Sashe 26
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar da Aysha ta samu labari kwana tayi tana bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba, "Ni zaka tonawa asiri, ni zaka ce zaka yi wa kishiya, baka isa ba, baka isa ba, itama tayi kadan ta shigo gidan nan a matsayin matarka. Idan abinci ne zanyi maka. Idan akan abinci ne torh abun ya tsaya a siyen abincin mana, miye na auren mai siyarwa da abinci. Ka rasa wacce zakayi min kishiya da ita sai er talla..." na katseta, "Food vendor dai." Tace, "Oho kuma baka isa kayi min kishiya ba. Miye kake son ci in girka maka?" Dariya ta bani, na murmusa nace, "Daga baya kenan."
Tana mita ta shiga kitchen ta had'a abinci ta jera akan dinning table, cokali daya nayi na maidoshi saboda yaji na da na ji, gishiri yayi yawa, mai yayi yawa, na b'ata fuska nace, "Wannan jagwalgwalon ne abinci, abu babu dadi. Idan baki iya ba kije wanda suka iya su koya maki." Tayi kasa da murya tace, "Ka bani numbarta inje ta koya min." Ta zaro waya tana jiran ya bata numbata ta kira tayi mata zagin k'are dangi, tayi mata gargadi akan mijinta.
Yayi mata kallon amma kin rainawa kanki wayo yace, "Kije wani wajen ki koya." A fusace tace, "Haka nike girka abincina kuma dole ka ci a yadda na girki ko kuma a dauko er aiki." Ya fashe da dariya yace, "Nine kike tunanin zan ci abincin mai aiki, ki daina rainawa kanki yawo da kanki." Tace, "Ka bani numbar yarinyar muyi ciniki da ita tazo tana girka mamu ina biyanta, ai diyar talakawa ce."
Yayi dariya sosai har da kyakyatawa tace,."Bilkisu ce zata zo maki a er aiki, idan kanki ya samu damuwa kije likita ya dubaki." Ya tsallaketa ya haye bene zuwa dakinsa, yana ji tana bala'i yayi mata banza, tun daga ranar fitinar rana daban, ta dare daban. "Baka isa kayi min kishiya ba, saidai a mutu, kai da k'ara aure saidai kaga wasu suna yi. Ban da butulci bayan duk kaunar da na nuna maka amma shine zakayi min kishiya. Ka rasa abun da zakayi min sakayya dashi sai kishiya." Ya d'aga kai ya kalleta yace, "A kaunar ne kika kasa min girki." Kanta tsaye tace, "Na ga kana zuwa gidanku ka ci, ni kuma ina siyowa daga restaurant."
"Da aurena sai in rink'a zarya gidanmu cin abinci, ina tadawa mahaifiyata hankali."
"Shine ni kuma yanzu zaka tada min hankalin."
"Kece kika janyowa kanki."
"Tun kafin ka aureni ka san ban san girki, ban iya ba."
"Nima kuma tun kafin muyi aure kin san ban cin abinci siye?"
Tayi dariya tana tab'a hannuwa tace, "Miye banbancin? Huh. Ina wahala da cikinka amma koda tausayina baka yi zaka min kishiya." Yace, "Ni ba kishiya zanyi maki ba...." ta katseshi a fusace tace, "Idan ba kishiya bace, wacece? Huh." Yace, "Abokiyar zama, idan kika rike girmanki zatayi maki biyayya, Bilkisu bata da damuwa."
Tayi ihu tana tab'a hannuwa tace, "Daga kai har ita Bilkin kunyi kadan ku tona min asiri. Koni ko ku? Wanda ya fasa ya raina kanshi."
Magabata sun shiga magana har an saka rana, biki saura sati biyu Aysha ta haifi Abdullahi, saboda bala'i taki komawa gida wanka, a satin bikin muka koma gidan da Umma take a zaune, a sashen da kuke a can ne Aysha ta zauna, yayinda aka kai Bilkisu a daya sashen.
Tunda aka kawo Bilkisu, Aysha ta hanamu zaman lafiya, fitinar rana daban, ta dare daban, a kullum Bilkisu k'ara shiga raina take tana sona tana kyautata min, tana girmama mahaifiyata, tana daukar Fatima kamar k'anwarta, tana baiwa Aysha girmanta duk da rashin mutunci da takeyi mata dare da rana.
Tare da Bilkisu muke shiga kitchen tana koya min girki, saida taga na kware, duk girkin da nike maki ita ce ta koya min.
Bilkisu ta samu ciki wanda yake wahalar da ita, a lokacin ne kuma ta fara gane-gane tana mafarkai kamar yadda kikeyi, ta rame ta fita hayyacinta, cikin yana da wata biyar aka nemeta aka rasa, munyi mata neman duniya muka rasa.
Ranar na shiga sashen Aysha na samu tana hira da k'awarta suna tattaunawa akan yadda suka haukata Bilkisu tabi duniya.
Saidai ganina tayi a dakin, ta zaro idanu fahimtar naji komai.
Ji nike kamar in rufeta da duka, na dauki biro da takarda na rubuta mata saki biyu, na mik'a mata ina zubar da hawaye nace, "Aysha kin cuceni, kije na sakeki saki biyu, kin cuceni, kin cuci Bilkisu. Allah yana gani kuma shine zaiyi mamu sakaya."
A lokacin ta yaye Abdullahi yana wajen Momcy, tun daga wannan lokacin nike neman Bilkisu amma babu ita babu alamarta, Bilkisu ta kula da ni, ta kaunaceni, ta girmama ni, ta kwantar min da hankali, ta bani shawarwari a rayuwa wadanda naga amfaninsu.
Shine ranar naji muryarki kina magana, na dauka Bilkisu ce har na bude maki Niqab kika mareni, muryarki tana KAMANNI da muryar Bilkisu, a dukkanin lokacin da kikayi magana kina tuna min da ita shiyasa nike yawan janki hira, nike sakawa kina karanta min jarida.
******
Hafsat ta fara girgiza kai tana hawaye tana mai cewa, "Hisham ka cuceni, ka tarwatsa min rayuwa, ka sakani a cikin bala'in da bai shafeni ba, kasan abun da yake damunka amma ka aureni, ka yaudareni ka saka na yarda da cewa kana sona, ashe baka tab'a sona ba, ashe muryata ce ta janyoka."
Hisham ya kama hannunta ta fizge tana mai ja da baya, yace, "Amma Hafsat saida nayi k'ok'arin in sanar dake amma kika ki saureni kika ce baki da buk'atar sani."
Hafsat ta fasa ihu tace, "Kasan girman duk da nace haka sai ka sanar dani, kai da kanka ka tabbatar da cewa da nasan wannan bala'in ne tun kafin ka fad'a min zan gudu da kafafuna, babu mamaki ka kasa auruwa, wacece zata aurarwa kanta tikitin hauka. Kana sane da bala'in dake zagaye da kai amma ka yaudareni ka aureni. Ashe duk akan muryata ne, ka yaudareni ashe muryarta kake bi, shiyasa kake sakani karanta maka jarida da littattafan hausa, shiyasa baka tab'a yaba kwalliyata ba saboda ba kaunata kake ba, muryata ce kake da buk'ata. Don haka bazan iya ba, ka sauwake min, ka sakeni in koma gidanmu. Na gama aurenka. Na fasa auren." Ya girgiza kai yana kama hannunta, ta fizge ta fasa ihu tace, "Baka isa ba, dole ka rabu dani."
Hisham yayi baya da sauri tareda toshe kunnuwansa saboda karfin ihu da tayi, tana kuka tana fad'in, "Hisham. Ka sakeni. Sai ka sakeni."
Hisham yayi mata tsawa yace, "Angel ki dawo hayyacinki." Ta ware idanu tace, "Ina a hayyacina shiyasa nace ka rabu dani, wacce take a cikin hayyacinta ce zata nemi hanyar rabuwa da kai domin ta kub'uta da hankalinta. Ko ka sakeni, ko baka sakeni ba, na fasa auren gidanmu zanje." Ta juya ta haye saman bene ta zuba kaya a akwati ta janyoshi ta fito tareda saukowa parlour, yasha gabanta yace, "Angel babu abun da zakije." Ta rab'a ta gefensa tace, "Bani zama da kai in hauka ce." Yace, "Ba zan sakeki ba." Tace, "Idan ta samu labarin bani gidan zata shafa min lafiya, kai kuma idan ka gaji da jiran gawon shanu sai ka sakeni. Miye na turjewa akan ba zaka sakeni ba, bayan da ni da kai mun san cewa ba sona kake ba, muryata ta janyo ka, ko muhimmanci muryar a gareka yafi hankalina."
Ya daka mata tsawa yace, "Cikina kike dashi, ba zaki bar gidan nan ba har sai kin haifar min cikina, tunda ba dashi kika zo ba, bayan nan idan kika ce min in sakeki zan sakeki, amma yadda kikazo ke daya haka zaki koma ke daya, ba zaki wuce min da gudan jini ba."
Ta fashe da kuka tace, "Dukkanin tada jijiyoyin wuya da kakati ashe akan cikin da nike dashi ne, torh ba zan zauna ba."
Ya daka mata tsawa a karo na biyu yace, "Idan kin isa ki fita ki gani."
Ta durkushe tareda fashewa da kuka, ya tsallaketa ya wuce sama, tayi kuka har ta godewa Allah, tayi kira numbar Umma ta fashe da kuka ta kasa magana, tana ta kuka ta tayarwa Umma da hankali.
Hankali a tashe Umma take tambayarta dalilin kukanta. Tana sheshshekar kuka tace, "Umma na boni. Hisham ya cuceni. Ashe bai tab'a sona ba, dukkanin abun da yake ashe akan muryata ne, saboda ina da irin muryar matarshi ta biyu, wacce matarshi ta farko ta haukata ta shiga uwa duniya tana hauka, babu wanda yasan inda take. Dukkanin abubuwan da na fad'a maki a ranar da na zo da gaske sun faru, ba mafarki bane, matarshi ta farko ta saka aljannu suke wasan kura da ni, har gida tazo tayi min gargadi idan ban rabu dashi ba nima zata haukani in gudu a rasa inda nike."
Umma ta dafe kirji idanunta a waje na jin abun da yake shirin faruwa da gudan jininta, tace, "Na boni. Hafsat ki tattara kayanki ki dawo gida dolenshi ya sakeki, dolenshi ya rabu dake." Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma yace ban isa in bar gidan ba, ciki gareni, yace sai na haifa mashi cikinsa sannan in bar gidan."
Umma ta ware idanu tace, "Yana nufin ki zauna kema ta haukataki kamar yadda ta haukata waccen, tunda ance mashi ban kaunarki, ki tafo karki zauna ko kuma inzo da kaina in wuce dake."
Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma yace kada in sake in fita, gwara mu bishi a hankali, idan muka ce za mu bi ta tsiya mune a kasa. Na riga na saka kaina a tsaka mai wuya, fitata a cikin sauki ba mai yiyuwa bane ba."
Umma ta fashe da kuka, yau ne rana ta farko Hafsat taji Umma tana kuka, tace, "Umma ki daina kuka." Daga daya bangaren Umma tana mai cigaba da kukan tace, "Hafsat kiyi hakuri ki yafe min, son kudina ya janyo na sakaki a cikin hatsari, kudi sun rufe min idanu babu bincike na aura mashi ke. Hafsat nice na cuceki tun farko."