Sashe 35
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ashraim ya murmusa sannan yace, "Inzo a motata?" Hafsat tace, "Ehhh."
Yace, "Wacce? Ki zab'a min." Saida tayi rolling idanu sannan tace, "Idan na tuna zan fad'a maka."
Yace, "Ina son ganinki. Inyi maki video call?" Saida ta kalli kanta sannan tace, "Babu damuwa."
Ya tsinke kiran tareda mata video call, yana zaune a ofishinsa tana mashi shagwab'a yana biye mata, Little Aliyu ne ya shigo yana kama hannunta yace, "Ki zo in ji Abba ya rama min tsawar da kikayi min." Tayi dariya tace, "Ina zuwa Babana yana kira."
Ashraim yace, "Okay. Ki bani Little." Ta mik'awa Little Aliyu wayar sannan ta wuce harabar gidan wajen Aliyu, yana ganinta ya juya baya yace, "Mun b'ata." Tace, "Tuba nike, kaina a kasa."
Aliyu ya juyo yace, "Torh a daina wa Little tsawa." Tayi dariya tace, "Na daina."
Aliyu ya tsura mata idanu, ta k'are fuskarta tana dariya, yace, "Kin ji dadi abunki. Da kyawunki kike koda ba ki yi kwalliya ba. Ba kwalliya bace ta ke yi maki kyau, kece ki ke yi kwalliya kyau." Yana mata video tana k'are fuskarta yana dariya har Ashraim ya gaji ya tsinke kiran bayan da Little ya bungire bacci, saida ta koma sannan ta tuna tana kira ba ya picking ta tura mashi sako yace _Busy_ duk sai taji bata kyauta ba.
*********
RANAR ASABAR
Ta koma bacci bayan sallar subh, wajen karfe tara na safe, Umma ta tayar da ita, tace,."Kina da bako a waje."
Hafsat tace, "Bako kuma, waye?"
Umma tace, "Ba su fad'a ba, ya dai ce a mota yake."
Tayi jim sannan ta duro daga saman gado ta wuce bandaki tayi wanka ta jima sannan ta fito ta cancara kwalliya ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skirt ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, ta suri mayafi ta fita, tayi turus ganin Hisham a tsaye, tun da ta fito yake kallonta ba ya koda kyaftawa, ta murtuke fuska tace, "Aniyar kowa ta bi shi. Mutum ya daina kallona."
Yayi murmushi yace, "Gorgeous. Dukkanin wannan kwalliyar ni aka yi mawa." Ji take kamar tayi kwallo dashi. Ta harareshi tace, "Ko a mafarki."
Hisham ya kanne ido daya yace, "Har da kallon so."
Zuciya ta kawo mata wuya ta murtuke fuska, "Da na san kaine doguwar Hijab da niqab zan saka, hakanan kato ya rink'a kallewa Aliyu mata." Ya ware idanu yace, "Nine kato." Ta taso mashi tana bala'i, "Ka godewa Allah da ban ce katon banza ba."
Yace, "Ki kira min yarona nayi mashi alkawari zan kaishi Park."
Hafsat ta nuna mashi kofar parlour tace, "Gaka ga gidan, ka shiga ka fito dashi." Yace, "A'a. Ki kira min shi." Tace, "A'a. Ka shiga da kanka. Umma ce a ciki, naga ba bakuwarka bace, idan kace ta baka zata baka." Yayi shiru, ta gane mai yake nufi da shirun da yayi, tace, "Ohh. Ashe kasan kunya. Sai ni da ka raina kake min haka."
Ta juya ta hango Little mak'ale a kofar parlour tayi mugun kallo tace, "Zaka koma ciki ko sai naci ubanka. Ubanka nace."
Da gudu Little Aliyu ya koma ciki yayinda Hisham ya ware idanu yace, "A gabana kike zagina." Ta juyo tace, "Ko zaka rama ne." Ya girgiza kai, "A'a, na gane duk a cikin so ne."
Tayi mashi kallon tsana sannan tace, "Hisham ko a mafarki ka ga na ce ina sonka ban yafe ba." Ya murmusa yace, "Ina sonki Angel. Tun da baki barshi ba zan koma, tun da na ganki naji sanyi a raina." Tayi tsaki ta juya ta shige ciki, yabi bayanta da kallo yana murmurshi.
Bilkisu ce ta kirashi ya d'aga yace, "Hello. Eh. Ina wajen Najeeb."
A ranar ta saka security su hanashi shigowa gidan, ta hanashi ganin Little saidai ya tarar dashi a makaranta, shima tayi gargadi idan ya bishi sai tayi mashi shegen duka, abubuwa sunyi mashi yawa sai a lokacin ya k'ara tantance yana sonta, idan ya ganta tare da wani zuciyarsa ta rink'a kuna, ya kora mata samari ya fi a kirga.
Ranar wani ya aika kiranta tana fitowa ta tarar Hisham yana korashi, "Nine wanda zai aureta har an saka rana." Ta ware idanu tana kallonshi, yace, "Ki tsaya inyi maki bayani."
Ta girgiza kai, "Babu bayanin da zakayi koda kayi bayani bazan saurareka ba. Ashe kaine kake kora min samari. Ka janyo wa kanka, da abun da ka ke yi yanzu, da wanda kayi min shekarun baya, sai na shuka maka rashin mutunci." Ta juya ta koma ciki, kwana daya, biyu, sati daya, sati biyu, ya ga ba ta yi komai, sai da ta bari ya manta sannan ta durar mashi, yana zaune a parlour tareda boys dinsa, Abdullahi wanda ya girma sosai, Muhammad wanda yake da shekaru tara sai Sulaiman (wanda bilkisu ta haifa) sai dai ganinta yayi, ya ware idanu yayinda gabanshi ya yanke ya fad'i, yana wiki-wiki da idanu yana kallon Bilkisu wacce take zaune a daya bangaren.
Hafsat ta bi yaran da kallo, Abdullahi wanda kallon sani ya ke mata, Muhammad wanda yake KAMANNI sak da ita, da Suleiman wanda Bilkisu ne sak.
Bilkisu ta dubeta da mamaki tace, "Saidai ban wayeki ba?" Hafsat tana kallon Hisham tace, "Ayyerh, ai ba za ki wayeni ba, na zo makotanku ne kuma ba su nan, kishirwa nikeji ki taimaka min da ruwa."
Bilkisu ta mike ta wuce kitchen, Hisham ya mike da sauri yace, "Angel. Miye haka?"
Hafsat ta murtuke tace, "Ko kayi min shiru ko kuma in fayyace mata komai, dukkanin abun da zai faru ya faru, babu ruwana, ai kaine ka fara." Zaiyi magana ya hango Bilkisu tana fitowa, yayi shiru ya koma ya zauna.
Bilkisu ta mik'a mata bottle water, Hafsat tace, "Sannu. Na gode." Bilkisu tace, "Yauwa." Tana fita compound, Abdullahi ya biyota, "Aunty Hafsat." Ta tsaya tare da juyowa yayinda hawaye suka ciko idanunta saida taga Muhammad a yau da taga Muhammad ta k'ara jin tsanar Hisham akan rabata da yayi da gudan jininta, tasha wahalar cikinta, ta haihuwa a wahalar ce amma ya rabata dashi babu tausayi babu tausayawa.
Ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Abdullahi. Kana lafiya?" Yace, "Lafiya lau." Tace, "Allah yayi albarka." Abdullahi yace, "Amin. Bari na tafo maki da Muhammad."
Sai Hafsat ta samu kanta da tsayawa babu jimawa suka dawo tare, Muhammad yayi tsuru yana kallonta, Abdullahi yace, "Ka gaidata mamarmu ce."
Muhammad yace, "Ina wuni?." Idanunta suka ciko da hawaye tana mai kallon gudan jininta, tace, "Lafiya lau. Ya kake?" Muhammad yace, "Lafiya lau." Ta juyar da kai tare da goge hawayen da suka zubo akan fuskarta Tace, "Allah yayi albarka." Yace, "Amin."
Ta dubi Abdullahi tace, "Abdullahi, na gode. Na gode sosai. Ka kula min dashi." Abdullahi ya gyad'a kai.
Ji tayi hawaye zasu zubo mata, ta shige mota da sauri, ta kama hanyar gida, tun da ta koma gida take tunanin Muhammad, da irin wahalar da tasha da cikinsa, har ta kasa hakuri, "Saidai duk abun da zai faru ya faru amma sai na amso yarona tunda ba wani bane yayi min nakudarsha. Da uban mi yake takama da har zai korar min da samari." (Ni kuwa na ce Hisham ya janyo wa kanshi 🤣🤣🤣).
Da dare suna zaune a dinning table suna cin abincin dare, Hafsat tace, "Umma cikin satin nan zan je Abuja gidan Hajiya Babba, tare da Little da Muhammad."
Umma ta dubeta na wasu dakiku tana mamakin sunan Muhammad da ta fad'a yaron da ba'a hannunta yake ba. "Muhammad kuma?" Hafsat ta gyad'a kai ba tare da ta ce komai ba, har Umma za ta yi magana sai kuma tayi shiru.
Washegari, da misalin karfe sha daya na safe ta shirya cikin leshe dinkin bubu, ta kashe dauri, ta yafa mayafi akan kafad'a, ta fita a motarta kirar Range Rover da ta siya shekarar da ta wuce, kai tsaye ta wuce gidansu Hisham, tayi sa'a ta samu yaje gaida Momcy, ya mike da sauri yana kallonta yace, "Hafsat. Mi ya kawoki?" Ta murtuke fuska tace, "Muhammad na zo amsa tunda ba kai bane kayi min nakudarshi ba."
Ya kalli matakalar bene yace, "Kina hauka ne." Tace, "Idan kana tantama ka hanani yarona a lokacin ne zakaga hauka ganin idanunka." Ta zauna ta daura kafa daya akan daya, ya nufo inda take ta daka mashi tsawa, "Kada ka fara ko kuma a yau in nuna maka ainihin kalata idan raina ya b'aci. Try me, I will do my worst. Saidai a mutu, rashin mutunci ne kowa ya iya."
Sautin takon Momcy ta tilasta mashi komawa mazauninsa, Hafsat ta gyara zamanta tare da cire kafa da ta d'aura akan daya.
Momcy ganin Hafsat, ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi tace, "Bakuwa mukayi. Hafsat." Hafsat ta rusuna tace, "Momcy, Ina kwana? Mun sameku lafiya?" Momcy ta zauna akan kujera mai daukar mutum ukku tana mai amsawa da, "Lafiya lau." Ta maida dubanta akan Hisham da ke mazurai tace, "Zaka tashi ka bamu waje ko kuma mu tashi mubar maka falon." Ba don ransa yaso ba ya mike ya fita balcony.
Momcy ta ce, "Angel na rasa da wani idanu zan kalleki, kunyarki ta ke ji akan abubuwan da Hisham yayi maki na butulci. Ina mai baki hakuri akan abubuwan da suka faru. Ban san gaskiyar abun da ya faru ba sai watanni baya da suka wuce. Ce min yayi zaman yaki dadi a tsakaninku shine kika nemi saki kika bar mashi yaro, sai da ya ga Little Aliyu sannan ya ke fad'a min gaskiya, raina ya b'aci sosai na ce na fidda hannuna tun da har ya mayar da ni mutumiyar banza. Ki gaida Ummarki, ki bata hakuri a madadina, kuma zanzo har gida."
Hafsat tace, "Za ta ji. Momcy nazo ne domin in amshi Muhammad ina so zan je da su Abuja." Momcy tace, "Babu damuwa." Ta d'aga waya ta kira numbar Hisham.
Hisham ya dawo, kallo daya Hafsat tayi mashi ta dauke kai, Momcy tace, "Hisham ka kira a kawo Muhammad za ta je wani gari da shi." Hisham ya zaro idanu jin abun da tace, yace, "Muhammad kuma? Ina zasuje?"
Momcy ta murtuke fuskarta tace, "Ka tutsiyeni in fad'a maka, zaka kira a kawoshi su wuce ko kuwa sai na sab'a maka KAMANNI."