← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 47

Sashe 3

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zauna tareda zuba mashi kunun, "In saka maka suger?" Ta tambaya. Ya girgiza kai, "A'a. Kin sanni bana sonshi da suger, na fi son dandanonsa a yadda yake."

Har ta mike sai kuma ta koma ta zauna tace, "In tsaya inyi maka hira." Yace, "A'a, ina son kasancewa ni kadai." Ta ware idanu, "What! Amma mun dade da maganar nan kayi min alk'awari akan zaka rage sakawa kanka damuwa." Ya dafe kai, "Fatima ba haka nike nufi ba, ina nufin ki bani waje zanyi wanka in huta, kinga na gaji."

"Ka tabbata ba tunani zaka zauna kayi ba."

Ya gyad'a mata kai yana kirkiro murmurshi, tace, "Shikenan. Na tafi. Ka kula da kanka." Tana fita ya ajiye kofin ya janyo wayarsa ya shiga gallery hotonsa ne tareda wata kyakykyawar yarinyar wankan tarwada.

A hankali yace, "Bilkisu kina ina ne? A wani hali kike ciki? Tunda kika b'ata nike a cikin damuwa. A yau na hadu da wata mai irin muryarki sak, the more take magana the more nike tunawa dake, ina son k'ara haduwa da ita saboda KAMANNI da muryarku ta ke yi."

Ya dauki kofin yana sirfing kunun a hankali, wayarsah tayi ringing, ganin bakuwar number yayi jim kamar ba zai amsa ba sai kuma yayi picking yana fatan labari ne akan inda Matarsa Bilkisu take.

Daga daya bangaren Aisha tace, "Ranka shi d'ad'e."

Da sauri ya cire wayar daga kunnansa tareda tsinke kiran, wani kira ya k'ara shigowa, yayi rejection kiran tareda kashe wayar baki daya, ji yayi komai ya fitar mashi a kai ya mik'e ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi shower yayi tsaye yayinda ruwa suke sauka akan jikinsa, yana tuna abubuwan da aka aikata mashi wadanda sune sanadin rushewar farin cikinsa, ya jima a hakan sannan ya d'aura towel ya fito ya fad'a akan gado ya zubawa ceiling idanu yana tuna baya.

The following day, a hankali yake saukowa daga stairs yana sanye da suit brown cikin shirinsa na zuwa aiki, yayi matuk'ar kyau, sumar kanshi irin ta buzaye tana a kwance, yana tafe yana baza kamshi mai sanyi, kai tsaye ya wuce dinning table, yaja kujera ya zauna yana mai gaishe da Momcy. Ta amsa da kulawa.

Fatima da ta ajiye flask tace, "Ina kwana yaya Hisham?" Yace, "Lafiya lau. Kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau. D'iyar direba babu lafiya a asibiti suka kwana, please ka sauke ni a school."

"Babu damuwa, uhmm musha hira abunmu."

"Haka, muyi gulmar Momcy."

Momcy tace, "Ji min yara nema kuke ku mayar da ni kakarku. Zan hadu daku ne." A tare sukayi dariya.

Fatima tayi serving dinsu sukayi breakfast, saida ya ajiye Fatima a makaranta sannan ya wuce company, yayi parking motarsa a parking lot dinsa wanda yake underground, ya fito yana dauke da briefcase, Najeeb ya amshi briefcase din saying, "Good morning sir."

Hisham yace, "Morning. Bana son hayaniya zanbi private elevator dina."

Najeeb yace, "An gama ranka ya dade."

Hisham yana gaba Najeeb yana biye dashi heading to the elevator, Najeeb ya danna bottom din, ya bud'e suka shiga, ya danna floor na ashirin da daya 21 wanda shine floor na karshe a inda ofishin CEO yake, suka fito suka bi wani corridor, Hisham ya danna hannunsa akan wata na'ura, ya dauki finger print dinsa sannan kofar ta bud'e suka bayyana a wani katon office, gini ne na glass.

Najeeb yace, "Sir Hisham, Coffee ko Tea?"

Hisham yace, "Ka koma ofishinka, idan ina buk'ata zanyi wa secretary magana." Najeeb yace, "Okay sir." Ya juya ya nufi kofa, Hisham ya kira sunansa, "Najeeb." Najeeb ya juyo saying, "Sir."

Hisham yace, "Na gode sosai Najeeb da tsayawa da kake akan al'amurana. Ina matuk'ar godiya, Allah ya saka da alheri."

Najeeb yace, "Allah ya bayyana Bilkisu." Ya juya heading out yana mai tausayinsa. Hisham yace, "Amin."

Tunda yaji muryarta ya kasa sukuni, the more yake tuna Bilkisu the more muryarta (Hafsat) take mashi amsa kuwwa a kunne a lokacin da take baiwa k'awarta labari.

Wani kamshi mai ne ya doki hancinsa ya rumtse idanu yayinda b'acin rai ya bayyana k'arara akan fuskarsa, ba tareda ya kalli wacce ta shigo ba ya danna landline yace,
"Secretary, how dare you let her walk into my office. Waye ya bata izinin shigowa ofishina."

Daga daya bangaren yace, "I'm sorry sir, she didn't listen to me, ina mata magana tayi banza dani, ta bangajeni ta shigo."

Cike da b'acin rai yace, "Huh haka aka yi? Baka da yadda zakayi da ita shiyasa ka barta ta shigo? Alright then."
Secretary yace, "Sorry sir."

Da kakkausar murya yace, "Damn it, daga yau idan ka kuma bari ta shigo ofishina ka rasa aikinka. Idan ta bangajeka ta shigo, aikinka ta bangaje, ka rasashi."

Ya d'ago ranshi a b'ace ya daka mata tsawa, "Aisha!."
She is chubby, brown skin mai matsakaicin tsawo, tana sanye da atamfa dinkin half gown, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, fuskarta dauke da simple makeup, tasha Jan lipstick, kafafunta rufe da takalma kirar half cover, da mayafi akan kafad'arta, tana kallonsa tana wani shegen murmushi, tayi tako tareda d'aura hannu akan desk dake gabansa ta rik'e kugu da daya hannun tace, "Tabbas Aysher shine sunana saidai tsawarka ba zata saka in koma inda na fito ba har sai na aiwatar da abun da ya kawoni tukunna."

Ya daka mata tsawa a karo na biyu, "Ki fitar min daga office, tun kafin in hadaki da security." Saidai tsawarsa bata razanata ba, sai murmushin gefen baki da tayi tace, "Kwantar da hankalinka, koda baka ce ba ai dole zan fita tunda ba ofishin ubana bane ba, na zo ne in k'ara tuna maka abun da ka riga ka sani, jiya na kira ka tsinke min kira, ina baka shawara gwara ka hakura ka mayar da ni, idan har Bilkisu ce kake jira ba zata sake dawowa ba, ta tafi kenan, tana garari akan titi tana hauka. Ni ce kadai wacce zakayi rayuwa da ita a matsayin matarka a zauna lafiya, babu macen da ta isa inyi zaman kishiya da ita a gidanka. Tun wuri kayi wa kanka fad'a ka mayar da aurenmu. Hisham da wata mace ta rab'eka gwara kowa ya rasa. Ba Bilkisu ba, kowace mace da zata rab'eka sai na b'atar da ita, sai na zame mata guguwar bala'i. Kaje ka dawo ina nan ina jiranka."

Hisham ya kira sunanta a tsawace,
"Aishaaa!."

Duk da ta razana da tsawa da yayi mata a wannan karon saidai bata nuna ba, ta kanne ido guda daya sannan tace,
"Kana wahalar da kanka ne domin tsawarka ba zata tab'a razanar da ni ba, domin ban fito ba saida na shirya. Ya yarona Abdallah?" Yayi banza da ita kamar baiji abun da tace ba, tayi dariya mai sauti, "Koda yake na tabbata yana a cikin koshin lafiya a tare da danginka, ka fad'a mashi ya k'ara idan ka gama zagaya duniya ka tabbatar da dukkanin wacce ka nuna interest a kanta fad'awa take taskon rayuwa, daga karshe dole zaka dawo gareni, ni duwawu ce zama dani dole, kishiya a gidana babu. Na barka lafiya." Ta juya tana tako daidaya yayinda baki daya jikinta yake girgiza, juyowa tayi fuskarta dauke da wani shu'umin murmushi tace,
"Da fatan ka rik'e gargadin da nayi maki, idan kana ganin barazana ne ka kwatanta ka gani idan har zaka rab'i wata mace ni kuma zan kassara rayuwarta. Idan baka gaji ba, nima ba zan gaji, a shirye nike a koda yaushe domin kassara rayuwar dukkanin wacce ta rab'eka ko kuma ka rab'eta."

Hisham yace, "Mugun abu jakada ne idan ka aikeshi komai daren dadewa sai ya dawo zuwa gareka domin ya sanar da kai cewa yaje."

Aisha ta girgiza kai tace, "I totally disagree with this proverb, whatever. Saidai idan mutum bai iya takonsa ba, kamar yadda Bilkisu take a uwa duniya tana hauka, wannan shine kwatankwacin abun da dukkanin wata mace daka rab'a zata fuskanta, shawara ka taimaka karka tilasta min tarwatsa rayuwar wata, ka taimaka masu ka dawo zuwa gareni sai a zauna lafiya. Ka rage sakawa kanka damuwar wacce ba zata tab'a dawowa ba. Ayyerh Bilkisu, tana zamanta lafiya a akurkin gidansu ka janyo mata fitina."

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 3

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

Hisham ya daka mata tsawa yayinda idanunsa suka kada sukayi ja ya nuna mata kofa, "Ki fitar min daga office." Ta razana har saida tayi baya, duk da haka bata karaya ba tace, "Idan naki fita ba, miye kake ji zaka iya aikatawa. Nace or else what? Do your worst I don't care."

A fusace ya mike ganin haka ta juya ta fita, ya fad'a akan kujera tare da dafe saitin zuciyarsa yana maida lumfashi, ya jima a haka kafin ya bud'e idanunsa wadanda suke sauya launi a sanadin b'acin rai, ya danna landline yace, "A fito min da mota yanzu." Ya jingina da kujera ya lumshe idanu yana sauke lumfashi ransa a matuk'ar b'ace.

*****

Hafsat da Umma ne zaune a saman tabarma akan baranda yayinda sauran matan gidan suke zaune a bakin bishiyar mangoro dake a tsakar gidan, Hafsat tana jerawa Umma celatap zata saka mata lalle, lokaci zuwa lokaci wayarta tana tsuwwa, tun tana tsinke kiran har ta kashe wayar baki daya.

Umma tace, "Hafsat ki amsa kiran."
Chapter 3 · 0% Book details