Sashe 29
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta kira numbar Jalila, "Jalila. Hisham ya sakeni, ya amshe Muhammad. Ki zo gida yanzu, ki tafo min da kaya guda daya sannan itama Umma ki tafo mata da kaya guda daya, har hijab da takalma." Sai kuma ta tsinke kiran.
Mintina ashirin a tsakani sukaji k'arar mota, Hafsat ta fita da sauri, ba motar Hisham bace, aka yi parking, Jalila ta fito daga bangaren mai zaman hakanan yayinda Aliyu ya fito daga mazaunin direba, Hafsat ta juya ta koma ciki ba tareda da tace dashi komai ba.
Aliyu ya gaida Umma sannan yace, "Jalila ta fad'a min abun da ya faru, bai kamata a barshi haka ba." Ranshi yayi matuk'ar b'aci.
Hafsat tace, "Yaa Aliyu ku barshi da yaron, dukkanin ranar da na tashi amsarshi sai yayi nadamar sanina da yayi. Na rokeku da girman Allah kada wanda ya sake min wannan maganar. Umma ki tashi ki sauya kaya muje."
Hafsat ta sauko tana sanye da kayan da Jalila ta kawo mata, babu jimawa Umma ta sauko, Hafsat ta tara masu aikin gidan tayi masu bankwana, suna ta jimami.
Umma ta zauna a baya, Jalila ta zauna a daya bangaren, Hafsat ta bud'e bangaren mai zaman hakanan ta shiga, tace, "Yaa Aliyu ka biya dani in sayi waya, sannan ina ne zan samu gidan haya."
Da mamaki Aliyu yace, "Gidan haya kuma? Angel idan har ina raye kin fi karfin zama a gidan haya." Tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Saidai kuma wannan Hafsat ta daina dogara da wani, zan nema a wajen Allah, zan jajirce in gina kaina da kaina." Da kakkausar murya yace, "A gidana zaku zauna, magana ta k'are."
Zatayi magana yayi mata kallon cikin idanu babu shiri ta juyar da kanta yayinda bugun zuciyarta ya k'aru, yayi dariya yace, "Kin fasa maganar ne?" Tayi mashi banza.
A bakin wani plaza yayi parking, Hafsat da Aliyu suka fito suka shiga ciki, k'aramar waya ta dauka keypad, tareda waya Samsung, aka yi mata bill dubu dari biyu, Aliyu ya mik'a katinsa.
Da kakkausar murya tace, "Ni na sayi waya, da kaina zan biyaka kudinka, idan ka zare a katinsa saidai in ajiye maka abunka inje wani wajen in siya."
Aliyu yayi shegen murmurshi yace, "Tare muke, nine zan sayi wayar, ka had'a mata da iPhone zan biya."
A fusace ta juya ta koma mota, ya mik'a mata leather ya tada mota, alert ya gani ta saka mashi kudinsa ya ware idanu yana kallonta, tace, "Saidai kuyi hakuri dani."
Ya wuce dasu gidanshi dake a sabuwar kasuwa, da kanshi ya fito ya bude get ya shiga da motar, gidan ba zai fi wanda suka fara komawa a lokacin da suka tashi ba, dakuna gida biyu room and parlor, sai kuma fallen daya guda biyu, kitchen, store, bandaki tareda k'aramin tsakar gida wanda zai dauki motoci biyu, sai parlour dake a tsakanin dakunan.
Yace, "Ku zauna a nan kafin in gyara gidana dake a dutsen safe sai koma a can." Ji yayi tace, "Jalila ku tayani mu duba gidan idan yayi."
Jalila ta dubeta da mamaki, Hafsat tace, "Eh ku tayani dubawa tunda kudin haya zan biya." Aliyu ya murtuke fuska yace, "Hafsat lokacin da nace maki ina sonka da gaske ina sonki, na saka kinyi k'arya ne saboda bani da wata mafitar bana fatan auren mahaifiyata ya mutu a dalilin nawa auren, na sa ni ina da kasona na laifi akan abun da Hisham amma ina ganin ban cancanci wannan hukuncin ba, ki duba na mayar maki da kudin da kika saka min." Muryarta a sanyaye tace, "Inyi maka sadaka dasu?" Ya juyo yace, "Idan kikayi sadaka Allah zai baki lada, kudinki ne ba kudina ba." Ya ajiye mata makullin motarsa ya fice ya amshi motar da direba ya kawo mashi.
Jalila ta raka Hafsat kasuwa ta siya masu tsohuwar katifa guda biyu, sutura, kayan abinci da sauransu, da marece sosai suka koma gida.
Ta shiga daki ta kulle sannan ta kira numbar Aliyu yana d'agawa ta fashe da kuka, hankalinsa a tashe yake tambayarta abun da yake faruwa, tana mai sheshshekar kuka tace, "Ina neman alfarma guda biyu a wajenka kamar yadda ka nema a waccen ranar nayi maka ina son a yau ka mayar wa kura aniyarta nima kayi min alfarma." Ya lumfasa sannan yace, "Ina sauraronki." Tace, "Na farko ina son kayi min alk'awari akan ba zaka tab'a tursasani komawa gidan Hisham, ka rokar min Umma da Jalila suyi min wannan alfarmar nasan dalilin da ya saka nayi wannan maganar. Na biyu ina son kayi min hanya in sayi gida a wani wajen gidan da ba ya da alaka da kai, kayi min hanya in sayi mota, ka taimaka min da dukkanin karfinka amma ban da kudinka, soyayyar da zaka nuna min a yau shine ka kyaleni in fuskanci kalubalen rayuwa a yadda suka zo min, inyi surviving a karan kaina." Yayi shiru na wani lokaci kamar zatayi kuka tace, "Aliyu." Ya ware idanu yace, "Yaushe ne kika fara kirana da sunana kai tsaye." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Tun daga lokacin da na fad'a soyayya da sunan."
Yayi mata hanya ta sayi gida a dutsen safe, babba ne sosai, ta dubeshi tace, "Wannan gidan yafi karfina." Ya murtuke fuska yace, "Irinsa ne nike da hanya idan kuma kin san dilallin gidaje muyi mashi magana ya nema maki gida a cikin kwatoci muga idan zaki iya kwana biyu a ciki." Ido ba mudu bane amma yasan daidai, kudin da aka fad'a mata tasan gidan yafi karfin haka, ba tayi kasa a gwuwa ba ta biya domin bata son yaga kamar tana hukuntashi akan abun da ya faru ne.
Ta raba dare tana tunanin kasuwancin da ya kamata tayi, Washegari suna zaune a falo, tace, "Jalila wani kasuwancin kike ganin ya kamata in fara?"
Jalila tayi jim sannan tace, "Siyar da abinci online tunda kin kware a girki." Hafsat ta ware idanu tace, "Abinci dai? Sana'ar wacce aurena ya mutu a kanta, kawo wata ban da wannan, girki ci min rai yake."
Jalila tayi jim sannan tace, "Tunda kina da numbobin mata, matan masu kudi, ina ganin ki fara kasuwancin siyar da shadoji, atamfofi, leshe, mayafai, material, abaya, jilbab, jikkuna da takalma, kina d'aurawa a status, wanda yake so yayi payment a turo, sai in hadaki da wanda nike siya a wajenshi. Sai ki k'ara da kayan shiga da wankan na maza su kuma ki rink'a d'aurawa a Facebook da Instagram."
Ji tayi hawaye sun zubo mata ta rungumeta tace, "Jalila na gode, ke k'awa ce ta gari, bazan tab'a mantawa da halarci da kikayi min a rayuwa ba." Jalila tace, "Angel ya kamata ki koma makaranta, ki ida session daya da kikayi difering."
Hafsat tace, "In shaa Allah. Jalila rashin daukar shawarar da kika bani tun farko shine ya janyo min wadannan abubuwan." Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "A lokacin da na ji maganarki, da ban yanke hukunci a cikin gaggawa ba, da duk haka ba ta faru ba."
A gidan Jalila ta wuni saida marece sannan Hafsat ta rakata ta hau kekenapep ta wuce gida, ita kuma ta juya ta koma gida.
Kwana biyar a tsakani Jalila ta wuce Sokoto inda a can ne aka turata bautar kasa.
******
Hafsat ta dage kasuwanci, kuma Alhamdulillah tana samun ciniki, duk da wasu lokuttan abun yana tsayawa, idan mutum yayi order ta siya a turo mata daga Kano ya amsa, idan kuma a wani garin yake daga Kano take tura mashi zuwa garin da yake, tana fasa dila a gida ga wadanda suke zaune a garin Katsina.
Numbobinta na what'sApp suna mata ciniki sosai, tana samun shawarwari a wajen Aliyu, kuma tana hakuri da mutane, idan ta samu order na Ready made na maza, ta sayi yard ta bada shago a dinka sannan ta aikawa mutum garin da yake, zabuni, manyan riguna aiki mai aska duk tana yi.
******
Ta tashi da tashin zuciya da kasala, Umma ta matsa mata taje asibiti, awo ya nuna tana dauke da ciki, ta kule a daki tana kuka, Umma tayi tambayar duniya amma bata sanar da ita ba, tana kuka ta kira numbar Jalila tace, "Jalila na boni. Ciki ne dani."
Jalila tace, "Baki boni, ciki ne da ubansa, kuma da aure kika sameshi. Kije ki samu Hisham ki sanar dashi, idan kin dawo ki kira ki sanar dani yadda kukayi. Idan kuma baki kira ba, karki nemani." Ta tsinke kiran, ta lura idan sukayi wa Hafsat saku-saku a banza ciwon zuciya zai kamata.
Hafsat ta jima tana nazari kafin ta mike ta zura dogon hijab ta fita, ta tsaida kekenapep tare da sanar dashi inda zai kaita, yana ajiyeta ta bashi kudinsa, ta kwankwasa kofar dake gefen get, Mai guard ya bude yana ganinta yayi murmurshi tareda matsa mata, yace, "Barka da zuwa, Hajiya. Ki shigo."
Hafsat ta girgiza kai tace, "A'a baba adamu. Ina wuni?" Ya amsa da, "Lafiya lau Hajiya."
"Yana nan kuwa?" Ta tambaya. Ya gyad'a kai yace, "Eh yana nan, ki shiga." Ta girgiza kai tace, "A'a, ba sai na shiga ba, kayi min magana dashi." Ta zauna akan bench.
A tare suka dawo, tun daga nesa yake kallonta har ya k'araso inda take, saida ya rufe kofar sannan yace, "Angel, miye haka? Na fad'a maki abun da zai faru da matata idan ta ganki, ko taji zancen kishiya." Ji tayi hawaye sun zubo mata ya fara korarta tun kafin yaji abun da ya kawota, ta share hawayen tace, "Amma dai, ka tsaya ka ji abun da nike tafe dashi sannan."
Hisham ya had'e hannayensa waje guda alamar roko sannan yace, "Please, ki tafi, kada ta fito ta ganki." Tace, "Mu hadu a ofishinka." Ya kama hannunta yana janta har bakin get yace, "Please ki fita daga rayuwata." Tace, "Abun da nike tafe dashi fa?" Ya dafe kai yace, "Angel mi yasa kike haka? Bana son rasa matata, idan ta ganki aka fad'a mata zata iya mutuwa. A yau zan tattara matata, yarana, mahaifiyata da k'anwata mu koma London. Idan matsalar kudi ce, ki turo min account number."