← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dauki cokali ya ciko da abincin ya nufi bakinta dashi, ta ture cokalin tace, "Ban son cokalin da hannunka nike so ka bani." Yayi banza da ita tareda tura mata abincin a baki, cokali na biyu ta goce tare da datsa mashi cizo a hannu tana gunguni, ya b'ata fuska yace, "Ouch." Tayi rau-rau da idanu tace, "Yunwa."

Na ukku ta amsa, na hudu ta goce ta k'ara mashi cizo, na biyar ta rink'a gocewa tana wahalar dashi, idan ya ajiye ta turo baki tace, "Yunwa."

Saida ta gama wahalar dashi a wajen cin abincin, ta mashi cizo sunfi biyar, bayan ta koshi ya bata ruwa tasha ta koshi, ta ture hannunsa tana turo baki, ji tayi yayi sama da ita ya dauketa, ya ajiyeta a saman kujera yayi pillow da kafafunta ya mik'a mata newspaper da yake karantawa yace, "Tun da kin cije hannuwan da nike rikewa dasu sai ki karanta min da kanki."

Ta cune fuska tace, "Bacci." Yace, "Ko muje a yi abun da mukayi jiya a saman gado." Ta zaro idanu gane abun da yake nufi. Ta amshi jaridar tana mai turo baki, kasa-kasa tace, "Shi mutum kullum sai yayi ta sakaka magana amma idan kayi kwalliya bai iya cewa kayi kyau ba."

Hisham yayi murmurshi, ya lumshe idanu tana karanta mashi, tana turo baki, da gangan take tsallake ya saka ta dawo baya, tana gunguni zata dawo ta had'a da inda ta tsallake.

Bilkisu bata da shagwab'a amma muryar Hafsat tana mashi dadi idan tana shagwab'a.

Bacci yayi awon gaba dashi, ta mike ta wuce kitchen ta had'a masu abincin rana ta jera akan dinning table, bayan ya dawo daga masjid, ta tarbeshi da fara'arta, tace, "Yaa Hisham, abincin rana ya sauka." Ya nuna mata kwandon dake hannunsa yace, "Momcy ta aiko mamu."

Tace, "Kaci wanda na girka, da daddare sai muci na Momcy, zan saka maka wargi saboda santi."

Ta jashi dinning table ta zuba mashi fried rice da romon kai data girka, ya kalli abincin, a rayuwa girkin mutum biyu yake ci, Umma da Bilkisu sai kuma k'anwarsa Fatima ko kuma idan ya girka da kanshi. Yace, "Hafsat abincin Momcy zanci, bamuyi dake ki shiga kitchen, idan kina son girki kiyi min magana in girka mamu."

Ta soma bubbuga kafafu tana fad'in "A'a." Tana shagwab'a akan yaci wanda ta girka.

Ya ture abincin da ta girka ya zuba wanda Umma ta aiko, da mamaki take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa itama ta zuba taci ta ajiye wanda ta girka da nufin su ci da dare, saidai ga mamakinta da daddare da kansa ya shiga kitchen ya girka masu tana mashi maganar wanda ta girka yayi banza da ita ya kyale, karshe saidai mai guard ta mik'awa girkin da tayi, abun ya bata mamaki da kuma haushi.

Daga wannan ranar bai k'ara mata komai ba, suna zaman lafiya, ya hanata shiga kitchen da kanshi yake masu girki, idan ta girka yaki ci saidai taci abunta ita daya, idan tace suci a plate daya yayi mata banza, kullum cikin daukar wanka take amma ba ya yabawa saidai yawan saka tayi mashi hira da karanta mashi jarida, abun yana damunta saidai ta rasa yadda zata b'ullo mashi, koda tayi mashi korafi ba ya gyarawa.

Jalila tazo tareda k'awayensu, Fatima itama tazo tayi masu wuni.

BAYAN SATI DAYA.

Hafsat sakarwa kanta shower tayi brush ta fito ta zura guntuwar rigar barci ta kwanta tana mai janyo laptop dake a gefe, tana kallon series, tunda daga episode na daya takeyi wa kanta karyar bari in k'ara guda daya sai in kwanta, har ta raba dare tana kallon bata ajiye ba saidai ta sauya kwanciya tare da sauya mazauni wa laptop da take kallo a ciki, kadaici ya dameta ba ya kulata tana kunyar samunsa da kanta, lokaci daya taga wutar dakin ta dauke yayinda wani jan haske ya bayyana, wata murya mai amo ta fara ihu tana kiran sunanta ana fashewa da mahaukaciyar dariya.

Hafsat ihu take tana guje-guje amma a banza, babu mai jinta, tayi iyakar k'ok'arinta domin ta bude kofa amma abun yaci tura, da gudu ta haye gado ta kwanta tareda jan bargo ta rumtse idanu ji tayi ana lilo da dagon yayinda ta fara sautin fashewar glass, tana bude idanu taga dakin ya wuya sama ta koma kasa, an fasa kayanta.

Ta toshe kunne tareda fashewa da kuka, har karfe ukku ana abu daya, dakyar ta samu bacci yayi awon gaba da ita.
Hisham ya shigo dakin yana tayar da ita, da sauri ta bude idanunta zata fasa k'ara taga komai daidai, ta mike zaune tana k'arewa dakin kallo ganin komai yana zaune a mazauninsa, yana kallonta da mamaki yace, "Kina neman wani abu ne?" Tace, "Wayata." Yace, "Ki tashi kiyi sallah."

Ya juya ya fita, ta maida kallonta akan system dake a gefenta, a inda ta tsaya a nan yake, an saka pause kuma ta tabbata ita dai bata saka pause, saidai kuma rashin sauyawar dakin ya saka ta soma tantama, kanta ya kulle, shin mafarki ne tayi ko kuma ya faru da gaske, saidai tambayar shine; Shin waye ya danna pause? Da mamaki tareda tsoro a ranta ta shiga bandaki tayi alwalla ta fito ta tada sallah, bayan ta gama ta kasa komawa bacci tana tsoron ta k'ara mafarkin da tayi jiya, a cewarta mafarki ne, babu wanda ta baiwa labari amma abun ya tsaya mata a rai, wuni tayi tana tunanin abun.

Daddare a tsorace ta kwanta, saidai ga mamakinta ta nemi bacci a idanunta ta rasa, gani tayi dakin ya fara juyawa ta mike da sauri tare da kama gefen gado, dakin ya fara girgiza yana juyawa, idan ya juya baki daya kayan su koma a daya bangaren, kamar yadda ake juya waina a cikin tanda hakanan dakin yake juyawa, tana ihu tana kururuwa amma babu mai cetonta, baki daya kayan dake a dakin sun fashe sun tarwatse ruwa suna kwaranyowa daga bandaki. Kuskuren da Umma tayi a rayuwa shine rashin saka baiwa Hafsat ilimin addini sosai, tunda ta gama sekondire ta ajiye karatun islamiyya saidai boko.

Har aka fara kiran sallar asuba ana abu daya, gilashin mirror ne ya nufo fuskarta gadan-gadan, ta rumtse idanunta kamar daukewar ruwa taji shiru sai kuma takon tafiyar mutum, tana bude idanunta taci karo da Hisham, yace, "Har kin tashi kenan." Ta gyad'a kai, ya kalli hannunta da sauri yace, "A ina kika ji ciwo?"

Da mamaki take kallon ciwon dake a hannunta, sai kuma ta maida dubanta wa dakin wanda yake kamar yadda yake, babu abun da ya sauya. Babu jimawa ya dawo da first aid kit, ya gyara mata ciwon yana tambayar yadda ta sameshi, ta rasa amsar da zata bashi, ta ware hannuwa alamar bata sani wanda yayi daidai da kai dubanta da tayi akan mirror wanda taga ya tsage, ta k'arasa inda yake da sauri, da gaske ya tsage, Hisham dake bayanta, yace, "Ya aka yi ya fashe? Ko dashi kikaji ciwon?"

Ta girgiza kai tareda ware hannuwa, da mamaki ya kalleta sai kuma ya fita ya wuce Masjid, ta shiga bandaki tayi alwalla ta fito tayi sallah, bacci da ba ta koma ba kenan, duk bacci ne cike da idanunta amma tana tsoron komawa har barawon bacci yayi awon gaba da ita, bayan ta tashi ta shiga bandaki tayi wanka ta fito da nufin tayi kwalliya a gaban mirror maimakon taga fuskarta sai taga fatalwa a mazauninta, ta fasa ihu tare da komawa gefe, ta k'ara lek'awa amma still fatalwa ta gani, tayi tunanin watakila ta fara gane-gane ne, ta shirya ta fita tareda kama hannunsa, tace, "Kazo kaga idan nayi kyau." Tayi hakane domin tabbatar da fatalwa ta gani da gaske ko kuma gane-gane ne takeyi.

Tayi tsaye a gaban mirror duk da fatalwa take gani amma ta dake tana son jin abun da zaice, tace, "Ya kalleni ta cikin wannan madubin ka fad'a min idan nayi kyau." Ga mamakinta ji tayi yace, "Kinyi kyau MATAR HISHAM. Muje ki karantawa mijinki jarida." Ya tabbata ita kadai take gane-ganenta, a ranar ta saka zani ta rufe dukkanin madubi dake dakinta, ganin wannan fatalwar tada mata hankali yake, tun daga ranar bata sake duba kanta a madubi ba saidai tayi wanka ta shafa cream ta goge fuskarta.

Hisham bai lura ba, da yake ba damuwa da yayi da kwalliyarta ba, abubuwa suka taru sukayi mata yawa, ta rasa wanda zata sanar mawa, babu wanda zai yarda da ita, abun ya fi kama da mafarki amma sai yake mata shige da zahiri; Shin miye yake faruwa da ita? Tambayar da take fatan tana da amsarta.

Dare yana farawa jikinta ya soma rawa, ta takure a jikin gado tana rawar jiki, dakin ya fara girgiza, da gudunta ta nufi kofar da ta bari a bude, saidai kafin ta k'arasa kofar ta rufe kanta da kanta, yayinda wasu kananun halittu suka bayyana suka yanyameta suna cizonta, tana ihu tana kururuwa amma a banza, sukaji mata ciwo, jini ne yake ta zuba daga jikinta.

A hankali ta bud'e idanunta ta tsinci kanta kwance akan gado, ta mike da sauri tana bin jikinta da kallo, babu koda kwarzane a fatarta, sawun cizo daya ta gani a gefen hannunta, ta ware idanu.

Hisham ya bude kofar ya shigo sai kuma ya tsaya daga bakin kofa yace, "Har kin farka kenan." Ta gyad'a kai ba tareda tayi magana ba, ya juya da nufin ya wuce yana mai cewa, "Ki tashi kiyi sallah." Ganin zai fita tayi sauri tace, "Ranka shi dade." Hisham ya juyo tareda zuba mata idanu, tace, "Tsakar dare ina bacci na rink'a jin ihu da kururuwa."

Ya girgiza kai yace, "Ban ji komai ba."

Tace, "Ina jin banji daidai bane."

Ta duro daga saman gado ta wuce bandaki tayi alwalla ta fito ta tada sallah ta gama tayi kuri da idanu, duk da idan ta koma bata gane-ganen amma tsoron komawa take, tana zaune tana karantar wasikar jaki har bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 11

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
Chapter 22 · 0% Book details