← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 47

Sashe 32

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba yace, "Aliyu fa? Mutane zasuyi mashi kallon marar uba, kuma a kwana a tashi wata rana shi da kansa zai so sanin waye ubansa, a kwana a tashi rana zata zo da zai fahimci ba Aliyu bane mahaifinsa, a lokacin sai kice dashi mi."

Hafsat tace, "Ni ce Mamarshi, Ni ce Babanshi."

"Mi yasa kika saka ake kiranshi da Aliyu Aliyu?" Abba ya tambaya. Tace, "Saboda babu abun da Hisham ya sani na daga wahala dashi. Aliyu shine ya tsaya mamu, ya taimakeni a lokacin, shine ya zama gatana."

Abba yayi jim sannan yace, "Ki shirya gobe zan kaiki wajen dangina, daga nan zamu wuce wajen dangin mahaifiyarki in basu hakuri nine sanadin lalacewar zumunci da tsakanin Hajara da danginta."

Washegari ya kaita wajen danginsa, sunyi matuk'ar farin ciki da ganinsa, suna ta haba-haba da ita, dangi masu dadi, daga nan suka wuce wajen dangin mahaifiyarta a babban gidansu na gandu inda kakanninta suke zaune, Abba da kanshi ya basu hakuri akan abun da ya faru, suma sunyi nadamar abun da sukeyi, suna ta neman Umma saidai basu san inda take ba, sunyi matuk'ar farin ciki da ganinta, a can Hafsat ta kwana. Washegari ta koma ta dauko Umma suka koma tare.

Tun daga wannan ranar gidanta ba ya rabo da mutane, danginta suna akan hanya, musamman cousin dinta na bangaren Abba, tana yi tana tsawatarwa saboda wasu daga cikinsu basa ji ko kadan, sun so mayar da gidanta dandalin tara samarinsu ta tsawatar sai a lokacin ta k'ara fahimtar da dalilin da ya saka Umma taki maidata wajensu a lokacin da danginta suka ki karbarta.

Umma da Hafsat suna zaune, Hafsat tace, "Umma. Ina son muyi magana saidai ban san yadda zaki dauki maganata ba." Umma tace, "Akan miye?" Saida Hafsat tayi jim sannan tace, "Akan Abba ne."

Umma ta murtuke fuska sannan tace, "Akul, karki kuskura kiyi min maganarshi, mahaifinki ne don haka ba zan hanaki mu'amala dashi ba amma ni bani da wata dangantaka da shi. Karki kuskure koda wasa kice zakiyi min maganarsa ko kuma ki dangantani da shi. Nayi nadamar auren Haruna da nayi, shiyasa ake son ka zab'awa y'ay'anka uba na gari. Kina ganin halayen da y'ay'an en uwansa suke a gidan nan, koda ba'a fada ba nasan ban yi maki adalci ba. Har gobe har jibi danginki ne kuma ni na janyo maki idan aka goranta maki a kansu."

*****

Hafsat tana wa Aliyu shirin makaranta yana rigima har ya makara, sukayi wa Umma sallama, ta bud'e mashi daya bangaren ya shiga sannan ta zagaya bangaren direba, sanye take dakekken leshe dan ubansu anyi mata doguwar riga bubu, ta zura takalma half cover, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, ta d'aura mayafi akan kafad'a tana zuba kamshi.

Sunyi nisa motar ta tsaya, ta daki starry tace, "No." Tana duba lokaci. Ta jingina da motar tana tunanin yadda za ta yi, Little Aliyu ya fara kuka za'ayi mashi bulala idan ya makara.

Tun daga nesa Ashraim ya hangota har ya gotata ya dawo da baya, yayi kasa da gilashin motarsa yace, "Angel." Ta zaro idanu tana kallonsa da namaki jin ya kira sunanta saidai ba ta ce komai ba, yayi mamakin ganinta rabonshi da ita tun lokacin da aka sanar dashi tayi aure. "Motar ta tsaya ne?" Ya tambaya. Ta gyad'a kai tace, "Eh, kuma Babana ya makara." Ji tayi yace, "Mu je in sauke ki." Tayi jim sai kuma ta nuna mashi motarta, yace, "Za'a kawo maki ita har gida." Tayi jim tana shawarar ta shiga ko kuma ta tsaya, ganin bata da wani zab'i da ya wuce ta bishi la'akari da lokaci ya kure, ta bude mazaunin baya ta saka Little Aliyu sannan ta zauna a bangaren mai zaman hakanan, ta fad'a mashi sunan makarantar.

Ashraim yace, "Abokina miye sunanka?" Little Aliyu yace, "Aliyu Aliyu... Are you my father? Shin kaine babana?" Ashraim yayi mamakin tambayar da yaron yayi mashi, ya ware idanu yana kallonta tunda tayi aure ya dakatar da bibiyar rayuwarta da yake.

Little Aliyu ya dora da cewa, "Wata mata tace Abba ba shine babana ba. Ammi waye Babana? Dama akwai wadanda basu da Baba."

Hafsat ta daka mashi tsawa tace, "Kayi min shiru a nan tun baka sha mari ba."

Little Aliyu yayi shiru tunda take dashi ranar ne ta fara d'aga murya a kanshi har tana barazanar zata dokeshi.
Yayi parking a harabar makarantar ta fito tareda b'alle murfin baya, Little Aliyu ya fito yana mata rigima ta kaishi har class kada Aunty ta dokeshi.

Ta rakashi har class, tayi mamaki dawowa da ta tarar da motar, ta lek'a tace, "Ba sai na wahalar da kai ba, zan tari kekenapep. Na gode." Ya girgiza kai yace, "Mu je har na kira mai gyara min mota, yana akan hanya."

Tayi jim sannan ta b'alle murfin motar ta shiga, ya koma dasu inda motarta ta tsaya, suka tarar da mai gyara, ta bashi makullin motar ya bashi, tana zaune a mota har ya gama gyaran, Ashraim ya maido mata makullin motarta. "Nawa ne kudin?" Ta tambaya. Ashraim yace, "Na biya." Tayi mashi godiya tana k'ok'arin fita daga motar sai kuma ta dakata tace, "D'azu ka kirani da Angel, sunan da ba kowa ya ke kira na da shi ba. Shin mun san juna ne?"

Ashraim ya sakar mata murmushi sannan yace, "Sunana Ashraim Hamid. Na soki tun kafin ki yi aure sai dai ban furta maki ba sannan ban tunkareki ba, a lokacin da na shirya bayyana kaina a gareki a ranar ne aka daura maki aure, tun daga ranar ban k'ara bibiyarki ba sai yau na ganki. Yaronki Aliyu, babanshi ya rasu ne?" Magana ce wacce bata son yi don haka tace, "A'a, karka damu." Ya zaro card dinsa ya mik'a mata yace, "Please ki kirani." Ta amsa tareda fita daga motar ta b'alle murfin motarta ta shiga tayi mata key ta wuce, saida yaga tafiyarta sannan yaja motarsa ya wuce.

Wunin ranar ta b'ata shi ne tana tuna maganar da Little Aliyu yayi mata; Shin wacece ta sanar dashi haka? Tun yaushe? Garin ya? Ba ta da wanda zai ba ta amsa.

*******

Kai tsaye Ashraim ya wuce kamfaninsa, ya hau elevator zuwa ofishinsa dake a hawa na karshe ofishin CEO, ya zauna tareda kiran numbar Habib yana sanar dashi ganin Hafsat da yayi. "Buddy yau naga Angel?" Daga daya bangaren Habib yace, "Angel kuma?"

Ashraim yace, "Eh, Hafsat, Angel. Dazu na ganta motarta ta b'aci akan hanya, har da yaro take dashi, amma akwai abun da na ji wanda ban gane ina. Ina son kayi min bincikie, ina son sanin abun da ya faru da ita a tsayin wadannan shekaru."

Habib yace, "An gama ranka ya dade." Ashraim yayi dariya yace, "Yauwa ranka ya dade." A tare sukayi dariya. Yace, "Wait... Waye wanda ta aura a lokacin?"

Habib yace, "Hisham Mahmoud."

Ashraim yace, "Hisham Mahmoud, kamar ya dawo Nigeria bayan shekaru shidda da yayi a kasar. Komai kenan ka kirani."
(Ku zo ku tayani dubawa; Ga Aliyu, Ga Ashraim, Ga kuma Hisham wanda ya dawo Nigeria, shin miye zai faru a lokacin da Hisham yayi tozali da Little Aliyu?).

Tun da ta dawo ta ajiye jikkarta ba ta k'ara tunawa ba, tana da jikkuna da yawa shiyasa yake daukarta lokaci kafin ta maimaita, wata rana tana duba abu a jikkar ta ci karo da katin, tayi jim tana son tunawa, ta ware idanu tare da dafe kai, ta copy numbar tare da kira.

Tana sallama ya gane muryarta, kamar mai rad'a yace, "Angel."

Kunya ce ta kamata tace, "Na ajiye jikkar kuma yana a ciki, ban tuna ba sai yau ina neman abu a ciki naci karo dashi." Daga daya bangaren yace, "Na ji dadi da kika kira. Ya Aliyu? Ya Umma da Abba?"

"Lafiya lau."

Ji tayi yace, "Ranar na je school dinsu." Tayi mamaki domin Little bai sanar da ita, tace, "Bai fad'a min ba."

Yace, "Inzo?" Tayi jim tana juya maganar da yayi, ta yarda da wani abu kowane namiji da salonsa, tace, "Sai ka zo."

Washegari da marece ya kirata akan yana akan hanya, ta mike ta shiga wanka ta jima tana durje jikinta da sabulai masu kamshi sannan ta sakarwa kanta shower, ta fito ta cancara makeup tare da shiryawa cikin expensive atamfa dinkin riga da zani, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiya, simple kwalliya ce akan fuskarta, ta zuba gold wuya da hannu, da piecer a hancinta, ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, ta zura takalma half cover ta fita bayan da ta amsa kiransa ya sanar da ita yana a compound, ta saukeshi a parlour da take sauke bakinta, aka ajiye mashi snacks da drinks.

Ta kasa jure kallon da yake mata har saida tayi da kanta, tace, "Barka da zuwa. Na gode da taimakon da kayi min a wannan ranar." Ya gyad'a kai yace, "Da fatan kin san abun da yake tafe da ni." Cikon ranta tace, "Ikon Allah." Amma a zahiri sai tayi rolling idanu tace, "Ina jinka." Ya ce, "Gorgeous. Kinyi matuk'ar kyau."

Abun da ya tashi kanta a kansa shine yadda yake karin hularsa a kaikace samfurin da zata iya kira da ture kaga tsiya. Ya tsura mata idanu the more yake kallonta the more take k'ara mashi kyau, sai yake ganin ta fi da kyau a yanzu, saida ya lumfasa sannan yace, "Hafsat a shekarun baya nayi zurfin ciki wanda ya saka na rasaki, kuskure ne da nayi nadamar aikatashi, ba zan maimaita wannan kuskuren ba a yanzu. Hafsat ina matuk'ar sonki a shekarun baya da kuma yanzu. Ina da mata daya da yaro daya." Ya lumfasa sannan yace, "Da fatan ban yi maki tsufa ba?" Tayi murmurshi ba tareda tace komai ba, yace, "Samarinki nawa?" Ta ware idanu, ya gyad'a kai yace, "Mace mai kyau kamarki ba za'a rabata da samari ba, tun da wuri in san aikin da yake a gabana, kada in zauna bacci wani yayi min kafa, a yi min wuff da ke." Dariya ya bata tana k'are fuskarta tana dariya.
Chapter 32 · 0% Book details