Sashe 12
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Naja'atu ta k'araso wajen motar da murmurshi akan fuskarta tace, "Yaa Hisham." Ya mayar mata da martanin murmurshi yace, "Naja'atu, ga matata ko ince wacce zan aura Hafsat, Angel."
Naja'atu tayi mata murmurshi tace, "Sannu Angel." Hafsat ta mayar mata da murmurshin tace, "Yauwa." Ya dubeta yace, "Kije da ita idan kuka gama zan dawo in daukesu." Naja'atu tace, "Okay, Angel muje."
Naja'atu, Hafsat da Jalila suka wuce ciki yayinda Hisham yaja mota ya wuce office, bayan hour biyu Naja'atu ta kirashi ya koma, tun da suka fito yake kallon Hafsat yana mamakin matuk'ar kyawu da take dashi, mai kyau ne matuk'a, kyakykyawa ta karshe, farar mace sol har yellow fatarta take saboda haske, tana sanye da leshe dinkin rigar half boubou da straight skirt, da sarkar hanci akan hancinta, ta murza dauri da yayi suiting shigarta, tana rike da poss, mayafi akan kafad'a, tana tafiya da rashin sabo da mayafi da bata saba sakawa ba.
Idanuwansa a kanta ya saki murmurshi yace, "Naja'atu aikin yayi kyau."
Naja'atu ta murmusa tace, "Naga alert na gode, Allah ya k'ara budi."
Ta bude daya bangaren Hafsat ta shiga yayinda Jalila ta zauna a baya.
Kai tsaye ya wuce dasu katon shopping mall wanda yake mallakinsa ne, tun a waje take mamakin girman wajen, lokacin da suka shiga ta zuba idanu tana mamaki a ranta, yayinda ysoro ya kamata, Anya bata dauko ruwan dafa kanta ba? Anya bata kai kanta inda ya fi karfinta ba? Hausa suka ce idan akwai kwadayi akwai wulakanci, bata da kwadayi saidai ta gujewa kanta wulakanci da zai iya biyo baya akan zab'in da tayi.
Dukkanin inda suka gitta employee ne suke kwasar gaisuwa saidai ya d'aga masu hannu kawai. Ya juyawa Jalila yace, "Kawarmu ki zagaya ki dauki dukkanin abun da kike so, zan taya Angel."
Ta gane nufinsa ta gyad'a kai kawai, har zata zauna sai kuma tayi wani tunanin ta juya ta wuce bangaren turaruka.
Hafsat da Hisham suka jera, ta nuna mashi pointing trolley, yace, "Babu buk'ata dukkanin abun da kike so ki nunashi kawai."
Tana yawan kamashi yana kallonta saidai tayi murmurshi, ta sani ita mai kyau ce kuma tayi matuk'ar kyau a yau, suna zagaya tana pointing dukkanin abun da yayi mata wanda ya had'a da sutura, takalma, jewelry, jikuna, mayuka, mayafai, dogayen riguna, turaruka da sauransu.
A wajen turaruka suka hadu da Jalila, suka wuce inda ake biyan kudi ya mik'a card dinsa aka zare kudin suka fito aka biyosu da manya-manyan ledoji da suke dauke da tambarin shopping mall din, saida ya fara sauke Jalila sannan ya wuce da ita gida, ya saka yara suka shigar mata da ledojin, da mamaki akan fuskarta take kallon ledojin, ido ba mudu bane duk da nuni kawai takeyi amma tana da tabbaci akan kayan sunfi karfin shopping da tayi.
Ta dubeshi tace, "Babban mutum amma siyayya da nayi bai kai wadannan kayan ba, kaya kamar wacce zata bude shago." Saida ya murmusa sannan yace, "Girmanki ne, beside tun jiya na fara maki shopping ke kuma kika k'arasa a yau. Ki gaida Ummi. Zan shigo gobe inyi saukeki school."
Ta girgiza kai, "A'a zan bi school bus ba sai ka wahalar da kanka." Ta fad'i hakane domin gujewa kanta cin bashi da bata da kudin da zata biya. Bata san abun da zai faru a gaba ba, ya tsura mata idanu, kwarjini yayi mata tayi kasa da kanta yace, "Matar Hisham a motar Hisham zataje school."
Kafin tayi magana Rahama makotansu tazo wucewa har ta gittasu gulma ta dawo da ita, tana kallonsa tace, "Angel." Hafsat ta dubeta tace, "Rahama." Rahama tace, "Kece da Umar."
Rahama tasan ba Umar bane itama Hafsat tasan Rahama tasan ba Umar bane, gulma ce da neman fad'a domin ta kora mata saurayi. Tayi wani shegen murmurshi sannan tace, "Umar ay talaka ne ni kuma daga ganina babu tambaya matar masu kudi ce. Rahama ki duba da kyau, wannnan mai kudin da zan aura ne, koda ganina baki buk'atar ki tambaya domin kallo daya zakiyi min ki gane cewa ban yi kama da matar talaka ba."
Rahama tace, "Eh hakane." Hafsat ta murtuke fuska tace, "Tunda kinyi gulmar da ta kawoki sai kiyi gaba, Allah ya raka taki gona, kina fama da kanki amma baki daina gulma da neman fitina ba."
Rahama zatayi jaraba ta lura da bodyguard dinsa dake a gefe, ta juya da sauri ta wuce har tana tuntub'e.
Hisham yace, "Mi yasa kikayi mata haka?" Tace, "Tana magana ne akan tsohon saurayina wanda d'an unguwar nan ne, mutumin da suka tashi a tare zata ce ta manta kamanninsa, gulma ce ta ciyota shine tazo tana min maganarshi tana nuna tayi zaton kaine. Hisham na yarda da aurenka ne saboda kana da kudi domin burin ummana shine in auri mai kudi domin bata son in maimaita kuskuren da tayi a rayuwa."
Hisham yace, "Amma Hafsat bakya ganin ya kamata kin san dalilin da ya saka nike son aurenki." Ta girgiza kai tace, "Bani da buk'atar sani, na wuce, sai munyi waya." Yana tsaye har saida yaga shigarta gidan sannan ya shiga mota.
Washegari har ta manta da ya fad'a mata zaizo ya kaita school, tayi turus ganin motarshi a gefen gidansu, fuskarta dauke da mamaki take kallonshi, bata yi tunanin zaizo ba, kasancewar tace mashi sha biyu take da lectures saida asuba da ta duba sannan taga ashe takwas ne, ta dauka laraba ashe alhamis ne.
Hisham ya bude bangaren direba ya fito yana jefarta da murmurshi, suit gray color ne a jikinsa, sumar kanshi tana a kwance tayi lub, yana baza kamshi mai sanyi, ya zuba mata idanu a kullum idan ya d'aura idanunsa a kanta sai yaga ta k'ara mashi kyau, yana matuk'ar mamaki akan kyawu da take dashi.
Tana sanye da abaya ta yane kanta da mayafi, fuskarta dauke da simple makeup, handbag dake a hannunta da kuma flat shoes dake a kafarta brown ne, ta zuba gold wuya da hannu, har ta k'arasa inda yake ta tsaya gefenshi bai ya lura ba, tayi tapping hannunta a kusa da fuskarsa yayi firgigit, dariya ya bata, tana k'are fuskarta tana dariya.
Ta bude bangaren mai zaman hakanan ta shiga, yana tuki a nutse yace, "Miye labari. Ki bani labari."
The more yake tare da ita, the more yake son yaji muryarta domin tana tuna mashi da Bilkisu, mai gadon zinarinsa.
Tace, "Babu wani labari. Na dauka ba zaka zo ba, nayi mamakin ganinka, ashe takwas ne, nace maka sha biyu." Yace, "Serious students, tsakiyar semester amma kina manta timetable, na dauka farkon semester ake manta timetable, tsakiya da karshe an riketa a saman kai."
Tayi rolling idanu tace, "Yaushe mukayi da kai nace ni serious students ce."
Sai kuma tayi shiru, yana son cigaba da sauraren muryarta, ko rabin tafiyar ba suyi ba, da gangan yake tafiya speed kadan, bashi da topic da zai kawo da zai saka ta cigaba da magana.
Yace, "Zan koya maki mota." Ba tareda ta d'ago ba tace, "Na hutar da kai, Yaa Aliyu ya koya min."
Hisham ya ware idanu da mamaki kwance akan fuskarsa yace, "Waye Yaa Aliyu?" Yana son yasan waye Aliyu a lokaci guda yana farin ciki da ya samu hirar da zaiji muryarta.
Ta maida dubanta a kanshi sannan tace, "Gidan da Ummana take aiki, babban yaron matar gidan ta biyu, muna mutunci sosai kamar wasa yace zai koya min mota, kuma ya koya min."
Yace, "Ya hutar dake na fara tunanin kaiki makarantar koyon mota, ashe har kin kware daga nan har legas."
Dariya ya bata ta girgiza kai, "A'a daga nan har batagarawa dai." Yana son hirar tayi tsayi amma sai yaga tayi shiru.
Tana duba note da ta dauki hoto a wayarta, ji tayi yace, "Idan na dawo daukarki zan shigo maki da wayarki da system." Ba tareda ta d'ago ba tace, "Na gode. Allah ya k'ara budi." Yace, "Amin."
Shiru ya ratsa wajen, ji tayi yace,
"Miye sunan littafin da kika ce min kin siya jiya?"
Hafsat ta mayar da wayarta a handbag, bata son yaga kamar bata kyautawa, idan ta shiga makaranta ta duba kafin su fara lectures, tace, "Sunanshi Matar Aliyu labarin soyayyar Fatimazahra da Aliyunta, ka san kuwa kuwa tun marubuciyar tana amfani da pen name Hafsat Hisham nike bibiyar rubutunta har zuwa yanzu da take amfani da ainihin sunanta Aysher Angel."
Yace, "Ina kallon films da series, ina karanta English Novel amma ban tab'a karanta na hausa ba." Tace, "Ka karanta kaga yadda za'a tashi kanka kakai karfe biyun dare a zaune kana karatu saboda suspense. Amma ko na yaki tunda naga maza sunfi karanta littafin yaki." Ya girgiza kai, shiru ne ya ratsa a tsakani, ya girgiza kai yace, "Not again." Jin kamar yayi magana tace, "Kace?"
Yace, "Kina min rowar littafin ne, ki karanta min inji yadda yake, watakila ya dauki hankalina idan mukayi aure ki rink'a karanta min."
Ta bude jikkarta tare da zaro waya tace, "Mu fara da shafukan kyauta tukunna."
Da muryarta mai sanyi da dadi ta fara karanta mashi littafin wanda yaja hankalinsa sosai, yayi dariya har da kwolla na diramar Fatima da Aliyu. Ya gyad'a kai yana mai jin dadin muryarta wacce take tuna mashi da Bilkisu matarshi.
Yana parking a faculty dinsu, ya fito ya bude bangaren da take ta fito, ya bude gidan baya ya zaro leather ya mik'a mata yace, "Breakfast dinki."
Ta dubeshi da mamaki tace,
"Saidai nayi breakfast."