← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 47

Sashe 10

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa ta hango motar, tafiya ta fara tana lura da ita, ganin zai gane nufinta tayi kamar hankalinta ba ya akan motar, tayi wuff ta tare gabanta tana kwankwasa gilasin motar.

Bashir yayi kasa da gilashin yana kallonta idanu a waje, saida ta kare mashi kallo sannan tace, "Ka fita daga motar ko kuma in tara maka jama'a."

Bashir ya b'alle murfin motar ya fito, ta kalleshi daga sama har kasa, tace, "Mi yasa kake bibiyata? Wa ya saka kake bibiyata?"

Bashir yace, "Ni kuma?"

Wayar dake hannunsa ce tayi tsuwwa yayinda sunan _BOSS_ da manyan haruffa ya bayyana akan majiginta, kallonta yayi ya ware idanu ganin itama sunan take kallo, ta girgiza kai tace, "Da alama sakaka aka yi kana bibiyata." Ta fizge wayar ta amsa kiran, kafin yayi magana ta riga shi, "Na kama wanda ka saka yake bibiyar rayuwata? Waye kai? Mi yasa ka sakashi yake bibiyar rayuwata? Idan kana da damuwa dani ne ka tunkareni? Wannan Motar dashi wanda yake tukata bazasu bar inda suke ba har sai kazo da kanka ko kuma in tara mashi jama'a." Ta tsinke kiran.

SHIN MI ZAI FARU?
SHIN WACECE BILKISU? MI YA FARU HAR TA B'ACE? SHIN A WANI HALI TAKE CIKI? SHIN HAFSAT ZATA AURI HISHAM? SHIN MI ZAI FARU DA ITA IDAN TA AURESHI? SHIN AISHA ZATA AIKATA ABUN DA TA FAD'A KUWA? SHIN MI ZAI FARU IDAN BILKISU TA BAYYANA? SHIN INA OMAR YAKE? SHIN WAYE ASHRAIM?

Muje zuwa

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 6

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

Hisham ya saki murmurshi yana kallon majigin wayar, ya ajiyeta yana mai cigaba da duba file dake a gabansa.

******

Hafsat ta duba agogo dake a hannunta, a fusace tace, "Tunda shi bazai zo, ka kaini inda yake domin a yau za'a yita ta k'are sai ya fad'a min dalilinsa na sakawa ana bibiyata."

Bashir ya share zufa yana zare idanu, ta murtuke fuska tareda b'alle murfin mota ta zauna a gidan baya, Bashir ba ya da wani da ya wuce ya koma mazauninsa ya tada motar ya dauki hanyar kamfani inda yake kyautata zaton zai sameshi, babban kamfani ne, wanda ya dauke da dogon gini iya ganinta, ginin glass, ta jingina da motar ranta a b'ace tace, "Wanda ya saka kake bibiyata kaje ka fito dashi, ayita ta k'are." Ya share zufa da ta karyo mashi yace, "Na'am." Ta kalleshi ta watsar, ganin zai b'ata mata lokaci, tace, "Waye ya saka kake bibiyata?" Muryarsa tana rawa yace, "Mai wannan kamfani."

Hafsat tayi jim sannan tace, "Kana nufin CEO na kamfanin." Ya gyad'a kai.

Ji tayi ranta ya k'ara b'aci ta shige ciki fuu, tayi tsaye tana k'arewa katon kamfanin kallo wanda yake kamar a kasar waje.
Najeeb ne ya hangota, ya k'arasa inda take yace, "Ma'am." Ta murtuke fuska tace, "A wanne floor ofishin CEO yake?"
"Hawa na ashirin da daya." Ya bata amsa yana mamakin ganinta a wajen.

Ta raba ta gefensa ta wuce fuu zuwa elevator, sau biyu ta danna da alama akwai wadanda suke a ciki, gani tayi zai b'ata mata lokaci ta juya ta bude wani kofa tabi ta emergency stairs (ni kuma nace sauri kuma, ina sauri wa wanda yabar elevator yabi emergency stairs har hawan bene na ashrin da daya, tab 😂😂😂), ranta a b'ace yake shiyasa ko gajiyar hawan benen bata ji ba, tana haurawa tana kallon numbobin dake a saman kofar kowanne floor da take wucewa domin tabbatar da bata wuce hawan benen da yake ba.

Najeeb ya zaro wayarsa ya kira numbar Hisham, daga daya bangaren Hisham yace, "Buddy. Ya ake ciki?" Najeeb yayi dariya sannan yace, "Hafsat tazo, she is in this building, tana akan hanyar ofishinka. Ya haka?" Hisham yayi jim sannan yace, "Ta kama Bashir yana bibiyarta." Najeeb ya kyalkyale da dariya yace, "Kace yau akwai daru kenan domin ranta a matuk'ar b'ace, sai nike ga kamar ka taka samun barawo ne." Hisham yace "Ina nan ina jiranta."

*****

Ta jima tana haura matakalar benen kafin ta k'arasa hawa na ashirin da daya wanda shine hawa na karshe.

A fusace ta bamka kofar ta kutsa kai cikin ofishin, ranta a matuk'ar b'ace yake, tun daga bakin kofa take zazzaga mashi bala'i, idanunta a tsatsaiye, dama neman wanda zata sauke fushinta a kansa take.

"Waye kai? Miye haka? Mi yasa ka saka ake bibiyar rayuwata? Ina tambayaraka. Ka amsa min tun kafin na fara tara maka mutane."

Hisham yayi relaxing akan kujera yana kallonta, yadda take magana a lokacin shine kwatankwacin yadda Bilkisu take masifa idan aka kaita bango, Bilkisu mutum ce mai hakuri saidai idan aka kaita bango bata da hakuri.

Ji tayi ranta ya k'ara b'aci ganin yana kallonta yana murmurshi, ta doki teburin dake a gabanshi, "Ina maka magana ka mayar dani mahaukaciya."

Hisham yayi murmurshi yana shafa gemunsa yace, "Angel. Miye?"

Ji tayi ranta ya k'ara b'aci, tambayarta yake miye bayan yasan abun da yake magana a kai, ji take kamar tayi ball dashi, a tsiwace tace, "Nace waye kai? Mi kake takama dashi da har ka saka ake bibiyar rayuwata?"

Bai san lokacin da ya k'ara murmusawa ba, the more take magana the more take tuna mashi da matarshi Bilkisu.

Ta daka mashi tsawa tace, "Heyyy! Da kurma nike magana ko kuma raina min hankali da kayi ne ya saka ina kumfar baki kana min dariya."

Tambayar da take jira mashi ya amsa a takaice, "Sunana Hisham. Na saka ana bibiyar rayuwarki ne saboda ina da burin aurenki."

Duk da haka bata ji ta huce daga haushinsa ta watsa hannuwa a iska idanunta a waje, da tsiwa tace, "Idan aurena kake so, gidanmu zakaje ka gabatar da kanka, daga rana irin ta yau idan na k'ara ganin wani yana bibiyata jama'a zan tara mashi, idan kunne yaji jiki ya tsiri."

Ta juya ta kama hanyar fita, ji tayi yace,
"Hafsat. Shin baki son sanin dalilin da ya saka nike son aurenki?" Ba tareda ta juya ba tace, "Ban damu in sani ba." Ya ware idanu da mamaki akan fuskarsa domin baiyi tsammanin samun wannan amsar daga gareta ba, yace, "Ki tsaya in rage maki hanya."

Ta juyo a fusace tace, "Nasan hanya tunda ba kai kawoni ba." Ta juya ta fice, kamar d'azu emergency stairs tabi.

Hisham ya danna landline yayi jim sannan yace,
"Ka fito mota zan fita yanzu." Ya mike tareda zura kot ya b'alle cufflinks, ya fita yana tafiya a nutse zuwa private elevator dinsa, sarai ya gani ta emergency stairs tabi wannan ya saka ya rigata kaiwa kasa.

Ta fita daga harabar kamfanin ta rik'e kugu, sai a lokacin taji kafafunta sun fara ciwo, ji tayi ba zata iya k'ara koda tako guda daya ba, ta durkushe tana maida lumfashi.

Hisham ya fito daga katuwar Jeep dake a gabanta, ya zagaya ya bude bangaren mai zaman hakanan ya dubeta yace, "Muje, inyi dropping dinki a gida daga nan sai in gaida Umma."

Ta dan kalleshi tace, "Ban so." Ya dan dubeta yace, "Kin tabbata?" Saida tayi mashi mugun kallo sannan ta shiga motar ya rufe tareda zagayawa bangaren direba, ya danna horn aka bud'e mashi get, yana tuki a nutse yayinda ta juyar da kanta tana kallon waje abubuwa da yawa suna dawo a kai, ji tayi hawaye sun zubo mata.

Da sauri ta saka hannuwa ta goge hawayen da suka zubo mata, har yayi parking a kofar gidansu babu wanda yayi magana a tsakaninshi da ita, ta b'alle murfin motar ta fita, ta tarar da Umma zaune akan tabarma tayi jigum, tana ganinta ta mike tana jera mata tambaya. "Hafsat ina kika shiga, tun d'azu nike jajenki?"

Hafsat tayi iyakar k'ok'arinta domin b'oye b'acin ran da take a ciki, tayi kamar kamar abun da ya faru d'azu bai tab'a wanzuwa ba, tace, "Umma ban tab'a fad'a maki bane, na jima da lura da ana bibiyata da motoci mabanbanta, a yau na rutsa matukin motar har saida ya kaini wajen wanda ya saka yake bibiyata, yace yana sona da aure ne shiyasa ya saka ake bibiyata, yana a kofar gida zai shigo ya gaidaki."

Umma ta dubeta da mamaki saidai ba tace komai ba, Hafsat tace, "Bara inyi mashi magana ya shigo ya gaidaki."
Tana gaba yana biye da ita suka shiga gidan, yana mai karewa gidan kallo, ya zauna akan tabarma da aka shimfida a gefen bango, ya gaishe da Umma. Ya dora da cewa, "Umma na gama gyara gidan da zaku koma wanda yake a G.R.A, nan da kwana biyu sai ku tare."

Umma ta dubeshi da mamaki sannan tace,
"Mu tare kuma?"

Ya gyad'a kai yace, "Umma da ni da Hafsat duk daya ne a wajenki." Ya zaro kudi da bai san adadinsu ba yace, "A saka mamu albarka."

Umma tace, "Allah yayi albarka amma kudin sunyi yawa...." Kafin ta k'arasa magana har ya fita, tace, "Hafsat ki mayar masa da kudin nan."

Hafsat tace, "Koda na mayar mashi ba amsa zaiyi ba, kuma surukinki mai kudi ne, wannan ba wani abu bane a wajenshi."

Ta fita ta bar Umma a zaune kamar wacce aka dasa tana mai nadamar abubuwan da tayi mata.
Chapter 10 · 0% Book details