zaka min tsawa, haba sister koda ya kawar da kai ke kanki kin san baki kyauta ba, let say yayi maki tsawa, ay kin san mijinki, na fad'i hakane saboda abun da za ki yi wa wani namijin ya yi dariya yana tsokanarki kina shagwab'a idan ki ka yi kuskuren yi wa wani namijin watalila sai kin samu tagomashin mari, mu je maganar da nike magana a kan ta, ya yi maki tsawa ay kin san mijinki kin san halinsa idan mutum mai son shagwab'a ne ki marairaice you can be like please mana ka bar min tsawa yana tsoratani, idan kuma mutum ne mai son girma ki ce, kayi hakuri daga nan ki yi shiru koda kuwa ke ce ki ke da gaskiya daga baya ki sameshi da lalama ki zayyana mashi komai, amma ranshi yana a b'ace ranki yana b'ace sannan ki ce dole sai kin nusar da shi ke ce mai gaskiya, anya kuwa abun zai yi kyau, idan yayi sama ke ki sauko. Ohhh ni MATAR ALIYU daga magana daya na buge da dogon sharhi).

Hafsat ta yunkura ta ce, "Ka tsaya in kira doctor." Ya rike hannunta gam ya ce, "A'a ki kyaleshi hannunki ne yana min dadin tab'awa ashe haka hannunki yake da taushi ALIYU ya yi dacen mata." Ta yi rolling idanu ta ce, "Itama MATAR ALIYU ta yi dacen miji." Ya murmusa ya ce, "Bani labari."

Kafin ta yi magana Batuul ta shigo tayi turus ganinsa a farke, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tana k'arasowa inda suke, ya mik'a hannu ya rike hannunta ya janyota kusa da shi yana murmushi ya ce, "Ranki ya d'ad'e." Echoe da ya ji har tsakiyar kansa ne ya tilasta mashi sakin hannunta ya dafe kansa yana sakin ihu tare da ture dukkanin abun da ya tari gabansa.

Batuul ta tsorata ta yi baya da sauri ta nufi hanyar kofa, Hafsat ta matsa kusa dashi tana k'ok'arin rikesa ya tureta ta fad'i a kasa warwas, likitoci suka shigo suka dukufa a kansa.

Ya farka ya warware sai dai gabobin jikinsa da suke mashi wahalar motsawa sai kuma ciwo da ya ke da shi a kansa, dalilin abubuwan da yake SUBDURAL HEMATOMA ne yake damunsa na jini da ya taru a kwakwalwarsa a sanadin ciwukan da ya ji, shine yake saka pressure a kwakwalwarsa yana janyo mashi abubuwan da suke faruwa dashi na abubuwan da yake, Abbi ya yi duba da akwai hatsari akan aiki da za'a yi mashi yana ganin Aliyun zai iya kamuwa da ciwon mantuwa ya manta da komai na rayuwarsa amma tunda jinin ba ya da yawa, jikinsa zai iya janye jinin ya samu lafiya ba tareda aikin ba.

Abbi ya girgiza kai ya ce, "Babu buk'ata aikin, Allah ya bashi lafiya." Suka amsa da, "Amin."

Washegari Umma tazo ta dubashi, ba ta dade da wucewa ba Abba ya zo tare da matanshi su biyu Aunty Halima da Aunty Jamila.

"Ya mai jiki?"

"Da sauki."

"Allah ya k'ara sauki."

"Amin."

Abba ya ce, "Sannu ka ji. Allah ya k'ara sauki." Aliyu ya ce, "Amin Abba, na gode."

"Allah ya sa albarka."

"Amin."

"Sannu kin ji Hafsat, Allah ya yi albarka."

"Amin."

Sun jima kafin suka wuce, kamar jira yake ya kama hannunta yana murzawa a hankali, ba ya gajiya da rike hannunta, ta murmusa ta ce, "Hannuna yana maka dadin rikewa." Ya sakar mata murmushi ya ce, "Eh saboda taushi da yake da shi, yana min dadin murzawa a cigaba da kula min dashi kin ji MATAR ALIYU."

Batuul ta turo kofa ta shigo, Hafsat tana kiciniyar kwace hannunta ya ki saki ta kalleshi ta kalli Batuul, gani tayi shi ko a jikinsa, ya mik'a hannuwa ya rike hannunta ya sumbata ya ce, "Ranki ya d'ad'e." Ta murmusa ta ce, "Ina wuni?" Bai amsa ba saidai gaisuwar da ya mayar mata, "Ina wuni?" Ta zauna a daya bangaren tana mai amsawa da, "Lafiya lau." Yace, "Daga zuwanki har yawuna ya tsinke, kin iya kin huta ta wajena, na karya maki hula." Har da yi mata alamar karya hular, ta yi dariya ta ce, "Na gode." Ya girgiza kai ya ce, "Nine da godiya ranki ya dade." Ya juya wa Hafsat ya ce, "Yane MATAR ALIYU." Ta yi murmushi kawai. Ta k'ara ji Aliyu ya shiga ranta saboda ba ya da b'oye-b'oye.

A bayyane yake yana matuk'ar son Hafsat sai dai kuma yana girmama Batuul matuk'a yana ganin girmanta, idan kana son ganin b'acin ransa ka nuna rashin kunya gareta, duk da kallo daya za ka yi masu ka fahimci ya girmeta nesa ba kusa ba amma yana bata wannan girman tamkar ita ce babba saboda ta zauna dashi duk da ta san akwai wacce yake so, duk da ta san cewa ba ita ba ce ba a zuciyarsa.

Batuul ta zuba mashi abinci tana bashi yana lumshe idanu yana santi, tana mashi dariya, lokaci zuwa lokaci yana saka Hafsat a cikin hirar, babu zato babu tsammani abun yazo ya dafe kansa yana mai fasa k'ara ya ture plate din dake hannun Batuul abincin ya tarwatse a kasa, ya tureta har saida kanta ya bugi bango saidai ba ta ji ciwo, ta yi baya da sauri ta gudu kofa tana waiwayensa yayinda tsoro ya bayyana k'arara akan fuskarta, tana da matuk'ar musamman a yadda yake abu kamar wanda ba ya a cikin hankalinsa.

Hafsat ta rikeshi tana k'ok'arin rungumeshi, "Ka nutsu, Aliyu ka nutsu." Da hannu daya yayi wurgi da ita ta bugu da bango tana mai sakin k'arar wahala tana shafa kanga taga jini.

Batuul ta zaro idanu ganin abun da ya yi wa Hafsat, ficewa ta yi da saurinta ta kira likita ta tsaya daga kofa tana lek'e, tana da tsoro sosai musamman na mahaukata shiyasa ta tsorata sosai da abun da Aliyu yake yi, ji take kamar zuciyarta zata buga saboda tsoro.

Har mamakin Hafsat ta ke yi ganin still tsaye a wajen duk da abun da ya aikata ba da jimawa ba, ta ga k'ok'arinta, abu ne wanda ba za ta iya ba tsoro zai iya ajalinta.

Tun daga ranar bata k'ara dawowa asibitin saidai ta aiko mashi da abinci, tun yana tambaya har ya gaji, har Ummi ta lura ta tambaya, "Ni kuwa shan banban nike da Fatima ne?" Ta tambaya, Aliyu da Hafsat su ka yi shiru aka rasa wanda zai bata amsa.

Ta dubi Hafsat sannan ta ce, "Daughter mi ya faru?" Hafsat ta yi jim kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, ta lumfasa ta ce, "Ina ganin ba ta da lafiya ne?"
Chapter 44 · 0% Book details