Sashe 33
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya jima sannan ya wuce bayan da ta rakashi har mota, katuwar leather shake da chocolate ya baiwa little Aliyu, tayi mashi godiya, zuciya tana da son mai kyautata mata, Hafsat tana matuk'ar son Little Aliyu, Ashraim yana nuna kulawa a gareshi, ya daukeshi tamkar D'an da ya haifa, wannan ya saka take ganin girmansa sosai, tana ji har a ranta zata aureshi saboda tana sonshi, ta yanke shawarar ta hakura da Aliyu tunda mahaifiyarshi bata sonta, ta saka a ranta cewa tana son Aliyu tana matuk'ar sonshi kuma tana addu'a na yarda da cewa IDAN HAR RABONTA NE zata sameshi.
Ashraim yana yawan kiranta susha hira, yana zuwa a weekend.
******
Hamida diyar k'anin mahaifin Hafsat, za ta je bikin gidansu k'awarta ta tafi da Little Aliyu, bayan sun dawo sun fito daga kekenapep zaya bada kudi.
Tunda ya hawo titin idanunsa suka sauka akan yaron, gani yake kamar gizo ne yake gani, har ya gotasu yayi reverse ya dawo da baya tareda gangarawa da motar a gefen titi, ya fito ya k'arasa inda suke yace, "Hi boy."
Little Aliyu ya juya ya tsura mashi idanu, Hisham ya ware idanu ganin matuk'ar KAMANNI da yaron yake yi dashi kamar kobo da kobo, Little Aliyu ya kama hannunsa yace, "Kasan Ammi na?" Hisham yace, "Wacece Amminka?"
Little Aliyu yace, "Ammi mana. Idan baka santa ba, you are stranger ban yi maka magana." Hisham yayi murmurshi yace, "Na santa. I'm not stranger."
Ya juya baya don haka ba ta hango fuskarsa, ta janyo Little Aliyu tana mai cewa, "Malam. Ya haka?" Ta ware idanu ganin matuk'ar KAMANNI da su ke yi.
*******
Hafsat tana zaune a parlour tana waya da Ashraim, Hamida ta fad'o falon a rikice tana fad'in, "Little Aliyu." Hafsat ta mike da sauri tana mai dafe kirji idanunta a waje tace, "Na boni. Mi ya samu Babana?"
Hamida ta ce, "Yaga wani mai KAMANNI dashi ya makale mashi ina mashi magana yaki biyoni."
Hafsat ta ware idanu tace, "What! Hisham! Ya sake ya tafi min da Little Aliyu sai yaga tashin hankali da bai tab'a gani ba. Ko wa ya tsaya mashi a garin nan bai isa ba. Saidai a mutu." Ta warware mayafi dake a saman kanta ta yaneshi ta zura takalma ta fita zuwa compound, "Muje." ta fita ta kofar dake a kofar get.
Tana a gaba Hamida tana biye da ita, Hisham yana tsaye ya daurashi a saman bayan mota, tun da suka tafo ya tsura mata idanu yana jin wani yanayi yayinda zamansu yake dawo mashi a kai, the more take tunkaro inda yake the more take k'ara mashi kyau, sai yake jin wani yanayi a zuciyarsa.
Ba tayi wata-wata ba ta sauke Little Aliyu daga saman motar tare da watsa mashi mugun kallo tace, "Ban hanaka magana wa strangers ba. Tun da har baka jin magana, sai na fad'awa Aunty Jalila tayi min maganinka." Little jin zata fad'a wa Jalila ya fara kuka yana bada hakuri, "Kiyi hakuri kada ki fad'a mata. Shine yace min ya sanki that he's not stranger."
Kanta tsaye tace, "K'arya yake. Makaryaci ne." Little Aliyu ya kama baki yana kallonta idanu a waje kamar wacce tayi babban zagi.
Hisham ya ware idanu yace, "Nine nike k'arya." Ta murtuke fuska tace, "K'arya ka ke yi mana, ka sanni ne, a ina ka sanni?"
Hisham yace, "Shin d'ana ne? Is he my son?" Tayi dariyar rainin wayo tace, "Yaushe mukayi haka da kai, daga ganin yaro sai kace d'anka ne, ka bani ajiya ne, daga yau idan na k'ara ganinka a kusa dani ko yarona sai na shuka maka ranshi mutunci. Daidai nike da kai. Aikin banza aikin wofi." Ta fizgi Little Aliyu suka wuce, Hisham ya d'aga murya yace, "Mi za ki ce akan KAMANNI da ni ke yi da shi."
Hafsat ta juya tareda buga tsaki tace, "KAMANNI manya. Hisham! Hisham! Hisham! Ka fita daga hanya ta tun kafin nayi maka atishawar tsaki domin yanzu ba shekarun baya bane."
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 15
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Umma ta tareta da tambaya kasance taji maganganu da takeyi kafin su fita. Hafsat tace, "Hisham ne, kuma nayi mashi gargadi, don a wannan karon idan yace zai shiga gonata saidai a mutu."
Little Aliyu yace, "Ammi, is he my father? Muna KAMANNI." Ta fusata ta daka mashi tsawa, "Daga yau idan ka k'ara ganin wani kace mashi babanka sai nayi maka dukan tsiya, sai in zaneka ai ba wancen Aliyun bane, sunanshi kawai kake dashi. Ni da kake gani," tayi nuni wa kanta ta dora da cewa, "Ni ce uwarka, ni ce ubanka. Babu wani kato da ya isa ya kawo min wargi tunda ba tare muka sha wahalarka ba. Idan kuma mutum ya fusatani har wancen sai in bi in amso abuna tunda ba wani ya tayani nakudarsa ba. Tun da nike ban tab'a shan wahala irin ta cikin Muhammad ba amma babu tausayi babu imani aka rabani dashi."
Ishaq daya daga cikin k'annanta ya kawo mata wayarta da take ringing. Ashraim ne sai a lokacin ta tuna tana wasa dashi aka kawo mata maganar Little Aliyu yana tare da Hisham. Ta ce, "Ranka ya d'ad'e."
Daga bangaren Ashraim yace, "Da fatan babu abun da ya samu Little Aliyu."
Ta girgiza kai kamar yana a gabanta tace, "Hisham ne, kuma nayi mashi gargadi, wannan karon sai dai a mutu tunda ba tare da shi nayi nakuda da wahalar yaron ba."
Ashraim yace, "Yace zai amshi yaron ne?"
Hafsat tace, "A'a, tambaya yayi idan D'anshi ne, sai ka ce wanda ya ba ni ajiya." Lura da ranta a matuk'ar b'ace yake, yayi mata sallama akan zai kira anjima.
******
A karo na biyu Hisham yace, "Momcy."
Momcy tace, "Idan ba zaka fad'a min abun da yake tafe da kai ba, ka tashi ka bani waje, ina da abun yi."
Yana tabbaci idan ta ji labarin abun da yayi ba za ta yi mashi da sauki ba shiyasa yake shakku akan fad'a mata saidai gwara taji a bakinsa akan taji maganar a wani wajen.
Saida yayi kasa da kanshi sannan yace, "Momcy abun da na fad'a maki a shekarun baya akan rabuwata da Hafsat k'arya na yi maki. Ba Hafsat ba ce ta nemi saki, sannan ba ita ba ce ta bar min Muhammad. Ni ne na saketa sannan na amshe shi daga wajen ta, bayan wasu en kwanaki ta dawo ban saurareta ba, a ranar ne kuma muka wuce London. A yau na ganta tare da wani yaro mai KAMANNI dani kamar kobo da kobo."
Momcy ta ware idanu tana kallonshi tana salati, tace, "Hisham ni za ka mayar mutuniyar banza, kayi min k'arya, ka mayar dani sakara, ka mayar da ni mai son zuciya, da wanne idanu zan kalli iyayen Hafsat. Yarinyar da ka yaudara ta aureka ba tareda sanin abun da yake faruwa a rayuwarka ba, ka rufeta amma daga baya da ta samu zab'i tayi min alfarma ta zauna da kai amma da yake kai butulu ne shine ya ka rabu da ita saboda matarka ta dawo. Na rasa da wasu kalmomi zanyi tur da Allah wadai da abun da ka aikata."
Hisham yace, "Momcy yaron da yake KAMANNI da ni, ina ganin D'ana ne idan ba haka ba taya zai yi KAMANNI dani sak."
Momcy ta daka mashi tsawa tana nuna mashi tace, "Ka fitar min daga gida, tun da ka aikata abun da ranka ya ke so, nima na zare hannuwa daga lamarin nan, babu ruwana. Kuma ka saurari hukuncin da zai biyo baya domin ba zai yi maka dadi ba."
********
Najeeb yace, "What amma a lokacin ba haka kace min ba, kaine kake da laifi, amma sai ka dauki laifin baki daya ka daura akan Hafsat. Hisham, ka cuci Hafsat, shiyasa bayan faruwar abun da na je gidansu tana ganin ni ne ta koma ta kulle kofa, ko saurarena ba ta yi ba." Hisham ya dafe kai yace, "Miye mafita yanzu?"
Najeeb ya ware hannuwa yace, "Ban sani ba. Kai yanzu tunanin amsar waccen kake shima. Na jinjina maka. Da ni ne ita har wanda yake hannunka sai na amshi abuna." Ya mike ya fita ba tareda ya k'ara bi ta kan Hisham dake mashi magana ba.
Hisham ya rasa yadda zai yi, tun da yaga yaron a kullum yana manne a ranshi jinsa yake sosai a ransa, tun da yayi tozali da Hafsat tunaninta ya tsaya mashi a rai, da ya rufe idanu fuskarta yake gani, ya rasa gane miye yake faruwa dashi.
********
Abun yana damunsa sosai, tunaninta da tunanin yaron ya tsaya mashi a rai, ranar ya ka sa hakuri, tun da safe yake tantamar ya je ko kada ya je, yana akan hanyar komawa gida, ya juyar da motar ya nufi gidansu Hafsat, tun daga nesa ya hango mota a parker, Little Aliyu yana a saman motar yayinda Aliyu yake a tsaye yana mashi wasa, Hisham yayi parking motarsa ya fito zuwa inda suke, ya mik'a hannu wa Aliyu.
Little Aliyu yace, "Abba kada ka gaisa dashi. Ba mu sanshi ba kumq makaryaci ne, ranar yayi min k'arya ya saka Ammi tayi min ihu."
Aliyu ya ware idanu yace, "Little kada ka k'ara fad'in haka."
Ji Hisham yayi muzanta, nauyi ya kamashi. Little Aliyu yace, "Da gaske nike, ranar yayi min k'arya ya ce ya san Ammi, Ammi ta ce ba ta sanshi ba, kuma k'arya haramun."
Hisham yace, "Angel fa?"