Sashe 34
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyu yace, "Tana ciki, ka shiga." Yana nuna mashi kofar parlour.
Hisham ya girgiza kai yace, "A'a. Zan jira ta fito." Ya zauna a bayan motarsa yayi parking a harabar gidan.
Ya juya ya koma motarsa, yana ganin kiran Bilkisu ya ki d'agawa, karshe ya kashe wayar baki daya yayinda yake jin kuna a cikin ranshi, mintina biyu a tsakani ta fito tana sanye da atamfa mai golden, dinkin doguwar riga wacce ta dace da ita, ta kashe dauri tayi mashi dauri ya zauna daram, mayafinta, jikkarta da flat shoes dake a kafarta brown, saida zuciyarsa ta buga yana yaba kyawunta, tun da ta fito yake kallonta har ta k'arasa inda motar take ta sauke Little Aliyu daga kan motar ya wuce parlour yayinda Aliyu yake mata magana ta juyar da kai tana dariya.
Ji Hisham yayi kishi ya kamashi, ya b'alle murfin motar ya fito, kallo daya tayi mashi ta juyar da kai tana mai tab'e baki, yace, "Angel. Ina da magana dake."
Hafsat ta murtuke fuska tace, "Sai kuma aka ce maka da kowane kato nike magana, torh ba haka nike ba."
Aliyu yace, "Angel ki je ki ji abun da ya ke tafe da shi." Ta murtuke fuska ba tareda ta bashi amsa ba har saida ya maimaita tace, "Shin ka manta da alkawari da kayi min." Ya hade hannuwa a waje yace, "Tuba nike ranki ya dade."
Aliyu ya juya mashi yace, "Malam ka koma inda ka fito ba za ta ganka ba." Hisham yace, "Waye zai da zaka fad'a min haka." Hafsat ta tari lumfashinsa tace, "Har tambaya kake, torh a matsayinsa na wanda zan aura yake fad'a maka hakan don haka tun wuri ka ja motarka ka fitar min daga gida tun kafin na saka a daukeka kamar kayan wanki a watsar a bola." Jikinsa a sanyaye ya juya ya nufi motarsa, yana gani tana shagwab'a Aliyu yana mata magana, ta juyo tareda nufo inda ya ke, ta tsaya a gefenshi tace, "Miye?"
Hisham yace, "Abun da kikayi min kin kyauta kenan, kin saka D'ana yana kirana makaryaci a gaban bare."
Hafsat ta murtuke fuska tace, "Waye bare? Waye na gida? Kaine bare, Aliyu shine na gida, ka gode Allah da na manta da had'a da fad'a mashi butulcinka ba, butulu kawai. Shi wanda kake kira bare albarkacinsa ka ci na zo inda kake. D'azu kamar ki kira Little Aliyu da D'anka. Yaushe aka yi da kai cewa D'anka ne."
Hisham yace, "Dukkanin wanda ya ganni ya ganshi yasan D'ana ne."
Hafsat ta fashe da dariyar rainin wayo tana tab'a hannuwa tace, "Kai yanzu ba ka ji kunyar kiranshi da jininka ba, kana ina a lokacin da na dauki cikinsa na tsayin watanni tara? Kana ina a lokacin da nayi nakudarsa? Kana ina a lokacin da nike hakilon neman abun da zan ciyar da kaina a lokacin da nike da cikinsa? A lokacin da naje sanar da kai wanzuwarsa korata kayi ka kulle kofa ka dauki danginka kuka wuce London..." ya katseta yace, "Amma ai baki fad'a min ciki kike dashi ba."
"Ka tsaya ka saurareni ne, ko kuma ka bani damar da zan sanar da kai abun da nike tafe dashi."
"Kiyi hakuri. I'm sorry."
Hafsat tayi mashi kallon rainin wayo sannan tace, "Shi sorry da kace zai gyara b'arnar da kayi min ne, ka ga Malam tun muna shaida juna ka fitar min daga gida, gidana ba wajen zuwan kowane kato bane."
Yana kallonta da mamaki yace, "Kato? Gidan ki?" Kanta tsaye tace, "Gidana, idan kuma akwai kobonka a ciki sai kayi magana, ba na tunanin ka na da gadona."
Hisham yayi goya hannuwa a kirji yace, "Amma yarana suna da gadonki?"
"Kai yanzu baka jin kunyar kiran Little da jininka? Kaga Hisham ka fitar min daga gida ina mai taya kaine bakin da na zauna ina magana da kai."
Ya ware idanu yace, "D'ana ne, gudan jini ne." Ta gane maganar da tayi yayi mashi zafi shiyasa ya kauce mata ya bata wannan amsar. Ta rike kugu tace, "Eh yana dauke da kwayar halittarka amma babu abun da ka sani akan wahalar da nayi dashi. Don haka ni ce uwarshi, ni ce ubanshi."
Yace, "Ki kirashi in ganshi." Ta nuna mashi kofar parlour tace, "Ka shiga yana wajen Umma." Ya girgiza kai, "A'a."
Hafsat tace, "Ohhh... Ashe kana da kunya? Nayi zaton zaka shiga ne. Tun da ka gama b'ata min lokacin sai ka san inda dare yayi maka tunda ba gidanka vane inda ka gware da cin mutunci da gadara a ciki." Yana mata magana tayi banza dashi ta wuce wajen Aliyu, ta turo baki tace, "Ka turani ya b'ata min rai, har yana da karfin halin da zai kira Little Aliyu da jininsa."
Aliyu ya hade hannayensa waje guda yace, "Tuba nike MATAR ALIYU."
Kiranta da yayi MATAR ALIYU ya sakata dariyar farin ciki sai kuma ta make kafad'a tace, "A'a, sai ka goya ni sannan zan hakura." Ya kanne mata ido daya yace, "Idan goyo ne kada ki damu, zan goyaki idan mukayi aure, ranar da kika zama matata zan kasance a matuk'ar farin ciki, kin sani ina matuk'ar kaunarki. Amarya a gidan Aliyu. Amarya bakya laifi." Ta juyar da kanta tana dariya.
Ashraim yayi parking kusa dasu, yayi still yana kallonsu saida gabanta ya yanke ya fad'i tana kallon motar, Aliyu ya kalli motar yace, "Waye?" Muryarta tana rawa tace, "Ashraim ne." Aliyu yace, "Alright, sai munyi waya, ki kula min da kanki." Ya shige mota har mata blowing kiss. Saida ya wuce sannan ta juya zuwa motar Ashraim, ya fito yana kallonta yace, "Angel. Kina kasheni da kyawunki."
Tayi dariya tana k'are fuskarta, ji tayi yace, "Waye?" Ta ware idanu tace, "Na'am. Kace?" Duk da kuwa taji abun da yace.
Ashraim yace, "Wanda ya tafi. Waye?" Tace, "Ohhh. Aliyu ne. Babana."
Ashraim ya gyada kai yace, "Wanda Little ya ci sunanshi." Tace, "Eh." Ya duba agogo dake a hannunsa yace, "Little Aliyu fa. In ba shi sakon shi."
Ta lura kamar yanayinsa ya sauya sai taji kuma bata kyauta mashi yana sonta amma tana b'ata mashi lokaci akan Aliyu mutumin da bata da tabbacin samunsa wannan shi ake kira sakin na hannu kamun na dawa.
Ta make kafada tace, "Ba zan kirashi ba nima sai ka bani sakona tunda wariyar launin fata kake nuna min."
Ashraim ya ware idanu yace, "Zaki sha chocolate?" Ta gyad'a kai tana mashi shagwab'a tace, "Eh ina so."
A tare sukayi dariya, ganin yana duba agogo tace, "Bari na turo maka shi. Sai anjima. Ka kula min da kanka." Ashraim yace, "Kema ki kula min da kanki."
Ta shiga ciki tare da turo mashi Little Aliyu da ta samu a tsakar parlour yana buga ball, ya ruga da gudu jin Ashraim ne, babu jimawa ya dawo da katuwar leather yana nuna mata, tace, "Ina fatan kayi mashi godiya."
Little Aliyu yace, "Eh. Na ce mashi na gode."
Hafsat ta shafa kanshi tace, "Yauwa yaron kirki kaje ka nunawa Umma."
Little Aliyu ya dauki leather din ya wuce dakin Umma.
Ranar litinin bayan ta dauko Little Aliyu daga makaranta, yana gama cin abinci ya fara mata hira, "Wannan mutumin da muke KAMANNI ya je makarantarmu, ya ce shine Babana, ya saka aka maida sunana Aliyu Hisham. Ya siya min chocolate, ya ce zaizo hutun karshen mako ya fita da ni."
A karo na farko a rayuwa, ta daka mashi tsawa tace, "Ka b'ace min daga gani, tun kafin inyi maka dukan tsiya. Duk wahalar da na sha da kai, yanzu daka girma ya dawo shine zaka koma mashi, butulu." Little ya fashe da kuka, tace, "Zaka tashi ko kuma sai na mareka, don kana da sunan Babana ai bashi bane. Kuma ya zo ka bishi inyi maka dukan tsiya a gidan nan." Little Aliyu ya mike da gudu yana kuka, ta bishi da mugun kallo tana bala'i tace, "Da uban miye yake takama da garin nan."
****
Little Aliyu yana kuka yace, "Ammi ta min tsawa, ta ce min butulu, za ta mareni." Umma tayi matuk'ar mamaki la'akari da bata tab'a dukansa ba koda laifi yayi mata tana dariya take mashi fad'a wanda tasha mata gyara akan hakan. Tace, "Duka kuma, ba k'aramin abu kayi mata ba."
Little Aliyu ya turo baki ya wuce dakinsa ganin Umma bata goya mashi baya ba, Umma tace, "Ina zaune zaka dawo ka sameni ne."
Little Aliyu ya dauki wayarsa ya kira Aliyu, shiru-shiru suka nemeshi suka rasa kuma ba ya gidan Abba.
Hafsat ta fara bala'i, "Idan Hisham ne ya zo ya daukeshi zai ga danyen kai, sai naga wanda ya tsaya mashi a garin nan, da shi da wanda ya tsaya mashi daidai nike da su."
Aliyu ne ya kira numbarta tana d'agawa yace, "Shine kikayi wa mai sunana tsawa, kika ce mashi butulu zaki dokeshi."
Ta sauke ajiyar zuciya tace, "Kuna tare?"
Daga daya bangaren Aliyu yace, "Muna tare."
Ta koma ta zauna tana cewa, "Na dauka Hisham ne har fara tuna rashin mutuncin da zan yi mashi."
Aliyu yayi dariya yace, "Ba Hisham bane. Aliyu ne, shi wani rashin mutuncin za'ayi mashi."
Kamar yana gabanta ta mak'e kafad'a tace,."Oh, Oh."
Aliyu yace, "Aliyu ne, wani iri za'ayi mashi."
Cike da shagwab'a tace, "Shi soyayya za'ayi mashi."
Ya murmusa yace, "Na gode."
Kira ne ya shigo, ta duba taga Ashraim ne, da sauri tace, "Ashraim yana kira."
Aliyu yace, "Okay, ki kula da kanki." Tace, "Ka kula min da kanka."
Tayi tsinke kiran tare da amsa kiran Ashraim tace, "Ranka ya dade."
Daga daya bangaren Ashraim yace, "Angel. Da wa kike waya?" Tace, "Babana. Aliyu." Ashraim yayi shiru, sai a lokacin ta ankara da katob'arar da tayi, da sauri tace, "Little ne yayi min laifi nayi mashi tsawa, shine ya kirashi, muka nemeshi muka rasa, ashe Aliyu ya kira, torh shine ya kira yana sanar dani suna tare."
Ashraim yace, "Okay. Yaushe zanzo?" Tace, "Kazo yanzu, yanzu nike son ganinka." Yace, "Yanzu kuma?"
Tace, "Eh kayi tsuntsuwa kazo."
Saida yayi murmurshi sannan yace, "Tsuntsuwa kuma, ni da bani da fuka-fukai. Ayi min afuwa, gobe in zo da kafafuna."
Ta mak'e kafad'a kamar yana a gabanta sannan tace, "Shine zaka wahalar min da kanka. Indai a kafa ne kada ka zo."