Sashe 36
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hisham yace, "Amma Momcy na cancanci in san inda za ta je min da D'a."
Momcy ta fusata tace, "Ohh ita kuma bata cancanta ba shiyasa ka rabata dashi tun yana zanen goyo. Zaka kira ko kuma ban isa ba. Sai in dauko wayata in kira da kaina. Ka ce a kawo da kayanshi idan sun dawo an kai mashi sauran." Ya zaro idanu kamar zaiyi kuka yace, "Momcy ban gane ba." Momcy tace, "Daga yau Muhammad ya koma hannun mahaifiyarsa daga yau har abada. Idan kuma kana da ja inji, idan iyakata zaka nuna min."
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 16
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Duk Ac dake a falon amma zufa ce take karyo mashi, ya juyawa Hafsat yace, "Please ki ce mata unguwar kawai kike son zuwa dashi idan kika dawo zaki maido dashi." Ta kalleshi ta watsar tace, "Ka kwaceshi a hannuna babu tausayi babu tausayawa, a yau Momcy tayi hukunci wanda shine adalci sannan kake son in bada mata kasa a idanu. Kallon uwa nuke mata har gobe don haka na amsa da godiya. Momcy na gode Allah ya k'ara girma."
Momcy ta murtuke fuska tana mai tsareshi da idanu, kamar zaiyi kuka ya kira, mintina talatin a tsakani direba ya shigo dashi, yana jaye da luggage, Muhammad yana biye da shi, Muhammad yayi hugging Momcy yace, "Nayi kewarki kaka." Momcy tayi murmurshi tace, "Nima nayi kewarki," ta nuna mashi Hafsat sannan tace, "Wannan ita ce mahaifiyarki ka je ka gaidata." Ya gane ita ce wacce taje gidansu watan da ya wuce har Abdullahi ya sanar dashi itace Mamarshi. Ya isa inda take yace, "Ina wuni?" Tayi murmurshi mai tafowa da hawaye tana kallon gudan jininta tace, "Kana lafiya?" Muhammad yace, "Lafiya lau."
Momcy tace, "Itace mamarka, za ku je unguwa tare, ban da rashin ji, ka rink'a jin maganarta. Tasha wahala sosai lokacin da take dauke da cikinka har hauka tayi."
Muhammad ya gyad'a kai, kwatankwacin abun da Abdullahi ya sanar dashi kenan duk da karancin shekarunsa amma ya tsinci wasu abubuwan a ciki.
Hafsat ta rasa da kalmomin da zatayi amfani dasu tayi mata godiya akan karamci da tayi mata, tace, "Na gode sosai Momcy. Allah ya k'ara girma." Momcy tace, "Amin. Ki fad'awa Ummarki ina nan zuwa."
"Fatima fa?" Tambaya ganin tunda tazo bata ga gilmawarta ba. Momcy tace, "Fatima tayi aure a London, a zamanmu a can ta samu miji bature." Hafsat tace, "Okay a bani numbarta."
Muhammad yayi hugging Hisham yace, "Mun tafi Abbu." Hisham yace, "Allah ya tsare hanya." Hafsat ta kama hannunsa suka fita.
Sai a lokacin Hisham ya samu zarafin tada maganar yace, "Momcy. Amma Bilkisu fa?" Momcy ta murtuke fuskarta tace, "Ita ta yi mata rainon ciki ko kuma ita ce tayi mata nakudarsa. Tambayarka nike, ita tayi mata rainon cikin ko nakuda. Kuma koda wasa naji wani labarin sai na sab'a maka."
Washegari Hafsat ta wuce dasu Kano inda sukayi boarding flight zuwa Abuja, Hisham ya dameta da kira ta saka numbarsa a blacklist, saida su ka yi watanni biyu sannan suka baro Abuja ta biya ta sokoto ta barsu a wajen Jalila sannan ta dawo Katsina ita kadai.
Washegarin da ta dawo sai ga Hisham kamar wanda aka jefo, ganin da gaske ba tareda yaran tazo ba, yace, "Hafsat ina kika kai min yarana?" Ta murtuke fuska tace, "Ka kawo sauran kayan Muhammad ne. Momcy ta yanke hukunci akan yaro ya dawo a hannuna don haka babu abun da zaka fad'a da zai saka na daukeshi na baka." Yace, "Ina kika kai min yara?" Tace, "Ban sani ba ka je ka tafo da wanda ya tsaya maka ya amsar maka. Tun da har ka ce ba zan zauna lafiya ba, kaima ka yi kadan ka zauna lafiya. Dani kake magana." Yana mata magana tayi mashi banza ta koma ciki, yana ji yana gani ya juya ya koma gida, yana matuk'ar jin kunyar Umma bazai iya had'a idanu da ita ba.
Umma take sanar da ita zuwan Momcy da hakuri da ta bata akan bai sanar da ita gaskiya ba, Hafsat tace, "Momcy uwa ce ta gari." Umma tace, "Kwarai kuwa, matar bata da damuwa, yaro ne ka haifeshi baka haifi halinsa ba."
Sati daya, sati biyu da dawowarta amma har zuwa wannan lokacin bata niyyar dawo da yaran ko ta sanar dashi inda suke, idan yayi mata tace, "Ka aiko mai karfin gidanka ya zo ya tambayar maka." Yace, "Idan kin isa kice gidanmu." Tayi murmurshi mai ciwo tace, "Gidanku gidan Momcy kenan ita kuma uwa take a wajena. Allah ya saka mata da gidan aljanna domin uwa ce ta gari mai adalci ko kuma hakan zai b'ata nata rai."
*****
Hisham ya tusa Momcy a gaba yace, "Momcy please ki kira Hafsat ta fad'a min inda ta kai min yarana, ta fad'a min inda suke, na cancanci insan inda suke."
Da gatse Momcy tace, "Gaskiya ne, ka cancanci kasan inda suke." Abun da bai sani ba shine Hafsat ta sanar da ita inda suke har waya takeyi dasu.
Hisham yace, "Kin gani."
Momcy tace, "Hakane bari a kirata ta fad'i inda ta kaisu." Ta janyo wayarta ta kira numbar Hafsat, bayan ta amsa gaisuwar da Hafsat tayi mata tace, "Jiya nayi waya dasu Muhammad sun fad'a min sai hutunsu ya k'are sannan zasu dawo."
Hisham ya ware idanu fuskarsa dauke da mamaki jin abun da Momcy ta fad'a a waya.
Daga daya bangaren Hafsat tace, "Hakane."
Momcy tace, "Hafsat waye ya dauki cikin Muhammad tsawon watanni takwas?"
Hafsat bata gane dalilin tambayar amma sai tace, "Ni." Wanda shine amsar tambayar da tayi mata.
Momcy ta jefo tambaya ta biyu, "Hafsat waye yasha wahalar cikin har na tsayin watanni takwas?"
Hafsat mamaki ya kamata amma sai tace, "Ni."
"Shin akwai wanda ya tayaki nakudarsa?" Momcy ta jefa mata tambaya ta ukku. Hafsat tace, "Babu."
Momcy tace, "Don haka kamar yadda na fad'a maki hukunci da na yanke yana nan idan sun dawo ki rikeshi a wajenki, tsakaninshi da Hisham saidai ziyara shima idan kin amince, ko kallon banza yayi maki ki kirani yaga yadda zamu kwashe dashi."
Hafsat tace, "Na gode sosai Momcy. Allah ya k'ara girma."
Momcy ta amsa da, "Amin. Allah yayi albarka." Hafsat tace, "Amin."
"Ki gaida Ummarki da Abbanki."
"Za su ji."
Momcy ta tsinke kiran, Hisham yace, "Amma Momcy." ta daka mashi tsawa sannan tace, "Idan ka isa ka tada maganar kaga yadda zamu kwashe da kai. Kadan nayi maka idan aka duba girman zalunci da butulci da aikata mata don haka ka gode Allah. Consider yourself lucky da ban ce ta hanaka ganin yaran ba. Ka tashi ka bani wuri." Zaiyi magana tayi mashi tsawa, ya mike ya fita.
Bilkisu har ta gaji da tambaya.
Hisham yana ji yana gani tsakaninshi da yaran saidai ziyara ko kuma hutun karshen mako ya fita dasu.
Momcy ta tusa Hisham a gaba yaje yaba Umma hakuri akan abun da ya faru, ta saka aka rakashi ya gaida Abba, daga wannan ranar ya soma shiga har cikin gidan.
Mostly zaka sameshi a gidan ya kasa ya tsare, yana fakar idanu yana korarwa Hafsat samari, tace ya fitar mata daga gida, yace bai fita tunda Umma tana ciki, suyi ta fad'a.
A ranar da ta kira ta sanar da Momcy korar mata samari da yake a ranar ne yaga b'acin ranta, ta inda take shiga bata nan take fita ba, ta tusa keyarsa har gidansu Hafsat, ta nemi ganin Hafsat.
Momcy tace, "Hafsat shin baki da hankali ne da har kika sakar mashi fuska yake korar maki samari, a yau ya ce min yana sonki. Shin kin shirya komawa gidansa ne? Ina son inji ne domin in yabawa shashancinki." Hafsat ta girgiza kai tace, "Bayan abun da yayi min koda shine autan maza na yafeshi koda kuwa zan mutu babu aure. Aliyu shine wanda nike so shine wanda zan aura."
Momcy ta juya wa Hisham tace, "Na gode Allah da tayi wa kanta karatun ta nutsu a kanka domin koda idan nice na haifeta tace zata koma gidanka sai na kaita gidan mahaukata an duba kwakwalwarta sannan. Na sani saboda ni suka bari kake shigowa amma ka rasa da abun da zaka biyani dashi sai korar mata manema don haka a yau na hana daga yau idan yazo wajen yaransa ya tsaya a compound, su kasa a saka maku idanu a kansa domin bamu san wata tsiyar zai kulla a gaba." Ta mike ta fita.
*****
Tun daga ranar Bilkisu ta kasa gane kansa a kullum cikin tunani yake, tunanin Hafsat ne manne a cikin zuciyarsa, sai a yanzu ya gane matuk'ar son da yake mata, idan ya ganta tare da wani ji yake kamar zuciyarsa za ta fashe, idan ya ganta tana murmushi wa wani ji yake kamar zuciyarsa zata tarwatse, ya ganta a kusa dashi shine farin cikinsa koda kuwa bak'ar magana ce za ta fad'a mashi.
Hankalin Bilkisu ya tashi ganin da sannu da sannu ciwo yake cinsa, yana da damuwa amma tayi tambayar duniya bai fad'a mata ba, ranar da ta tutsiyeshi a gaba akan ya fad'a mata gaskiya, ganin ba zata fitar mashi daga daki ba ya janyota waje ya danna makulli, tana knocking tana mashi magana yayi mata banza da ita.