← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 47

Sashe 45

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaushe rabonta da zuwa?" Ummi ta tambaya. Hafsat ta ce, "Tun ranar abun ya faru." Ummi ta yi jim tana jinjina kai sannan ta ce, "Watakila ba ta da lafiyar ne amma abun akwai mamaki domin muna waya da ita, ina ganin saidai idan wani abun aka yi mata."

Da sauri Hafsat ta girgiza kai ta ce, "Babu abun da nayi mata." Ummi ta girgiza kai ta ce, "Kada ki damu daughter na san halinki, na san halin Aliyu, zan yi shaidarku akan ba za ku yi mata abu da gayya ba saidai a rashin sani ko kuma kuskure." Kafin ta rufe baki Hajiya Fadila mahaifiyar Batuul (Mommy) ta shigo, bayan ta gaidashi da jiki, ta amsa gaisuwar da Hafsat ta yi mata, da mamaki ta ce, "Ina Batuul ne kullum na zo bana samunta idan nayi magana ta ce mun sha banban ne." Ummi ta ce, "Abun da nike tambayarsu kenan suke sanar dani rabonta da zuwa tun ranar da abun ya faru, na ce watalila wani laifin su ka yi mata, tuhumar da nike masu kenan." Mommy ta girgiza kai ta ce, "Kai A'a duk yadda aka yi itace ba ta da gaskiya domin kullum idan na yi mata maganar sai ta ce mun sha banban ashe zuwa ne ba ta yi, mu je gidan in ci mata mutunci." Ummi ta ce, "A'a mu bi abun a hankali." Mommy ta murtuke fuska ta ce, "Hajiya Zaynerb za ki tashi mu je ne in ci mata mutunci ko kuma ban isa ba." Ummi ta yi dariya ta ce, "Zan je domin in kare diyata."

Mommy ta ce, "Allah ya k'ara sauki, ka yi hakuri ban san haukan da ta yi ba kenan." Suka fita tare da Ummi.

Daga Aliyu har Hafsat babu wanda yake da gamsasshiyar amsa akan dalilin Batuul na kin zuwa da kuma k'aryar da tayi wa Mominta.

*****

A fusace Mommy ta shigo falon tunda bakin kofa take fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

Batuul ta mike da sauri tana wuri-wuri da idanu ta raina gaskiyarta yayinda baki daya jikinta yake rawa, ta sanin Mommy farin sani, duk a kanta ta san cewa tana da dalilinta na rashin zuwan da kuma k'arya da ta yi amma tana tabbaci akan Mommy ba zata karbi uzurinta ba, ta yi sa'a idan a fad'a ta tsaya bai kai ga mari ba.

"Mijinki yana kwance a asibiti amma ke kina zaune a gida kin mika kafafu saidai ki girka ki aika masu da shi wato kin fi karfin kije dubashi, wato kin fi karfin ki kai abincin da kanki, ba muzurai za ki yi min ko wuri-wuri da idanu na rashin gaskiya, bude baki za ki yi ki sanar da ni uwar mi ki ke yi a gidan da har ba za ki je ki yi jinyar mijinki."

Batuul ta dubi inda Ummi take ta yi shiru, ba zata iya fad'in dalilinta a gaban Ummi ba, ta marairace fuska ta ce, "Mommy ina da dalilina, zan fad'a maki."

Mommy ta zauna akan kujera ta yi kwafa ta ce, "Ina sauraronki isassa."

Batuul ta yi kasa da kai ba ta son tayi maganar a gaban Ummi amma Mommy ta ka sa fahimtarta, ta ce, "Mommy zan fad'a maki. Mu je asibitin." Ta fad'a domin ta kawar da maganar.

Mommy ta yi mata tsawa, a fusace ta ce, "Babu inda za ki je sai kin sanar da ni dalilinki na kin jinyar mijinki saidai kike aike abinci, babu inda za ki je sai kin sanar da ni dalilin ki na min k'arya kika ce kina zuwa shan banban mu ke yi bayan kuma zuwan ne ba ki yi."

Sai a lokacin Ummi ta saka baki ta ce, "Adda Fadila kiyi mata a hankali, na tabbata tana da dalilinta."

A fusace Mommy ta ce, "Dalilin nike jira ta fad'a min tun kafin hakurina ya k'are inyi ta dukan tsiya."

Ummi ta ce, "A'a ban da duka."

Mommy ta yi kwafa ta ce, "Ta bari in k'ara magana a wajen ta gani idan ban yi mata dukan tsiya ba, idan tana tunanin zaki iya hanani torh ina mai tabbatar mata da cewa kema na isa dake tunda nice babba bugu da kari kina ganin girmana."

Batuul ta yi tsuru-tsuru da idanu ta rasa abun da yake mata dadi, Mommy ta sakata a tsaka mai wuya akan maganar da bata son tayi a gaban Ummi duk da tana da dalilinta amma akwai kunya.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 20
*KARSHE.*

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

Batuul ta yi kasa da kanta ta ce, "Ummi, Mommy, duk da abun da zan fad'a abu ne da kuka riga da kuka sani amma ina mai baku hakuri tun kafin na furtashi. Mun ina k'arama har zuwa girmana ina da tsoro, tsawa kanta tsoratani ta ke yi, ranar da abun ya fara faruwa na tsorata matuk'ar tsoro, na daure na karfafa ta cigaba da zama duk da tsoro da yake addabata, tsoro yake bani, ji nike kamar zuciyata za ta buga. A ranar da abun ya k'ara faruwa a ranar ne na tabbatar da ba zan iya ba, idan na tsaya zuciyata zata iya bugawa shiyasa na dawo gida na zauna."

Mommy ta fasa kuka tana mai taba hannuwa ta ce, "Fatima butulcin da za ki yi mamu kenan, Aliyuna yana da wacce yake so amma er uwata ta dage akan cewa sai ya aureka saboda gida bai koshi ba'a kai dawa ba, Aliyu miji ne na gari da kowace uwa za ta yi wa erta fatan samunsa, Aliyu yana ganin girmanki yana girmamaki duk da kuwa shine babba, amma butulcin da za ki yi mashi kenan, Fatima kin cika butulu."

Batuul ta fashe da kuka ta ce, "Please Mommy ki bar zubar min da hawaye, tsoro nike shiyasa ina gudun kada zuciyata ta buga."

Mommy ta kalleta da takaici ta ce, "Ba ke kikeyi wa kuka ba, kukan takaici nike da na dana sani na amincewa da nayi Aliyu ya auri butulu kamarki."

Sai a lokacin Ummi ta saka baki, ta ce, "Adda Fadila amma maganar Fatima abun dubawa tunda har shi Aliyu yasan tana da tsoro."

Mommy ta taso mata ta ce, "Idan ba zaki tayani jajen had'a Aliyu da wannan butulun da mu ka yi ba torh kiyi min shiru kawai ki barni inji da takaicin da yake damuna, na yi magana kun ce tsoro, ita wacce take zaune dashi ce maku tayi bata tsoron ne, ina ce a ranar har ciwo ya ji mata a kai, ko jiya da abun ya tashi saida yaji mata ciwo a hannu amma hakan bai saka ta gujeshi, yarinyar da muka kyamata saboda talaka ce, yarinyar da muka hana ya aura, yarinyar da muka fito kiri-kiri muka nuna masu sonta dashi, bugu da kari ba jininsa bace amma hakan bai saka ta gujeshi ba, yana kwance akan gadon asibiti a halin doguwar suma ta aureshi, ta zauna ta kula dashi, har yanzu da ya samu wannan matsalar bai gujeta. Sai ita da take jininsa ita ce zata bada mamu kasa a idanu, ta kunyatamu a idanun duniya, ta muzantamu, ta yi mamu butulci," ta nuna Batuul kafin ta ce, "Ba zan tabbatar da kina da tsoro ba sai kin kashe auren sannan tunda ke dai butulu ce." Mikewa ta yi tace, "Zaynerb ta shi mu wuce kafin zuciya ta debeni in yi mugun furuci akan butulun." Ganin ta dauki zafi sosai ya saka Ummi bata mu sa ba ta mike suka fito, Batuul ta biyosu tana baiwa Mommy hakuri amma koda kallon inda take ba ta yi ba ta saka Nauwara da Sultan a mota suka wuce.

***

Bayan Ummi ta koma gida tayi tagumi tana tuna abubuwan da ta yi wa Hafsat, ta nuna mata kiyayya ta yi mata gorin talauci, ta yi mata gorin asali, ta wulakantata, ta hana Aliyu ya aureta amma wannan bai hana Hafsat aurensa a lokacin da yake kwance a doguwar suma ba saboda bata rama sharri da sharri, gashi a yanzu lalura ta sameshi that ita er uwarshi da Ummi ta tilasta mashi aura ba zata iya kula dashi ba that tsoro yake bata saboda hali da ta tsinci kanta na tsoro tun a kananun shekaru. Hafsat wacce suka nunawa tsana ita ce take kula da shi, ba ta ga laifin Batuul ba domin tana da uzuri, nadama ta ke yi na abubuwan da tayi wa Hafsat, da ace hannun agogo yana komawa baya da ta tariyo baya ta goge dukkanin abubuwan da tayi wa Hafsat ta bari Aliyu ya aureta tun daga asalin farko.

Godiyarta wa Allah da ya ganar da ita gaskiya ta roki Hafsat ta auri Aliyu tun kafin lokaci ya kure mata, da a ce a wannan lokacin babu aurensa da Hafsat da damuwa ta yi mashi yawa, da ba ta san inda za ta saka kanta ba, ta share hawayen da suka zubo mata tana mai nadama abubuwan da ta aikatawa Hafsat a wadancen shekarun.

****

Batuul ta durkushe a wajen tare da fashewa da kuka, ta sani ta wata fuskar ba ta kyauta amma mi zai saka ba zasuyi mata uzuri ba, tana dalilinta wanda dukkanin wanda ta tashi a gabansa yasan yarintarta da girmanta ya kamata yayi mata uzuri, ta mike ta share hawayenta ta koma ciki ta yi wanka ta shirya ta dauko abinci ta shiga motarta ta kama hanyar zuwa asibiti.
Chapter 45 · 0% Book details