← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 47

Sashe 17

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

*This Page Goes To Fahau's Chambo, Hajara B B, and Bhatool Diamond. MATAR ALIYU ina gaishe daku. Nace maku; Wait for it, well here is it, drama iya drama 😅 🤣 😂*

Har Hafsat ta mike sai kuma ta koma ta zauna tace, "Umma gidan aikinki fa."

Umma tace, "D'azu nike tunanin haka, daga daukar hutu sun jini shiru, ya kamata inje inyi masu bayani."

Hafsat ta gyad'a kai tace, "Gobe sai muje tare a motata."

Umma tace, "Makarantar fa?"

Hafsat tana mike tana tunkarar matakalar bene tace, "Test kadai zamuyi kuma yace sai wancen satin. Bani da komai gobe."

Ta zauna a balcony dake a bedroom dinta, ta kira numbar Jalila, tace, "Yau sai ga ranka shi d'ad'e ya turo mamu en aiki, sai mamaki nike wai mune da en aiki, dariya ta kusa kufce min na fuske, na tuna yadda ake yi a novel."

Jalila tayi dariya tace, "Hajiya Hafsat Haruna. Hisham's Angel. Bani labari?"

"Da farko na tambayi sunayensu, na sanar dasu girki da gyaran dakunanmu zanyi da kaina, ban san ganinsu kusa da bedroom dinmu ko kitchen. Suyi girki suci suba maza masu aiki. Nace ban san k'azanta, hayaniya, gulma, shiga harkar da babu ruwanka, magana da maza masu aiki, suna gama ayyukansu ban san ganinsu a bangarenmu. Kowace ta zab'i aikin da zatayi."

Jalila ta fashe da dariya har tuntsurawa tace, "Hajiya Hafsat. Mata a gidan Hisham." Hafsat tace, "Idan aka barsu sakaka, kowace cewa zatayi tayi abun da ranta yake so, wasu lokuttan kana zafi ne domin a zauna lafiya."

Daga daya bangaren Jalila tace, "Yaushe zaki shigo?"

Hafsat tayi jim sannan tace, "Gobe zamuje gidansu Yaa Aliyu tareda Umma tayi masu bayani. Saidai jibi zan biyo in daukeki mu wuce school."

Jalila tace, "Gobe zan shiga school, course da nike carrying, muna da test." Hafsat tace, "Allah ya taimakeki da aka fasa wancen." Jalila tace, "Ke dai bari. Allah ne ya dubi al'amarina, kadan nayi karatunshi, na maida hankali akan wannan, sai kuma Allah ya taimakeni aka fasa."

Hafsat ta saka dariya tace, "Wannan semesterr idan muka gama jarabawa, idan nayi bacci, hutu, sai na mayar da jikina."

Sun jima akan waya, Hisham ya kira ta tsinke kiran ta amsa kiransa, kamar kowane lokaci tana picking yace,

"Angel. Ya aka yi? Ki bani labari."

********

Washegari bisa umarnin Hafsat, bayan sallar asuba masu aiki suka shigo suka gyara gidan ban da kitchen, dakin Umma da dakin Hafsat.

Karfe goma na safe Hafsat ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar Magrib, ta janyo wayarta dake akan bedside drawer ta duba sannan ta mike zaune ta duro kafafunta kasa ta wuce bathroom, ta jima tana hade jikinta a kwamin wanka sannan ta sakarwa kanta shower, ta d'aura towel ta fito ta bude closet wanda yake shake da kaya kala daban-daban wadanda koda zatayi shekaru tana sakawa ba zasu k'are ba, ta saka doguwar riga marar nauyi, ta yane kanta da mayafi ta gyara dakinta, ta wanke bandaki sannan ta dauki wayarta ta fita parlour.

Umma tana kallon wa'azi, tayi hugging dinta daga baya, tace, "Ummana. Ina kwana?"

Umma ta shafa kanta tace, "Lafiya lau. Kin tashi lafiya?"
Hafsat tace, "Lafiya lau. Umma bara inje in gyara maki bedroom."

Umma ta rike haba tace, "Sai in zauna zaman jiranki, tun da asuba na gyara dakina, abincin safe yana akan teburin cin abinci."

Hafsat ta dafe kai tace, "Ina son in samu lada amma barcin safe ya janyo min. Sun zo sun gyara gidan ne?" Ta tambaya. Umma tace, "Tun da asuba, suka gama suka wuce."

Hafsat tace, "Ya fi, ban san ina yawan cin karo da mutane."
Umma ta girgiza kai tana mamakin wannan halin na Hafsat na rashin son mutane, "Angel na rasa inda kika samo wannan halin na rashin son mutane, duk duniya k'awarki daya, Jalila sai kuwa k'awayenki na boko, suma idan kina dasu kenan."

Hafsat tayi murmurshi tace, "Jalila, aminiyata ta kaina, saboda tana son ta cigaba da karatu kuma mahaifinta ba ya da halin daukar nauyinta shiyasa ta fara kasuwanci, take fad'i tashi domin ta samu ilimi."

Umma tace, "Allah yayi maku albarka."

Hafsat ta amsa da, "Amin." Ta wuce dinning table, bread ne, kosai da kunu, taci ta koshi sannan ta koma parlour dake a saman bene ta kunna kallo.

Ta koma dakinta ta shirya cikin lifaya fara mai tsada, ta zuba gold masu tsada, a wuya da hannu, piecer, ta zura takalma half cover ta feshe jikinta da turaruka, duk da simple makeup ce akan fuskarta amma tayi matuk'ar kyau.
Ta dauki hotuna a balcony, ta samu Umma zaune a parlour dake kasan bene, suka fita harabar gidan, ta gangara da motarta inda Umma take, ta shiga, ta danna horn mai guard ya wangame mata get, ta danna motar waje, tana janta a nutse.

A wani katon gida tayi parking, Umma ta fito tace, "Bari in fara zuwa bangaren Hajiya Kaka."

Hafsat tace, "Ina bangarensu Yaa Aliyu."

Aliyu yana zaune a parlour yana karanta jarida, kyakykyawa gaske, kyakykyawan namiji mai cikar kamala, kakkarfa, son kowa kin wanda ya rasa, ta zauna a hannun kujerar dake a zaune, tace, "Yaa Aliyu."

Aliyu ya d'ago tareda zuba mata idanu ba ya koda kyaftawa, har saida ta k'ara kiransa yayi firgigit yace, "Lovely."

Ta murmusa sannan tace, "Amma kana nufin tun da na shigo baka lura dani ba saida nayi maka magana."

Aliyu ya ajiye newspaper dake hannunsa tareda maida hankalinsa a kanta yace, "Na bari ne ki gama kare min kallo abunki. Har haka kike son Angel." Ta saka hannu ta rufe fuskarta tace, "Babu ruwana." Yace, "A ranar aurenmu akwai ruwanki."

Wasu en mata guda hudu suka sauko daga saman bene suna kallonta da mamaki, daya daga cikinsu tace, "Angel."

Hafsat tayi masu murmurshi, ta lura da kallon da suke amma tayi kamar bata gane ba, tace, "Na'ima. Rumana. Oumsalmerh. Hajjo. Kuna lafiya."

Kallonta suke da mamaki, idanunsu akan gold dake a wuyanta wanda yake da dogon igiya mai fad'i, ta lura dasu saidai ta nuna kamar bata sani tana wa Aliyu hira, wanda ya mayar da hankalinsa baki daya a kanta.

Halima ta shigo da mamaki tace, "Naga sabuwar mota a compound. Munyi baki ne?" Rumana tace, "A'a."

Halima tace, "Yaa Aliyu, ka sayi sabuwar mota ne."

Aliyu ya girgiza kai. Halima tace, "Kuzo kuga motar, sabuwa, ta linka motar Yaa Aliyu kudi sau ukku."

Hagsat ta gane akan motarta suke magana amma ta zab'i da tayi shiru abunta, "Yaa Aliyu. Da fatan zata zo aurena?" A lokaci yanayin fuskarsa ya sauya, ya tsareta da idanu yace, "Kin tab'a ganin inda ango ya rasa aurensa." Ta fashe da dariya tace, "Waye angon? Waye amarya?" Ya murmusa yace, "Hafsat ce amarya. Aliyu angonta."

Hajiya Zainab ce ta sauko falon tana kallonsu yayinda ta murtuk'e fuska, kallon kaskanci da tayi wa Hafsat, saida Hafsat taji ta muzanta.

Aliyu ya dauki jarida da ya ajiye, Hafsat ta koma ta zauna akan kujera tace, "Ummi. Ina wuni?"

A takaice Ummi tace, "Lafiya."

Umma ce ta shigo ta gaidata ta amsa a takaice, yaran gidan suka zagaye Umma suna fad'a mata yadda zasuyi kewarta.

Aliyu yace, "Maman tuwo zamuyi kewarki." Suna kiranta da maman tuwo ne saboda ita ce take kula da tuwon Alhaji Muhammad Abbansu.

Hafsat ta wuce sauran sassan gidan, Aliyu ya mike, Ummi ta murtuk'e fuska tana kallonsa ya koma ya zauna, jim kadan ya fakaici idanunta ya fita.

Hafsat ta fito daga bangaren Hajiya Kaka wanda shine na shiga karshe, ta jingina da motarta tana jiran fitowar Umma daga bangarensu Aliyu, bata son komawa lura da Hajiya Zainab ba ta sonta.

A fusace Aliyu ya fito daga bangaren ya durfafo inda take kamar mayuwacin zaki, ta tsorata matuk'a, ta takure a jikin mota tana jiran ya wanka mata mari duk da bata san abun da ya b'ata mashi rai amma daga yanayinsa ba k'arami bane ba, ya daka mata tsawa saida tayi baya da sauri. A fusace yace, "Aka ce aure zakiyi?" Ta gyad'a kai muryarta tana rawa tace, "Eh." Tana tantamar idan shine abun da ya b'ata mashi rai, hargowa da yake ne ya janyo hankalin mutanen gidan suka fito sukayi cirko-cirko suna kallonsu. Ya daka mata tsawa yace, "Ni kuma sai kiyi ya dani? Ina kike son in saka sonki da na dauki shekara da shekaru ina ginawa a cikin zuciyata." Da mamaki take kallonsa da tsoro a bayyane a fuskarta, tace, "Ban gane abun da kake nufi ba." Ya daka mata tsawa a karon da bata san adadinsa ba yace, "Kina nufin baki son ina sonki ba." Ta gyad'a kai alamar eh hakane, ya fashe da dariyar takaici yace, "Kina nufin dukkanin alamomin da nike nuna maki baki gane ba. Waye kike son ki rainawa wayo? Huh. Kiranki waya da nikeyi mu jima muna hira, sakonni da nike tura maki ina tambayar halin da kike ciki, kasancewa a tare dake, ziyara da nike kai maki makaranta akai-akai, duk kina nufin baki dauki haske ba, duk kina nufin baki gane sonki nike ba, torh hafsat kaunarki nike, wacce irin kwakwalwa gareki ko kuma kina sone sai na fasa kirjina na dauko zuciyata na baki sannan zaki fahimta, a tunani na koda kallon da nike maki mai hankali zai gane so da kauna dake tattare da kallon."
Chapter 17 · 0% Book details