Sashe 13
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace, "Na sani umma ba zata barki ki fito da yunwa ba, da kaina na shiga madafa na girka maki, kiyi karatu, ban da wasa. Guruwa." Tayi rolling idanu tace, "Gurguru."
A tare sukayi dariya, ta juya ta kama hanyar venue da zasuyi lectures, ta zauna kusa da Jalila, wanda yayi daidai da shigowar lecturer din.
Karfe goma daidai suka gama ajin, suna da lokaci har hour biyu kafin su k'ara shiga wata lecture, suka bi k'awayensu hostel, Jalila ta bude abincin yayinda kamshi ya bade dakin, suka zagaye suna ci.
Farida tace, "Yayi dadi."
Jalila tace, "Ina ya siya maki shi?" Hafsat ta ware hannuwa tace, "Ban sani ba saidai na tambayar maki shi inda ya sayi kayan hadin abincin domin da kanshi ya girka."
Sunyi matuk'ar mamakin jin da kansa ya girka. Jalila tace, "Yayi maki girki."
Farida tace, "Saurayi mai kulawa kamar wannan, ki rikeshi da kyau."
Saura mintina talatin su shiga lectures suka dawo faculty, karfe biyu tana fitowa daga inda suke sallah a faculty din taci karo dashi jingine da mota yana jefarta da murmurshi, wata motar ce daban yazo da ita.
Farar shadda ce a jikinsa ya daura zabuni a samanta, ya murza hula tangaram, yana kallonta yana murmurshi.
Ta lumshe idanu ta bude, da mamaki akan fuskarta tace, "Har ka dawo, nayi tunanin ba zaka zo ba, har zan hau bus sai kuma na tsaya nayi sallah."
Yana jefarta da murmurshi yace, "Matar Hisham zaki zama, na siya maki mota, da ita zaki rink'a zuwa unguwa da makaranta da dukkanin inda zakije." Tace, "Ka rufa min asiri gidanmu kofa ce, bani da wajen ajiye mota." Yace, "Akwai a gidan da na siya maku. Ya kikaga wannan motar." Ya k'arasa maganar yana nuna mata mota da yazo da ita, bata fahimci dalilin tambayar ba, tace, "Tayi kyau." Yace, "To shikenan tunda tayi maki kyau zan sauya maki da irinta."
Ta zaro idanu tace, "Wannan tafi karfina, waccen ma ban ce zan amsa ba, nayi godiya ne kawai, wannan motar tayi min tsada, mota kowace iri ce, tafi karfina."
Ya gyara tsayuwa yana mai tsareta da idanu yace, "Bata fi karfinki ba, Matar Hisham ake magana." Tayi kasa da kanta, yace, "Jalila fa?" Tace, "Jalila suna tana da lectures karfe biyu zuwa hudu, tana carrying 200 level course." Yace, "Okay, muje." Ya bude mata daya bangaren ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba, shiru ne ya ratsa motar, yana tuki yana satar kallonta, gani yayi ta janyo littafi zata fara dubawa, da sauri yace, "Ki cigaba da karanta min littafin, yayi min dadi." Ta rufe littafi tareda janyo wayarta tace, "Ban san in takura maka shiyasa nayi shiru, idan yayi maka dadi zakayi magana."
Tana karanta mashi yana gyada kai har yayi parking gefen gidansu, zata fita ya danna lock.
Ta dubeshi da sauri, yace, "Baki gama karanta min littafin ba, yayi min dadi kuma."
Hafsat ta ware idanu tace,
"Tab, bazai k'are a yau ba, wata ranar sai in k'arasa maka." Ya girgiza kai, "A'a. Nidai ki cigaba da karanta min." Yana mata shagwab'a tana daukarshi video tana dariya, the more yake mata shagwab'a the more yake mata kyau.
Ganin bazai barta ta fita ba ta turo baki tace, "Yunwa." Ya zura hannu a backseat ya zaro warmer tareda bottle water da zobo ya ajiye mata, "Kici, idan kika gama sai ki cigaba da karanta min, babu inda zanje sai an cigaba da labarin tunda yayi min dadi."
Ta kalleshi ta kalli warmer da ya ajiye mata, yana nufin a gabanshi zata saki baki tana cin abinci. Kamar ya fahimci abun da take tunani yayi kasa da kujerar da yake a kai, yayi relaxing tareda lumshe idanu, yace, "Da kaina na girka maki, kici hankalinki kwance masoyiya." Yana maganar ne ba tareda ya bude idanunsa ba, fankasu ne da miya da taji naman rago, girkin d'azu yayi mata dadi sosai, tana budewa kamshi mai dadi ya doki hancinta ta lumshe idanu, ta ci sosai, ta kora da ruwa tareda zobo wanda shima ba dai dadi ba.
Idanunsa a lumshe tana karanta mashi yana gyad'a kai, mintina talatin har awa daya da rabi, tunda motar tayi parking yake lura da ita har zuwa wannan lokacin, ganin babu wanda ya fito daga motar kuma tinted gareta, ya karasa tareda taping glass dake a bangaren seat.
Hisham yayi kasa da gilashin a daidai lokacin da suke dariya wa diramar Fatima da Aliyunta, makocinsu ne, ya kalli Hisham sannan kalli Hafsat dake a bangaren mai zaman hakanan, ya girgiza kai ya juya ya koma inda yake zaune ba tareda yace dasu komai ba.
Hisham ya ware idanu yayinda Hafsat ta tab'e baki tareda mayar da wayarta a handbag, ta b'alle murfin motar ta fito wanda yayi daidai da fitowar Hisham shima.
A daidai lokacin ne wata bakar Jeep tayi parking a kusa dasu, ta zaro idanu ganin Omar ya fito daga motar yana sanye wata dakakkiyar shadda golden color.
Kanshi tsaye ya durfafi inda take ranshi a matuk'ar b'ace yace, "Tunda naje nayi kudin sai ki rabu dashi ki dawo gareni."
Hisham ya murtuke fuska yace, "Hey!.." Hafsat ta juyawa Hisham tace, "Ranka shi dade na rokeka da girman Allah dukkanin abun da zai faru karka ce komai ka barni dashi."
Ta juya wajen Umar tace, "Na fad'a maka, ka rasani koda kudinka ba rabonka bace, sannan idan ka manta zan k'ara maimaita ni Hafsat bazan auri wanda yace zaiyi kudi ta kowace hanya ba saboda ina tsoron haram, ina gudun haram."
Umar yana huci yace, "Shi wanda kike tare dashi kina da tabbacin dukiyarshi ta halal ce. Hafsat k'arya kike! Ke tawa ce, ni kadai!."
Hafsat ta daka mashi tsawa tace,
"Karya kake!."
A fusace yace, "Ki bar ganin ina sonki, nima taimaka maki zanyi, kowa ya sani baki da asali, ke diyar macece, ubanki mahaifi dan chacha, mashayi."
Ta fashe da dariya sannan tace, "K'arya kake ina da asali, da uba aka haifeni don haka kayi karya ka kirani da marar asali. Ka iya bakinka wa aibata mahaifina."
Yayi dariya yace, "Ki musa idan k'arya nike, da bamu san asalin barbabela ba sai tace daga masar take. Ubanki mahaifi dan caca ne mashayi, ki gode Allah da ya gudu kafin ya sakaki a caca, yadda kike da kyau zakiyi daraja." Ji tayi hawaye sun zubo mata ta gogesu tace, "Careful! Ka iya bakinka."
Umar yace, "Hafsat dolenki ki aureni, kudi ne ina dasu a yanzu, itama mota ina da ita, kayan da ya siya maki da gold nima zan siya maki. Idan har ina lumfashi baki isa ki auri wani ba, yadda na rayu da sonki, haka dole in rayu dake."
Umar yana bata mamaki koda yake rashin ilimi ne yake damunsa, babu Arabia babu boko, tace, "K'arya kake wannan dake a bayana shine muradina. Da in aureka gwara in mutu."
A fusace yace, "Haka kikace, torh bari in saka a illatashi sai inga ta yadda zaki rayu dashi. Shege ku fito kuyi mashi dukan tsiya, kuyi mashi jina-jina, iya illar da kukayi mashi iya kudaden da zani baku."
Hafsat ta zaro idanu ganin kartai guda hudu en shaye-shaye sun durfafo inda suke.
Hisham yace, "Angel. Ki matsa, babu abun da zasu iya min. Daidai nike dasu." Kallon dan hutu take mashi marar karfi, ta d'aura hannu a kai tace, "Na boni. Baka ganin makamai dake a hannunsu ne."
Saida ya murmusa sannan yace, "Makami a hannun wanda bai san yadda zaiyi amfani dashi ba, aikin banza ne."
Ta had'e hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Na rokeka da girman Allah ka tsaya a inda kake a bayana, duk haukanshi bazai bari su tab'ani ba, shima ba zaiyi gigi ba." Tayi tsaye a tsakaninsu tace, "Idan ka isa nima ka saka su dokeni."
Umar yace, "Idan dukan kike so da kaina zan dokeki idan har shine yaren da zai saka ki aureni." Ya juyawa en shaye-shayen yace, "Shege ku sauyawa motar KAMANNI."
Kamar jira suke su dura akan mota suna fasa gilashintq, Hafsat ta janyo Hisham suka koma gefe, ta fashe da kuka ganin yadda suke fasa motar sun sauya mata KAMANNI, ta koma kamar ba ita ba.
Mutane sunyi taro suna kallo amma an rasa wanda zai hana, suna tsoron suyi magana Umar ya had'a dasu tunda ba ya jin kunyar uban kowa.
Tana mai fashewa da kuka tace, "Umar na tsanenka, nayi nadamar soyayya da nayi da kai. Umar ka fita daga rayuwata, soyayya ce nace bana yi, ana dole ne. Ni Angel nace bazan aureka sai kaje ka nemi wata."
Umar ya nunata da hannuwa da gargadi yace, "Keh, diyar mace, mara asali, diyar mashayi kuma dan chacha, dolenki ki aureni ko kina so ko baki so. Idan ban sameki ba, saidai kowa ya rasa. Sai na sameki ta kowace hanya."
Shiru yayi jin k'arar motar Jami'an tsaro wanda Hisham ya kira, shege da sauran yaranshi suka fara neman hanyar gudu amma tuni sunyi masu k'awanya.
Bodyguard din Hisham suka zagayeshi suna mazurai.
Jami'an tsaro sun kama Umar, shege tareda yaransa suka tusa kewarsu a motar da suka zo dashi. Daya daga cikin yaja motar da Umar yazo da ita.
Hafsat ta durkushe tareda fashewa da kuka tana kallon asarar da sukayi mashi, sun fasa mashi mota.
Hisham yace, "Please mana Matar Hisham, mota ce, ina dasu da yawa."
Tana mai cigaba da kuka tace,
"Amma asara bata da dadi, musamman b'arnar da akayi wa mutum da gangan. Kaje, zan wuce gida."
Hisham ya ware idanu yace,
"Wani gida? Zamanku a wannan unguwar ya k'are, bakiji furucin da yayi ba, ku dauko abubuwanku masu muhimmanci mu wuce, ba komai zaku daukq ba, na zuba maku komai a can."
Har zatayi magana sai kuma ta gyad'a kai, bata fatan ta k'ara ganin tashin hankali da ta gani a yau, ta juya ta nufi hanyar shiga gidan, mutane suka bita da idanu kasancewar har yanzu akwai taron mutane basu watse ba, bodyguard dinsa guda biyu suka rakata har kofar gida, ta samu Umma bata dawo ba, dama tayi mamakin rashin fitowar Umma.