← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 47

Sashe 18

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fashe da kuka tace, "Yaya Aliyu kai yayana ne, ina daukarka ne a..." ya daka mata tsawa, "Kiyi min shiru a nan tun kafin na falla maki mari a wajen. Tun da kwakwalwarki da zuciyarki basu gane ba, yanzu zanyi maki da yaren da zaki fahimta." Ya lumfasa sannan ya saka hannu ya d'ago da fuskarta ya tsura mata idanu da kallonsa mai rikita zuciyarta yace, "Hafsat ina sonki, ina kaunarki, a shirye nike da yin rayuwa ta har abada dake, kije kiyi tunanin idan zaki iya rayuwa da wannan bawan Allahn wanda ya shafe shekara da shekaru yana dakon soyayyarki a zuciya." Ya zaro handkerchief ya goge mata hawayen dake fuskarta ta lumshe idanu yayinda kamshinsa ya ziyarci hancinsa. Saida ya kalli tsakiyar idanunta yace, "Hafsat ina matuk'ar sonki." Sannan ya juya ya wuce bangarensu.

Dukkanin abun da yake faru Alhaji Muhammad yana tsaye a balcony yana gani. Mutanen sukayi cirko-cirko aka rasa mai bakin magana.

Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tana tuna abubuwa masu yawa a tare dashi wadanda da ta kalleshi ta fahimcesu sosai a wancen lokacin zata gane yana sonta, kaiconta yana sonta amma wautarta tana mashi kallon yayanta.

Tana tuka motar tana kuka har suka iso gida, ganin Hisham a compound ta tsaya ta wanke fuskarta sannan ta nufi inda yake fuskarta a murtuke, da mamaki yace, "Waye ya b'atawa gimbiyata rai inji dalili." Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Hisham daga yau karka k'ara dawowa sai na nemeka da kaina." Ya ware idanu yana kallonta yayi mamakin kiran sunanshi da tayi kai tsaye da kuma furucinta. Yace, "Hafsat." A fusace tace, "Idan har ba kaine ka siyi goron sunana ba torh ka dakata da kiran sunana haka. Na rantse da Allah idan ka matsa min a yau zan kawo karshen soyayyarmu dama goguwa tayi gaba tubalin soyayyar marar foundation." Ta juya ta shige ciki.

Jiki a sanyaye ya shiga mota ya wuce, yana kiranta bata d'agawa ya shiga damuwa matuk'a, yana son ya tambayi Umma saidai ba ya da numbarta, gashi Hafsat tayi mashi gargadi da gaskiyarta take maganar, ba ya fatan abun da zai rabashi mai tuna mashi da mai gadon zinarinsa.

******

Kwana Hafsat tayi tana kuka tana d'aura laifin komai a kanta akan rashin gane Aliyu yana sonta, tunda safe ta shirya ta fita Umma tasan wajen Aliyu zataje amma tana hanata.

Aliyu yana daya daga cikin mutanen da Umma take ganin mutuncinsu matuk'a domin yana ganin girmanta, yana girmamata, a shirye take ta bashi Hafsat koda shine ya fi kowa talauci, ta shirya ta bashi Hafsat koda itace zata ciyar dasu. Namiji wanda kowace uwa da ta san ciwon kanta zata so diyarta ta samu.

A compound ta tsaya ta kira numbarshi har ta tsinke bai d'aga ba, ta d'aura kanta akan starry tayi shiru. Wayarta tayi tsuwwa shine yake kira ta d'aga.

Daga daya bangaren yace,
"Amincin Allah ya tabbata akan furen zuciyata mai haskaka zuciyata."

Ba ya da ra'ayi akan irin wannan soyayyar amma ya shirya sauyawa saboda ita, saboda sonta, tayi murmushi tace,
"Tare da kai."

Yayi dariya yace, "Ya aka yi baby na? Kinyi kewata ne inzo ki ganni."

Saida ta murmusa sannan tace,
"Ka fito ina layin gidanku."

Ya ware idanu yace, "Har haka kike sona." Ta gyad'a kamar yana a gabanta tace, "Har haka nike sonka Aliyu, sai jiya na fahimci matuk'ar son da nike maka." Ya saki k'aramin ihun nasara yace, "Gani fitowa."

Babu jimawa ya fito tun daga get yake sakar mata murmushi har ya shiga motar yace, "MATAR ALIYU, zinariyar zuciyata." Ta rufe fuskarta da tafukan hannuwa tana mai sakin murmushi.

Ya ware idanu yace, "Haka zamuyi soyayyar da kunya." Tayi shiru, yace, "MATAR ALIYU daga nan sai ina zamuje?" (ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION Kuyi mashi gargadi ya daina kiranta da sunana, sunan MATAR ALIYU na marubuciya Aysher Angel ne).

Ta turo baki tace, "Makaranta kuma ban ci komai ba." Ya shagala da kallonta, yace, "Kina nufin kallona da kikayi bai kosar dake ba, akwai inda naga ance kaunarka ta saka naji na koshi, bana iya cin komai sai na kalleka."

Dariya ya bata, ta fashe da dariya tace, "Anya kuwa? Ina gaya maka yunwa bata da hankali." Ya ware idanu yace, "Tunda hakane ina zamuje matata tayi kalaci." Ta ware hannuwa, "Ban sani ba." Yace, "Ni na sani."

Ya amshi tukin motar ya jata zuwa babban gidan cin abinci wanda ziyartarsa sai mai kudi da ya amsa sunansa mai kudi.

A tare suka ci yana mata hira tana dariya, sai take mamaki kamar bashi ba, tare sukaje makaranta ya tsaya gama lectures suka juyo.

Tun daga bakin get suke jiyo hargowa da ake yi cikin gidan. Ji tayi hawaye sun ciko idanunta ba zata manta wannan muryar ba, Hajiya Zainab ce.

A sanyaye suka fito daga mota. Hajiya Zainab tareda wata mata ne tsaye suna wa Umma tujara saidai abun mamaki koda uffan Umma bata ce. Wannnan ya k'ara tabbatarwa da Hafsat girman da Aliyu yake dashi a wajen Umma domin ta tabbatar da wani ne da ba wannan zancen ake yi.
A fusace Hajiya Zainab ta nufi inda suke ta d'aga hannu ta wanke Aliyu da mari, tayi wa Hafsat kallon kaskanci tace, "Tun wuri ki fita daga harkar yarona, tun dare baiyi maki ba." Ta juya wa Aliyu ta daka mashi tsawa, "Muje shashasha wanda bai san inda yake mashi ciwo ba, ina ganinka da izza ashe fanko ne, ka rasa wacce zaka furta kana so sai diyar er aiki, dangin tsiya da talauci marassa asali."

Hafsat ta durkushe ta fashe da kuka saida tayi mai isarta sannan ta mike wuce ciki.

A bangaren Aliyu suna komawa gida Alhaji Muhammad ya gyare Hajiya Zainab akan ta sanar dashi inda taje domin ya kira inda tace zatace a tabbatar mashi da bataje ba. Tayi shiru, ya dakawa Aliyu tsawa yace, "Ina kuka hadu?" Aliyu yayi kasa da kai yace, "Gidansu Hafsat." Alhaji Muhammad ya dubeta ranshi a b'ace yace, "Na hanaki shine kika je, torh gobe zanje da kaina neman mashi aurenta, ki kwantata wani abun kiga yadda zamu kwashe dake a gidan nan, aikin banza aikin wofi."

*****

Washegari da safe ta samu kiran Aliyu, daga yanayin maganarsa ta fahimci damuwa da yake ciki, saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ina son na rokeki wata alfarma." Tayi jim sannan tace, "Wacce alfarma?" Kamar ba zaiyi magana yace, "A yau Abbana zasu zo neman min aurenki a wajen mahaifin Jalila, ina son idan sun nemi ganinki kice mashi kina da wanda kukayi alkawarin aureshi." Ta fashe da kuka tana mai girgiza kai tace, "Amma ina sonka Aliyu." Yace, "Na sani. Abun ya fi karfina. Please kiyi min wannan alfarmar, ina maki fatan alheri a rayuwarki." Kyit ya tsinke kiran ta fashe da kuka, kuka take da dukkanin karfinta, kuka take kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa tana son Aliyu tana kaunarshi.

Wuni tayi tana kuka ta kasa cin komai, kallo daya mutum zaiyi mata ya gane taci kuka ba kadan ba, wajen karfe hudu Malam Jafaru mahaifin Jalila ya kirata akan yana son ganinta. Ta zura dogon hijab ta jata motarta zuwa gidan.

A can ta tarar dasu Alhaji Muhammad. Malam Jafaru ya nemi ganinta, a gabansu ya tambayeta, "Hafsat sun zo nemarwa Aliyu aurenki, miye ra'ayinka?" Ta fara kokowa da lumfashin tana tuna alfarmar da Aliyu ya nema da kuma kaunarsa da takeyi. A hankali tace, "Nayi alk'awarin aure da wani, sai daga baya ya fad'a min yana sona, bayan da nayi wa wani alk'awarin aure. Kuyi hakuri."

Alhaji Muhammad yace, "Babu komai diyata. Kije abunki, Allah yayi maki albarka." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Amin." Ta mike ta fita.

Tana tuki tana ganin hanya biyu-biyu ikon Allah ne kawai ya kaita gida lafiya. Tayi parking ta wuce ciki tana tafiya tana raba hanya, tana shige parlour ta zube a kasa.

Umma tayi kanta tana bubbugata saidai bata motsa ba, hankalinta a tashe ta janyo wayarta ta kira Hisham. Yana kusa da gidan hankali a tashe ya iso ya dauketa ya saka a mota suka wuce asibiti. Likitoci suka dukufa a kanta domin ceto rayuwarta, likita ya tabbatar mashi da damuwa ce tayi mata yawa, su guji b'ata mata rai. Ciwo tayi sosai, taji jiki kamar ba zata rayu ba, saukinta suna hutun tsakiyar semester ne, wannan yasa ciwon bai shafi lafiyarta ba, watanta biyu a asibiti sannan aka sallamota kuma Alhamdulillah tana samun lafiya saidai damuwa wacce har a lokacin take manne a zuciyarta.

Ranar talata sun fita unguwa da Umma, akan hanyarsu ta komawa Umma tace, "Muje gidansu Jalila, ina son inyi magana da Malam Jafaru akan turowa da Hisham yake so yayi."

Hafsat tayi saurin share hawayen da suka zubo mata ta sauya akalar motar zuwa unguwarsu a baya, tana parking suka fito, en unguwa suna ta kallonsu, Hafsat ta girgiza kai kawai kamar bata san suna yi ba.

Daga bayanta taji ance, "Sai shegen fi'ili sai kace bamu san asalinta ba, ubanta dan chacha, mashayi, uwarta er aikatau, uban ya gudu ya barsu, uwarta korarra ce daga danginsu, wacce danginta suka yafe." Wata tace, "Ke kada ta ji ki." Wacce tayi maganar tace, "Taji mana, ai ba karya nayi ba, ina sone ta tanka in casata saidai duk abun da zai faru ya faru."

Hafsat a cikin ranta tace, "Ba zanyi fad'a dake ba mai karfin maza. Ban had'a kashi dake, hakanan kawai ki goga min talauci."

Ta juya ta d'aga masu tana murmurshi, ta kular dasu ba kadan ba.

Umma tana a tsakar gida tana magana da Baba, Hafsat ta wuce dakin jalila wacce bata dade da dawowa daga makaranta ba.

Saida marece sannan suka koma gida, da mamaki take kallon motoci guda hudu dake a wajen ajiye motoci, Benz guda biyu, Jeep and range rover new model.

Yana zaune a bayan motarsa dake a gefe, ya gaida Umma, ta amsa da kulawa tana tambayarshi mutanen gida, ta wuce ciki.

Hafsat ta k'arasa tareda tsayawa a gefenshi, tace, "Da fatan ban shanyaka ba, ranka shi dade?" Ya girgiza kai yace, "Ko kadan." Ta murmusa tace, "Ba ka ce min zaka zo ba, kuma muka wuce gidansu Jalila."
Chapter 18 · 0% Book details