← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 47

Sashe 8

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tayi jim sai kuma tace, "Alright ina zuwa." Ta wuce ciki tana tafiya yana bin bayanta da kallo yana hadiye yawo.

"Har ya wuce ne?" Umma ta tambaya. Ta girgiza kai, "A'a, yace ne zai shigo ya gaidaki."

Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Kije ki shigo dashi. Amma wannan ledar fa?"

Hafsat tace, "Da ita yazo, akwai sakonki a ciki." Umma tace, "Kuma kika amsa." Tace, "Ya matsa ne shiyasa amma zanyi maki bayani idan ya tafi."

Tana gaba yana biye da ita suka shigo, yana kallon dakunan dake a jere yana yatsine fuska, idan yaga zata juyo sai ya wayance.

Suka shiga dakin, Al'ameen ya zauna akan tabarma yana k'arewa dakin kallo ya gaishe da Umma ta amsa da fara'a, "Ya wajen tsohin?" Yace, "Lafiya lau suke." Yana ji kamar yana zaune a saman allura.

Tace, "Munga abun alheri mun gode, Allah yayi albarka." Yayi murmushi yace, "Babu komai."

Sai kuma ya zaro en dubu daya sabbi dal dami biyu ya ajiye akan tabarmar yace, "Gashi. Zan wuce." Umma ta ware idanu tana kallon kudin tace, "A'a bazan amsa ba, ka dauki kudinka, na gode."

Al'ameen yayi wani shegen murmushi yana tuna maganar da yaji tayi a waya, yace, "A'a." Ya mike ya fita.

Umma tace, "Hafsat ki maida mashi kudin nan bazan amsa ba."

Ta dauki kudin tabi bayanshi har ya shiga mota ta dafa murfin motar tace, "Ga kudin Umma tace ba zata amsa ba." Yayi murmushi yace, "A tunaninki akwai wanda ba ya san kudi." Tace, "Ban gane ba." Ya d'aga mata hannu yana murmurshi yace, "Karki damu, na wuce sai munyi waya." Ya rufe murfin motar ya jata ya wuce ya barta a tsaye tana k'ok'arin had'a ma'ana wa maganar da yayi mata. Tyi jim tana juya maganar da yayi mata sai kuma ta d'aga kafad'a ta juya ta koma ciki.

Umma tace, "Ya kika dawo da kudin?" Ta zauna a gefen gado tareda zare mayafi dake a jikinta tace, "Bai amsa ba."
"Ki ajiyesu a wajenki, idan ya dawo ki mayar masa."

Hafsat ta zazzage leather da ya bata, waya ce babba kirar Samsung tareda iPhone, da turare, a gefe atamfa ne da leshe, Umma tace, "Ki tattarasu ki ajiye, ba zamuyi amfani dasu ba."

Hafsat ta maida kayan a cikin leather ta saka kudin a ciki, ta turasu a karkashin gado, ta fita waje jin ana kiran sallar Magrib, bayan ta gama sallar Isha'i ta dauko handout tana dubawa, kiransa ya shigo wayarta sai a lokacin ta tunda da ya kamata ta kirashi, ta dafe kai, "Gosh. Ya kamata ace na kirashi." Ta amsa kiran ta kanga wayar a kunne.

Daga daya bangaren Al'ameen yana sakin lumfashi tareda sakin gurganin iskanci yace, "Hafsat ki taimaka min ciwon mara zai kasheni." Ta tsorata, idanunta a waje, "Kaje asibiti." Innocent her bata fahimci manufarsa ba, yace, "Please ki taimaka min in rage zafi." Da mamaki tace, "Pardon me, ban gane ba."

Al'ameen yana kukan iskanci kamar wanda yake tarayya yace, "Ki turo min hotunanki in rage zafi, gobe zan shigo in daukeki muje muji dadi, zan aureki, zan baki kudade masu yawan gaske, zan siya maki mota irin wacce nike hawa, zan baki gida babba."

Hafsat ta ware idanu tace, "Subhanallahi!." Daga daya bangaren taji yace, "Angel kina abu kamar wacce bata waye ba." A fusata tace, "Idan har wannan itace wayewa, torh ina rokon Allah da ya kasheni a wacce bata wayewa domin bana buk'atarta a rayuwata."

Yace, "Please ki bani hadin kai zan sakar maki naira kiji dadin rayuwarki, zan siya maku gida babba da motoci na alfarma, kuma zan aureki." Ji tayi hawaye sun zubo mata, tayi shiru tana sauraren kalamansa na yaudara, yana so yayi lalata da ita har yake ikirarin zai aureta daga muryarsa ta fahimci ba akan ya fara ba, maganganunsa karya ne yana fad'a ne domin ya samu abun da yake so, tana da tabbaci akan ba aure bane ya kawoshi ba musamman idan tayi la'akari da maganganu da ya yab'a mata wanda sai a yanzu take fahimci izgili ne da wulakanci.

Jin shiru yace, "Kina jina?"

Tace, "Sai kazo." Ya saki murmushi nasara, "Ki fara tura min hoton."

Hafsat ta rumtse idanu tana iyakar kokarinta domin daidaita fushinta, "Sai kazo." Ta fad'a a takaice ta tsinke kiran, tayi wurgi da takarda (aww nima na koyi hausar can) tayi wurgi da handout din ta kwanta akan tabarma tayi lamo tana share hawaye wasu sabbi suna zubowa.

Umma tace, "Ki tashi kici abinci."

Hafsat ta mik'e zaune hakanan take tura abincin ba domin yayi mata dadi ba, ta wanke hannuwanta tayi alwalla ta kwanta saida ta raba dare sannan ta samu dakyar bacci yayi awon gaba da ita.

**********

Al'ameen ya daka tsalle, "Yeah. Gobe akwai jin dadi." Yana sakin wani shegen murmurshi na nasara, yace, "Hafsat kin fad'a tarkona."

Washegari Hafsat ta tashi da ciwon kai a sanadin kukan da tayi da daddare, wunin ranar bata fita ba.

Da misalin karfe sha biyu na rana tana kwance akan gado tayi lamo tana hawaye, kiranshi ya shigo wayarta batayi picking ba har ya tsinke ta saka numbarshi blacklist, ta mik'e ta zura hijab ta janyo leather da ya bata jiya, kudin da komai suna a ciki, ta hangoshi yana jingine da mota, tunda ta fito yake kallonta yana murmushi har ta k'arasa inda yake, yace, "Hafsat. Muje." Tayi murmurshi takaici tace, "Muje ina?" Yace, "Hotel muji dadi." Tayi dariyar takaici tace, "Are you kidding me? Nayi maka kama da wacce take zuwa hotel ne."

Yace, "Sai muyi a mota." Da alama dukkanin maganarta yana da amsa, tace, "A hotel, a mota, ko a gidanka, a ko'ina ba zaka sameni ba domin ba haka nike ba." Ta nuna kanta tace, "Ni ba er iska bace ba, er mutunci ce, daga gidan mutunci da tarbiyya."

Tayi mashi mugun kallo sannan tace,
"Ka kira kana min maganar banza, well ni ba haka nike ba." Ta dungure mashi leather dake hannunta, "Here abubuwan da ka kawo jiya har da kudadenka, daga yau kada na k'ara ganinka a kofar gidanmu." Yayi dariya yace, "Gidanku ko kuma gidan haya."

Tayi murmurshin takaici tace, "Afuwan, zan gyara, Aminu daga yau kada na k'ara ganinka a kofar wannan gidan da nike haya." Yace, "Idan kuma na kama daki haya fa." Tayi dariya tace, "Mata masu zaman kansu da maza basu samun haya a ciki." Ya tafa hannuwa, "Ita kuma Umma a wani take naga bata da aure ko tana dashi ne." Ji tayi hawaye sun zubo mata, tana mai zubar da hawaye ta nuna mashi kofa, "Aminu ka dauki motarka ka koma inda ka fito ko kuma in tara maka jama'a, suyi maka dukan tsiya."

Ya rike kugu, "I dear you to give it a try, ruwa ba sa'an kwando ba. Idan kudin ne sukayi maki kadan ki fad'i farashinki na biya muje na biya buk'atata na maidoki."

Ta fashe da kuka, "Aminu kaji tsoron Allah." Yace, "Angel kina b'ata min lokaci." Tana mai zubar da hawaye tace, "Well ba haka nike ba, kudinka basu isa su sayi mutuncina ba." Ya gyara tsayuwa yana mai karewa kallo, yana mata kallon kaskanci tace, "Ita kuma tsohuwa fa, naga burinta shine ki auri mai kudi." Tayi mamakin jin wannan furucin, tana tantamar a inda yaji magana, ta juya domin shiga gida taji yace, "Zabi biyu ne ki tsaya muyi cinikin ko kuma inyi cinikin da tsohuwa tunda mayyar kudi ce." Ya fahimci bazai sameta haushin rashin samun abun da yake so ya saka ya tsaya yana datsa mata maganganu. Ta daka mashi tsawa, "Karka kuskura ka kara fad'in magana marar dadi akan ummata domin ban hadata da komai ba..." ya katseta, "Sai kikayi rashin sa'a bata had'a kudi da komai ba. Kwara ki daina b'oye-b'oye ki shiga mota muje inyi in gama, biyanki zanyi."

Ba zata iya jurar maganganun da yake yab'a mata ba, ta juya ta shige gidan da gudu, ta dauki buta ta shiga bandaki, ta takure a bango tana kuka marar sauti, mutanen gidan idan tayi kuka mai sauti ta shiga gulma ana janyo mata bala'i daban-daban.

A rayuwa rahama ne idan kana da dakinka wanda zaka shiga kayi kuka ka wanke fuska ka fito, tana so tayi kuka a cikin salama amma bata da iko domin koda mintina ukku ba tayi ba salme ta fara mita, "Wanene ya shiga bandaki yayi shiru kamar mai naquda, koda sauya fata mutum zaiyi yaci ace yama don haka koma waye ya fito ya wani waje in sauke abun dake damuna a ciki domin kudin haya basufi kudin haya ba." Hafsat ta wanke fuska ta fito tun maganar bata tada bala'i a gidan ba, domin akwai mata da yawa da suke jin haushin juna wata akan mijinki yafi nata samu, wata akan kin fita sutura, wasu kuma en neman fitina ne, ta tabbata kadan suke jira su zauna a kai a fara zubar da habaici, bata shirya zama sanadin fitina ba.

Ta koma daki ta zauna akan kujera tayi shiru kawai tana maida lumfashi, ranta a b'ace yake. Umma wacce bata ga fitarta ba tace, "Miye?" A takaice tace, "Babu komai, ina nazarin karatu ne."
Chapter 8 · 0% Book details