Sashe 28
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SHIN WANI HUKUNCI NE ZATA YANKE? ZATA HAKURA DA RUFETA DA YAYI KO KUMA ZATA NEMI SAKI? SHIN IDAN TA NEMI SAKI ZAI IYA RABUWA DA ITA? SHIN ZAI BARTA TA TAFI DA YARON KO KUMA ZAI AMSHI YARONSA KAMAR YADDA YA FAD'A? SHIN INA LABARIN BILKISU?
MUJE ZUWA
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 13
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Momcy ta kawo karshen shirun da ya wanzu a falon, ta hade hannuwa a waje guda alamar roko sannan tace, "Hafsat na rokeki da girman Allah kiyi hakuri karki tsinke auren nan, ki tsaya ki kula da yaronki, Ina mai baku hakuri a madadinshi da ni kaina."
Hafsat tayi jim sannan tace, "To shikenan." Suka zuba mata idanu suna neman karin bayani, Hisham ya kasa hakuri yace, "Hafsat ina buk'atar karin bayani. Bamu fahimceki ba."
Hafsat ta mike tare da mashi wani mugun kallo tace, "Idan na yanke shawarar rabuwa da kai, mika hannu zanyi ka bani takardata tunda ba tsoronka ni ke ji ba. Baba, Umma, Momcy, Allah ya kiyaye hanya. Momcy don Allah ku ara min Abdullahi yayi min hutu a nan." Momcy tace, "Fatima zata kawoshi." Hafsat tayi godiya ta mike ta wuce saman.
Momcy tana komawa gida, ta turo Fatima ta kawo Abdullahi.
Hafsat ta shiga kitchen ta had'a masu abincin rana, ta soya waina, ta girka miya, ta jera komai a dinning table, ta zubawa Abdullahi sannan ta zubawa kanta, suna ci ya sauko yaja kujera ya zauna yana kallonta yace, "Angel ina nawa?" Ba tareda ta kalleshi ba tace, "Ka tab'a cin abun da na girka ne, da kanka kake girkawa, gaka ga kitchen." Ta k'arasa magana tana nuna mashi kofar kitchen, Hisham ya bude warmer yace, "Duk da ba dani kika girka ba, akwai saura sai inci." Abdullahi ya washe baki yace, "Abba muci tare." Hisham yace, "Kaci naka, nima zan zubawa kaina."
Yana ci yana lumshe idanu saboda dadi, dadi ya wuce shi, yana nadamar girkinta da bai ci ba, suka gama ta tattara kayan da suka b'ata ta wuce dasu kitchen ta wanke, zama suke babu yabo babu fallasa, bata mashi magana, bata fara'a idan yana kusa, ya bata hakuri har ya gaji amma a banza, bata bashi abincinta, saidai ya zuba da kanshi yaci, kib'ar da tayi har tsoro take bata, tayi muni, har bata son kallon kanta a madubi, ta fara ragewa, da gangan take barin kanta da yunwa sannan tana motsa jiki, ta dawo kamar yadda take kafin aurensu, kullum cikin kwalliya take, yayi ta binta da kallo, tana lura dashi.
Ranar ya fito ya sameta ta cakare ta kure kyawu, kayan sun matseta komai ya bayyana, ya kasa hakuri yayi sama da ita ya ya wuce master room ya rufa a kanta yana murzata tun tana tureshi har tayi lamo ta bada kai. Daga ranar suka daidaita kansu, soyayya suke babu kama hannun yaro, a kullum suna manne da juna, Abdullahi ya dawo da zama a wajen Hafsat, ta had'ashi da Muhammad ta rike, bata nuna banbanci a tsakaninsu.
*******
A tare suka fito a jere, yana mata magana tana murmushi ta mik'a mashi briefcase ya amsa tare da sumbatar kumatunta, tana tsaye tana d'aga mashi hannu saida taga wucewar motarshi sannan ta juya ta koma ciki.
Karfe hudu da rabi ya danno motarsa a cikin gidan, ta fito da murnarta domin ta tarbarshi, tayi turus hango wata mata kamar mahaukaciya ta shigo gidan, tana goye da yaro, tayi baya da sauri, Hisham ya tarota tareda juyawa domin ganin abun da ya tsoratar da ita, ya zaro idanu yana fad'in, "Bilkisu."
Ya saketa saidai jinta tayi a kasa, ta buge kugu, Bilkisu ta sulale a kasa, ya dagota yana kiran sunanta. "Bilkisu. Nanerh. Ki farka mai gadon zinare."
Hafsat ta mike tsaye yayinda gabanta ya yanke ya fad'i.
Hisham ya dauki Bilkisu ya saka a gidan baya sannan ya dauki yaron ya kwantar a bangaren mai zaman hakanan, kai tsaye ya wuce asibiti.
Hafsat ta kira Momcy ta sanar da ita bayyanar Bilkisu sannan ta shirya yaran tabi bayanshi asibiti, suna a can dangin Bilkisu suka zo suna ta kuka.
Da Daddare Umma tazo, Bilkisu tana jin jiki, Hisham ne yake jinyarta, a kullum yana manne da ita, a kullum Hafsat ce take girki ta kai masu, na safe, na rana, da na dare, kullum tana akan hanyar asibitin, ranar suna zaune, wasu mata biyu suka shigo, Ummin Bilkisu tace, "Sadiya ce, makociyarmu, wannan kuma kishiyarta ce."
Da sauri Bilkisu tace, "Kishiya." Yayinda jikinta ya fara rawa, ta soma girgiza, jikinta ya rikice, dakyar likitoci suka samu nasarar ceto ranta, likita ya gargadesu akan maganar kishiya a gabanta, tana da trauma na kishiyar idan suka cigaba zasu iya rasata.
A lokacin da Hafsat taji labari saida gabanta ya yanke ya fad'i, haka take wuni jikinta sukuku, ta rasa dalili.
*****
Hafsat tana zaune a gefen gado tana rike da Muhammad, Hisham ya shigo ya zauna a kusa da ita yace, "Gobe za'a sallameta." Tace, "Allah ya kaimu."
Saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ina mai baki hakuri akan abun da zan sanar dake, Hafsat dole in rabu dake, matata tana da trauma na Kishiya, kalmar kishiya kawai idan taji tana yi kamar zata mutu ballantana kuma ace tana da ita. Dukkanin abun da ya faru da Bilkisu nine na janyo mata, nine sanadi."
Hafsat ta tsareshi da idanu tace, "Ni kuma dukkanin abun da ya faru dani kwadayi ne ya janyo min, ni ce na janyo wa kaina."
Da sauri yace, "Ba haka nike nufi ba." Ta katseshi, "Torh mi kake nufi Hisham?" Yayi shiru, da karfi tace, "Tambayarka nike." Muhammad ya fara kuka ta mike tana rarrashinsa.
Ba tareda ya had'a idanu da ita ba yace, "Hafsat kiyi hakuri, na sakeki saki daya. Dukkanin abubuwan da na baki har da gidan da Umma take ciki, na bar maki. Ina maki fatan alheri a rayuwa."
Ta durkushe a kasa tareda fashewa da kuka, ta rasa abun da yake mata dadi, tayi hakurin zama dashi despite abun da yayi mata amma a yau shine yayi mata butulci ta hanyar sakinta. Tana sheshshekar kuka tace, "Hisham ka cuce ni. Ka tarwatsa min rayuwa. Kudinka ba na so, gidanka bana so, bana son komai da ya fito daga gareka. Yadda na shigo gidanka ni kadai, hakanan zan fita ni kadai, kayan da suke a jikina zan ajiye maka a wancen gidan."
Ta juya ya kamota tareda amsar Muhammad dake hannunta, da mamaki take kallonshi, ta fasa ihu tace, "Baka isa ba, baka isa ka rabani dashi ba."
Hisham yace, "Angel kiyi hakuri amma bazan raba kan y'ay'ana ba." Hannu daya ya saka ya fitar da ita waje, ta share hawayen dake a fuskarta tana mai kiran sunansa, "Hisham." Ya juyo tace, "Ka sani Allah ba ya zalunci, na yarda na zauna da kai bayan yaudarata da kayi amma sai ka zab'i kayi min butulci, dukkanin abubuwan da kakeyi min na tabbatar domin kana ganin bani da gata ne. Ina mai tuna maka Allah ba ya zalunci, alhakina bazai barka ba, akwai ranar kin dillanci wacce itace ranar da ka gurfana a gabana saidai bakin alkalami ya riga ya bushe, ka tab'a rawarka da tsalle, koda maza na duniya sun k'are, koda kaine autan maza bazan tab'a komawa gidanka ba, a dukkanin lokacin da alhakina ya juyo kanka ka tuna da wannan maganar, ka tuna da cewa nace koda kaine kadai namiji da ya rage a duniya bazan koma gidanka ba, ka tuna da cewa da nayi koda kaine autan maza bazan koma gidanka domin ina da zuciya, domin nasan mutuncin kaina." Ya juyo ya kalleta sai kuma ya maida kofa ya rufe, tayi ihu da hargowa amma a banza, ATM dinta wanda take dashi tun kafin aurenta, kudadenta da take ajiyewa a lokacin da kuma wadanda ta samu na haihuwar da tayi ne kawai a ciki, shi kadai ta dauka ta dauki wayarta ta fita, ta hau mota ta wuce gidan Umma, Umma tana zaune a parlour, Hafsat ta shiga ta durkushe tareda fashewa da kuka tace, "Umma, Hisham yayi mamu butulci. Umma, Hisham ya yaudaremu, duk da na zab'i na zauna dashi a wancen lokacin amma a yau ya zab'i da ya sakeni sannan ya amshi Muhammad."
Umma ta dafe kirji idanunta a waje tace, "Mi ya faru?"
Hafsat tana sheshshekar kuka tace, "Saboda matarshi tana tsoron kishiya, sunan kawai yana sakawa ta kusa mutuwa."
Umma ta fusata ranta ya b'aci tace, "Ki tashi muje gidansu, bai isa ba."
Hafsat ta girgiza kai tace, "Umma ki rabu dashi, yana ganin bani da gata ne shiyasa yayi min haka."
A fusace Umma tace, "Waye yace mashi baki da gata? Ki mik'o min waya in kira Aliyu muga da uwar da yake takama da har zakisha wahalar nakuda sannan ya amshe yaron bayan mune aka cuta, muka hakura amma shine ya zab'i yayi mamu sakayya da butulci."
Hafsat tace, "Umma ki rabu dashi, akwai lokaci, a duk lokacin da na waiwayi yarona ba zaiji da dadi ba, dukkanin fitinar da za'ayi sai ya bani shi tunda ba tare dashi nayi nakuda ba."
Umma tace, "Ki zauna kici abinci."
Hafsat ta ware idanu tace, "Abinci? Ai dukkanin wani abu na Hisham bana so, dukkanin abun da ya mallaka min na mayar mashi da abunsa, zan tashi in nema, zan jajirce na nemi gumina, in gina kaina, sai na nuna mashi na fi karfin wulakanci."