Sashe 15
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jalila ta kunna tv a parlor tana kallon series da tayi missing jiya.
Umma ta shiga kitchen ta dama koko, ta soya kosai, ta zuba ta zubawa Jalila ta ajiye na Hafsat a warmer, kokon kuma ta zuba a flask.
Knocking sukaji, Umma ta saka Hijab, Jalila ta bi bayanta, daya daga cikin bodyguard din Hisham ne. Ya rusuna ya gaishe da ita, "Mama. Ina kwana?"
Umma tace, "Lafiya lau."
Ya mik'a mata basket dake hannunsa yace, "Inji ranka shi dade."
Jalila ta amsa, Umma tace, "Mun gode. Ka tsaya in baka sako ka kai mashi." Ta juya ta koma ciki. Ya gyad'a kai yana mai gyara tsayuwa.
Jalila tabi bayanta, Umma ta dauki abincin da ta ajiyewa Hafsat, ta mik'awa Jalila tace, "Ki kai mashi, ya kai mashi." Jalila ta fita ta mik'a mashi.
Ruwan shayi ne, bread, dankali da kwai, jalof rice wacce taji nama.
Duk da Jalila taci kosai da kokon da Umma tayi amma saida ta k'ara.
*******
Hisham ya kalli koko da kosan ya girgiza kai yace, "Ba zan ci, idan ina da buk'ata zan kira Momcy ta girka min."
Najeeb ya dubeshi da mamaki yace, "Amma kai ta aikomawa." A takaice yace, "Ba zanci abun da suka girka ba, ban san yadda tsaftarsu take ba." Najeeb yace, "Kai ka sani, ni ina ci, ina laifin wanda ya yaba da kai har ya aiko maka abinci, kai da aika masu suka amsa sun san tsaftarshi." A takaice yace, "Ni nasan tsaftata." Najeeb yace, "Suma sun san tsaftarsu."
Najeeb yana cin kosai yana korawa da koko yana gyad'a kai yana jin dadi a tsakiyar kansa, Umma ba baya ba akan girki. "Uhmm. Yummy. Hisham dadi ya wuceka."
Hisham yayi banza dashi ya kira numbar Momcy, "Momcy a girka min koko da kosai, zan aiko a amsar min."
Bayan ya tsinke kiran ya maida akalar kiran zuwa numbar Hafsat.
Daya daga bangaren Hafsat tace,
"Na gode da abinci. Allah ya k'ara budi."
Ya amsa da, "Amin." Ya dora da cewa, "Nima kiyi min godiya a wajen Umma."
Hafsat tayi dariya tace,
"Umma dai, nawa ne fa, har ta ajiye min, ta bada aka kawo maka. Nayi magana tace ay ina barci ta shiga madafa ta dafa don nima in shiga in dafa da hannuna."
Ya lumshe idanu yayinda muryarta take mashi matuk'ar dadi a kunnuwa, yace, "Umma tafi ji da ni, kuma yayi dadi sosai." Ya k'arasa maganar yana kallon Najeeb dake cin kosai yana lumshe idanu, yana tsokanarta tana biye mashi, hayaniya ya fara jiyowa yace, "Waye?"
Hafsat wacce ta d'aga labule dake a parlour tace, "Makotanmu ne suka zo." Hisham yace, "Alright, na barki lafiya."
Najeeb yace, "Kamar da gaske har da cewa da dadi bayan baka ci ba." Hisham yace, "Ka isheni da santi, nima nawa yana akan hanya."
******
Hafsat ta zare wayar daga kunnanta tana kallon makotansu da suke shigowa, wasu bayan wasu, tawaga guda. Jalila kallonsu take ido waje baki bude.
Umma tana ta masu sannu da zuwa da fara'arta mutum rahama ne.
Murjah tace, "Angel ki bada kudi a baiwa masu kekenapep, guda hudu muka ciko."
Hafsat tace, "Kun san baku da kudin kuma kukazo." Jalila ta amsa da cewa, "Sai kace zuwan ya zama dole."
Da kakkausar murya Umma tace, "Hafsat ki basu. In k'ara jin bakin mutum a wajen in sab'a mashi, miye laifin wanda yazo inda kake tayaka murna, bakonka annabinka."
Hafsat ta juya ta koma ciki, jim kadan ta fito ta mika masu dubu ukku.
Ta samu har Umma ta shimfida masu tabarma a tsakar gida. Saida suka gama yawo suka zagaye gidan baki daya sannan suka zauna.
Nafisa tace, "Angel. Nifa ko kalaci ban yi ba na biyosu kada su tafo su barni kuma bani da kudin zuwa."
Jalila tace, "Da kin sani kin bari kinyi kalaci sannan ki tafo, yadda muka biya kudin zuwanku a tare, sai a biya a rabe."
Umma tace, "Angel ki dauko mata abincin da Hisham ya aiko." Hafsat ta ware idanu tace, "Wanda zanci ne kawai kuma nima yunwar nikeji."
Umma ta murtuke fuska tace, "Nace ki tashi kije ki dauko mata, ita da yake yunwa takeji da gaske tayi magana ke kuma tun d'azu kina ganinsa kika zauna bakici ba." Ba don ranta yaso ba ta dauko mata, Nafisa tayi wuff ta amsa ganin zasu saka mata wawa ta koma gefe ta rantse babu wanda zaici tunda ita daya aka kawomawa.
Murjah tace, "Nima yunwar nikeji amma sai kice ke daya zakici, kin fi wani ne." Nafisa tace, "Oho." Ganin zasuyi masu fad'a Jalila tace, "Murjah kiyi amfani da cikon kudin da suka rage ki siyo abinci kici, magana ta k'are."
Jumala tayi karaf tace, "Yunwar nan kowa jinta yake, nima ban yi kalaci ba."
Umma tace, "Gashi kuma bamu sauran abinci amma bari in tashi in girka maku."
Tana rufe bakinta aka soma shigowa da manya_manyan kuloli wadanda suke da dauke da jalof na shinkafa da taliya da nama.
Yaran da suka shigo dasu suka ce, "Gashi inji ranka shi dade."
Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Mun gode. Allah yayi albarka." Suka amsa da, "Amin." Duk yawan abincin saida su Jumala suka cinyeshi, ci sukayi na tsiya har da guzuri.
Ta kira Hisham ta fashe da kuka hankalinsa a tashe yake tambayarta abun da yake mata, tana sheshshekar kuka tace, "Umma ce ta dauki breakfast da ka aiko tayi kyauta kuma yunwa nikeji, Umma ta daina sona, wayyo cikina yunwa." Ya ware idanu yace, "Kuma ban jima da aiko abinci ba na bakin da kukayi, da na sani da na aiko maki dashi." Jin kamar yana cin abinci ne, tace, "Miye kake ci?" Yace, "Koko da kosai Momcy ta aiko min."
Da sauri tace, "Ka gutsara ne a yanzu?" Yace, "Ehh." Yana kallon sauran kosan da yake a hannunsa, kanta tsaye tace, "Ka mayar dashi ka rufe ka aiko min." Dariya yayi yace, "Amma wasa kike." Kyit ta tsinke kiran.
Ya kira har ta tsinke bata amsa ba, saida ya ajiye mata miss call ukku bata amsa ba kuma tana kallon kiran, Umma ta aiko mata da abincin da ya kawo taki ci, a dole ita tayi zuciya.
Umma tayi kwafa, "Yunwa ce ba k'anwar uwa bace, idan zakiji shawarata ki tashi kici yunwa da kike ganinta bata da hankali."
Ta kwashe abincinta ta wuce dashi bayan da ta balbaleta da fad'a, "Kuma ko yunwa zata kayar dake ba zakici wannan abincin ba saidai kije ki girka da kanki, da ni kike magana."
*******
Hisham ya dubi Najeeb yace, "Miye mafita?" Najeeb yace, "Mafita kenan ka aika mata dashi idan kana son zaman lafiya." Kamar zaiyi kuka yake kallon koko da kosan. Yana ji yana gani yana son yaci domin yayi mashi dadi amma dole ya bada aka wuce mata dashi. Ya ajiye mata sakon text message.
"Za'a kawo maki yanzu."
Tana ganin sakonsa ta mike ta wuce tsakar gida ta janyo farar kujerar rubber ta zauna kusa da get tun kafin Umma ta amshi abincin ta kyautar dashi.
Ana knocking ta bude ta amsa, ta wuce parlour dashi, Umma ta girgiza kai kawai.
Kosan da kokon yayi mata dadi sosai, tana ci tana gyad'a kai, gutsiren da ta saka ya mayar dashi ta fara. Saida taci ta koshi sannan ta kira, tace, "Na gode da abinci." Cike yake da ita ya saka Momcy tayi mashi girki tayi kwace karfi da yaji that yana ji yana gani ya aiko domin a zauna lafiya.
Yace, "Ina zuwa." Ya kira Momcy ya hadasu a kiran gamayya. Yace, "Momcy tana jinki kiyi mata godiya da kanki." Ta zaro idanu ta dauka da wasa yake har saida taji muryar Momcy, a kunya ce ta gaidata tayi mata godiya.
Bayan ya cire Momcy daga kiran tace, "Mi yasa zakayi min haka?" Yace, "Ramawa nayi, kikayi min karfi da abinci, kuma dolena na aiko domin a zauna lafiya." Tayi dariya tace, "Umma ta aiko maka sannan Momcy ta aiko maka kuma in barka dashi saboda yunwa bata dameni ba." Yace, "Na rama mun zama daidai." Sun jima suna waya hakan yayi mashi dadi sosai. Ta biye mashi ne saboda Umma cike da take da ita, idan ta fita ko kallon arziki ba zatayi mata ba.
Jalila tana wajen Umma tana tayata hidima da mutanen.
Misalin karfe biyu na rana ya k'ara aiko masu da abinci, shima saida suka cinye har da guzuri. Abincin da ya aikowa su Umma daban yake. Jalila ta zubawa Hafsat, Umma ta murtuke fuska, "Tazo da kanta ta zuba ko kuma ta wuni da yunwa, kuma ta saka ya aiko abinci daban a gabanta inyi kyauta dashi inga k'arar taurin kai." Jalila ta tura mata text message yadda sukayi da Umma.
Babu arziki ta fito ta zuba da kanta, Umma tace, "Kika ce taurin kai gareki." Hafsat tayi dariya tace, "Ayyerh Umma kiyi hakuri na tuba." Ta zauna a parlour tana ci, cokali daya tayi ta lumshe idanu tace, "Wannan girkin Hisham ne." Jalila tayi mamaki tace, "Ya kika gane?" Hafsat tayi murmurshi sannan tace, "Saboda Hisham ne, ni kuma MATAR HISHAM." Umma tace, "Torh mara kunya a gabana." Hafsat ta mike ta wuce daki da abincin tana dariya.
Jalila ta biyo bayanta, Hafsat ta kalleta ta watsar tace, "Sai yanzu kika san hanyar dakina." Jalila ta harareta tace, "K'aramin aikina ne in koma inda na fito. Ke a haukanki sai in biyoki d'azu fushin da Umma takeyi yake ya shafeni, babu ruwana."
Saida marece sannan su Jumala suka tafi bayan da Hafsat ta basu kudin mota amma suna fita kofar gida suka rabe kudin, kadan daga cikinsu ne suka hau kekenapep, sauran suka nanike kudinsu a kugunsu suka taketa a kafa, tawaga guda.
Tun a daren suka fara yada gulma a unguwa, suna cewa kwadayi ya kai Umma ta siyar da diyarta, kafin washegari kowa yaji a unguwar, suna ta en tsugunne-tsugunne suna zagin Hafsat da Umma suna cewa kwadayi ne da son abun duniya sunga mai kudi sun manne mashi saboda yana basu.
****