← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 47

Sashe 37

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganinshi a cikin damuwa yana tada mata hankali, tana matuk'ar sonshi, bata da burin ganinsa a cikin damuwa, ranar yaje ya tarar da Hafsat tare da Aliyu, ya dawo gida ranshi a b'ace, Bilkisu ta tareshi da fara'arta tana sanar dashi abincinsa yana akan dinning table. Tsawa yayi mata, a fusace yace,."Na ce maki ban ci, ana dole ne. Ki je ki zuba a shara."

Bilkisu tayi mutuwar tsaye tana bin bayanshi da kallo, mijinta da yake matuk'ar kaunarta, mijinta da yake bata kulawa shine ya koma haka, bata gane mashi kamar an sauya mata shi.

Washegari taje har gida ta sanar da Momcy abun da yake faruwa. Momcy ta fayyace mata komai akan abun da ya faru tun daga haduwar Hisham da Hafsat har rana irin ta yau.

Bilkisu tayi still tana wiki-wiki da idanu yayinda baki daya jikinta yake rawa, ta janyo maganinta tasha, ta mike tace, "Na wuce Momcy."

Momcy tace, "Ki gaida gida. Ki cigaba da hakuri."

Bilkisu bata nuna mashi tasan gaskiya ba, ta daina shige mashi idan ba ya a cikin yanayi mai kyau, itace kullum a cikin damuwa, idan ta tuna abun baki daya jikinta rawa yake, tsoro ya kamata, ta rasa yadda zatayi ta ceci mijinta daga halin da yake ciki.

*********

Hafsat tana zaune a parlour ana mata lalle, ta jiyo muryar Bilkisu a tsakar gida tana gaida Umma, tayi still tana tantamar anya kuwa ta jiyo daidai ko kuma kunnanta ne yake mata gizo idan ba haka ba miye zai kawo Bilkisun Hisham har gidan.

Umma tayi still tana kallon Bilkisu sai kuma tace, "Lafiya lau. Ki zauna."

Bilkisu ta zauna a gefen tabarma yayinda Muhammad tun da ya ganta ya manne mata, Bilkisu tace, "Matar Hisham ce, Bilkisu."

Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Sai yanzu na gane. Kuna lafiya?"

Bilkisu tace, "Lafiya lau. Little, zo." Ganin yaron baije ba, Umma tace, "Aliyu, kazo ka gaidata."

Little Aliyu yace, "She is stranger, Right? Ammi tayi min fad'a."

Umma tayi mashi dakuwa tace, "Karka k'ara min wannan yaren, ni ina nike jinsa."

Bilkisu tayi murmurshi, Little yace, "Ina wuni?" Bilkisu tace, "Kana lafiya?" Yayinda ta tsura mashi idanu ganin matuk'ar KAMANNI da yake yi da Hisham kamar kobo da kobo.

Umma tace, "Hisham mutumina, d'azu yana nan muka sha hira, bai jima da tafiya ba."

Bilkisu tace, "Hakane. Angel fa?" Ta tambaya. Umma tayi mata alama wa kofar shiga parlour tace, "Tana parlor ki shiga."

Bilkisu ta mikawa Muhammad da Little Aliyu chocolate da tazo masu dashi.

Hafsat wacce ta zubawa kofar parlour idanu, ta waresu tana kallonta, Bilkisu ta tsura mata idanu yayinda gabanta ya yanke ya fad'i ganin matuk'ar kyau da Angel take dashi, tserayyar dake a tsakaninsu banbancin a bayyane yake, the difference is clear.

Mariya da ke yi wa Angel kunshi tace, "Ki shigo mana." Bilkisu ta zauna akan kujera tace, "Na gode." Mariya ta fita.

Hafsat tace, "Barka da zuwa. A kawo maki ruwa?" Bilkisu tace, "A'a. Daga gida nike." Hafsat tace, "Okay. Ayyerh."

Bilkisu ta lumfasa sannan tace, "Sunana Bilkisu... Matar Hisham..." Hafsat ta jinjina kai tace, "Eh na sani."

Bilkisu ta damke daya hannunta da yake rawa sannan tace, "Nazo wajen ki ne akan Mijina." Hafsat ta ware idanu tace, "Ki saka ranki a idanu domin mijinki ba ya a gabana koda daura min shi aka yi a kafa zan kwance in gudu da kafafuna."

Bilkisu tace, "Hafsat. Hisham yana sonki, yana matuk'ar sonki. Momcy ta sanar da ni dukkanin abubuwan da suke faruwa. Dukkanin abubuwan da suka faru a sanadina ne, ina mai baki hakuri akan hakan. Hisham yana cikin damuwa, yana matuk'ar sonki, ki taimakeni ki yarda ki aureshi." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Ciwon y'a mace na y'a mace ne, amma abun da kike nunawa a yanzu son zuciya ne, da bakinki kika ce ya fad'a maki abun da ya faru amma har kika samu karfin gwuwa na zuwa inda nike da wannan magana. In tambayeki mana, idan kece yayi wa abun da yayi min zaki koma gidansa, ya samu damarsa yayi wasa da ita, a lokacin an bani zab'i kuma na zab'i zama dashi saboda ina son in kyautata amma shi da ya samu zab'i watsar dani yayi, yayi min butulci. Godiya wa Aliyu wanda ya tsaya a lokacin da ban san halin da zai shiga ba."

Bilkisu ta hade hannayenta waje guda alamar roko sannan tace, "Please. Hisham yana a cikin wani hali, idan baki aureshi ba zai iya shiga matsananciyar damuwa."

Hafsat ta d'aga mata hannu tace, "Kinga maganar gaskiya muyi ta da gaskiya, mijinki ne bazan aura ba, akwai wanda zan aura Aliyu Muhammad, na tabbata kin sanshi."

Bilkisu ta cigaba da rokonta, "Amma Hisham yana matuk'ar sonki."

Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Aliyu yana matuk'ar sona, kada ki zama mai bakin ciki mana, na fad'a maki ina da wanda zan aura Aliyu Muhammad, kin sanshi, ya fi mijinki kyau, ya fi mijinki nutsuwa, ya fi mijinki kudi, ya fi mijinki sona, don haka ba zanyi wa kaina salalar tsiya ba. Kema saidai ki so kanki amma kin san Aliyu ya fi mijinki komai, bugu da kari shine wamda ya kula dani a lokacin da mijinki ya watsar dani. Bayan dukkanin abun da ya faru ko kece a mazaunina aka ce ki zab'a ba zaki zab'i Hisham ba," ji tayi hawaye sun zubo mata tana tuna abubuwan da yayi mata a shekarun baya, ta saka hannu ta share hawayen tace, "Bilkisu mijinki Hisham butulu ne, marar tausayi, don haka please ban da bakin ciki, kiji da mijinki nu kuma in auri wanda ya fi sona, namiji mai nutsuwa. Mijinki Hisham tsoro yake bani domin ba ya da tabbas. Kiyi hakuri amma bazan iya auren mijinki ba, na barki lafiya. Shawarar da zan baki itace kije ki kula da mijinki ki fad'a mashi gaskiya akan ya manta dani" Ta mike ta wuce saman bene.

*******

Ashraim yayi parking motarsa, Hafsat ta bude backseat Little Aliyu da Muhammad suka shiga sannan ta zauna gefen direba, ya ja motar zuwa katuwar shopping mall, da kanshi ya bude bangaren da take ta fito, suka wuce ciki tana rike da hannun Little Aliyu, yana rike da hannun Muhammad.

Ashraim yana jan trolley yayinda Hafsat da yaran suke daukar dukkanin abun da yayi masu suna sakawa, suna sanye da shadda iri daya dinkin babbar riga.

Ashraim ya biya aka saka masu kaya a booth suka kama hanyar gida, wayarta ce tayi ringing tana dubawa taga Aliyu, ta manta tana tare da Ashraim tace, "Hello, love." Gabanta ne ya yanke ya fad'i tunawa da Ashraim dake a gefenta yana tuka motar, ta wayance tace, "Jalila, k'awata. Ya ake ciki? Ok zan kiraki, anjima. Ina tare da ranka shi d'ad'e."

*******

Aliyu ya zubawa wayar idanu da damuwa kwance akan fuskarsa, yana sonta, yana matuk'ar sonta, amma Ummi tayi mashi katanga da aurenta, ya dafe zuciyarsa dake mashi matsanancin ciwo.

Batuul ta sameshi a wannan halin kamar ba zatayi magana sai kuma ta zauna, tace, "Miye?" Yayi shiru. Bata takura ba ta mike tana tafiya tana magana, "Ka bar dawo min gida da damuwar wata idan har kana sonta kayi yaki a kanta, bana tsoron kishiya ko gudunta, damuwa ce bana so."

Ya bita bayanta da kallo har ta fita, ya kira numbar Hafsat ta sameta a kashe, bai ga laifinta don ta kula wasu, lokaci yayi da ya kamata ya daina yaudarar kansa, lokaci yayi da ya kamata ya barta tayi aure.

*****

Tana a balcony maid ta sameta, ta dubeta da mamaki tace, "Miye?" Safiyya tace, "Wata mata ce take sallama dake." Da mamaki tace, "Take sallama dani ko kuma take jirana a parlour." Safiyya ta girgiza kai tace, "A'a tana a bakin titi a motarta taki shigowa."

Tayi matuk'ar mamaki saidai bata san dalilin wacce ta aiko na kin shigowar ba wannan ya saka ta warware mayafi dake a saman kanta ta yaneshi ta fita. Tayi turus ganin Bilkisu ce wacce take sallama, tace, "Ki shigo." Bilkisu ta fito daga mota tana mai girgiza kai tace, "A'a ba sai na shiga ba, na dawo ne akan maganar ranar nan, Hisham yana cikin damuwa, sonki ya hanamu farin cikin kullum yana cikin damuwa da fushi, abu kadan zai fara fad'a ba ya ji ba ya gani, please ki yarda ki aureshi bana son in rasashi." Hafsat tayi dariya tace, "Nana kina da abun dariya, yanzu da bakinki kike fad'a min matsalolin da kike samu dashi amma shine har kike rokona in aureshi. Malama kije kiji da mijinki wannan MATAR ALIYU ce. Idan har kina sona kiyi min addu'a akan Allah ya bani Aliyu." Bilkisu tace, "Idan kuma Hisham ne alherinki." Hafsat tayi murmurshi tace, "Zan amsa da godiya domin shine ma fi sani akan abun da yafi zama alheri a rayuwa don haka kije gida ki nutsu kiyi tunani akan hanyar zaki bullowa matsalar da kike fuskanta a gidanki. MATAR ALIYU nike ba Hisham ba. Na barki lafiya."

Washegari tana kwance akan gado tana waya da Ashraim, Little Aliyu ya shigo yana video call da Aliyu, ya mik'a mata wayar yace, "Abba ne." Ta manta da akan waya take da Ashraim. Ta amshi wayar ta saki baki suna hirar soyayya.

Aliyu ya d'aga mata hannu yace, "Barka da wannan lokacin gimbiyata." Ta gane barkwanci yake ji tayi dariya tace, "Barka da warhaka yariman zuciyata. MATAR ALIYU tana gaishe da Aliyu."

Yaja lumfashi yana mai tsura mata idanu yace, "Nayi kewarki." Tace, "Nima nayi kewarka."

Dukkanin wannan hirar da takeyi Ashraim da har lokacin bai tsinke kiran ba yana ji.

Daga daya bangaren Aliyu yace, "Yaushe ne MATAR ALIYU za ta yi min kwalliya in zo in ganni." Tayi mashi fari da idanu tace, "Dukkanin lokacin da Aliyu yake so MATAR ALIYU za ta yi mashi kwalliya ya zo ya gani."

Sun jima akan wayar dukkanin hirar da sukayi akan kunnan Ashraim, jin suna sallama yayi sauri ya tsinke kiran.Hafsat ta manta da waya take ta cigaba da harkokinta.

washegari da marece tana kallo a parlour taji k'arar shigowar mota tayi mamaki domin babu wanda sukayi zai shigo, jim Maid ta shigo ta sanar da ita zuwan Ashraim. Tace, "Okay, ki ce mashi ina zuwa."
Chapter 37 · 0% Book details