← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 47

Sashe 11

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hisham yana jingine da mota, tunda ta fito yake kallonta har ta tsaya a gefensa, tana da matuk'ar kyawu saidai muryarta shine abun dake k'ara sakawa yaji yana son kasancewa tare da ita. "Zuwa ranar alhamis zaku tare a sabon gidan da na siya wa Umma." Da mamaki tace, "Har gida ka siya mata?" Ya sakar mata murmushi yace, "Ki shirya tunda gobe ajin safe kawai gareku idan kuka gama zanzo in daukeki in kaiki kiyi siyayya. Kiyi wa Jalila magana ta rakamu."

Da mamaki kwance akan fuskarta tace,
"Ban yi maka maganar Jalila ba, amma ka ambaci sunanta kamar ka santa, sannan waye ya fad'a maka gobe lecture safe ne kawai nike dashi."

Saida ya murmusa sannan yace, "Mai son dan tsuntsu ne yake binsa da jifa, shin a cikin abubuwan da na fad'a akwai k'arya?" Tace, "Kana nufin kasan komai a game da ni?" Ya gyad'a kai, "Na san komai akan wacce nike son aura." Tace, "Kuma a hakan kake da burin aurena. Ka tabbatar da ka san komai kuwa?"

Hisham ya gyara tsayuwa yace, "Angel, babu abun da ban sani ba a game dake. Sai goben idan mun hadu, zan tafo maki da wayarki da system."

Ta nuna mashi wayarta wacce take a hannunta, tace, "Wayata tana a hannuna." Hisham ya girgiza kai yace, "Ina nufin wayar da na siya maki." Ya juya ya shiga mota yayi mata key tare da ficewa daga santar saida taga fitar motar sannan ta juya ta koma ciki, ta tarar matan gidansu akan tabarma sun hade kai suna kuskus wanda tana da tabbaci akan Umar suke magana kasancewar unguwar baki daya gulmar da ake yi kenan, kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Basu ganin abun da yayi mata sai ita suke cewa ta yaudareshi bayan rufa mata asiri zaiyi.

Ta zauna a gefen katifa tace, "Umma yau dai na kawo maki surukinki."

Umma tace, "Hafsat amma?"

Hafsat ta had'e hannayenta a waje guda fuskarta tana zubar da hawaye tace, "Umma na rokeki da girman Allah karki tayar min da wancen maganar, kiyi kamar bai tab'a faruwa ba. Ni Hafsat. Zanbi zab'inki koda zuciyata bata so. Kuma a yau na kawo maki suruki irin wanda kike so, mai kudi, ba kiga kamfanin da yake dashi ba. Yace gobe zamuje shopping tareda Jalila, na fita zanje gidansu in sanar da ita."

Ta goge hawayen dake akan fuskarta sannan ta fita, ta zura takalma ta fice daga gidan zuwa gidansu Jalila, dukkanin kallon da mutane suke mata akan hanya ta sane da abun da yake nufi amma bata da lokacinsu, ta barsu suji da damuwarsu.

Mama tana a tsakar gida tana wanke-wanke, Hafsat ta gaishe da ita, "Mama. Ina wuni?" Mama tace, "Lafiya lau. Ki shiga tana ciki."

Hafsat ta kutsa kai a dakin. Jalila ta dubeta, "Hafsat kin san kuwa abun da yake faruwa a unguwar nan."

Hafsat ta girgiza kai tana mai zama a gefen tabarma tace, "A'a saidai nasan da yawansu suna gulmata akan rabuwata da Umar."

Jalila ta ajiye scissors dake a hannunta tace,
"Kasan asalin abun da ya faru ba kenan, Umar ya tattara kayanshi ya tafi har yanzu babu wanda yasan inda yake, a cewarsa ya tafi ya nemo kudi a dukkanin infa suke haram ko halal, ta kowace hanya, domin ya aureki."

Hafsat ta tab'e baki tace, "Wannan kuma damuwarsa ce, yayi min gori, ya aibata Ummana, sannan kuma ni bazan auri mai dukiyar haram ba, shi kuma yace ta kowace hanya zai nemi dukiya, duk girman dukiyar da zaiyi da abun da zai zama a fagen dukiya bazai tab'a samuna ba. Jalila ba wannan ne ya kawoni ba, nayi sabon kamu, sunanshi Hisham, har yaje gida ya gaida Umma."

Jalila kallonta take fuskarta dauke da mamaki tace, "Hisham?" Ta jingina kai, "Shine wanda ya saka ake bibiyata, har gida ya siyawa Umma, yace gobe idan mun gama lectures zaki rakamu shopping...."

Jalila ta katseta, "Angel tsaya. Kina nufin kin yarda zaki aureshi, daga haduwa babu bincike, babu fahimtar juna. Kina hauka ne." Hafsat tace, "Yana da kudi kuma Umma tace sai mai kudi kuma aurena zaiyi, shikenan magana ta k'are." Jalila ta zaro idanu jin furucin da Hafsat tayi, tace, "Hafsat ina rabaki da aikin gaggawa, ina guje maki aikin gaggawa."

Hafsat ta mike tana mai cewa,
"Kinga bani a yanayin da zan tsaya ina juya magana this and that." Jalila ta kamata ta zaunar da ita ta fuskanceta sannan tace, "Hafsat akwai abun da yake damunki wanda shine ya sakaki yanke wannan hukuncin, amma san ki tsaya kiyi wa kanki fad'a domin abun da kike k'ok'arin kiyi babban kuskure ne, kina k'ok'arin tafka babban kuskure a rayuwarki. Angel karki tarwatsa rayuwarki da kanki, ban ce ki bijurewa zab'in umma ba amma kibi zab'inta da taka tsantsan domin gujewa dana sani na abun da zai biyo baya. Ki je kiyi bincike kisan waye shi, mi yasa yake son aurenki."

Hafsat ta fizge hannunta ta mike tsaye tace,
"Kinga, eh akwai abun da yake damuna wanda ya saka na yanke wannan hukunci, ban sanar dake ba kuma bazan sanar dake ba. Siyayya ne idan zaki rakamu ki fad'a min, idan ba zaki rakamu ba babu dole sai muje mu biyu. Kowa yana da sirrinsa shi kuma ciki ba anyi shi ne domin zuba abinci kawai ne ba."

Jalila tace, "Allah ya kaimu goben, zan rakaku siyayya."

Hafsat ta had'e hannayenta waje guda alamar roko sannan tace,
"Please na rokeki da girman Allah wannan ya kasance karo da karshe da zamuyi wannan magana, ke k'awata ce tun a yarinta bana fatan mu samu damuwa." Ta juya ta fita.

Jalila ta bita da kallo cike da mamaki, a ranta tana mamakin miye ya faru da ita, ba halinta bane ba. Shin miye ya saka ta yanke wannan hukuncin wanda zai iya zama sanadin tarwatsewar rayuwarta.

*****

Tana komawa gida tace, "Ummana mi zan dafa maki?"

Umma tayi jim, Hafsat tace,
"Koda yake sai na girka taliya da wake abun da kikafi so."

Ta zage ta girka abincin dare, tana iyakar k'ok'arinta domin b'oye b'acin ranta, tana yi kamar babu abun da ya faru amma a cikin zuciya abun yana mata ciwo, daurewa kawai take saidai ta fakaici idanu ta goge hawayen da suka kasa daina fita daga idanunta tana yi kamar hayaki ne yake sakata hawayen.

*********

Washegari tunda asuba ta mike ta had'a masu kalaci, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta material ta zura dogon hijab ta fita tareda biyawa gidansu Jalila suka wuce makaranta.

Jalila bata yi mata maganar jiya ba itama bata tada maganar ba.

Misalin karfe goma daidai suka fito daga lecture threater, da mamaki kwance akan fuskarta take kallonshi, yana jingine da mota yana aika mata da sakon murmurshi, kamar mai rad'a tace, "Hisham."

Jalila ta juya ta kalli inda take kallo, Hisham ya bude bangaren mai zaman hakanan da murmurshi akan fuskarsa, ta mayar mashi da martanin murmurshi ta shiga.
Jalila ta bude gidan baya ta shiga, yana mai murza key yace, "Jalila."

Jalila tace, "Har ta fad'a maka sunana."

Hisham ya danna motar akan kwalta yana cewa, "Ba ita ta fad'a min sunanki, nine na sanar da ita na sani. Sannu dear kunyi lectures an gaji, zamu fara zuwa restaurant."

Hafsat ta gyad'a kai kawai, Jalila tace,
"Restaurant kuma?"

Hisham yace, "Ehh, kun kwaso gajiya na lecture."

Jalila tayi mamakin da Hafsat ta ba yarda babu gardama akan zuwa restaurant.

Hafsat tayi zuru tana karanta wasikar jaki akan abubuwan da suka faru.

Muryarta kawai yake son ya ji saidai taki magana har abun ya fara damunsa, yace, "Angel, fushi ake dani ne har yanzu bakiyi min magana ba, bani labari."

"Ba ni a yanayin bada labari." Ta fad'a a takaice.

Ya ware idanu yace, "Shine kike sauke komai a kaina, hakanan jiya na tabbatar da sawon barawo na taka domin fushin da kika nuna yafi karfin na abun da nayi kawai."

"Wani labari kake son na baka?" Tace domin kawar da maganar. "Kowanne iri, muryarki kawai nike da burin saurare."

Ta gyara zama tana bashi labarin LITTAFIN AYSHER ANGEL da ta karanta wanda yayi mata dadi sosai ya tashi kanta sunan littafin MUTUWA A MAKOSHI na siyeshi akan naira dari shidda 600 daga baya da yayi mata dadi ta cika dari hudu 400 ta koma Vvip, murmurshi yake har yayi parking a wani katon wajen cin abincin zamani, fitowa yayi tareda bud'e bangaren da take, ta fito suka jera zuwa ciki yayinda Jalila ta mara masu baya, direct VIP suka wuce, su ukku ne kadai a wajen, waiter ya kawo masu menu, Hafsat tabi menu da kallo, tana mamakin shin yana nufin a gabanshi ne zata ci abinci, wasa yake.

Hisham da kanshi yayi ticking abun da za'a kawo masu.

Babu jimawa aka jera masu komai akan table, fried rice ce, pepper chicken da suya, ta kalleshi, ji tayi yace,
"Ki ci ta yadda za ki ji dadin bani labari, kiji dadin da zakiyi siyayya sosai."

Dukkanin maganar da yayi kanshi yana akan wayarsa da yake dannawa lura da tana jin kunyar taci abincin a gabansa, a nutse suka ci abinci, bayan sun gama ya biya bill, ya bude mata bangaren mai zaman hakanan ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba, ya murzawa motar makulli yace, "Angel a haka zamuje shopping mall. Gaskiya da sake, kin kusa zama matar Hisham, ya kamata ki fara ado da shiga irin na matar Hisham. Shopping mall da zamuje mallakina ne." Da mamaki tace, "Na'am..." Tana k'ok'arin fahimtar abun da yake nufi, ta kalli kayan da suke a jikinta bataga aibu akan kayan dake jikinta ba. Yace, "Kiyi min murmurshi kawai."

Murmurshi tayi wanda iyakarsa akan labb'anta ne kawai, the more ta tuna da abun da Umma tayi mata the more take jinta a cikin matuk'ar damuwa da b'acin rai.

A daidai wani katon waje yayi parking ya zaro wayarsa yayi jim sannan yace, "Naja'atu gani nan a bakin titi... Alright..." ya dubeta yace, "Zata zo ta tafi daku, zatayi maki manicure, pedicure, ta baki kayan da zaki saka."

Tayi jim sai kuma ta gyad'a kai tace, "To shikenan."

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 7
Chapter 11 · 0% Book details