Sashe 5
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jalila tayi mata wani mugun harara tace,
"Dalla kiyi min shiru, ke dama idan mutum ya biye maki sai ayi mashi dukan tsiya sannan ya bada hakuri, yau sai Umar yasan ya b'ata maki rai."
Ta kira numbarsa yana picking tayi mashi tas, ta inda take shiga bata nan take fita, dukkanina aibun gidansu da ta sani sai ta amayar, yayi rashin sa'a Jalila basu da abun fad'a, saida tayi mashi wankin babban bargo sannan ta tsinke kiran tana sauke lumfashi ranta a matuk'ar b'ace.
Bayan Kwana Hudu,
Hafsat ce take waya da Jalila, tace, "Besty, kizo ki amshi tsarabarki Umma ta bud'e jaka." Daga daya bangaren Jalila tace, "Ayyerh k'awata, kunyarki nikeji akan abun da na janyo Umar yayi maki shiyasa kikaji ni shiru." Hafsat tayi dariya tace, "Kai babu komai tunda kin rama min kuma dolensa yayi shiru tunda kowa ya tabbata gidanku basu da aibu." Jalila tace, "Kiyi hakuri ban san zai b'ata maki rai bane shiyasa." Hafsat ta girgiza kai kamar tana gabanta sannan tace, "Na fad'a maki babu komai beside kin rama min abun da yayi min, a tunaninsa ni ce kadai nike da abun da za'a fad'a amma kin tuna mashi shima cewa shima iyayensa suna da abun fad'a kowa ya sani, kara kawai muke masu muna yi kamar bamu sani ba." Jalila tayi dariya sannan tace, "Naso ace ke fitinanna ce." Hafsat ta sauya hirar lura da kallon da Umma take mata, kallo ne da yake nuni da cewa ta fahimci wani abu akan wayar da take, tana jira ta gama ta fad'a mata ba'asi akan abun da ya faru. Tace, "Ki zo ki amshi tsarabarki." Jalila tace, "Alright, Angel, zan shigo yanzu kuwa Allah yasa har da alkaki." Hafsat tace, "Har dashi kuwa."
Tana tsinke kiran Umma ta tutsiyeta da kallon tuhuma tace, "Mi ya faru?" Tayi shiru, Umma ta daka mata tsawa, "Zaki fad'a min ko kuma sai na kira Jalila na tambayeta tunda ita tana ganina da mutunci zata fad'a min." Hafsat ta girgiza kai, "Umma ba haka bane, abun b'acin rai ne shiyasa." A ranta tana tunanin k'arya da zatayi Umma domin ta tabbata idan ta fad'a mata gaskiya sai rai b'aci domin babu abun da zai hanata zuwa gidansu Umar. Umma tace, "Ina sauraronki, mi fad'a min abun da ya faru, yadda ya b'ata maki shima sai ranshi ya b'aci." Ta lailayo ashar ta saki, zama da mutanen haya na gidan ya saka Umma ta koyi fitina, zagi da rashin hakuri.
Hafsat tayi dariya tace, "Bayan kin tafi biki yaje gidansu Jalila da nufin yayi min cin mutunci da gori, kin san Jalila babu hakuri ta fita tayi mashi wankin babban bargo, tayi mashi gori akan abun fad'i na gidansu, har kuka yayi domin kowa yasan gidansu Jalila basu da abun fad'a, basu da aibu." Tayi mata k'arya.
Umma ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Shiyasa yake da mu nemawa yaranmu iyaye na gari, kaicona na bujurewa iyayena na aureshi duk da halayensa amma soyayya ta rufe min idanu, saidai tun ba'aje ko'ina ba nike ganin ba daidai ba, ya gujeni, gashi yau har mutane suna maki gori akan zab'i marar kyau da nayi. Ki yafe min." Hafsat ta share mata hawaye, "Ummana ta kaina ki daina kuka, ki barni inyi tunanin yadda zani samo maki suruki irin wanda kike so." Umma tace, "Yauwa er albarka." A tare sukayi dariya.
Jalila ta bude labule saying, "Mu shigo ko mu koma." Umma tace, "Shigo er albarka, yanzu Hafsat take bani labarin yadda kukayi da Umar." Jalila ta zauna akan tabarma tace, "Ba ya wayo ko kadan, shi a ganinsa babu wanda yasan abun fad'a da suke dashi, yana tunanin bamu da labari akan dalilin da ya saka suke dawo cikin gari, kakan kakansa ya addabi kauyensu da haurawa gidajen mutane yawon kwartanci, suka koresu shine suka dawo cikin gari da zama. Shiyasa yake da kyau mutum ya tauna magana kafin ya fad'a, idan mutum ya biyewa b'acin rai sai yayi maganar da zai dawo yana nadama, koda ka baiwa wanda ka fad'awa hakuri ya hakura wannan bazai saka ya kwanta da ciwon maganar ba."
*********
Gidansu Hisham, Ranar Asabar,
Momcy ce zaune a parlor tana kallon News, Fatima tana daga gefe idanunta akan laptop dake gabanta yayinda Abdallah yake wasa da ball, Hisham ya fito daga study room yana sanye da dogon trouser da farar vest, Abdallah ya ruga inda yake, ya daukeshi yana mashi wasa suna dariya, kammanin yaron daya sak da Hisham, babu abun da ya baro na kamanninsa, har dariyarsu iri daya ne, ya saukeshi, yace, "Okay, kaje ka cigaba da wasanka."
Abdallah ya ruga ya dauki ball yayinda Hisham ya zauna kusa Momcy ya d'aura kanshi akan shoulder dinta yace, "Momcy." Tace, "Na'am Fad'a min abun da yake damunka."
Saida yayi jim kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace, "Kwanaki na hadu da wata yarinya muryarta daya sak da Bilkisu." Jin abun da yace ta cire idanunta daga kallon da take ta fuskanceshi, "Hisham don muryarta daya da Bilkisu, wannan bazai mayar da ita Bilkisu ba." Yace, "Momcy ba haka nike nufi ba." Ta maida hankalinta a kansa fahimtar akwai abun da yake son sanar da ita, tace, "Ina sauraronka." Saida ya lumfasa sannan yace, "Muryarta iri daya ce sak da muryar Bilkisu, the more take magana the more nike tunawa da Bilkisu, banbancin muryarsu daya ne shine ita tana da saurin magana..." jin yayi shiru, tace, "Ina jinka." Domin tana da tabbaci ba'a nan maganar ta tsaya ba, kamar ba zaiyi magana sai kuma yace, "Ina son in aureta."
Momcy ta dubeshi da mamaki sai kuma ta saki murmushi tace, "Hisham yau kaine kake min maganar aure. Alhamdulillah. Wacece ita?" Yace, "Sunanta Hafsat amma ana kiranta Angel, tana rayuwa tareda mahaifiyarta, mahaifiyarta ta bujurewa iyayenta ne ta auri mahaifinta, ashe bashi da kirki, bayan ta haifi Hafsat din ya gudu, danginta sunyi fushi da ita sukaki karbarta har sai ta maida diyar zuwa ga dangin mahaifinta ita kuma ta kiya saboda a cikin dangin mahaifin yarinyar babu na kirki, dukkanin inda ta bada diyarta rayuwarta zata tarwatse, a haka suka rayu a gidan haya, mahaifiyar tana aikatau."
Momcy tace, "Amma kana jin furucin da Aisha tayi, kada a k'ara maimaita abun da ya faru da Bilkisu." Hisham ya girgiza kai, "Barazana ne kawai takeyi." Momcy ta jinjina kai tace, "Amma kana tunanin idan sukayi bincike sukaga wannan matsalar zasu dauki diyarsu su baka?" Ya girgiza kai yace, "Babu bincike da zasuyi." Da mamaki take kallonsa jin abun da yace. "Ba zasuyi bincike ba saboda mahaifiyar yarinyar burinta kawai shine diyarta ta auri mai kudi." Jin haka tace, "Ya halayyar yarinyar yake kada azo a maimaita na Aisha." Yace, "Bata damuwa na fahimci hakane ta yadda ta sadaukar da farin cikinta domin ta cika burin mahaifiyarta."
Fatima ce ta dawo kusa dasu tareda zama akan hannun kujera tace, "Yaa Hisham yaushe zaka kaini in ganta?" Ya girgiza kai, "Ban yi mata magana ba, uhmm, saidai na saka ana bibiyarta, bayan auren zaki ganta." Fatima ta ware idanu jin abun da yace, tace, "Yaa Hisham kayi sauri ka gabatar da kanka a wajenta tun kafin ai maka wuff da ita. Muga hotonta?"
Ya fiddo wayarsa ya lalubo hotonta guda daya da yake dashi a wayar, ya mik'a mata yace, "Ita ce farar." Ta ware idanu tana yab'a kyawunta, "Wow, ta had'u, tana da kyau kamar jinin Arab. Amma ina ka samu hotonta?" Ta tambaya. Yace, "A social media k'awarta ta d'aura."
Fatima ta matsa wajen Momcy tana nuna mata hoton, "Momcy kin ganta, itace farar."
Momcy ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Masha Allah."
Hisham ya janyo dayar wayarshi yayi kira yayi jim sannan yace, "Tana ina?"
Daga daya bangaren aka ce, "Sir tana shopping mall." Saida yayi jim sannan yace, "Tare da wa? Okay, na gane." Mikewa yayi yace, "Momcy zan shirya in fita."
Fatima tana dariya tace, "Yaya yana kishi, yana gudun samari suyi mashi wuff da ita." Ya amshi wayarsa ya dungure mata kai, yace, "Gulma. Uhmm, yaushe zaki kawo min saurayinki."
Ta rufe fuskarta ta mik'e ta gudu tana cewa, "Babu ruwana."
Hisham da Momcy suka bita da kallo suna dariya.
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 4
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Shopping mall,
A jere suke tafiya a cikin shopping mall din, Hafsat tace, "Ina zamana lafiya kika tadoni, gashi ina ganin abu ina so babu damar in dauka tunda ban zo da shiri ba." Jalila tayi fuskar dariya tace, "Ki dauki dukkanin abun da kike kike so zan siya maki." Hafsat ta kai mata duka, ta goce saying, "Na sanki da kaunar chocolate. Ki zabi kowane iri kike so zan siya maki."
Hafsat ta kumtse dariya tana kallon tulun chocolate dake wajen tace, "Amma kin tuna kince kowane iri..." Jalila ta katseta, "Amma idan bai fi karfina ba."
Hafsat tace, "Kince duk wanda nike so, kuma kin dawo kince idan har baifi karfinki ba, wacce maganar zan dauka a ciki." Jalila tace, "Maganar hankali."
A tare sukayi dariya, suna zagayawa Jalila tana daukar perfumes, cream, lipstick, brusher yayinda Hafsat take busy tana duba chocolate.