← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 47

Sashe 6

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jalila tace, "Ki gama dubawa ki zabi wanda zaki dauka mu wuce." Ta kalleta ta watsar, "Tunda na jiraki kika gama, dolenki ki jirani in gama, ina zamana a dakin Ummana ina hutawa kika tadoni." Jalila tace, "Ki zo ki daina zaman banza ko data ne ki fara siyarwa." Hafsat ta zaro idanu tace, "Da kuwa dake da kika bani shawara, dani da na dauka duk sai Umma taci kaniyarmu." A tare sukayi dariya, suka wuce inda ake biyan kudi aka lissafa masu, Jalila ta mik'a card dinta aka zare ta amsa aka zuba masu kayan a leathers suka fito suna tafiya a hankali.

Jalila tana bata labarin dalilin fitowar, "Ciniki nike sosai a cikin kwanakin nan shiyasa nace gwara in fito inyi wa kaina shopping inci mai kyau, kin san abaya guda biyar na siya amma ukku kawai na nunawa Mama, suma ban fad'a mata aihinin kudinsu ba." Hafsat ta fashe da dariya tace, "Sai ranar da tace kije ki siya mata irinsu ne, a ranar ne zaki gane k'arya babu kyau. Ya kikayi da sauran?" Jalila tace, "Na b'oye na saka a kasan akwati."

Wani kyakyatawan saurayi ne yasha gabansu yana murmushi, sukayi turus suna kallonshi cike da mamaki, idanunsa akan Hafsat yace, "Kamar na sanki." Ta gane sarai bai santa ba, kawai neman hanyar da zaiyi magana da ita yake yi, tace, "Laa kamar baka sanni ba." Ya dubi Jalila yace, "K'anwata kinji ta fa?."

Jalila tace, "Na rasa bakin magana." Yace, "Ko kuma kina san ki tarewa k'awarki ne. Sunana Al'ameen."

Hafsat tace, "Besty muje."

Yace, "Idan babu damuwa muje sai in saukeku a motata." Ya k'arasa maganar yana nuna masu dalleliyar kirar Mercedes Benz ash colour dake a parker, Hafsat tace, "Mun ce maka muna shigar mota dukkanin wanda yayi mamu tayi ne. Bamu shiga motar samari."

Al'ameen yayi murmurshi yana mai yaba kyawunta, yace, "Shikenan." Ya mik'a mata katinsa, "Ga katina ki kira mu k'arasa hirar, tunda na daura idanu a kanki kyawunki ya tafi dani."

Hafsat ta raba ta gefensa ta wuce ba tareda ta amshi katin ba, ta k'arasa bakin titi ta tsaida kekenapep, Jalila ta shiga, Hafsat tace, "Kofar kaura."

Jalila tayi dariya tace, "Kuna dirama." Hafsat ta tab'e baki sannan tace, "Yana da naci."

Jalila tace, "Ya bani katin na saka a cikin biscuits dinki."

Hafsat ta kalleta da sauri tace, "Mi yasa kika amsa?" Jalila tace, "Naga abun nema ne ya samu, dama mai kudi ake jira kuma yana dasu tunda kinga motarsa." Hafsat tace, "Hakanan kin saka na saka mayafi ina yawo a takure." Matar dake a ciki tace, "Miye na cewa sai mai kudi?"

A fusace jalila tace, "Ke kuma miye ya saka bakinki a maganarmu. Ki dubeta sosai, kyawunta ya kai shiyasa tace sai mai kudi, ke idan kin isa kice sai mai kudin kiga idan baki shekare a gidanku ba, koda yake daga gani babu tambaya wahala kike sha shiyasa kikeyi wa wasu bakin cikin su huta." Ganin da matar tayi idan ta tanka ba zatayi masu kyau ba ya saka tayi shiru har saida tazo inda zata sauka sannan ta dubi Jafsar tace, "Na lura ke kina da kunya, ina mai baki shawara ki zab'i miji na gari akan mai dukiya." Ta juyawa Jalila, "Ke kuma kiyi hakuri shawara mai kyau na bayar ba neman fad'a ba."

Har suka koma gida maganar mata tana damun Hafsat a zuciya, suka yada zango a dakin Umma, Umma tace, "Har kun dawo kenan." Jalila ta zauna tana mai cewa, "Dama mun ce ba zamu jima ba."

Umma tace, "Fatan kunyi min wuff da masu kudi." A tare Hafsat da Jalila suka kalli juna, Hafsat ta girgiza kai tana mata gargadi da idanu, Umma ta lura tayi mata dakuwa, "Ungo nan." Ta juyawa jalila, tace, "Rabu da ita ki fad'a min." Jalila tace, "Angel tayi babban kamu har da motarsa kamar zatayi lumfashi."

Umma tace, "Masha Allah, wannan labari da d'ad'in ji yake." Hafsat tace, "Umma!." Umm ta murtuke fuska tace, "Ke dalla rabu da ni. Jalila bani labari."

Jalila tace, "Ya bata katinsa taki amsa amma na saka mata shi a ledar biscuits dinta." Umma ta saki gud'a tace, "Tafiya tayi kyau." Jalila da neman magana tace, "Kuma Umma kin ganshi kyakykyawa mai gemu."

Hafsat ta janyo pillow ta wurga mata, ta goce tana dariya, Umma tace, "Ki gama b'ata fuskar zaki dauko katin ne ki kirashi."

Hafsat ta mik'e ta fice tana turo baki, Jalila ta biyo bayanta tace, "Haba k'awata."

Gidansu Jalila suka wuce, Hafsat tace, "Kin bani haushi."

Jalila tace, "Kece wallahi, yana da kudi kuma daga gani ba ya da damuwa, idan na barki kina iya bari ya kufce maki bayan kuma kin fad'a min abun da Umma tace akan maganar nan, shiyasa na fad'a mata."

Hafsat tace, "Duk da haka, ba nufina bazan kirashi ba. Ina sone inyi tunani a kai."

Jalila tace, "Uhmm. Angel, torh yaushe zaki kirashi?" Tayi mata banza, saida ta dameta sannan tace, "Ban sani ba, ay kin janyo min, ina gaya maki daga yau na boni da fad'an Umma na safe daban na rana daban na dare daban har sai na kirashi sannan zan samu salama." Jalila tace, "Sai ki kirashi a zauna lafiya."

*****

Bayan Sati Daya

Umma ta shigo dakin tana fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba, tace, "Ace sati guda ina maki magana akan ki kirashi amma kinyi kunnen uwar shegu dani, torh maza ki dauki waya ki kirashi ko kuma inci maki mutunci a gidan nan." Kamar zatayi kuka tace, "Umma zan kirashi."

Umma tayi mata mugun kallo sannan tace,
"Abun da kike fad'a min kenan a kullum kuma ba kiran kikayi ba, hakanan kina nema kiyi min salalar tsiya, idan yaje ya samu wata fa sai muyi ya."

Ba kiran ne bata son tayi ba, haushinta daya card ya bata a maimakon ya amshi numbarta ya kira da kansa, tace, "Umma yanzu in kirashi kamar wacce bata da aji kuma..." Umma ta katseta, "Hafsat na lura dake kin amsa min zaki auri mai kudi ne kawai amma a zuciyarki ba haka bane." Tace, "Umma ba haka bane."

Umma ta dungure mata ta kasa ta tsare, tace, "Koma miye ki dauki waya ki kirashi ko kuma inyi mugun sab'a maki, bani son iya shege." Ta turo baki tace, "Babu kudi a wayar."
Umma ta daro kudi daga gefen zafinta ta mik'a mata tace, "Ina ce kati ne babu, amshi naira dubu daya kije ki saka katin, ki kashe sauran canzi ki sayi abun da yayi maki." Ganin bata amsa ta murtuke fuska, "Zaki amsa ko kuma na sab'a maki, nayi kasa-kasa dake a wajen." Ba domin ranta yaso ta amshi kudin ta zura Hijabi ta fita, kai tsaye ta wuce gidansu Jalila, ta samu wani dattijo zaune a kofar gida, ta rusuna ta gaishe dashi, "Baba Ina kwana?" Ya amsa da kulawa, ya dora da cewa, "Kina lafiya?" Tace, "Lafiya lau." Yace, "Allah yayi albarka." Tace, "Amin." Tana ganin girmansa saboda ba ya rabo da saka mata albarka, ba ya rabo da bata shawarwari wadanda idan ta dauka tana jin dadinsu sosai, ya dauketa kamar yadda ya dauki diyarsa Jalila.

Ta shiga ciki, Mama tana a kitchen, tace, "Barka da aiki Mama. Ina kwana?" Mama tace, "Lafiya lau. Ya ummarki?"
Hafsat tace, "Tana nan lafiya lau. Jalila fa?" Ta tambaya. Mama tace, "Tana daki tana yankan Hijabai da zata tura sokoto."

Hafsat ta wuce dakin inda ta sameta akan keken dinki, saida ta harareta sannan ta zauna akan tabarma, Jalila tace, "Ya da harara? Duk yau bamu hadu ballantana ince laifi nayi maki." Ta kalleta ta watsar sannan tace, "Hakanan kawai kin saka Umma ta hanani zaman lafiya, tunda safe ta tusani gaba tace ko in kirashi ko taci min mutunci, nace babu wayar ta bari idan na saka zan kira, kamar ta gane dubarata ta bani dubu daya tace in saka katin in kirashi shine na gudo nan." Jalila ta dakata da abun da takeyi tace, "Ki kirashi, wannan shine kadai mafitarki."

Saida tayi jim, kamar zatayi kuka ta zaro katin tana danna numbarsa tana mita, "Saboda ya rainani shine zai bani kati, idan numbana yake so ya tambaya mana." Tana cikin ringing daya ya tsinke kiran, ji tayi kamar ta fasa ihu ta kalli wayar ta tab'e baki tace, "Shi ya sani."

"Ya aka yi?" Jalila ta tambaya.

A kufule tace, "Tana ringing ya tsinke kiran." Tana rufe baki kira ya shigo wayar tana dubawa taga numbarshi, tace, "Shine." Jalila tace, "Kiyi picking."

Hafsat ta tab'e baki tace, "Ban yi."

Saida kiran ya kusa tsinkewa sannan ta amsa tayi shiru.
Daga daya bangaren yace, "Salaam alaikum." Saida tayi jim sannan tace, "Wa alaikassalaam." Yace, "Waye?" Ji tayi kamar ta fasa ihu tace, "Waye ko wacece ba."

Dariya yayi har tana jiyo sautinsa yace, "Wasa nike. Na gane, wacce muka hadu a shopping mall ce satin da ya wuce."

Kamar wacce aka yi wa dole tace, "Eh."

Yace, "Tun da muka rabu nike sauraren kiranki amma naji shiru." Tayi shiru, Al'ameen yace, "Alright, ina wani abu amma zan kiraki idan na gama cutiee." Ta tab'e baki jin sunan da ya kirata dashi, ta janye wayar daga kunnanta.

Jalila ta kalleta tana neman karin bayani, tace, "Wai yana abu zai kira anjima." Jalila da neman magana tace, "Wow. Ta tabbata kinyi wuff da zuciyarshi." Saida ta tab'e baki sannan tace, "Ke kika sani, bari ki gani in koma gida tun kafin Umma ta fusata dani ta biyo bayana."

Jalila tace, "Alright sai na shigo."

Hafsat tace, "Baki min rakiya ba."

Jalila tace, "A'a. Hijabs din nan gobe nace zan turasu ga shi lokaci ya k'ure ban so inyi k'aramar magana."

Hafsat tace, "Alright na wuce."
Chapter 6 · 0% Book details