Sashe 24
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mikewa yayi ya wuce kitchen ya dauki lokaci kafin ya fito ya zuba mata abincin ya koma parlour ta dauki cokali tayi bismillah kafin ta faraci, tana cin abinci tana sauraron karatun Alk'ur'ani mai girma, rabonta da taci abinci a cikin kwanciyar hankali har ta manta, taci tayi nak ta wanke hannuwanta ta sameshi a parlour, kallo daya yayi mata ya maida dubansa akan TV yayinda gabanta yake faduwa akan abun da zaije ya dawo game da abun da Aysha tazo ta fad'a mashi. Duk da yayi nufin fad'a mata tun farko saidai koda a waccen lokacin yayi nufin b'oye mata abun da ya faru da Bilkisu domin ya tabbatar da ba zata yarda da aurensa ba idan taji, abun da ya shirya fad'a mata shine yana sonta ne saboda muryarta saidai bata bashi wannan damar ba.
Tayi tsaye a kanta, zuciya ta kawo mata wuya ta fizgi remote ta kashe kallon baki daya, ya juyo yana mai tsareta da idanu yace, "Baki ga kallo nike ba." Ta rike kugu tace, "Na gani." Yace, "Kunna min." Kanta tsaye tace, "Fitina nike son muyi don haka bazan kunna ba." Ya mike ya nufo inda take da nufin ya rarrasheta, tayi baya da sauro tana mai fashewa da kuka tace, "Hisham karka tab'ani. Hisham ka amsa tambayoyina." Ta lumfasa sannan tana mai sheshshekar kuka tace, "Hisham miye akan muryata da ya saka ka aureni? Wacece wannan matar da tazo? Wacece Bilkisu? Miye ya faru da Bilkisu? Da gaske ne ta hauka ce." Ganin yayi mata shiru ta fasa k'ara tace, "Hisham a wani bala'in ka sakani."
Ya rungumeta yana bubbuga bayanta yace, "Ki nutsu. Ki nutsu." Ta kai mashi duka a ciki, babu shiri ya saketa ya dafe wajen, a fusace tace, "Kace min in nutsu. Da hankalina zan nutsu bayan abun da naji. Tana maganar ta haukatar da wata tana can ba'a san inda take ba, kuma nima abun da ya faru da ita yana jirana, shine kake cemin in kwantar da hankalina."
Ya nufota, ta dakatar dashi tana mai k'ara jefa mashi tambayoyinta na d'azu. "Waye kai? Mi ya saka aureni? Wacece waccen matar wadda ka kira da Aysha? Mi nayi mata da zafi da har ta saka aljannu suke wasan kura da ni tsayin kwanaki biyar? Shin wacece Bilkisu? Mi ya faru da ita? Tana ina a yanzu?"
Hisham yace, "Zan fad'a maki amma sai na dawo daga Paris."
Hafsat ta fashe da dariyar rainin wayo tana mai tab'a hannuwa tace, "Ba ka isa ba ka bar gidan nan ba har sai ka amsa min tambayoyin da nayi maka." Ya wuceta ya shige ciki, ta bishi har dakinsa, gani tayi yana zuba kaya a akwati, ya gama ya fito harabar gidan ya saka a bayan motarsa, ta zuba mashi tana al'ajabi, bai kyauta mata ba, shima kansa yasan bai kyauta mata ba amma ta tambaya ya kawo mata uzuri akan sai ya dawo daga Paris, a yayinda hankalinta ne yake tangal-tangal a wannan maganar, mi yake nufi da ita? Bilkisu ta hauka ce, ya aureta duk da sanin hakan. Shin ba ya ji a ransa cewa bai kyauta ba idan wani abu ya sameta? Shin ba ya ji a ransa cewa bai kyauta ba? Ganin da gaske tafiyar zaiyi kuma bazai amsa mata ba, tace, "Dukkanin inda zakaje ina zaune zaka dawo ka sanar da ni komai, sannan kasan yadda zakayi dani domi ba zaka tafi ka barni a wannan gidan ba hakanan ta saka aljannu su sauya min KAMANNI."
Ya raba ta gefenta ya shige motata, mamaki yake da yadda a yau da tasan gaskiya yake nuna halin ko in kula a kanta. Ta yarda da cewa bai tab'a sonta ba, muryarta ce yake bibiya, ji tayi hawaye sun zubo mata tana d'aura laifin komai a kanta, saida Jalila tayi mata gargadi akan yanke hukunci cikin fushi, saida Jalila tayi mata gargadi akan aikin gaggawa amma tayi burus da ita ta aureshi ba tareda bincike gashi tun ba'a je ko'ina ba ta fara nadama.
Ta tsaya gaban motar tace, "Babu inda zaka tafi ka barni." Ya leko yace, "Mi kike jira, ki shiga?" Ta bude bangaren mai zaman hakanan ta zauna, yaja motar, tana kallonshi tana ji haushinsa yana kamata akan rufeta da yayi ya aureta bayan yasan abun da zai iya faruwa, tana zaman zamanta ya sakata a cikin bala'i.
Gani tayi ya nufi hanyar gidansu, ta gane nufinta tayi saurin girgiza kai tace, "A'a. Ka kaini wajen Ummana." Yayi banza da ita ya kyale, saida yayi breakfast sannan ya wuce ya barta a wajen Momcy, tun daga wannan ranar bata k'ara razana ba ta dage da addu'a da karatun Alk'ur'ani, barci take hankalinta kwance ta daina gane-gane.
Ranar ta kunna kallo barci ya kwasheta mugun mafarki da tayi ya sakata tashi a firgice, ta fara razana tana ihu, tana zabura, tun daga ranar ta koma kwana dakin Momcy, tana zuba idanu tana kirga kwanakin dawowarsa, sati daya ya wuce har aka shiga sati na biyu bai dawo ba, yana yawan kiranta saidai bata amsawa ta tabbata da muryarta ce take sakashi kiranta.
******
Tunda ta tashi take jin tashin zuciya, tayi wanka ta sauko kasa domin taci abinci, tana sauke idanunta akan shinkafa da miya aka yi, amai ya tafo mata, da gudu ta fad'a bandaki dake parlor ta durkushe tana kwarara amai.
Fatima da Momcy suka biyo bayanta suna mata sannu, ta gama ta wanke bakinta, suka taimaka mata ta mike saboda jiri da takeji, ta zube akan kujera tana maida lumfashi.
Momcy tace, "Mi ya sakaki amai haka?" Hafsat ta ware hannuwa alamar bata sani ba sai kuma tace, "Tana bude abincin naji kamshinsa amai ya tafo min." Momcy ta zuba mata idanu tana nazarinta.
"Mi zan dafa maki?" Fatima ta tambaya. Tayi jim tana tunani sannan tace, "Taliya mai daudawa da ruwanta, ita kadai zan iya ci yanzu." Fatima ta wuce kitchen domin girka mata taliya da daddawa kamar yadda ta buk'ata.
Momcy ta kama hannunta tana dubawa sai kuma ta tale idanunta kamar mai son ganin wani abu, gani tayi murmurshi tace, "Ki gama muje asibiti." Hafsat ta girgiza kai tace, "Momcy babu inda yake min ciwo, Amai ne kawai, shima abincin ne ya janyo min."
Momcy bata bi ta kan maganarta ba, tace, "Ki gama muje."
Fatima ta gama girka mata taliya ta juye a plate ta fito dashi, matsakaicin plate ne ta cikashi har yayi soro amma abun mamaki Hafsat ta tadashi, da mamaki suke kallonta, tace, "Fatima akwai saura?" Fatima ta gyad'a kai tace, "Ehhh akwai saura." Ta amshi plate ta koma ta juye mata sauran, saida ta cinye fiye da rabinsa sannan ta ture plate din, tana maida lumfashi, ta kora da ruwa.
Momcy tace, "Fatima dauko mata dogon hijab muje." Hafsat tace, "Zan dauko da kaina." Momcy ta girgiza kai tace, A'a zata dauko maki." Har mota Fatima ta rakasu tace, "Momcy, anya ba ciki take dashi ba?" Momcy tace, "Nima abun da nike zargi kenan."
Fatima ta daka tsallen murna tace, "Yanzu zan kira yaya in fesa mashi."
Momcy tace, "A'a ki bari mu tabbatar."
Fatima taso ta bisu Momcy ta hana, sakamakon awo da aka yi mata yana fitowa sukaga ciki ne dan sati hudu, Momcy tayi handalah tana mai godewa Allah.
Hafsat ta ware idanu, ta rasa a yanayin da take a ciki, cikin ranta tace, "Sau daya ne fa. Har ciki ya shiga."
Tunda suka tafo Fatima take kira, Momcy ta d'aga kiran tace, "Ciki ne."
Fatima tayi tsallen murna tana mai tsinke kiran ta kira numbar Hisham, yana d'agawa tace, "Aunty Hafsat tana da ciki, d'azu tayi amai, sukaje asibiti."
Daga daya bangaren yace, "Ciki. Alhamdulillah. Allah shine abun godiya. Dole na baki babbar kyauta saboda wannan albishir da kikayi min." A lokacin yana dubai, a take ya sayi ticket ya kamo hanyar Nigeria. Tunda suka dawo take ganin gata da kulawa, mugun cin abinci da ya sameta ne yake matuk'ar bata mamaki.
Washegari tana zaune a balcony ta daga sama ta hango shigowar mota, Hisham ne ya fito, ta tab'e baki ta mik'e ta koma daki tayi kwanta abunta, idan ta tuna abun da ya faru da kuma rufeta da yayi ya aureta ya sakata da bala'i sannan ya nuna mata halin ko in kula sai taji ranta ya b'aci, haushinsa ya kamata.
Mintina biyar a tsakani ya shigo ya zauna gefen gado tare da daura hannunsa akan cikin, ta buge mashu hannu ta mike zaune ta murtuke fuska tace, "Tun da ka gama gudun ka dawo sai ka sanar dani abun da ya faru." Haushi ya kamata tana da tabbaci akan maganar cikin ce ta dawo dashi tace, "Sai ka amsa min tambayoyin da nayi maka a waccen ranar tunda cikinka ya saka ka dawo."
Ya kama hannunta yana murzawa a hankali yace, "Zan amsa maki idan mukaje gidanmu. Allah ya saukeki lafiya." Ta ware idanu tace, "Yaushe mukayi da kai zan koma waccen gida? Kaga Malam ka amsa min tambayoyina tukunna in yanke hukunci akan komawa gidanka ko kuma komawa wajen Ummana, ina da tabbaci akan baka da wata hujja da zaka bani ta saka in tsaya babu mai hankalin da zata zauna da kai bayan abun da taji, bayan yaudara da kayi ka rufe gaskiya." Yace, "Ki sameni a mota," Ya juya ya fita.
Cikin ranta tace, "Dani kake magana kana barin gidan nan zan wuce wajen Umma." Fatima ta leko ta sanar da ita yana jiranta a mota, bata son su fahimci abun da yake faruwa wannan ne ya saka ta zura hijab ta fita.
Fatima tace, "Har na gama maki jalof din shinkafa da daddawa in zubo maki ki wuce dashi." Hafsat ta girgiza kai tana mai zare hijab ta zauna akan kujera tace, "Ki zuba min in ci a nan." Cikin ranta tace, "In ci in ji dadin tada mashi hankali, inji dadin zazzaga mashi jaraba."
Hisham ya gaji da jira ya shigo, ya ware idanu yana kallon tulun abincin da aka ajiye mata, yayi mamakin ganin ta cinyeshi har ta nemi kari, aka karo mata ta cinye.