Sashe 39
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya dubi matar yace, "Gaskiya sai kin bani wani abu, dubu dari biyar ake magana." Da fad'a yake maganar har da zaro idanu tana ganin haka ta fito ta ce, "Daga inda ka daukoni zuwa nan nawa ne?" Ya ce, "Naira dari." Inda zai kaita dari shidda ne wadanda sune kadai kudin da ta ke da su, ta zaro ta mik'a mashi, ya yi tsaye yana neman ya yi mata tijara, ta murtuke fuska ta ce, "Ka kwata na karfi ne, kana tab'ani zan tara maka jama'a kaci duka, rashin mutunci ka shirya kayi mata saida kaga tana da kudi ka fara washe baki, ta taimakeni ne saboda na tausaya mata, naira dari biyar shine kudinka na wajenta shine abun da ta ce in baka don haka ko kobo bazan k'ara maka a kai ba."
A fusace ya ja kekensa yana mai kiranta da, "Muguwa, er wahala." Ta tsallaka titi ta ciri kudi a POS ta hau wani dan sahun yana sauketa ta bashi dubu biyar yace, "Hajiya sunyi yawa." Tace, "Kada ka damu, ka godewa Allah." Ta shiga gida.
*****
Mufida da sauran k'annansa ta hango, "Ina yake?" Ta tambaya, suka nuna mata ward ya ke, suka bi ta da kallo cike da tausayi ganin babu takalma a kafarta. Ta hangoshi kwance da na'urori a jone dashi.
Ji tayi kafafunta sun kasa daukarta ta durkushe a kasa tare da fashewa da kuka, ta rarrafa har wajen gadon, ta tsura mashi idanu tana kuka tana girgiza kai, Aliyu shine a kwance kamar gawa, Aliyunta.
Ta mike ta isa inda Ummi take, ta ce, "Ummi ya mai jiki?" Duk da ta ji ta amma ba ta amsa ba, ta matsa kusa da ita, Ummi ta kawar da kai. Hafsat ta girgiza kai hawaye suna fita daga idanunta ta ce, "Ummi miye nayi maki da zafi har haka da kika tsaneni? Ummi miye na aikata a gareki da zafi har haka da baki sona da Aliyu bayan kuma muna kaunar junanmu? Aliyu yana sona ina sonshi, miye laifinmu a nan? Miye laifina don na kasance diyar talakawa?"
Still Ummi bata tanka mata ba. Hafsat ta juya ta kalli inda Aliyu yake kwance tana mai zubar da hawaye ta ce, "Allah ya sani ina son Aliyu, ina matuk'ar son Aliyu." Ta juya ta fita tana mai zubar da hawayen tausayin kanta da kuma tausayin Aliyu.
Ta tsayar da kekenapep ya kaita gida ta amshi kudi a wajen mai guard ta ba shi, shiru gidan yake kasancewar yaran suna gidansu Jalila. Ta kira Umma, hankali a tashe take tambayarta a inda take. "Umma na je asibiti ne ganin Aliyu." Umma ta ce, "Shine ba za ki sanar dani ba kin tadawa kowa hankali, ba wannan ba, shin keda baki da lafiya miye na zuwa ganin wani." Hafsat tace, "Aliyu ne...." Umma ta katseta tace, "Kina tabbacin zaiji dadi idan yaji labarin ki fizge karin ruwa kin tashi daga gadon asibiti ba tareda likita ya sakeki ba kinje ganinsa."
Hafsat ta dafe kanta dake sara tace, "Umma sai kin dawo." Umma tace, "Kina nufin ba zaki dawo asibitin ba." Hafsat ta fashe da kuka tace, "Umma zan sha magani." Umma tayi jim sai kuma tace, "To shikenan zan biya in tafo da yaran."
Hafsat tayi lamo akan gado tana mai zubar hawaye. Aliyu ya fi Hisham kudi saidai kuma Ashraim ya fi Aliyu kudi amma tun da take da dangin Ashraim ba su tab'a mata kallon banza ko goranta mata kasancewarta talaka ba, saidai janta a jiki da sukeyi bata manta zuwa bikin diyar yayarsa da taje taga karamci har yau tana jinjinawa karamcinsu. Kasancewarsu masu kudi na gasken gaske bai saka sunyi wulakanci sai dai halin dattako da taimako da suke dashi domin dukkanin wanda ya sansu yasan hidimarsu na taimakon mabukata, hidima wa masallatai da sauransu.
*****
Mufida ta shiga ward din ta samu Ummi tayi tagumi, ta ce, "Ummi ta fito tana hawaye?" Ummi ta dubeta da damuwa kwance akan fuskarta ta ce, "Mufida ka sa had'a idanu na yi da ita saboda kunya, ina jin kunyar abubuwan da nayi mata a rayuwa. Ku zauna a wajen yayanku zanje gida in gyara abun da na b'ata da kaina." Ta mike ta fita, kai tsaye ta koma gida ta samu Alhaji Muhammad a falonsa. Da mamaki yake kallonta yace, "Wa kika bari a wajensa?" Ummi tace, "Mufida." Yayinda take tsoron abun da zaije ya dawo idan ta sanar dashi abun da ta aikata saidai fad'ar gaskiyar shine kawai mafita a gareta.
"Alhaji nice na hana Aliyu auren Hafsat, a ranar ya dawo har daki ya sameni ya rokeni akan in barshi ya aureta amma na hana, ya fita a cikin damuwa wanda bana raba daya biyu shine sanadin hatsarin da yayi." Ji tayi yace, "Ki fice min daga gida har sai na nemeki." Ta zaro idanu tace, "Na'am." Ya daka mata yace, "Za ki tashi ki fice min daga gida ne ko kuma sai na kira security na saka sun watsar dake a waje." Zatayi magana ya dakatar da ita, "Za ki fita ne ko kuma sai na nuna maki cewa kowa ya iya wulakanci kuma koda wasa naji labarin kinje ko kusa warc da Aliyu yake hukuncin da zan yanke ba zaiyi maki dadi ba." Jikinta a sanyaye ta mike ta fita. Ta wuce gidan yayanta tana ji tana gani bata damar zuwa duba Aliyu saidai ta kira k'annansa taji halin da yake a ciki, ta shiga damuwa ta rame, abincin kirki ba ta iya ci, tayi matuk'ar nadama akan abubuwan da ta aikata.
*******
Hafsat tana kwance akan gado tayi lamo tana son zuwa duba Aliyu amma Umma ta hanata, tayi magiya har ta gaji, k'arar shigowar motoci taji, ta fito balcony domin gani waye. Ganin mahaifiyar Aliyu ya saka gabanta faduwa ta dafe kirji tace, "Na boni, mi tazo tayi min kuma." Ta koma bedroom tayi tagumi, babu jimawa Umma ta leko tace, "Ki fito kina da baki a parlour." Ta juya ta koma.
Jiki a sanyaye Hafsat tabi bayanta ta samu Umma tana a falon, ta zauna akan kujera tayi shiru tana jiran gargadi da take tunanin shine Ummi tazo tayi mata. Ga mamakinta ji tayi Ummi tace, "Hafsat ki yafe min akan abubuwan da nayi maki, na nuna maki tsani, na nuna tsama wa talaka, na manta cewa arziki da talauci duka na Alheri, nayi nadama akan abubuwan da nayi saidai kash lokaci ya kure min, yarona ma fi soyuwa a gareni yana kwance akan gadon asibiti a doguwar suma a dalilina akan abun na hanashi wanda ba haram bane. Hafsat satina biyu bana gidansu Aliyu, ina gidan yayana, mahaifinsu ya hanani zuwa ganinshi, ina zaune ina jiran tsammani akan aurena da zai iya mutuwa a kowane lokaci. Ranar da kika zo na kasa had'a idanu dake ne saboda kunyar abubuwan da na aikata maki." Ta juya wa Umma, tace, "Maman tuwo please ki tayani bata hakuri ta yafe min, kema ki yafe min, Aliyu yana matuk'ar kaunar Hafsat nice nayi mashi katanga wa aurenta kaicona, ban kyauta mashi a rayuwa ba."
Hafsat tace, "Ummi ban tab'a rikeki a raina ba domin ina maki kallon uwa ne. Allah ya yafe mamu baki daya, gobe zanje in duboshi." Ummi tace, "Na gode." Ta juyawa Umma tace, "Ummar Hafsat ki yafe min abubuwan da nayi maku." Umma tace, "Babu komai, Allah ya yafe mamu baki daya."
Hafsat ta raba dare tana tunani akan maganganun da Ummi ta fad'a mata, idan ta bari auren Ummi ya mutu, dukkanin sadaukarwa da Aliyu yayi ya ta fi a banza.
Washegari gari ta shirya taje duba Aliyu tare da Umma da yaran, sun samu mufida ta amshi numbar Abbi a wajenta, suna dawowa gida ta kira, bai ganeta ba har saida tayi mashi kwatance. "Abbi a lokacin da nace maku nayi alkawarin aure da wani, na fad'i haka ne saboda Aliyu ya nemi alfarma a wajena, Aliyu yana yawan fad'a min cewa idan aurenku ya mutu a kansa bazai tab'a yafewa kansa ba, na rokeka da girman Allah ka bari Ummi ta dawo. Ina son Aliyu kuma nayi maka alkawari zan zauna dashi a kowane a hali, a shirye nike in aureshi koda a yau ne a yanzu. Amma na rokeka da girman Allah kayi min alfarma ka bari Ummi ta koma dakinta." Yayi jim sannan yace, "Babu damuwa, Allah yayi maki albarka." Ta amsa da, "Amin. Na gode, Allah ya k'ara girma."
Washegari Ummi ta koma dakinta, ta rasa da bakin da zatayi wa Hafsat godiya. Saidai tunda ta koma gidan bata samu fuska a wajensa ba, ranar tayi karfin halin samunsa da maganar, kallo daya yayi mata yayi shiru har saida ta k'ara magana, yace, "Lokacin da yaronki yana fa lafiya goranta mata kikayi kika hanashi aurenta, sai yanzu da kikaga ba shi da maraba da gawa ne kike k'ok'arin cutarta ta hanyar lika mata aurensa, ki tashi ki bani waje."
"Nayi magana ne saboda ranar da Hafsat ta sameni a asibiti da bakinta ta fad'a min cewa tana matuk'ar sonsa hat a wannan lokacin, yana daya daga cikin abun da ya saka jikina ya k'ara sanyi duba na gujeta dashi a lokacin da yake da lafiya amma wannan bai saka ta gujeshi a yanzu ba." Tana fad'in haka ta mike ta fita, tayi babban kuskure, ta sani daidaituwar al'amurra a tsakanin ta da Alhaji Muhammad zai dauki lokaci, burinta shine ta cika burin Hafsat da Aliyu, ta shaida aurensu.
*********
Washegari Hafsat taje duba Aliyu ta samu kiran Malam Jafaru mahaifin Jalila, akan taje gida yana nemanta a lokaci, ba ta yi kasa a gwuwa ba taja motarta ta kama hanya, motoci ta samu a harabar gidan wanda ya matuk'ar bata mamaki tayi parking motarta ta shiga ciki.
Ta samu Mama a sama ta gaishe da ita, ta amsa da kulawa tace, "Sannu kin sha hanya, kije yana falon baki idan kun gama ki dawo kici abinci mawa nayi da miya." Hafsat ta ware idanu tace, "Kai, har guzuri zanyi, Mama you are life saver."