← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 47

Sashe 20

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kiyi min voice kice ina sonka masoyi." Taji yace. Da sauri ta dubeshi tana mamakin abun da ya furta, ita da take a gabansa miye amfanin voice note. Har saida ya maimaita abun da yace sannan tace, "Gani a gabanka babu buk'ata inyi maka voice saidai in kalli cikin kwayar idanunka in fad'a maka abun da yake a cikin zuciyata na sonka." Ya girgiza kai yace, "A'a kiyi min voice note." Abun ya fara sakata a cikin kokonto mi yasa dole sai voice note bayan tana a gabanshi. Ta zaro wayarta ta shiga chat ta danna wajen voice note tayi jim sannan tace, "Ranka shi dade ina sonka."

Hishim ya girgiza kai yace, "Ba haka zakice ba. Cewa zakiyi ina sonka masoyi."

Da mamaki tace, "Miye banbanci ina ce ranka shi dade da nace yafi masoyi da kake son in fad'a. Yace, "Ki furta min inji." Ta kalleshi tace, "Ina sonka masoyi." Ta furta hakan ne Idanunta suna a kanshi.

Hisham ya lumshe idanu ya bude yayinda a lokaci guda yaga fuskarta ta rikide ta koma fuskar Bilkisu.

"Torh, Kiyi min voice." Taji yace. Tayi jim tana mamakin dalilinsa na san tayi mashi voice note, kamar ba zatayi ba sai kuma ta danna wajen voice note tace, "Ina sonka masoyi."

Ganin lokaci yaja tayi mashi sallama, ya rufe mata motar ta kama hanyar gida yayinda ya juya ya ciki.

Saida ya raba dare yana sauraron voice note da tayi mashi a lokaci guda yana tuna yadda Bilkisu take furta wadannan kalmomi a gareshi.

Maganar aure ta kankama, magabatan Hisham sun samu Baban Jalila sunyi magana sun bada kudin neman aure har an saka rana, watanni biyu masu zuwa. Maganar ta bugeta sosai musamman da har a lokacin Aliyu yake manne a cikin zuciyarta, ta hana kanta kwanciyar hankali yana zaune a office saidai ganinta yayi, ta fashe mashi da kuka, "Na rokeka Aliyu ka fad'a masu ban san aurenshi, ka fad'a masu kaine a cikin zuciyata." Kafin ya yunkura har ta zube a kasa warwas, hankalinsa a tashe ya sureta ya fice yaja motarsa zuwa asibiti, aka karbeta tareda bata taimakon gaggawa, yana tsaye yana kaiwa da komowa hankalinsa a matuk'ar tashe, idan ciwon zuciya ya kamata shine sanadi, ya daura laifin komai a kansa. Ta farfado tana barci likita ya k'ara tabbatar mashi da damuwa ce take damunta idan suka sake komai zai iya faruwa, damuwa da take a ciki ba kadan bane.

Ya rike hannunta yana murzawa a hankali ya kira sunanta, "Hafsat." Ta d'ago da hannunta ta kalleshi da muryarta da bata fita sosai tace, "Aliyu ina sonka." Ya gyad'a kai yace, "Na sani, ina matuk'ar sonki, saidai ba zamu iya kasancewa a tare ba, domin Hajiyata ta rantse idan na aureki sai ta tsine min, Alhaji yayi rantsuwa akan idan tayi yunkurin hanawa zai iya rabuwa da ita. Please Hafsat mu hakura da junanmu. Muyi wa junanmu fatan alheri, ba zan yafewa kaina ba idan na zama dalilin mutuwar auren iyayena hakanan idan kika samu damuwa a dalilina bazan tab'a yafewa kaina ba. Soyayya da zaki nuna min a yanzu shine ki hakura dani, ki auri wanda yake sonki." Ta fashe da kuka, "Hisham yana sona, kai kuma kana matuk'ar sona idan aka bani zab'i kaine wanda zan zab'a domin kaine burina." Ya girgiza kai, "Hafsat ki manta da ni." Ta girgiza kai, "Aliyu bazan iya ba." Sarkewa tayi lumfashinta ya fara sauka sama-sama, da sauri ya kira likita ya dukufa a kanta, kamar ba zata rayu ba, hankalinsa ya tashi ya kira Umma ya sanar da ita asibiti da suke, babu jimawa direba ya kawota hankalinta a tashe ganin halin da Hafsat take a ciki saidai tayi kuka. Ciwo tayi sosai kamar ba zata rayu ba, ta rame ta fita hayyacinta wanda ya tilasta masu k'ara kwanankin auren.

******

Momcy, Fatima, Hafsat da Jalila suka lula Dubai hado lefe daga nan suka wuce London suka k'arasa had'awa duk da mafi yawan lokuttan sunyi yawon bude idanu ne domin ragewa Hafsat damuwa da take a ciki, daga nan suka wuce Umrah, a nan suka hadu da Hisham, daga nan suka juyo gida Nigeria, biki ya matso, dukkanin bangaren sun dukufa shirye-shiryen biki.

*****

Hisham ne yayi parking motarsa, Hafsat ta fito tana nufar inda motarsa take tana tafiya a nutse, ta b'alle murfin motar tace, "Barka da zuwa ranka shi d'ad'e. Umma tace lallai-lallai in tusaka gaba mu shiga tare." Kallo daya yayi mata ya gane damuwa da take a ciki saidai bai tambaya. Ya fito yayi gaba tabi bayanshi, ya gaida Umma tare da zama akan kujera mai daukar mutum daya, Umma ta amsa da kulawa tana tambayarshi mutanen gida. Ta dora da cewa, "Tunda baka shigowa gaidani shine nace ta shigo da kai." Ya sosa keya yace, "Zan rink'a shigowa." Umma tace, "Madallah. Angel ki zuba mashi abinci." Ya ware idanu jin abun da tace. A rayuwarsa girkin Momcy da na Bilkisu kawai yake iya ci, sai wanda ya girka da kanshi ko kuma Fatima ta girka mashi, dadin dadawa har lokacin bai san yadda tsaftar girkinsu take ba, idan ya tuna wancen gidan da suka taso sai yaji kamar zaiyi amai, idan yaci abincin zai iya amaye dukkanin abun ya saka a cikinsa tun daga safiyar yau.

Dubara ce ta fad'o mashi, yace, "Angel kece kika girka?" Hafsat ta girgiza kai tace, "A'a. Umma ce ta girka."

Ya girgiza kai kamar baiji dadi ba yace, "Angel baki kyautawa kina a gidan kike barin Umma tana shiga kitchen. Zo muje in koya maki neman albarka tunda baki iya ba." Ya juya wa Umma yace, "Umma zan shiga kitchen in girka maki tuwo miyar kubewa." Umma tace, "A'a. Ba za'ayi haka ba." Ya girgiza kai yace, "Neman albarka zanyi, da ni da Hafsat duk daya ne a wajenki." Tace, "Allah yayi albarka." Yace, "Amin."

Ya mike ya nufi hanyar kitchen yana mai sauke ajiyar zuciya, Hafsat ta dauki wayarta tabi bayanshi, tana mashi bidiyo, ya saka afro yana girki cike da nutsuwa, the more take kallon yake girkin the more yake mata kyau, girki yana mashi kyau musamman yadda yake motsawa da karsashinsa na maza majiya karfi. Mamaki take sosai ganin kwarewarsa, yana tureta tana komawa tana mashi bidiyo, "Wow. Girki yana maka kyau."

Ya tuka tuwo ya gama miya, ya zuba mata a plate ya mik'a mata, ya zuba a daya plate ya zauna a kusa da ita.

Hafsat tace, "Muci tare." Da sauri ya dubeta sai kuma yace, "A'a. Kowa yaci abincinsa." Tana ci tana lumshe idanu yana mata dariya, suka gama ta tayashi suka wanke abubuwan da aka bata, ya dauko warmer da ya saka na Umma, ya ajiye mata a dinning table. Umma tace, "Ka zauna kaci." Hafsat tace, "Munci wanda ya girka a kitchen."

Umma ta jingina kai tace, "Allah yayi albarka." Suka amsa da, "Amin." Yayi Umma sallama, ya fita tabi bayanshi. Suka zauna a balcony tana kallon bidiyo da tayi mashi tana mashi hira tana murmushi, zuciya tana son mai kyautata mata, a kullum cikin faranta mata yake, sannu a hankali take jin sonsa yana shiga zuciyarta saidai tana tabbaci akan ba zata tab'a mashi son da takeyi wa Aliyu ba, kauna ce zallah, ya jima sannan ya wuce.

********

Biki ya matso, hidima ake to kowane bangare, a gidan da ya zauna da Bilkisu za'a kaita, bangaren da Aysha ta zauna, an gyara sashen, ya sauya mata komai.

Lefe akwatu guda ashirin da hudu aka kawo, yawa, tsad'a da kyawun akwatunan da yawan kayan da suke a ciki saida yaba Umma tsoro, satin biki yazo, Hafsat tasha gyaran jiki ciki da waje wanda aminiyar Umma ce take mata, tayi kyau fatarta tayi subul-subul, dukkanin inda ta gitta kamshi ne yake tashi.

Sunyi dinner, sunyi Lunch, sunyi Bridal shower and football, amarya da ango sunyi kyau, kyau ne ya hadu da kyau, Masha Allah, sai ka rasa da ango da amaryar wanene yafi kyau, naira tayi kuka, bikin ne kawai yake trending saboda yadda aka saki zallar naira.

Kwallo ne kawai en unguwarsu Hafsat sukaje duk da shima tasan gulma ce ta kawosu amma ta tarbesu da fara'arta, aniyar kowa ta bishi.

**********

RANAR DAURIN AURE.

Ashraim yace, "What? Kana nufin a yau za'a daura mata aure."

Daga daya bangaren Habib yace, "Labarin da nike samu yanzu kenan, sun sauya gida ne, shima wancen suka k'ara tashi shiyasa na rasa labarinta."

Ashraim ya kashe wayar tareda durkushewa ya dafe saitin zuciyarsa, yana matuk'ar sonta, ba ya da burin ya rasata.
(Aliyu yana kaunarta, Ashraim yana sonta, Hisham yana son muryarta irin ta matarshi Bilkisu. Muje zuwa.)

INA LABARIN AYSHA?

Duk abun da yake faruwa bata da labari sai a satin auren take samun labari kasancewar tana London, ta bar aikin bibiyar al'amuran Hisham a hannun K'aninta Jameel. Tunda ta saka kafa ta tafi, Jameel yayi zamanshi a gida yana cin kudaden da ta bar mashi, idan ta kira ta tambaya yace mata babu komai, sai a satin bikin take samun labari, babu shiri ta sayi tickets ta hawo jirgi zuwa Abuja, daga Abuja ta k'ara hawa wani jirgin zuwa Kano, direba ya sameta a Kano ya daukota zuwa Katsina.

Tun daga compound take huci tana bala'i. A fusace ta wuce dakinsa, yana ganinta yayi kasa da kai, saida tasa hannu ta wanka mashi mari sannan ta fasa ihu tace, "Jameel ka cuceni. Ka kassara min rayuwa. Ina can ina tunanin komai daidai ashe yana a nan yana shirin angwancewa da wata daban."

Jameel yace, "Kiyi hakuri."

Tayi mashi wani mugun kallo tace, "Hakuri dolena inyi tunda cuta ce ka cuceni. Ina kudadena? Nace ina kudadena? Tunda baka yi aikin kudin ba sai ka maido min abuna." Jameel yayi kasa da kai yace, "Babu su. Na kashe dukkanin kudin."

Ta daka mashi tsawa tace, "Ka iya ka zauna kabi takan kudadena amma baka iya kayi min aikin da na sakaka ba. Yaushe ne daurin auren?" Ta tambayeshi tana mai zare idanu. Yace, "Yau. Karfe biyu da rabi."
Chapter 20 · 0% Book details