← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 47

Sashe 23

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

A wannan daren Hafsat taga tashin hankali, sama aka rink'a yi da ita ana shillo, ana juyar da ita sama zuwa kasa ana dariya, ana fara kiran sallar asuba aka wular da ita kasa, tana bude idanunta ta ganta kwance akan gado, har zuwa wannan lokaci ta kasa ganewa, shin mafarki take ko kuma gane-gane? Ta rasa wanda zata tunkara da maganar tana gudun a yi mata kallon mahaukaciya.

Hisham ya shigo yaji k'arar ruwa a bandaki ya juya ya wuce Masjid, a ranar da ciwon kai ta wuni na rashin barci, ta wuni tayi kanta yana juya mata, ji take kamar zai fashe saboda ciwo tana son tayi barci amma ya kasa, ji take komai ya fice mata a kai, ta rasa abun da yake mata dadi, tana jin barci tana son abun da zaije ya dawo, wuni tayi sukuku, har ya tambayeta, ko karatun jarida ba tayi mashi ba, tayi shiru ita kadai tana tunani, ba zata iya ba koda k'aryata za'ayi sai ta fad'a.

Da daddare ta dauki katuwar rodi ta rike a hannunta tana jiran abun da zai faru, ji tayi an danneta yayinda iska ya fizge rodin daga hannunta, aka rink'a bugar mata fuska da kai dashi, dukanta rodin yake tana ihu yayi mata jina-jina yayinda dukkanin wani abu mai tsini dake a dakin yake farmakarta suna bullewa a jikinta, tana ihu yayinda wata murya mai amo take cewa, "Kinyi gangancin auren wanda ya fi karfinki, kinyi gangancin auren mijin wata, Hisham ya fi karfinki, tun wuri ki san inda dare yayi maki tun bamu haukata ki ba, mune muke maki komai, tsayawar wahalarki yana a hannunki." Ba karamar wuya tasha ba.

A hankali ta bud'e idanunta, ta ganta kwance a bandaki, ta mike da sauri tana dube-dube inda zataga rodin amma babu shi babu alamarsa, tunawa da tayi abun bedroom ya faru, ta fito da sauri domin ganewa idanunta, saidai komai yaja a inda yake, ta hargitsa dakin ta bincike komai amma babu rodi babu alamarsa.

Hisham yayi tsaye yana kallonta da mamaki, ganin ta hargitsa dakin, yana mata magana, ta tureshi ta wuce inda ta dauko rodin bata ganshi ba, ta zagaye gidan tana nema amma babu shi babu alamarsa.

Ta durkushe yayinda maganganun da aka yi mata suke dawo mata a kai, Hisham ya tab'ata, "Angel, miye kike nema?" Ya tambaya.

Abun da yake damunta yafi karfin tambayarsa, ya gama zama a gidan, ta tureshi tareda fasa k'ara, ta shige motarta ta mata ta fice zuwa gidan Umma, ko parking din kirki ba tayi ba, ta b'alle motar ta fito ta wuce ciki da gudunta, ta wuce su Iman a parlour suna gyarashi ta haura saman bene.

*****

Hankalin Hisham ya tashi sosai, da gudu ya koma ciki ya dauko makullin mota yabi bayanta saidai bai san hanyar da tabi ba, ya bugi starry yana mai fasa ihu, yana tsoron kada abun da ya faru da Bilkisu ne ya faru da ita.

*****

Da mamaki Umma take kallonta ganin daga ita sai daurin kirji, gashin kanta kamar na mahaukaciya sabon kamu. "Angel, lafiyarki?" Umma ta tambaya tana kallonta daga sama har kasa.

Hafsat ta fashe da kuka tace, "A motata nazo, Umma na gama auren Hisham, aljana ce ta aureshi, kullum sai tazo min da dare tana wahalar dani, tana tsoratani, abubuwan firgici da razani, rabona da inyi barcin kirki har na manta." Ta kwasge dukkanin abun da yake faruwa ta sanar da Umma.

Umma tace, "Muga cizon da kuma ciwon." Ta ware idanu ganin babu cizon babu ciwon, Umma ta kanga mata madubi tace, "Mi kika gani?" Hafsat ta ware idanu fuskarta dauke da mamaki ganin fuskarta a maimakon fatalwa da take gani, saida Umma ta maimaita mata tambayar sannan tace, "Umma, fuskata na gani."

Umma taja tsoki tace, "Hakanan saboda mafarki kinzo kin tada min hankali. Angel kece kallo da daddare, baki alwalla idan zaki kwanta, baki damu da addu'ar kwanciya bacci ba, wasu lokuttan kina kallo bacci zaiyi awon gaba dake, ai dole kike mafarkai, ke da kanki kika siyawa kanki." Ta lumfasa sannan tace, "Hafsat yaushe rabonki da karatun Alk'ur'ani?" Hafsat ta ware hannuwa domin ba zata iya tunawa ba, Umma tayi salati tana tafa hannuwa tace, "Kina nufin karatun Alk'ur'ani saidai na karatun sallah kikeyi, sannan kice zakiga daidai. Hafsat ki rike karatun Alk'ur'ani da azkhar, babu wani mugun mutum ko aljan da zai samu nasara a kanki, addu'a takobin mumini ce, Alk'ur'ani waraka ne." Hafsat ta gyad'a kai tace, "In sha Allah." Umma ta jingina kai tace, "Kiyi kalaci, kiyi wanka, ki sauya kaya ki wuce gidan mijinki."

Hisham ne ya fado kamar wanda aka jefo, ya sauke ajiyar zuciya ganinta, Umma tace, "Sai ki tashi kibi mijinki, motar direba zai kai maki. Daga mafarki sai ki biyo kafa ki tafo saboda sakarci."

Hisham yana tukin motar ya dubeta yace, "Miye ya faru?" Tayi shiru kamar bata ji ba har saida ya maimaita tace, "Mafarki ne kuma laifina ne ina sakaci da addu'a zan gyara." Daga nan bata sake magana ba har suka iso gida. Saida gabanshi ya yanke ya fad'i, hango motar dake a harabar gidan, ya gangara da motarsa suka fito.

Aysha ta b'alle murfin motarta ta fito tana tafiya tana murmusawa, murmushi na mugunta, Hafsat ta kalleta da mamaki, Hisham yace, "Aisha."

Aisha tace, "Ehhh Aisha shine sunana wanda aka daura mamu aure... Sannu Amarya Hafsat ko ince Angel. Hisham's Angel. Da fatan kina lafiya koda yake daga ganin yadda kike daga ke sai daurin gaba da wannan kan kamar mahaukaciya nasan aikina yayi aiki."

Hafsat ta ware idanu tana maimaita abun da tace, "Aikinki yayi aiki."

Aysha ta fashe da dariya tace, "Ohh yanzu na gane dalilin da ya saka ya rude a kanki, muryarki ce ta saka ya aureki."

Hafsat ta zaro idanu tana had'a abubuwan da suka faru tunda haduwarsu har zuwa wannan rana, tabbas biri yayi kama da mutum, sakata tayi mashi hira, ta karanta mashi littattafan hausa, ta karanta mashi jarida, a koda yaushe burinsa yaji muryarta.

Aisha ta kwashe da dariya tace, "Bari in gama dashi kafin in dawo a kanki."

Hisham ya daka mata tsawa, "Aisha!." Ba ta razana ba saidai rike kugu da tayi tana wani shegen murmurshi tace, "Hisham tsawarka ta daina tsoratar da ni don haka ka daina wahalar da kanka. Nayi maka gargadi amma ba kaji ba kaje kayi aure, kai a tunaninka barazana nike, babban kuskuren da kayi shine tsallake magana kuma ita ce zata girbeshi, zakaga aiki da cikawa, ni ce matarka ta farko, uwar gida ran gida, daga ni ka rufe, dukkanin wacce tace zata rab'eka ta janyowa kanta bala'i, kamar yadda na mahaukata amaryar da kayi min Bilkisu ta gudu har yanzu ba'a san inda take ba, kamar hakan ne zan haukata wannan idan ba tayi wa kanta karatun ta nutsu ba, ta gudu da kanta, tun kafin ta gudu a halin hauka."

"Miye kike cewa akan muryata? Wacece Bilkisu?" Hafsat ta jefa mata tambaya.

Aysha tayi murmurshin samun nasara, tayi aiki taga kamar bai ci ba shiyasa tazo ta ganewa idanunta sannan ta haddasa rikici a tsakaninsu ta hanyar fallasa abun da ya faru da Bilkisu domin ta tabbata dukkanin mai hankali ba zata aureshi ba idan taji abun da ya faru da ita. "Ki tambayeshi, yana da amsoshinki, ke a tunaninki kin samu daula a banza, kinga mai kudi, kin makale mashi babu bincike, kwadayin kudinki ya saka kin auri wanda ya fi karfinki, tun wuri ki san inda dare yayi maki tun kafin in fusata in haukataki kika bi duniya ba, kamar yadda Bilkisu take a can, sun nemeta har sun gaji. Kina ganin kin samu miji," ta nuni zuwa Hisham ta dora da cewa, "Torh mijina ne ni kadai, bake ba, ko wacece tace zata rab'eshi sai na illata rayuwarta, zai zame maku guguwar bala'i mai tarwatsa farin ciki. Abun da ya faru dake kwanaki biyar da suka wuce, gargadi ne, idan kikayi burus zaki hauka ce. Idan kina ganin k'arya nike, ki zauna ki gani." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo tana mai cewa, "Kin zo kina min barazana da asiri, a baya asirinki ya wahalar da ni ne saboda sakaci da nayi da addu'a amma a yanzu daidai nike dake, muje zuwa, ni fake shege ka fasa dan halak sai yanka." Ta juya ta shige ciki barci ne sosai a idanunta ji take kamar zata fad'i, ta rakasa dakinta tayi alwalla tayi sallar asuba, ta kunna karatun Alk'ur'ani tana mai binsa da kira'arta mai dadi yayinda nutsuwa ta sauka a dakin, taji nutsuwa har cikin zuciyarta, babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita, bacci mai cike da nutsuwa, ta samu barci sosai, lokacin da ta tashi ta nemi ciwon kan ta rasa, tana mai jinta a cikin nutsuwa, ta karanta addu'ar tashi daga barci kafin ta duro daga saman gadon ta wuce bandaki tayi wanka ta zura doguwar marar nauyi ta fito ta sameshi a parlour kallo daya tayi mashi ta wuce dinning table ta sameshi wayam, ta kalli inda yake tace, "Yunwa nikeji ko kuma har da horon yunwa ka shirya min bayan rufeni da kayi ka aureni duk da kasan abun da zai faru dani."
Chapter 23 · 0% Book details