Sashe 2
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jalila tace, "Har Umar ya bani tausayi. Yana matuk'ar sonki ba kadan ba."
Hafsat ta share hawayen da suka zubo akan fuskarta tace,
"Babu yadda zanyi, bani da wata mafita da ta wuce wannan, dolena in rabu dashi saboda Ummana ta fiye min shi a rayuwa. Na wuce kada Umma tayi fad'a. Yaushe ne muke da lectures?" Ta tambaya.
Jalila tace, "Jibi. Lecture safe ne, eight to ten." Hafsat tace, "Alright, muje kiyi min rakiya."
Jalila ta saka hijab suka fito, wata mata ce zaune akan tabarma tana kulla citta da sauran kayan miya a gabanta, Hafsat tace, "Mama na tafi."
Matar wacce ta kira da Mama tace, "Ki gaida Ummanki." Hafsat tace, "Zata ji." Jalila tace, "Mama zan rakata gida." Mama tace, "Torh."
Saida Jalila ta rakata har kofar gida sannan ta juya ta koma gida, Hafsat ta shiga ciki ta wuce dakinsu inda ta tarar Umma bata nan har ta wuce gidan da take aikatau.
Da marece, tana zaune tana kuncewa Umma kitso, Umma tace, "Hafsat wacce shawara kika yanke akan maganar da nayi maki d'azu da safe, zaki koreshi da kanki ko kuma in shirya korarshi da kaina, zuwa da kai yafi aike, gwara in fita da kaina in koreshi, karkiyi mashi k'aramar kora ya dawo washegari."
Hafsat ta rumtse idanu ta bud'e fuskarta dauke da damuwa tace, "Umma zan rabu da Umar in auri mai kudi kamar yadda kike so amma ina so kiyi min alfarma guda daya. Umma zan bi zab'in da kikayi min koda kuwa zuciyata bata so amma Umma a rayuwata ban san auren da zanje in fito ina sone inyi aure a inda zan zauna, Ina sone in auri miji na gari wanda y'ay'ana zasuyi alfahari da zab'in da nayi, ina sone ki barni in samu na gari wanda ba ya da damuwa, wanda yasan darajata."
Umma ta saki gud'a fuskarta dauke da fara'a tace, "Yauwa er albarka. Yana zuwa ki korashi, ki rink'a kallon kanki a madubi daga kallonki babu tambaya mutum zai tabbatar da Matar Manya ce, ba kiyi irin talauci ba, ke matar masu kudi ce, ta sakawa a gaban mota." Hafsat ta rumtse idanu yayinda hawaye suka zubo akan fuskarta.
Kafin ta k'ara magana yaro yayi sallama, "Angel ki zo in ji Umar."
Umma ta yatsine fuska sannan tace,
"Ka je ka ce mashi tana zuwa. Hafsat ki je na k'arasa kwantar kitson da kaina, ki je ki korashi ya k'ara gaba, saidai abi wani sarkin, kin fi karfinsa, kwalelen kare da hantar kura, kowa ce kworya da abokiyar gurbinta, ya je ya nemi daidai shi."
Mik'ewa tayi jikinta a sanyaye ta zura hijab ta fita kofar gida, inda ta sameshi jingine da bango ta tsaya gefenshi tace, "Ina kwana?"
Da murmushi akan fuskarsa yace,
"Lafiya lau. Angel mi ya b'ata maki rai?"
Tace, "Ka manta kawai."
Furucinta ya matuk'ar bashi mamaki, ya dubeta yace, "Ta ya za'a yi in manta bayan naga wacce nike matuk'ar so a cikin damuwa."
Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace, "Abun da ya had'amu shine zai rabamu a yau shiyasa nace maka ka manta. Umar ina san ka manta da ni, ka manta da mun tab'a da mun tab'a soyayya ka je ka nemi wata, ba zan iya aurenka ba." Ya zaro idanu yace, "What? Saboda mi?" Saida ta juyar da kai sannan tace, "Saboda baka da kudi, saboda kai talaka ne, Ummana tace sai mai kudi zan aura, sharadin shine gida da mota. Kai kuma baka dasu."
Da sauri yace, "Hafsat!." Tace, "Please ka rabu dani ka je ka nemi wata."
Ji yayi ranshi ya b'aci yace,
"Ke har ni zaki wulakanta bayan na bijirewa dangina da nayi nace sai ke. Mi kike takama dashi? Kyau ne kawai kike dashi amma baki da asali, zan taimaka maki ne kawai, bambamcinki da shegu shine saida aka d'aura aure sannan aka haifeki kuma ansan a inda dangin mahaifinki suke, ke da kike diyar mace, tun da aka haifeki mahaifinki ya tsallake ya gudu, ko kina tunanin bamu da labari ne, torh ubanki mahaifi d'an caca, mashayi."
Ta zaro idanu yayinda hawaye suka zubo akan fuskarta tace, "Umar ni kakeyi wa gori?"
Kanshi tsaye yace, "Ko nayi k'arya ne? Ay gaskiya na fad'a, ita ummarki saboda kwadayi don tana aikatau a gidan masu kudi taga yadda suke jin dadi shine take mafarkin zaki iya auren mai kudi, ki koma ki fad'a mata ko talakawa basu auren mace marar asali ballanatana masu kudi, ki fad'a mata ta sauya shawara domin wannan hanyar ba mai bullewa bace ba, nima taimaka maki zanyi in rufa maki asiri."
Ta fashe da kuka ta juya ta shige cikin gidan da gudunta tana gumjin kuka.
Umar ya dafe kai yana nadamar maganganun da yayi mata.
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 2
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Hafsat ta tsallake matan dake a tsakar gidan ta shige daki ta fad'a akan gado tana mai fashewa da kuka, Umma ta shigo tana kallonta da mamaki tace, "Hafsat mi ya faru dake ne kika shigo kina kuka kamar wacce aka ce mata na mutu?"
Hafsat tana mai cigaba da kuka tace, "Umma kinyi gaskiya da kika ce Umar BAI DACE DANI BA."
Umma tace, "Ki sanar dani abun da ya faru, yanzu sai in shukawa mutum rashin mutunci domin ban hadaki da kowa ba."
Tana mai sheshshekar kuka ta sanar da Umma abun da ya faru ta dora da cewa, "Umar yayi min gori akan mahaifina sannan ya kirani da diyar mace, yace min marar asali."
Saida Umma ta lailayo ashar ta watsa sannan tace,
"Lallai kuwa Ummaru ya janyo fad'an da ya fi karfin dukkanin danginsu, mik'o min mayafina inje har gida inci mutuncin iyayensa tunda bashi da kirki, sai yasan ya tab'oki, ni za'a yi wa rashin mutunci." Tasan halin Umma da fad'a idan taje gidansu Umar ba za'ayi da dadi ba, magana ce wacce bata fatan ta fita domin babu abun da zata janyo sai gulma da tsugunne-tsugunne a tsakanin mutanen unguwar wanda basu raina gulma.
Ta mik'e zaune tareda had'e hannayenta waje guda alamar roko, tana mai cigaba da kuka tace,
"Umma na rokeki da girman Allah ki rabu dashi, koda babu komai anyi walkiya na ganshi."
Umma tayi mata wani kallo ta janyo mayafi ta yafa zata fita, da sauri tace, "Umma idan kikaje zan janye alk'awarin da nayi maki na auren mai kudi."
Umma ta tsaya cak, ta dawo ta zauna tana maida lumfashi ranta a matuk'ar b'ace, "Shikenan na fasa amma duk ranar da ya k'ara maimaita abun da yayi sai yayi nadama, sai naje har gidansu anyi ta, har ya isa ya aibatani, yana kiranki diyar mace wannan diyar macen ta fi en uwanshi mata gata tunda bata tara samari tana rokonsu kudi, waye ba ya da labarin gidansu da rayuwar karya da danginsa mata suka sakawa kansu, yarinya anyi tuwo gidansu tace ba zata ci ba ta kira saurayi ya siya mata Indomie da nama, ya k'ara maki gori sai anyi tone-tone a tsakaninmu."
Hafsat ta koma ta kwanta tayi lamo yayinda hawaye suke zarya akan fuskarta, cikin ranta tana ayyana, "Tabbas baiyi karya ba, ubana mahaifi mashayi ne, dan caca, wanda ya gudu ya barmu a gararin rayuwa, har zuwa wannan ranar bamu san halin da yake ciki ba, yana raye ko ya mutu bamu sani ba."
*******
Katon parlor ne wanda yake zaune da setin expensive kujeru a kalla guda biyar, wata farar mata ce zaune akan kujera mai daukar mutum ukku yayinda wata kyakykyawar budurwa take zaune a gefenta tana kallo a TV.
Hisham yayi sallama tareda kutsa kai cikin falon yana tafiya a sanyaye kamar wanda bashi da lakka, ya zauna kusa da matar tareda bata side hug, fuskarsa babu walwala yace, "Barka da warhaka, Momcy."
Momcy tana mai shafa sumar kanshi cike da kulawa tace,
"Barkanmu, ya office?"
"Alhamdulillah."
Fatima ta gaisheshi ya amsa da kulawa. Ya mike da nufin ya wuce bedroom dinsa Momcy ta tsayar dashi, "Abinci yana akan dinning table." Yana mai cigaba da tafiya yace, "Na koshi, zan ci anjima."
Fatima tace, "Yaa Hisham. Coffee ko kunu?" Ba tareda ya tsaya ba yace, "Kunu."
Momcy ta girgiza kai fuskarta dauke da damuwa tace, "Aisha ta cuceni a rayuwa, Hisham mutum mai fara'a da barkwanci amma ta maida min dashi miskilin karfi da yaji. Ta kassara min yaro. Ta kassara mashi rayuwa."
Fatima ta share hawaye da suka zubo mata tace, "Allah shine zaiyi mamu sakayya akan abun da Aisha tayi mamu, ta rabamu da farin cikinmu, zanyi farin ciki idan yaya Hisham ya koma kamar yadda yake kafin faruwar wannan abun, koda kana cikin damuwa barkwancinsa kawai zai saka kayi dariya."
Momcy tace, "Allah ya bayyana Bilkisu."
Fatima tace, "Amin." Ta mik'e ta wuce kitchen domin dama mashi kunun.
*******
Hisham yana shiga bedroom dinsa ya fad'a akan gado, ya janyo frame dake cikin bedside drawer, ya k'urawa fuskarta idanu yana tuna muryar wannan yarinyar (Hafsat).
Fatima ce tayi knocking, "Salaam alaika."
Da sauri ya b'oye frame dake hannunsa sannan yace, "Wa alaikissalaam." Ya bata izinin shiga. Ta kutsa kai tana dauke da flask da cup, ya mik'e ya zauna akan kujera, ya kirkiro murmurshi wanda iyakarsa akan fuska ne yace, "Little sis kina ji dani fa."
"Dole inji da kai saboda kaine farin cikinmu a gidan nan. A koda yaushe ka rink'a tunawa da kaine farin cikinmu."