Sashe 40
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi kasa da kanta tana sauraronsu, Alhaji Muhammad ya lumfasa sannan yace, "Hafsat a ranar kin rokeki akan inyi maki alfarma in maidata kuma na mayar da ita. Nima a yau nazo ina rokonki da girman Allah kiyi min alfarma ki fad'a min gaskiya akan tambayar da zanyi maki, kada kiji kunyata ko nauyina ki cuci kanki. Hafsat shin akwai wanda kuka daidaita dashi a yanzu na maganar aure?" Ta girgiza kai tace, "Babu..."
"Ashraim fa?" Ya tambaya tayi mamakin jin tambayar saida tayi jim sannan ta ce, "Ya rabu dani saboda ya fahimci ba shi nike so, wanda nike so daban."
"Waye kike so?" Ya tambaya. Kamar ba zatayi magana sai kuma tace, "Aliyu." Yace, "Amma Aliyu ba shi da lafiya, mutumin da yake kwance kamar gawa, ba'a da tabbacin abun da zai tashi dashi ko kuma lokacin da zai tashi. Shin ba ki gujewa kanki zaman takaba? Shin ba ki gujewa kanki zama jiran wanda baki san ranar farkawarsa ba? Da yarintarki ko ba Ashraim zaki samu miji wanda yake sonki inda hankalinki basu kwanta."
Tace, "Saidai kash Aliyu ne a zuciyata, ita zuciya tana da son mai kyautata mata, koda Aliyu zai shekara hamsin a haka, a shirye nike da aurensa, Aliyu nike so, shi nike so, ina da tabbaci akan idan nice a wannan halin bazai gujeni ba." Ta mike ta fita.
Ta samu Mama a babban falo, babu jimawa Baba ya shigo ya zauna yana mai sanar da ita yadda sukayi. "Ya nemi a d'aura auren a sati mai zuwa? Mi kike gani?" Ta gyad'a kai tace, "Allah ya bamu zaman lafiya." Suka amsa da, "Amin."
"Abbanki fa kina ganin mu yanke hukunci ba tare da tuntubarsa ba?" Baba ya tambaya. Hafsat tayi murmurshi tace, "Mama kiji baba wai tambaya yake. Mama a yanzu a garin nan Abbana ba ya da wani amini da ya wuce Baba." Mama tace, "Hakane kuma. Malam dukkanin hukuncin da ka yanke ka sani bazai ce komai ba." Baba yace, "To shikenan." Ya koma falon baki wajensu Alhaji Muhammad.
Mama ta zubowa Hafsat masa da miya ta gyara zama akan carpet ta ci ta koshi ta kora da zubo. Ta gama suka sha hira da Mama. Hafsat ta kira Jalila tana mata tsiya, "Yarinya kinyi missing kin gani a gaban Mama ina ganin gata masa da miya in gaya maki naci har babu waje." Jalila tace, "Shine sai kin kira kinyi min gori." Hafsat tayi dariya tace, "Har kin bani tausayi koda yake bari na dauki hoto in tura maki." Daga daya bangaren Jalila tace, "Sai inja Allah ya isa." Hafsat tayi dariya tace, "Saboda kinga na samu gata, ke kuma sai kin shiga kitchen kinyi, yarinya ina gaya maki girkin Mama duniya ne har guzuri zanyi, in shige da abuna daki inyi kurmusu." Jalila tace, "Sai kikayi rashin sa'a ina da numbarsu, yanzu zan kira in fad'awa yarana kina zuwa su dauke abincin su cinye na basu, koda ban ci ba idan yarana suka ci kamar na ci, bugu da kari sun ayi halin rowa a gidansu." Hafsat ta zaro idanu tace, "Kai! Kyauta da abun wani." Tace, "Mama kinji ta wai labari zata kaiwa yaranta idan naje tayi masu kyautarsa." Mama tayi dariyarsu ta manya tace, "Idan Masa ce bata had'a fad'a kowa da kowa zai samu." Hafsat tace, "Jalila kinji kowa da kowa zai samu, ban dake." Tana dariyar shakiyanci. Sun jima suna waya ta sanar da ita abun da ya faru. Jalila ta tayata murna sosai tare da masu fatan alheri domin ita shaida ce akan matuk'ar son da Hafsat ta ke yi wa Aliyu, ita shaida ce akan matuk'ar son da Aliyu ya ke yi wa Hafsat.
Saida marece Hafsat ta wuce gida da cooler niki-niki, abincin dare da basuyi ba a gidan kenan, masar Mama ta wadatar.
Sati guda a tsakani Al'ummar musulmai, en uwa da abokan arziki suka shaida daurin auren Aliyu Muhammad tare da Hafsat Haruna (Angel), daurin aure da ya samu halartar mutane masu yawa, manyan masu kudi, mutane da yawa sunyi mamaki da al'ajabi duba da angon yana a doguwar suma wanda babu tabbacin ranar tashinsa, suna jinjina amaryar tayi matuk'ar k'ok'ari, ta nuna sadaukarwa.
Hafsat ta tare a asibiti jinyarsa, Batuul tana wuni saidai dare yana yi take wucewa gida. Hafsat ce a gaba a kula dashi, itace take mashi komai, ba ta tab'a korafi, Aliyu yayi mata abun da ba zata tab'a mashi butulci ba, tayi mashi kaunar da bata tab'a wa wani ba.
(INA LABARIN HISHAM?)
*********
Tun bayan auren Hafsat da Aliyu. Bilkisu ta kasa gane kan Hisham abubuwan sun k'aru, abu kadan zai fara fad'a yana tumfar baki, kullum shine cikin damuwa da tunani, idan tayi magana ya balbaleta da fad'a, yaronta Suleiman bai isa ya rab'eshi zai fara fad'a yana zare idanu yaron ya dameshi.
Ta gama abinci ta jera akan dinning table ta caba ado ta zauna a parlour tana jiran dawowarsa, ko kallon inda take baiyi ballantana amsa gaisuwarta da sannu da zuwa da ta tarbeshi dashi. Ya raba ta gefenta ya wuce upstairs, ba ta yi kasa a gwuwa ba tabi bayanshi, yana zaune a gefen gado tayi still tare da kiran sunansa, "Hisham." Ya d'ago da idanunsa da suka sauya launi yace, "Miye? Kin zo ne ki k'ara min akan damuwa da nike da ita, huh, ki fice min daga daki." Tace, "Amma ba ka ci abinci ba." Ya daka mata tsawa saida ta razana tayi baya da sauri, ya mike yana durfafo inda take kamar mayuwacin zaki yace, "Sai kuma aka ce dole sai abincinki ne zan ci, huh, na ce ki b'ace min daga gani." Tace, "Hisham kai mijina ne, ni kuma matarka, idan ban tambayeka damuwarka ba waye zai tambaya, nice muke zaune a gidan nan tare, Hisham tsoro kake bani a yanzu." Da hannu daya yaja ya wurgar a kofar daki, "Idan zaman da ni baki iyawa sai ki tattara ki wuce gidanku babu dole." Yaja kofa ya rufe har da murza makulli.
Jiki a sanyaye ta koma parlour, saidai bayar da abincin tayi, ta rasa abun da yake mata dadi, tayi tagumi a parlour har dare bai fito ba. Ta wuce sama ta kwankwasa, ta k'ara kwankwasa, "Abbansu." Da tsawa yace, "Miye kuma?" Tace, "Tun d'azu baka fito ba." Saida ya k'ara mata wata tsawar sannan yace, "Sai kuma aka ce dolene sai na fito zaki wuce daga nan ko kuma sai na fito na watsar dake a compound na kulle kofa tukunna." Za ta yi magana sai kuma ta fasa ta juya ta koma dakinta yunwa takeji sosai amma ta kasa saka komai a bakinta saboda damuwar halin da Hisham yake a ciki.
Tsakiyar dare matsananciyar yunwa ta tayar da ita dolenta ta shiga kitchen ta girka abincin taci har zata wuce dakinsa sai kuma ta dawo ta kanga kunne akan kofar, sheshshekar kuka taji, tace, "Abbansu kuka kake ne?" Ya bamko kofar ya kama hannunta ya wurgar da ita compound ya maida kofa yayi locking gashi kuma kofar baya ta kitchen a kulle take. Tayi tsaye tana zullumin yaro da ta bari a bedroom, tana knocking amma shiru har ta gaji ta sulale a kasa tana mai fashewa da kuka, haka ta kwana a zaune a harabar gidan, hankalinta ya rabu gida biyu a tsakanin tunanin halin da Suleiman yake a ciki, ya farka? Miye zaiyi idan bai ganta ba?
Cikon ikon Allah ya farka ya sauko falo tana jin motsi ta ce, "Waye a nan?" Suleiman yace, "Nine Momma." Da sauri tace, "Bude min kofa." Yace, "Waye ya rufe maki kofa Momma."
"Na fito ta rufe." Tayi mashi k'arya.
Ya bude mata kofa ta shiga tana tambayarta ta shareshi ta kama hannunsa suka wuce sama ta rufe dakinta zuwa yanzu al'amarin Hisham ya fara bata tsoro.
Bayan ta gama sallar asuba ta shiga kitchen ta had'a masu breakfast, ta soya masu kosai, ta dama kunu, ta soya dankali da doya da ruwan shayi tareda indomie saboda Suleiman, sanin da tayi koda tayi wa Hisham magana ba zai ci ya saka ta zuba a kwando ta saka mashi a mota.
Ta zauna tayi kalaci tareda Suleiman, bata jin cin abincin amma ta daure taci gudun kada yaron ya fahimci halin da take a ciki, ta shiryashi cikin uniform ta dauko lunch box direba ya wuce dashi makaranta.
Tana zaune a parlour lokacin da Hisham ya sauko parlour zai fita, ba tayi yunkurin mashi magana saidai cewa da tayi, "A dawo lafiya." Wanda bata samu zarafin amsa ba ya fice abunsa, ta bi shi da kallo fuskarta dauke da damuwa.
Bayan fitarsa ta fito harabar gidan taci karo da kwandon da saka mashi abincin a watse a kasa wanda ya tabbatar mata bata arziki aka fitar dashi ba, abincin da ta dauko lokaci ta shirya masa shine ya watsar a kasa, ji tayi hawaye sun zubo mata.
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 18
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057