← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 47

Sashe 31

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta fita tareda Aliyu wannan ya saka babu wanda yasan abun da ya faru. A ranar kwana tayi tana kuka, suka rasa gane kanta, wata biyu a tsakani aka d'aura auren Aliyu da cousin dinsa.

Hafsat ta maida hankali akan kasuwancinta da yake cigaba da bunk'asa har ta bude shago ta zuba yara suna kula mata dashi, ta sayi gidan dake a kusa dasu, ta k'ara fad'ad'a gidansu, ta sayi wani gidan a kusa dasu saboda Abbanta, a shekarar da tayi gyaran gidan a shekarar ne ta bud'e plaza da ta gina, ta zuba kayan sakawa, kayan Kitchen, kayan dinki, shagunan dinkin, wajen siyar da kayan dinki, shagon siyar da wayoyi da sauransu.

Arzikinta yana k'ara linkuwa, tana ji da Umma, tana ji da Little Aliyu, dukkanin neman da ta ke yi ta na yi ne sabo dasu, bata so su nemi komai su rasa, ta zame masu gata a rayuwa, ta zame masu bango majingina.

Shekaru sun ja, har matar Aliyu tayi haihuwa biyu, zuwa wannan lokacin ta fara hakura da Aliyu amma har a lokacin babu abun da ya sauya na kaunar da takeyi mashi, har zuwa wannan lokacin sonshi yana manne a cikin zuciyarta, maza suna fitowa neman aurenta saidai yawanci samari ne, ita kuma tafi son ta auri magidanci, Jalila tayi aure wani yaron mai kudi, a sokoto suka hadu saidai shima d'an katsina ne, Little Aliyu ya girma, shekarunsa biyar har ta sakashi a makarantar boko, tana nuna mashi gata sosai, ta dauki kaunar da takeyi wa Aliyu ta mayar a kanshi, dukkanin laifin da zaiyi mata bata dukanshi saidai ta tusashi gaba tana mashi fad'a tana dariya.

Umma ta kan ce, "Hafsat zaki sangarta yaronki ne da kanki." Sai Hafsat tayi murmurshi tace, "Umma bazan dukan Babana ba, mai sunanshi shine gatana a rayuwa. Mutumin da har yau nike matuk'ar so da kauna."

Tunda Little Aliyu ya tashi, Aliyu ya sani, yana kiranshi da Abba, kuma a daukarshi shine mahaifinshi, Aliyu yana nuna mashi kulawa matuk'a amma hakan bai saka ya sangartashi ba, tsoronshi yake sosai, kallo kawai ya isa ya saka ya shiga taitayinsa, wasu lokuttan idan yayi mata laifi saidai ta kira Aliyu tana dariya tana fad'a mashi, idan yace, "Angel ki daina sangartashi." Sai tayi murmurshi tace, "Aliyu ne bazan iya d'aura hannuna a kansa da nufin duka ba saboda mai sunanshi shine gatana a rayuwa."

Tunda ta haifeshi bata tab'a koda dungurinshi ba, ranar ta gama soya miya yace ta zuba mashi shinkafa, tace ya bari ta gama, ya fakaici idonta tana shiga daki ya shiga kitchen ya zuba shinkafa ya zuba miya, ya ci ya koshi ya b'arar da miyar.

Tana dariya take kallon miyar, Umma tayi tagumi tana kallon Ikon Allah, Jalila ce ta shigo tayi turus tana tambaya, "Umma mi ya faru take dariya?"

Umma da ta rasa bakin magana tana kallon ikon Allah, tace, "Aliyu ne ya b'arar mata da miya, b'arnar da gangan amma shine ta tusashi a gaba tana dariya." Ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta fad'a mata.

Kallo daya Jalila tayi mashi ya gudu bayan Hafsat, ta zaroshi daga bayanta ta zaneshi, saida ta saka yaba Hafsat hakuri yace bazai k'ara ba sannan ta rabu dashi, suna shiga daki, tace, "Ke dai Angel banza ce, yaro yayi maki b'arna amma kin tusashi a gaba kina dariya, salon yaji dadin k'arawa gobe."

Hafsat tace, "To ya zanyi dashi? Ni dai ba zan d'aura hannu akan Babana ba saidai inyi mashi fad'a."

Jalila ta harareta tace, "Kada ki rainawa kanki wayo, kina magana kina dariya shine fad'a, idan mutum yana fad'a murtuke fuska yake amma ke sai ki tusa yaro a gaba kina dariya sannan kice fad'a kike mashi. A yaushe kika tab'a ganin anyi haka? Kinga komawa zanyi inda na fito, ban iya zaman kallon wannan kayan haushin." Hafsat ta marairaice fuska tace, "Yi hakuri, k'awata ta kaina."

Jalila ta koma ta zauna tana cewa, "Angel, Mata a gidan Alhaji suleiman." Hafsat tace, "Kin san satinsa biyu a Paris.".Jalila tace, "Alhaji Suleiman shidai yana sonki."

Hafsat tayi murmurshi kawai, ta sani Alhaji Suleiman yana sonta sai dai ita Aliyu take so, kamar Jalila ta san abun da take tunani tace, "Hafsat babu ba zan ce maki ki hakura da Aliyu ba, saboda Aliyu miji da zamuyi maki murna idan kika aureshi, yayi maki sadaukarwa a rayuwa, amma ya kamata ki zauna kiyi tunani na kanki, ki nemawa kanki mafita, idan Aliyun ne ki tashi kiyi yaki a kanshi tunda mahaifinsa yana sonki."

Kafin tayi magana suka jiyo hayaniya daga compound, a tare suka fito, wani magidanci ne tareda mata guda biyu da yara wadanda yawansu zai kai goma sha biyu, Hafsat tayi turus tana kallonsu.

Umma tace, "Haruna." Wannan ta tabbatar mata da abun da take tunani, a yau taga mahaifinta, muryarta tana rawa tace, "Abbana." Ya fashe da kuka yace, "Hafsat ki yafe min, na cuceku, na zalunceku a rayuwa, Hajara ta soni da zuciya daya amma na gudu na barku, dukkanin abun da ya faru daku nine na janyo maku." Hafsat ta girgiza kai tana mai zubar da hawaye tace, "Abba kada kace haka."

Tayi masu gajora zuwa ciki ta tarar da kofar parlour a kulle, ta kira Umma, daga daya bangaren Umma tace, "Ku tsaya a balcony ku gama maganar da zakuyi ki saitasu gidan da kika siya, kika sake haruna ya tako kafarshi cikin falona zakiga b'acin rai ganin idanunki." Tace, "Ayyerh Umma, ki zama mai yafiwa." Umma ta fusata ta inda take shiga bata nan take fita, bata tab'a mata fadan da tayi mata a ranar ba, da sauri Hafsat tace, "Umma kiyi hakuri, za'ayi kamar yadda kika ce."

Umma tace, "Da ya fiye maku, akwai abinci a kitchen domin ni ban gaji rowa irin tashi ba, kiyi magana masu aiki su kai masu, kada su biyo dashi ta falona su bi ta kofar baya." Ta zare wayar daga kunnanta suka zauna a balcony, Abba ya gabatar mata da yaran tareda matan da yake tare dasu, "Hafsat, wadannan matana ne, wadannan kuma k'annanki ne." Hafsat ta gyad'a kai tace, "Okay, Jalila muje in budewa Abbana gidan da na siya mashi, su huta, akwai abinci da Umma tace a basu sai mu wuce masu dashi." Ta koma ciki domin dauko hijab tunda Aliyu ya nuna mata basa son yawo da take da k'aramin mayafi take k'ok'arin gyarawa. Tunawa dashi kawai ya saka ta saki murmushi tana mai jin tsimin sonsa dake a zuciyarta yana k'ara tsiro fure, ita dai tana son Aliyu, addu'arta a kullum shine Allah ya bata Aliyu, idan kuma babu alheri Allah ya mantar da ita Aliyu ya hadata da rabonta saidai a kullum k'ara sonshi take.

"Ina kika barsu?" Umma ta tambaya. Hafsat ta tsaya ta k'arasa falon tace, "Zan saka hijab ne in wuce dasu gidan da na siya mashi." Umma ta tab'e baki tace, "Shi kuma abincin da na ce ki basu fa? Ko kuma nema kike ki mayar da marowaciya kamar yadda ubanki yake, idan mugunta ce kanki kiyi wa, gwara ace ubanki marowaci, uwarki mai hannun kyauta, akan ace dukkaninsu marowata ce." Taji zafin maganar da Umma tayi saidai ba ta ga laifinta ba tunda har Umma ta iya wannan maganar a gabanta wannan yana nuni da cewa abubuwan da yayi mata ba kadan bane. Saidai uba uba ne duk yadda yake ba zaka zo a aibatashi a gabanka shiyasa a kullum yake da kyau mu zab'awa y'ay'anmu uwaye na gari domin guje masu gori, ku duba abun da ya faru da Umma, danginta su koreta saboda taki yarda ta mayar da Hafsat wajen dangin Haruna. Shin mi yasa taki maidata? Saboda babu mutanen arziki a danginsa na kusa wadanda ta sani. Da ace miji na gari ta aura daga dangin kirki ba zataji tsoron barin diyarta a hannunsu ba domin tana da tabbaci akan zata samu tarbiyya, er uwa kada ki bari so ya saka ki auri mutumin banza, auri rayuwa ce da ake zaman mutuwa ce zata raba don haka ki lura.

Hafsat tace, "Ayyerh Umma ba haka nike nufi ba." Umma ta taso mata tace, "Torh miye kike nufi? Kina nufin nima marowaciya ce kamar shi." Hafsat ta lura Umma a wuya take, ta zauna sannan tace, "Naga sun gaji ne shiyasa na ce mu kaisu gidan sai mu wuce masu abincin." Umma ta gyad'a kai kawai tace, "Torh naji." Hafsat ta mike ta wuce sama ta zura hijab.

Abba yana a motarta yayinda sauran suka cika Jeep guda biyu suka kama hanyar gidan wanda babu nisa a tsakani, bango daya ne dasu.

Abba yayi tsaye yana bin gidan da kallo yana kuka yana nadamar abun da yayi a rayuwa, yana nuna tuna wulakanci da aka yi masu a gidan haya wanda ya tilasta masu kwana a titi.

Suka ci abincin da aka tafo masu dashi, Hafsat tana matuk'ar ji da Abbanta, a ranar ta saka aka cika masu store da kayan abinci, ta zuba mashi furniture's a bangarensa, ta zuba wa matanshi da kuma k'annanta suma, ta saka k'annanta a makarantar kudi dake a kusa dasu, ta bud'e katon provision wa Abbanta yana amfani dashi yana hidimar kansa tana son ya ginu da kansa ne domin babu wanda yasan gawar farko, bata fatan mahaifinta ya wulakanta, fatanta shine koda bayan ranta ya fi karfin hidimar gidansa.

Ta zauna da Abba suka sha hira ya bata labarin abun da ya faru tun bayan tafiyarshi har zuwa matan da ya rink'a aura yana saki har zuwa korarshi da aka yi daga gidan haya, yawon da suka yi a titi, suka rink'a kwana a makarantar firamare.

"Hafsat na dade nadamar abun da na aikata saidai kunya ta hanani zuwa gareku amma kina a raina. A kullum kina a raina."

Hafsat ta kwashe dukkanin abun da ya faru da ita ta sanar dashi musamman b'igiren auren Hisham da tayi da kuma wulakanci da ya biyo baya, ta b'oye mashi abun da ya faru a tsakaninta da mahaifiyar Aliyu.

Abba ya fusata yace, "Har yanzu baku san inda yake ba?" Hafsat tace, "Tun daga ranar ban k'ara nemanshi ba, na shafe shafinsa daga rayuwata."
Chapter 31 · 0% Book details