Sashe 42
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta mike tace, "Mu je." Ya dubeta da mamaki yace, "Na'am." Ta murtuke fuska tace, "Za ka wuce mu je ne ko kuma sai na mareka a wajen." Ya yi gaba ba tareda ya k'ara magana ba, direba ya jasu zuwa gidan Momcy, ta kira direba ya dubashi ya yi mashi allurar barci, a take barci ya yi awon gaba da shi, ta zuba mashi idanu tana mai jin tausayinsa.
Bayan ya farka ta tusashi a gaba tana mashi fad'a, "Hisham mamaki kake bani, saboda nayi maka fad'a, na fad'a maka gaskiya akan ka rabu da ita tun da kuskure ne ka yi ka rasata ta auri wanda take so sai kayi hakuri ka rungumi kaddara, yanzu fushin, zafin kai da damuwar da ka sakawa kanka ina ta kaika. Ina fushi da kai, ciwon zuciya yana neman kamaka, matarka tana gidansu. Shin in tambayeka mana, waye gari ya wa ya a nan? Kai." Ta lumfasa sannan tace, "Ka rufeta ka aureta ta shiga tashin hankali da damuwa har hauka tayi da tsohon ciki amma a lokacin ta samu zab'i na roketa alfarma kuma tayi min ta zauna da kai, amma kai a lokacin da zaka samu zab'i sai ka zab'i kayi mata butulci, ka saketa, yaron da tasha matuk'ar wahala ka amshe, tazo ta sanar da kai tana ciki ka koreta, kayi min k'arya ka tattaramu muka bar kasar. Shin in tambayeka, Idan kanwarka Fatima aka yi mawa zakaji dadi? Shin idan kaine Hafsat zaka yarda ka koma gidan wanda ya aikata maka haka? Bugu da kari na tusaka mukaje muka bada hakuri amma mi ka aikata daga baya, korar manema aurenta, Shin abun da kayi ya kyautu kenan? Tambayata a gareka ita ce Shin ka tab'a rokon yafiyarta akan abun da kayi mata?" Ya girgiza kai yace, "A'a." Momcy tace, "Hisham alhakin Hafsat ne yake wahalar da kai a rayuwa, ka cutar da ita, ka zalunceta zalunci mai girma, ya rage maka ka sauke zafin kai, girman kai, da damuwa da ka d'aurawa kanka muje ka nemi yafiyarta, idan kuma ka zab'i zama da alhakin zaluncin da kayi mata a kanka to shikenan sai in ce ka je ka yi abun da ranka ya so." Hisham yayi kasa da kai yace, "Zan nemi yafiyarta."
Momcy tayi murmurshi tace, "Yauwa, Hisham kayi wa kanka fad'a ka fuskanci rayuwa a yadda tazo maka, ba komai muke samu ba, kowa da rabonsa, ka samu damarka kayi wasa da ita ka kufce maka don haka hakura da ita shine mafitarka a yanzu, ka dage sallar dare da karatun Alk'ur'ani mai girma komai zaizo maka da sauki. Har mamakinka nike Hisham mutum mai tausayi, taimako, wanda sallar Jam'i bata wuceshi shine ya dawo haka, Hisham kayi wa kanka fad'a." Tayi mashi fad'a sosai tareda nasiha, a wajen ya roki gafarta akan abubuwan da yayi. "Momcy ki yafe min." Ta shafi kansa tace, "Babu komai, na yafe, Allah yayi maka albarka." Ya amsa da, "Amin."
"Yaushe za mu je wajen Hafsat?" Ya tambaya. Tayi jim sannan tace, "Sai ka k'ara samun sauki tukunna."
Ya dage da karatun Alk'ur'ani, ya saka ransa hakuri, ya dauki dangana akan Hafsat, a cikin sati biyu ya murmure.
Hisham ne yake tuka motar a yayinda Momcy take zaune a mazaunin baya, ya dauki hanyar asibitin da aka kwantar da Aliyu, yace, "Na yi tunanin abroad zasu fitar da shi."
Momcy ta ce, "Mahaifinsa ne ya hana, yace mu barshi a nan, koda zai mutu ne gwara ya mutu a cikin dangi a kasarsa ta haihu yafi ayi zirga-zirga dashi, kwararrun likitoci ne daga kasashe daban-daban suke kulawa dashi."
Ita kadai suka samu, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi ta gaidashi, ta rungume Momcy tana mai cewa, "Sannu da zuwa uwata ta kaina." Momcy tace, "Yauwa diyata." Hafsat tace, "Yaya Hisham barka da zuwa, ka zauna." Suka zauna, suka k'ara gaisawa.
"Ya mai jiki?"
"Jiki da sauki."
"Allah ya k'ara sauki."
"Amin."
Momcy ta dafata, "Diyata ki k'ara hakuri, ki cigaba da hakuri, jinya saida hakuri, jinya akwai lada musamman ke da kike jinya na mijinki, Allah ya bashi lafiya."
Hafsat tace, "Amin, na gode." Tana ganin girman Momcy sosai, Momcy mutumin ce mai dattako, kowa nata ce.
Hisham yayi jim sannan yace, "Hafsat na rasa da kalmomin da zanyi amfani domin baki hakuri akan abubuwan da na aikata maki tun daga haduwarmu har zuwa yau, Angel na zalunceki na cutar dake wanda bana raba daya biyu shine yake bibiyata, shine ya hanani nutsuwa. Ina maki fatan alheri akan aurenki da Aliyu, Allah ya baku zaman lafiya." Ya lumfasa sannan yace, "Ina mai hakuri akan dukkanin abubuwan da nayi maka na butulci da zalunci, please na rokeki da girman Allah ki yafe min."
Hawaye ta gani a idanunsa wanda ya matuk'ar bata mamaki, bata tab'a tunanin rana zata zo da zaizo har inda take ya nemi yafiya, bata tab'a zaton rana zata zo da zai nemi yafiyarta ba tareda an tilasta mashi ba amma a yanzu abun da take gani a idanunsa tsantsar nadama ce. Tace, "Na yafe komai da komai, nima ka yafe min." Yace, "Babu abun da kukayi kuma koda kinyi na yafe." Tace, "Allah ya yafe mamu baki daya." Suka amsa da, "Amin." Sun jima kafin sukayi mata sallama suka tafi.
Da daddare ya samu Momcy da maganar Bilkisu, tayi murmushi tace, "Mi kake son inyi a kai?" Ya sosa kai yace, "Ki rakani mu bada hakuri." Momcy ta girgiza kai sannan tace, "Mi nayi da zan bada hakuri? Kai da kayi mashi ba daidai ba, kaine zakaje ka bada hakuri." Ya marairaice yace, "Please mana Momcy, ko har yanzu kina fushi da ni."
Ta girgiza kai tace, "Ko daya bana fushi da kai, ko wajen Hafsat ina da dalili da ya saka na rakaka, saboda in duba mai jiki, sannan bugu da kari ni ce sanadi da ya saka ta zab'i zama da kai a wancen lokacin. Kayi wa Bilkisu laifi ba karami ba, abun da ka aikata bai kyautu ba don haka ka shirye kaje ka bada hakuri, idan sun hakura shikenan idan kuma basu hakura sai ka rungumi kaddara ka girbi abun da ka shuka na fushi da zafin kai." Ya girgiza kai yace, "Bilkisu tana sona." Momcy tace, "Hisham, kana tuna abubuwan da kayi wa Bilkisu kuwa?"
Yana komawa daki ya kira numbar Bilkisu tana shirin kwanciya kiran ya shigo wayarta ta dubi wayar da mamaki ganin sunansa, saida ta tsinke ya k'ara kira ta kusa tsinkewa sannan ta amsa.
"Salaam alaiki."
"Wa alaikassalaam."
"Ki dawo gida."
Bilkisu tayi murmurshin takaici tace, "Su kuma wadanda ka baiwa ajiyata wata da watanni sai ince masu mi, Hisham kana bani mamaki matuk'a gaya, bayan abun da kayi amma har kana da karfin halin da zaka kira kace min in dawo gidanka, miye kake tunani that ni er dadi miji zan wanko kafa in dawo saboda bani da mafad'a, to na san ciwon kaina don haka kamar yadda kace in tafi ko kuma ka had'a min da takardata, idan ka tashi ka tafo da ita zan amsa a wannan karon." Ta tsinke kiran, ya k'ara kira ta datse kiran tareda kashe wayar baki daya. Takaici ya kamata ji take kamar ta fasa ihu bayan abun da ya aikata amma har ya iya kiranta yana ce mata 'Ta koma gida' ko nauyi da kunyar fad'a bai ji ba.
Washegari ya k'ara samun Momcy da maganar, "Please Momcy kiyi hakuri muje in basu hakuri, kunyar abun da na aikata nikeji." Momcy ta murmusa tace, "Tun jiya na gama magana babu inda zanje yadda kace mata taje ba tareda saka hannuna ko shawarata ba hakanan zaka dauki kafa a yau ko gobe kaje ka basu hakuri." Ya marairaice yana rokonta ta hakura suje tare, "Hisham babu inda zanje." Karshe da ya dameta ta koreshi, ta hana kowa yayi mashi rakiya. Sannan ta k'ara bashi deadline akan a ranar ko washegari yaje ko kuma tayi mugun sab'a mashi.
Bai je ranar ba washegari ta tusashi a gaba ya shirya ta korashi, kanshi kasa yake zaune a falon ya kasa had'a idanu dasu. Baffa yace, "Ina saurarenka." Hisham yace, "Nayi nadamar abubuwan da na aikata, ina mai baku hakuri, hakan ba zai sake faruwa ba." Baffa yace, "Ba wannan ba, ina so ne inji laifi da tayi ka korota gida." Hisham ya rasa bakin magana, Baffa yace, "Ina sauraronka." Saida Hisham yayi kasa da kai sannan yace, "Abun da ya faru ba laifinta bane laifina kuma ina mai bada hakuri."
Kwana biyu Hisham ya zarga gidan Baffa yaki sauraronsa, hakanan bai barshi yaga Bilkisu ba saidai Suleiman aka maido dashi gidan Momcy. Har ya cire tsammani a ranar ya samu kiran Baffa, daga daya bangaren Baffa yace, "Ka zo tare da wanda ya amsar maka auren Bilkisu."
Saidai gabansa ya yanke ya fad'i yace, "Baffa a yi hakuri."
Daga daya bangaren Baffa yace, "Ka zo tare da wanda ya amsa maka aurenta." Ya tsinke kiran.
Ya samu Momcy da maganar, ta jinjina kai tace, "Babu damuwa zan yi mashi magana." Kallonshi kawai take amma tasan komai akan abun da yake faruwa, ita ce ta saka sukayi mashi hakan domin ya shiga taitayinsa akan abubuwan da yayi ta yadda a nan gaba bazai yi gigin maimaitawa ba.
Abun da ya faru yasha banban da abun da yayi tunani, yayi fargaba akan zasu saka ya saketa ne saidai ba hakan ne ya faru, nasiha ne tareda fad'a aka yi masu ya dauki matarsa ya wuce da ita gida, kunya ta hanashi mata magana, yana so ya bata hakuri amma kunya ta hanashi magana, idan ya tuna abubuwan da yayi mata sai yaji kunyarta ta kamashi.
Bilkisu tana lura dashi tayi kamar bata gane ba, ta fito daga wanka ta sameshi zaune a gefen gado, zaiyi magana ta d'aga mashi hannu, tace, "Hakuri ne na hakura, shikenan, bana son doguwar magana." Ya gane tana son rama abubuwan da yayi mata ne yace, "Mi zaki girka mamu?" Ta ware idanu tace, "Kana nufin mi zaki girka kici ne ka tambaya kayi jimla domin a iya sanina ka daina cin abun da girka kuma naga ba'a dole." Ya murmusa yace, "Amma nace kiyi hakuri."