Sashe 41
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bilkisu tana zubar da hawaye ta tattara wajen ta wanke tana ji tana gani ta zubar da abincin a shara, abincin da ta shafe lokaci tana girkawa, ba tayi kasa a gwuwa ta girka taliya da shinkafa da miya wacce taji naman kaza ta zuba a kwando ta aika direba ya kai mashi office saidai tana zaune a inda ta bada sakon ya maido mata dashi cewa, "Ranka ya dade yace a maido maki dashi." Ta juyar da kai ta goge hawayen da suka zubo sannan ta kakaro murmurshi tace, "To shikenan babu damuwa."
Damuwa ya saka ta kasa cin abincin, kamar Suleiman ya fahimci halin da take ciki, ya dawo makaranta ta zuba mashi yaki ci, "Ka ci." Tace tana mai tura mashi abincin. Ya girgiza kai yace, "Mommah kici." Dole ta zuba suka ci a tare. Da dare tayi girka ta ajiye a dinning table, taci tareda Suleiman ya rage na Hisham ne.
Tun fitarsa da safe bai dawo ba sai karfe goma na dare, ta d'ago tace, "Barka da dawowa." Saidai koda kallon inda take baiyi ba, ya wuce, ta mik'a ta zuba abincin a tray tabi bayansa, k'arar ruwa taji ta fita, jim kadan ya sauko ya dubeta yace, "Ki zo." Tabi bayansa tana mamakin kiran, ya murtuke fuska yana nuna mata tray da ta ajiye mashi yace, "Dauki abunki ki b'ace min daga gani." Tace, "Amma..." bata rufe baki ba yayi kwallo da tray din abincin ya tarwatse a wajen, "Ki tabbata ki gyara wajen, aikin banza aikin wofi, na ce ban ci." Ya fita yana fad'a.
Suleiman ya leko, tayi mamakin ganin yaron tayi saurin goge hawayenta tace, "Suleiman har ka tashi." Ya gyad'a kai yace, "Mommah wa ya sakaki kuka?" Da sauri ta girgiza kai tace, "A'a abu ne ya shigar min cikin idanu."
"Mi aka yi wa Abbu yake ta fad'a?" Ya k'ara jefo mata wata tambayar, tace, "Wasu ne suka b'ata mashi rai, muje kayi barci." Ta maidashi dakinta ta sakashi barci sannan ta dawo ta gyara wajen tayi mopping ta zuba turaren wuta tana ji tana gani ta gama wahalar girki ya k'are a kwandon shara.
Washegari still ta saka breakfast dinsa a kwando ta ajiye mashi a mota, yana saukowa tace, "A dawo lafiya, kalacinka yana a cikin mota." Ya tsaya cak ba tareda ya kalli inda take ba yace, "Zaki je ki cire min daga mota ko kuma sai na b'arar dashi sannan."
Tace, "Amma..." bai tsaya saurarenta ba ya fita saidai jin k'arar fitar motarsa tayi tana fita ta samu ya fita a wata motar ne daban, ta dauki abincin ta baiwa mai guard ta koma ciki.
Wajen karfe sha biyu na rana ta tura mashi sakon text message 'Idan Suleiman ya dawo zanje gidanmu daga in biya ta gidan Momcy na gaidata.'
Amsar da ya maido mata ba ta yi mata dadi ba, 'Na hanaki zuwa ko kuma na rike kafafunki ne, idan bangon duniya zakije ke kika sani, ki dawo ko ki zauna a can ke ya shafa.'
Ji tayi kuka ya kwace mata ta k'ara tura mashi wani sakon, 'Nagode, in aiko maka da abinci ne.' Ya maido mata amsa, 'Eh idan baki gaji da wahalar banza ba.'
Ta tura mashi, 'Don nayi maka girki bazai zama wahalar banza ba domin mijina nayi wa.'
Ya maido mata amsa, 'Amma zai samu gurbin zama a shafin almubazzaranci tun da kin san bazan ci ba kika girka, wai mi yasa kika cika naci ne, idan nine ke tattara kayana zanyi in wuce gidanmu, haba ki kyaleni inji da kunci da damuwa da nike a ciki.'
'Dukkanin abun da ya faru, ya faru ne sabo da ni, ka aikata mata hakan ne sabo da ni don haka ba zanyi butulcin barinka a damuwar kai daya ba.'
'Ko da na bukaci hakan da kaina'
Ta maida mashi da amsar, 'Eh..' ya rubuta mata, 'Ni kuma ina son kasancewa ni daya ne, bana buk'atarki a rayuwata a yanzu.'
Ta rubata mata mashi, 'Kayi hakuri.'
Saidai babu amsa tana kira taji numbarsa a kashe.
Bayan direba ya dauko Suleiman daga makaranta tayi wanka suka fita ta tattara kayansa ta ajiyeshi a gidansu. Da mamaki Nene take tambayarta abun da yake damunta ganin tayi rama. Ta girgiza kai tace, "Babu komai." Daga nan ba ta sake tambayarta hakanan bata tambayeta dalilin kawo yaron ba lura da tayi da bata son magana a kai, tayi mata uzurin dukkanin ranar da ta shirya fad'a mata zata fad'a mata.
Ba ta jima ba ta wuce gidan Momcy, tana zubar da hawaye take sanar da ita abun da yake faruwa.
Momcy ta jinjina kai tace, "Ranar na kirashi nayi mashi fad'a tunda ranar bai k'ara zuwa ba, shi da yake D'a ya nuna yayi fushi ya dauke kafa daga gidana kinga kuwa ni bazan dauki kafa inje inda take ba, don haka sai dai in ce maki kiyi hakuri ki k'ara hakuri, wata rana sai labari, shi kuma ina mashi fatan Allah ya dawo dashi akan hanya. Ya ka sa tsaya ya dauki kaddara shiyasa yake samun damuwa, Hafsat ta auri wanda take so, zafin ransa da damuwarsa bazai sauya komai ba amma shi ya gagara tsayawa ya fuskanci wannan gaskiyar, Bilkisu babu abun da zan ce maki saidai ince kiyi hakuri sannan ki k'ara hakuri, idan kin je ki ce mashi ina nemanshi idan yazo zanyi mashi fad'a, idan kuma ya zab'i ya ki zuwa then babu abun da zan iya yi a kai."
Bilkisu tayi mata godiya ta wuce gida, tayi girki ta jera akan dinning table, tana zaune a parlour ya shigo, ta d'aga kai tace, "Sannu da dawowa, abinci yana akan dinning table." Yayi mata banza, tace, "Momcy tana nemanka." Ya tsaya cak ya juyo kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya haye sama.
Tun daga ranar ba ta k'ara matse mashi ba sai dai dare da safiya tana mashi gaishe dashi tareda sanar da shi abinci yana akan dinning table amma koda kallon arziki bata samu a wajensa amma bata karaya ba, tayi matuk'ar mamaki la'akari da Suleiman ba ya gidan kuma ba ta sanar da shi inda yake ba kuma bai tambaya ba.
Tun tana hakuri tana kawar da kai har ya kai ta wuya ya fusatata, yana shigowa falon ta tari gabansa ya zuba mata idanu, idanunta a tsaitsaye tace, "Ko zaka tureni ne."
Bai ce mata komai ba, tace, "Na gaji da wulakanci da kakeyi min a gidan nan." Ta fashe da kuka, "Wannan abun da mi yayi kama, ina binka kana wulankatani, wulakanci na yau daban na gobe daban. Ka dauki tsana da tsangwama na duniya ka dora min akan abun da ba ni ba ce na ce ka yi, laifina daya shine ka aikata abun a saboda ni ne, amma ay ban ce maka kayi ba kuma kana zab'i amma sai ka zab'i abun da aikata mata, kayi saboda gudun cutuwata kuma na gode amma wannan ba zai baka lasisin wulakantar da ni ba." Kuka ya ci karfinta wanda ya tilasta mata yin shiru.
Ya kama hannunta har compound, yace, "Kije gidanku." Tana mai zubar da hawaye tace, "Hisham..." ya katseta, "Za ki tafi hakanan ko kuma sai na hadaki da takardar saki." Zuciya ta kawo mata wuya tana ji kamar ta fad'a mashi ya saketan sai mi.
Ta girgiza kai tana mai kawar da tunaninta daga hudumar da shaidan ya ke yi mata, ta mik'a hannu tace, "Bani makullin mota." Ya mik'a mata makullin mota da ya dawo dashi, ta shiga ta kama hanyar gidansu.
Tana kuka ta sanar da Nene abun da yake faruwa, "Tun kafin tayi aure yake min abubuwan nan, hakuri kawai nikeyi, tace ba za ta aureshi saboda abun da yayi mata, tayi aure ta auri wanda take so amma hakan bai saka ya hakura ba, ya daina min magana, ba ya cin abincina, idan nayi mashi magana ya hau ni da fad'a, abu kadan zai fara ihu wannan shine dalilin da ya saka na dawo da Suleiman gidan nan." Nene tace, "Mi yake nufi dake yanzu?" Bilkisu ta share hawayen da suka zubo mata tace, "Ya ce inzo gida shikenan." Nene tace, "Yana nufin ki zo kiyi ta zama kenan." Yanayin fuskarta ya nuna tsantsar b'acin ranta. Bilkisu tayi shiru kawai domin bata da abun cewa.
Bayan sallar Isha'i Baffa ya shigo bayan sun gama cin abincin dare Nene ta sanar dashi abun da ya faru, ranshi ya b'aci matuk'a, yace, "Gobe idan Allah ya kaimu zan samu wakilinsa inji abun da yake nufi da turoki gida."
Bilkisu ta girgiza kai tace, "Baffa ku rabu dashi, zafin kai, fushi da damuwa da ya d'aura ransa ne suke damunsa idan aka sameshi zai iya tsinke igiyar auren, a rabu da shi. Baffa ka san Hisham, ka san halin sa, mu rabu da shi lokaci yana zuwa da zai gane abun da yayi bai kyauta ba, addu'a da zamuyi mashi shine Allah ya ganar dashi gaskiya."
******
Sai bayan aurenta sannan ya fahimci matuk'ar son da yake mata, ya rasa nutsuwarsa, ya rasa kwanciyar hankali, ya rasa farin cikinsa, komai haushi yake bashi, tun da ya kori Bilkisu gidansu ya daina fita, kullum yana zaune a gida, ya rame ya fara kasumba da sumar kai ya koma kamar samun kamun hauka.
Momcy tana sane ta rabu dashi tana fushi akan abun da yayi mata, daga tayi mashi fad'a ya dauke kafa daga gidanta, ta kyaleshi yaje taga inda zafin kansa da damuwar zasu kaisa, abun yayi yawa har yana neman tab'a lafiyar kwakwalwarsa, abokansa suka sameta suka bata hakuri.
A ranar ta shirya direba ya kaita gidan Hisham, halin da ta ganshi a ciki saida ta zubar da hawaye, tace, "Ka tashi kaje kayi wanka ka dawo kaci abinci muyi magana." Babu musu ya mike ya wuce ya jima a bathroom sannan ya fito ya shirya cikin riga da wando na kananan kaya ya fito ta zuba mashi abincin da tazo mashi dashi, ya girgiza kai yana b'ata fuska yace, "Bakina babu dadi." Ta murtuke fuska wanda ya tilasta mashi daukar cokali tana tsakurar abincin ta ka sa ta tsare har saida taga yana neman yayi amai saboda koshi.