← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momcy kamar tasan abun dake ranshi tace, "Kowace mai ciki da yadda yake zo mata, ita ci yake sakata, jalof da daddawa kawai take ci, zaka iya saka mata nama amma karka saka kifi amai yake sakata." Ya gyad'a kai.

Har compound suka rakasu, Abdullahi ya rungume Babansa yace, "Abba. Ina zaka tafi da Aunty Hafsat? Ka barta ta zauna a nan." Ta shafa kanshi tace, "Zan dawo wata rana." Ya b'ata fuska kamar zaiyi kuka.

Fatima ta kamashi, suna tsaye suna masu d'aga masu hannu har motar ta fita daga gidan, lokacin da suka isa gida ana kiran sallar zuhr yayi, yayi alwalla ya wuce Masjid, sai bayan sallar Asr sannan ya dawo ya shigo da kaya niki-niki ya wuce kitchen ta tab'e baki tace, "Gwara in ci in koshi, in dadin tutsiyeshi ya fad'a min gaskiya. Babu dole idan naji zan iya zama in zauna idan naji bazan iya ba in k'ara gaba." Ta d'aga murya tace, "Ka dafa min taliya da wake."

Hisham ya zage ya girka mata jelof na taliya da wake mai daddawa sannan yayi mata farfesun kaza shima mai daddawa, da gangan tace saidai ya bata da hannunsa, yana bata ta cije mashi hannu, da gayya ta cinye abincin baki daya har farfesun ko kadan bata rage mashi, ya tattara kayan ya wuce da su kitchen, ya dama kunu yasha sannan ya fito ya zauna a kusa da ita yace, "Angel. Ina jinki." Hafsat ta tab'e baki tace, "Ina jinka dai. Muryata da ka aureni saboda ita ba zakaji. Inyi magana saidai idan ta zama dole." Yace, "Mi kike son sani?"

Tace, "Waye kai? Mi yasa ka aureni? Miye akan muryata da ya saka ka aureni? Wacece wannan matar wacce ka kira da Aysha? Wacece Bilkisu? Mi ya samu Bilkisu? Shin tana a ina? Shin da gaske ta haukace?"

Hisham ya lumfasa sannan yace, "Zan fara da sanar dake waye ni, zaki samo amsoshin tambayoyin a nan." Ta gyad'a kai tace, "Duk da bashi na tambaya amma ina sauraronka ka gama zagaye-zagayen da jan lokaci dolenka daga karshe ka sanar dani gaskiya akan tambayoyin da nayi maka."

********

"Sunana Hisham Mahmoud, mahaifina Alhaji Mahmoud mutum ne mai tarin dukiya, Allah yayi mashi rasuwa shekarun baya da suka wuce, a lokacin Fatima tana jinjira, ya barni da tarin dukiya, na tashi mutum mai son mutane da kuma barkwanci, idan ka zauna kusa dani dole kayi dariya, nayi degree na farko da na biyu a kasar waje, a can ne na hadu da Aysha, wacce ta zo gidan nan, ta nuna tana sona, tun bana kulata har na fara kulata, zuciya tana son mai kyautata mata, itama er Nigeria ce, iyayenta suna zaune a can amma danginsu a nan suke, a garin nan, soyayya ta shiga a tsakaninmu, Aysha macece ta kasance mace mai son jiki komai saidai en aiki suyi mata, yaran gidansu basu ji kuma na gani amma sai nike gani zata sauya a dalilina, a lokacin da na kammala degree na biyu a lokacin ne ta had'a degree na farko, a shekarar ne aka saka mamu ranar aure, wata biyar a tsakani aka d'aura aure, tun farkon aurenmu muka fara samun damuwa, ba ta girki saidai na restaurant ni kuma bana iya cin abincin saye, da aurena amma saidai in je gidanmu in ci abinci, duk da Momcy bata min magana amma ranta yana matuk'ar b'aci akan abun har bana son zuwa saboda ban san ganin b'acin ranta.

A wannan lokacin ne Bilkisu ta shigo rayuwata, a ranar na kai ziyara wa abokina, muna hira a ofishinsa aka kawo mashi awara da yayi order a wajen wata food vendor a online, tunda ya bude awarar kamshinta ya dokeni na lumshe idanu ina ji yawuna yana tsinkewa.

Kabir yace, "Ka ci." Na girgiza kai, Kabir yace, "Kaci, tana da tsafta." Kamar ba zan ci ba sai kuma na dauki cokali mai yatsu na soki guda daya sau ukku ina gwada sakawa a bakina ina fasawa, karshe na yanke shawarar inci, na jinjina kai ina jinjinawa dadin da tayi, Kabir yace, "Abun da nike fad'a maka kenan."

Na janye takeaway daga gabansa tace, "Kayi order din wata, nima a kawo min takeaway biyu."

Kabir ya ware idanu yace, "Kuma sai ka amshe min wannan." Nace, "Kayi order."

A gabana Kabir ya kirata ya k'ara order na takeaway ukku, ya aika aka amso mashi, da abincin na wuce gida na ajiye a dakina, na ci da marece sannan na ci da dare, koda Momcy ta kirani nayi mata k'arya cewa Aysha tayi min girki ne shiyasa banje ba, duk da bata yarda ba saidai bata ja maganar ba.

Washegari bayan nasha coffee na wuce office, na soma jin yunwa na kira Kabir. "Kabir wannan yarinyar miye abubuwan da take siyarwa?" Saida yayi dariya sannan yace, "Yayi maka dariya ne har haka." Nace, "Ina jinka?" Yace, "Okay zan tura maka numbarta da business flyer dinta." Nace, "Alright."

Tare da tsinke kiran, koda na kira bata d'aga ba, na duba na ganta online na mata magana ta amsa, nayi order na Meatpie, Cincin, Awara and Dambun nama.

Sunanta Bilkisu, gidansu yana a kofar keke, da kaina na je na kira na sanar da ita ina kofar gidan. Ta aiko k'aninta ya kawo min, na amsa na wuce, tun daga ranar na dauke zuwa gidan Momcy cin abinci, ina zuwa amma ba kullum ba, ban tab'a ganin Bilkisu a idanu ba, koda nuna min ita aka yi ban cewa gata, hotonta ne a dp dinta saidai abaya ne a jikinta ta rufe fuskarta da niqab.

Maganar business takeyi kawai idan ka sako wata hirar tayi shiru, na shaku da ita har a zuciyata, kullum abincinta shine abincina, bata abinci amma ina biyanta tayi min.

Kabir yace, "Mi kake jira? Ka aureta kawai, ina guje maka ka tsaya ganin kallon ruwa kwado yayi mata kafa, idan wani ya aureta, kai ne za ka yi nadama." Damuwar shine koda nayi mata wata hirar bata amsa nasha tura mata hotunana saidai ta biyoni da sticker shikenan. Kabir yace, "Kai kasan yadda zaka bullo mata."

Nace, "Ba a nan gizo yake saka ba, ina gaya maka tun da nike zuwa gidansu bata tab'a fitowa da kanta ba saidai ta aiko k'annanta." Nayi jim yayinda dubara ta fad'o min, a tare dashi muka fito.

Kai tsaye gidansu muka nufa a motata, dama na saka order, kamar kullum ina kira ta aiko k'aninta, na bashi dubu goma nace, "Tsaya." Na gutsiri cincin guda daya na b'ata fuska nace, "Kace mata gani ban tafi ba, nace ya aka yi bai yi dadi."

Yaron bai jima da shiga ba ta fito tana sanye da dogon hijab har kasa, muryarta kawai na sani, a ranar ne na fara ganin fuskarta, doguwa ce, wankan tarwad'a, mai matsakaicin tsawo, tana da kyau daidai ita, idan aka kwatantata dake ba za'a kirata mai kyawu ba.

Ta tsaya gefenmu, tace, "Kuma duk wadanda suka siya babu wanda yayi korafi amma ina ganin wani abun ne ya fad'a mashi."

Kabir yace, "Ki rabu dashi, yayi dadi. Wajenki muka zo baki fito ba shiyasa. Ke ya kike haka, abokina yana sonki amma kina ja mashi aji, idan yazo baki fitowa, ace mutum yana tsoron d'an uwansa mutum."

Bilkisu ta girgiza kai tace, "Ba haka bane."

Kabir yace, "Torh, abokina yana matuk'ar sonki, ba ya da burin da ya wuce ya aureki, ya za'ayi?" Ta juyar da kanta gefe tace, "Allah ya zab'a mamu abun da yafi zama alheri." Ta amshi wayata ta saka min daya numbarta sannan ta juya ta koma ciki.

Ban boye mata komai ba, na sanar da ita matsala da nike dashi a gida, tun daga wannan ranar bata k'ara amsar kudina saidai na fad'a mata abun da nike so ta girka min na aika a amso, abinci ukku a rana itace take girka min na aika a amsar min, soyayya mai karfi ta shiga a tsakaninsu.

Bilkisu daga makarantar sekondire karatunta ya tsaya, tun da ta fahimci cewa Babanta ba ya halin da zai dauki nauyin karatunta ta hakura da karatun, abun da zasu ci a gidan wahala yake masu, wata ranar da yunwa suke wuni saida dare suci gari ko kanzo, bayan dogon tunani tayi wa kanta fad'a shine ta fara awara tana talla a dandalin sadarwa na yanar gizo, tana amfani da ribar ne tana taimakawa mahaifinta, a gefe guda tana siyan kayan kitchen tana ajiyewa, tayi classes da yawa na koyon girki, tana tuntub'ar na gaba da ita a harkar abinci, tana koyo daga garesu, cikin k'ank'anin lokaci ta fad'ad'a kasuwancinta ta fara dambun Nama, meatpie, cincin, donot, alkubus, waina da sauransu, har abincin biki tana amsa tayi a biyata, ta koyi dubulan, tana wa amare ana biyanta, k'anwarta Naja'atu tana gama sekondiri ta samu Miji, kayan Kitchen da Bilkisu take siya tana ajiyewa sune aka kai mata, tayi ciko wa carpenter da take barin kudin kayanta a wajenshi yayi kayan dakin Naja'atu, har abincin da aka yi wajen bikin Bilkisu ce ta bada rabin kudin, mahaifanta suka rink'a saka mata albarka.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 12

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057
Chapter 25 · 0% Book details