← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsakar gidan wayam, sai bayan shigarta sannan matan gidan suka fara shigowa daya bayan daya, daga wacce take rataye da kallabi, sai wacce ta daura hijab kamar mayafi duk a saurin fita ganin abun dake faruwa domin a samu na gulma.

Umma ta shigo tana mita, "Yaushe kuma kamun en daba ya zama abun tsayawa kallo?" Duk da tasan k'aramin aikin mutanen unguwar ne musamman wanda suka mayar da gulma halinsu.

Kallon da mutanen gidan suke mata ya saka ta gane akwai wata maganar bayan wannan, ta maida dubanta akan Hafsat tana neman karin bayani. "Umar ne yazo a katuwar Jeep ya saka en daba suka fasa motar Hisham."

Saida Umma tayi ashar sannan tace,
"Aikuwa ya tarowa kanshi abun ya fi karfin baki daya danginsu, muje har gidansu sai ubanshi ya biya b'arnar da ya saka aka yi."

Hafsat ta kamata tace, "Umma, Hisham ya kira Jami'an tsaro sun tafi dasu."

Umma tace, "Ki fad'a mashi babu yafiya har sai sun girbi abun da suka shuka."

Hafsat ta jata suka shiga daki suka zauna ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita, ta dora da cewa, "Umar yayi wasu maganganu na barazana a gareni, Hisham yace a yau zamu koma wancen gidan, ya zuba komai, mu dauki abubuwa masu muhimmanci."

Umma zatayi magana, Hafsat ta katseta,
"Please Umma, zamanmu a wannan gidan ya k'are, na tsorata da al'amarin Umar, wannan fitinar ta fi karfina, gwara mu koma wancen gidan ya fi kwanciyar hankali, ba zan iya kwana a wannan dakin ba wanda za'ayi kofar bugu daya ta b'alle."

Jalila ce ta shigo gidan da sauri, "Angel. Mi yake faruwa? Karima ta shigo gida tana ce mamu ana fad'a saboda ke, tace har da en daba da Jami'an tsaro."

Hafsat tace, "Babu wanda yayi fad'a saboda ni, Umar ne ya saka en daba suka fasa motar Hisham har yana barazanar zai saka su dokeshi." Ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da ita, Jalila ta gamsu ta shawarar da Hisham ya yanke, tace, "Umma, abun da Hisham ya yanke shine abun da ya dace, babu tsaro a wannan gidan ki duba kofar dakin nan bugu daya za'ayi mata ta b'alle. Bari na kira Mama na sanar da ita sai in tayaku hada kayan."

Jalila ta kira Mama ta sanar da ita abun da ya faru tareda dorawa da fad'a mata zata rakasu har sabon gidan, ta tayasu suka hada abubuwan da suke bukata wanda suturarsu ne kawai sai takardun makarantar Hafsat, suka fito tare saka kwado a kofa.

Umma tace, "Jalila idan zaki tafo zan baki makullin ki duba mamu, idan akwai abun da muka manta sai ki tafo mamu dasu, sauran kuma ki bayar."

Shamsiyya wacce dakinta yake a kusa da dakinsu tace, "Fita zakuyi ne."

Umma tace, "A'a ba fita zamu ba, tashi zamuyi zuwa sabon gidanmu."

Dukkanin matan dake a tsakar gida saida yanayin fuskarsu ya sauya zuwa na mamaki, wasu kuma na bakin ciki ne da hassada, sun tsani Umma saboda tana bakin k'ok'arin ganin Hafsat ba tayi rayuwar wahala da y'ay'ansu sukeyi ba, har suke ganin girman kai ne, isar baka isa ba, gulma iri daban-daban.

Salme tace, "Tashi kuma babu sanarwa."

Jumala ta sab'a diyarta a baya tace,
"Muje inga inda zaku koma, zuwa gobe sai muje muga sabon waje. Na tayaku murna, Allah ya saka da alheri."

Sun sani sarai gulma ce zata kaita, saidai basu ce da ita komai ba, ta bisu zaram-zaram, zani daban, riga daban, takalma ware da ware, bata lura ba saboda sauri taje taga gulma domin ta zama mutum ta farko da ta maida yadda aka yi.

Fitarsu ke da wuya, d'aya daga cikin bodyguard dinsa ya bude masu daya daga cikin Jeep da suka zo da ita, dayar motarshi da shege suka fasa har an wuce da ita.

Mama ta shiga tareda Jalila, Hisham yana ta kallonta tayi banza dashi, zata shiga, Jumala tayi wuff ta shige.

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 8

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

*This Page Goes To Mama Gee, Fahaus chambo, Diamond Bhatool, Mjungudo, Oum Hafsat, Maman Kamal, Mmn Useey, Mummy Khairat, Garba Fatima, Fauziyya Ibrahim Kam, Oum Aftnoor, Aeesharh, Nudar Rabiu, Hauwau Abdullahi and Muhammad Phatymerh Othman, ku yi yadda kuke so dashi.*

Hafsat ta dafe kai ta juya inda Hisham yake, ya nuna mata motar da zai shiga, ya bude mata baya ta shiga, bodyguard ya bude mashi daya bangaren ya shiga.

Gida ne madaidaici, wanda yake dauke da get da yake hade da tsakar gida, a gefe kitchen ne da toilet, store yana hade da kitchen, parlour guda daya ne da dakuna ukku, daya na Umma, daya na Hafsat, daya kuma na guest. Babu abun da babu.

Jumala ta saki baki tana kallon ikon Allah, gida har gida, gini mai kyau, yasha fenti, with complete tale.

Hisham yayi masu sallama ya wuce ana kiranshi gida, ta rakashi har mota, ya mik'a mata makullen gidan yace,
"Akwai kayan abinci a store. Akwai solar, idan sun dauke wuta ku kunna, akwai ruwa a tanki, idan da wuta zai cigaba da hawa. Ba sai kunyi girki ba zan aiko a kawo maku."

Tayi rolling idanu da murmurshi akan fuskarta tace, "Mun gode ranka ya d'ad'e."

Yace, "Yauwa ranki ya dade." Tayi kasa da kai tana murmurshi, ya juya ya shiga mota suka wuce, ta juya ta koma ciki.

Tana shiga parlour tace,
"Jalila na kira Mama na sanar da ita a nan zaki kwana." Da mamaki Jalila ta tambaya, "Yaushe kika kirata?" Ta zauna a saman kujera mai daukar mutum daya kafin tace, "Yanzu kafin in shigo." Jumala tana zaune akan daya daga cikin kujerun tana k'arewa gidan kallo tana daukar detail na gulmar da zatayi.

*****

Hisham ya fad'a akan kujera tareda lumshe idanu yace, "Wash!."

Momcy ta dubeshi da kulawa sannan tace, "Tun d'azu nike kiranka baka d'agawa sai daga baya ka amsa." Ya kwashe dukkanin abun da ya faru ya sanar da ita.

Momcy ta jinjina kai tace, "Allah ya tsare." Fatima tace, "Naso ace ta barka ka banbance masu tsakanin aya da tsakuwa, basu san abun da suke tunkara bane."

Momcy ta girgiza kai tace, "A'a gwara da bai biye masu yayi fad'a dasu ba, fitina a kwance take Allah ya la'anci mai tayar da ita."

Fatima ta turo baki tace, "Amma Momcy sune suka tsokaneshi har sukayi b'arna."

Momcy ta kusa kai mata duka, "Tashi ki bani waje. Miye motar da sukayi b'arna a kanta, motar da muke da kudin siyen dubunsu."

Fatima tayi baya da sauri kamar zatayi kuka. Hisham yace, "Didi ki kawo min kunu." Ta mike ta wuce kitchen ta b'ata lokaci ta had'a mashi kunu ta zuba a jug ta d'aura glass cup a kai. Ta tsiyaya mashi ta bashi tareda zama a kusa dashi tana turo baki wa tsawa da Momcy tayi mata.

Hisham yace, "Sun koma wancen gidan, zan siya mata mota ta rink'a zuwa school."

"Ta iya mota ne?" Momcy ta tambaya. Ya gyad'a kai yace, "Ta iya, yau da zamuje gidan na bata tayi driving dinmu saida muka kusa zuwa sannan na amsa. Bari na kira Najib ya saka a aika masu da abinci."

****

Har aka kira Magrib Jumala bata wuce ba, tana nan aka kawo masu abinci, taci har da guzuri a leather tace, "Ummar Hafsat ban fito da kudin komawa ba."

Jalila ta tab'e baki tace, "Kin san baki da kudin komawa kuma kika biyomu."

Hafsat tace, "Tunda ta saba da tafiya a kafa sai ta saka harama, tafiya a kasa ba bakonta bane. Ki tashi tun dare baiyi maki ba."

Umma ta tsawar masu, "Jalila. Angel. Bana son in k'ara jin bakinku a nan, tana sauri ta tayamu murna ne. Ke Hafsat bata kudin da zata koma."

Hafsat ta bude jikkarta ta zaro duba daya ta mika mata. Jumala ta amsa tana zuba godiya.

Jalila tace, "Tafiyar da bazai wuce naira dari ukku ba, shine har da bata dubu daya."

Hafsat tace, "Kin san idan mutum yafi karfin abu. Taje dashi."

Umma ta daka masu tsawa, "Angel! Ku tashi ku wuce daki."

Jalila ta mike, Hafsat ta mara mata baya, Umma tace, "Jumala, mun gode, Allah ya bar zumunci."

Jumala tana washe hakora tace, "Amin. Gobe zamu zo tareda en unguwa suga waje." Umma tace, "Sai kunzo, Allah ya kawoku lafiya."

Umma tayi mata rakiya har tsakar gida daga nan ta juya ta koma ciki sanin zaiyi wahala ta hau kekenapep bata son ta tursasata hawa.

Jumala tana fita, ta kalli dubu daya da aka bata, ta daura abinci da tayi guzuri a saman kai, ta taka a kafa har gida tana tafiya tana tsara yadda zata zuba gulma, fad'a ba'a tambayeka ba.

******

Babu abun da bai saka masu ba, har da sutura suka ci abinci sukayi hira, Umma ta wuce dakinta.

Jalila ta kwanta akan gado yayinda Hafsat ta kwanta akan doguwar kujera tana waya da Hisham saida suka raba dare yana janta da hira, ya koma mata kamar k'aramin yaro, yana zuba mata shagwab'a yana mata dubara yana k'ara tsayin hirar domin ya sakata tayi magana yaji muryarta. The more suke waya the more take k'ara sonshi.

Bayan an dauke wuta, ta kunna masu solar, Ac, iska ta ko'ina, bacci sukayi mai dadi har saida suka kusa makara sallar asuba.

Hafsat tana gama sallar asuba ta koma bacci kasancewar basu da lectures, kuma bacci ne sosai a idanunta.
Chapter 14 · 0% Book details