Sashe 7
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida tayi sallama wa Mama sannan ta fita zuwa gida, a daki ta tarar da Umma zaune, tana ganinta ta murtuke fuska, tace, "Daga tafiya siyan kati shine kikayi zamanki kika barni a nan ina jiran gawon shanu, kika barni Ina zaman jiranki kamar wacce bata da mafadi, ko nace maki ne bani da aiki, nayi maki kalar zaman kashe zani ne." Ta jefo mata tambaya, kadan ya rage ta kai mata duka, tayi baya da sauri tace, "Umma na je gidansu Jalila ne na kirashi a can." Umma ta kalleta na wani lokaci sannan tace, "Angel k'arya ba halinki bane ba karki fara, zanyi mugun sab'a maki ne." Tace, "Da gaske nike."
Umma tace, "Idan ma k'arya kike zaki hadu dani ne, kuma ba zaiyi maki kyau ba." Wayar ce tayi ringing saida ta duba sannan tace, "Shine."
Umma tace, "Ki d'aga kadda ta tsinke."
Sanin idan ta tsaya jan aji Umma zata iya kai mata duka, tayi picking tareda kanga wayar a kunne.
Al'ameen da yake kishingide akan wani katon gado yace, "Hello." Tace, "Salaam alaika." Ya gane nufin ta yace, "Sorrry. Wa alaikissalaam. Ya kike?" Tace, "Lafiya lau."
"Tun daga ranar da naga baki kira ba nike zuwa wajen ko zamu sake haduwa amma shiru."
Tace, "Bamu sake zuwa bane."
"Yaushe zaku k'ara zuwa?" Ya tambaya. Tace, "Babu tabbas."
Kamar mai rad'a yace, "Cutiee."
Tace, "Sunana Hafsat."
Yace, "Okay, Hafsat tun da na hadu dake kika mallake min zuciya. Ina sonki." Ya lumfasa sannan yace, "Hafsat ke kyakykyawa ce dukkanin wanda yayi tozali dake zai tabbatar da hakan, Hafsat ina sonki." Tayi dariya tace, "Torh na gode."
"Yaushe zanzo gidanku in ganki tunda muka rabu nike missing dinki?" Ya tambaya. Ganin Umma tana sauraron amsar da take bashi, kuma idan ta bashi amsa kai tsaye zata gane tambayar da yayi, sai tace, "Okay, torh na gode, zanyi abu sai anjima." Daga daya bangaren yace, "Alright."
Umma ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi sannan tace, "Ko ke fa, kwara ki saki jiki ku fahimci juna, na fad'a maki bazan baiwa talaka aurenki ba, sai mai kudi zaki aura, sharadin shine gida da mota, shiyasa na saka kika kori Ummaru."
Dukkanin maganar da Umma takeyi akan kunnen Al'ameen ne kasancewar kiran bai tsinke ba, yana jin shiru yayi sauri ya tsinke kiran yana wani shu'umin murmushi, yace, "Dawa tayi nama. Kunzo hannu, tunda har kike da idanun cin naira ni kuma zanyi amfani dasu in b'ata rayuwar diyarki, tun da dora idanuna akan zubin halittarta naji ina son kasancewa tare da ita, ta mallaki komai, zan watsa maki naira na more rayuwa da diyarki, babu aure a tsarina saidai jin dadi kawai. Yarinya tazo hannu, dole sai na tsallakeki."
Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰
*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_
*NA*
*AYSHER ANGEL*
Page 5
*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*
1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary
WhatsApp 09169472057
Tun daga wannan lokacin yana yawan kiranta sannan yana saka mata kudi a layinta sosai, idan ta kirashi ba ya dauka saidai idan ta tsinke ya biyo kiran, ta rasa dalilin da ya saka har zuwa wannan lokacin bata jin wani abu a dangane dashi, tana iyakar k'ok'arinta domin cusashi a ranta amma abun yaci tura.
****
Somewhere in Europe
Wani handsome saurayi ne tsaye a saman dogon bene yana kallon garin, ya zaro waya tareda kiran numbar Nigeria, daga daya bangaren aka ce, "Ashraim." Yace, "Habib. Miye labari akan Hafsat?" Ya fad'a mashi halin da ake ciki ya dora da cewa, "Shiyasa nace maka ka bayyyana kanka a gareta tun kafin ka tafi."
Ashraim yayi murmurshi karfin hali yace, "Nan da shekara daya zan dawo, IDAN HAR RABONA NE aje a dawo zan sameta."
Habib yayi karfin hali yace, "Idan ka dawo zai fiye maka idan ka ajiye miskilanci ka bayyana soyayyarka a gareta."
Ashraim yayi murmurshi sannan yace, "Hafsat zuciyata ce, koda ban fad'a mata ba, idan ta kalli kwayar idanuwana zata fahimci yadda nike matuk'ar sonta." Habib yayi dariya yace, "Miskili kawai." Ashraim ya tsinke kiran yana kallon hotonta dake akan majigin wayarsa.
****
A daren wata rana Hafsat tana kwance akan tabarma har ta fara barci, Al'ameen yayi mata video call, da mamaki take kallon majigin wayar sai kuma ta mik'e zaune ta janyo hijab ta zura kafin ta amsa kiran, ta zaro idanu ganin daga shi sai guntun boxer daidai cinya, har tana hango tudun joystick dinsa, da sauri ta tsinke kiran, ya k'ara kira amma wannan karon voice call ne, taki picking, ta kashe wayar baki daya tana mamakin wannan al'amari.
Washegari tun da safe ta soma shiri kasancewar tana da lectures na safe, tana gama sallar subh ta shiga wanka ta shirya tayi kalaci, Umma ta zaro dari biyar ta bata tace, "Gashi kiyi amfani dasu, Allah ya bada sa'a." Ta amsa da, "Amin."
Ta saka kudin a jikarta ta fice, ta biya gidansu Jalila kafin suka suka wuce school, a makaranta ta wuni sai karfe biyar sannan ta koma gida ta samu Umma bata dawo daga gidan da take aikatau ba.
Tun wannan kiran bata k'ara amsa kiransa ba, kiransa ne ya shigo wayarta saida tayi jim kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa, "Yanzu kuma... Amma ba ka ce min zaka zo... No, ba haka bane, ban jima da dawowa daga makaranta bane amma babu damuwa... Sai kazo.."
Ta rage kayan dake jikinta tayi daurin kirji ta d'aura hijab akai sannan ta fita tsakar gida ta janyo ruwa a rijiya ta cika bucket ta shiga bayi ta jima tana cuda jikinta sannan ta fito ta shirya, powder da kwalli kawai ta saka a fuskarta, ta shirya cikin leshe dinkin riga half bubu, straight skirt, ta kashe dauri samfurin ture kiga tsiye, ta fesa jikinta da turaruka masu saukin kamshi, har ta dauki hijab sai kuma ta ajiye ta yafa mayafi akan kafad'a ta saka flat shoes, ta fita tana tafiya a hankali.
Mota ce fara sabuwa dal Jeep, ya bud'e bangaren direba kadan yayinda ya zuro kafafunsa, yana sanye da kananan kaya, ta k'arasa tareda jingina da motar tayi mashi sallama. Ya amsa da murmurshi akan fuskarsa, ya kurawa kirjinta idanu yana wani shegen murmurshi saidai bata lura ba kasancewar inda take kallo daban. Ganin bata da niyyar shiga motar yace, "Ki shigo." Ta girgiza kai, "Na fad'a maka bana shiga motar samari." Ya ware idanu yace, "Saboda baki yarda da ni ba." Ta girgiza kai tace, "A'a ba haka nike nufi ba." Yace, "Then ki shigo." Still girgiza kanta tayi tace, "A'a nan yayi, bana shiga motar samari."
Al'ameen ya d'age mata gira daya yace, "Kin tab'a saurayi mai mota ne?" A bazata tambayarsa tazo mata, ta kalleshi fuskarta dauke da mamaki sai kuma tace, "Eh, ga shi nan a kusa dani." Al'ameen yace, "Ohhh."
Ganin ba zata shiga motar ba ya fito ya tsaya a gefenta ta matse mata har tana iya jin saukar lumfashinsa, da sauri ta matsa, yace, "Miye?" Tace, "Babu komai." Ya k'ara matse mata, ta matsa, yace, "Naga kin matsa ne."
Tace, "Kana matse min ne sosai." Ya d'aura hannuwansa akan motar yana mai kura mata idanu yace, "Miye don na matsa kusa dake kina abu kamar er kauye, ke babbar yarinya ce, karki cuci kanki kiji dadin rayuwarki, ki more rayuwarki."
Taso ta gane inda maganarsa ta dosa saidai bata son tayi mashi mummunar fahimta, tace, "Pardon me amma ban gane ba."
Ganin bai samu fuska yace, "Ohhh. Ina zuwa." A ranshi yana ayyyana idan kin san wata baki san wata ba, ya bud'e gidan baya ya fiddo leather, ya mik'a mata yace, "D'azu kin ce baki shiga motata, idan kika ki amshi kyauta da na baki hakan ba zaiyi min dadi ba. Waya ce Samsung da iPhone sai kuma tablet, akwai kudi a ciki da kuma sakon Umma." Jin yawa da tsadar abubuwan da ya lissafa tace, "Amma..." Da sauri ya katseta, "Amma idan baki amsa ba, raina zai b'aci, zanga kamar kina min kora da hali tunda dama kinki shiga motata bayan ni aurenki zanyi."
Bata da wani zab'i da ya wuce ta amsa, tace, "Na gode, kuma kayi hakuri ban ki shiga motarka da wata manufa ba." Ya kanne mata ido daya ya karkace kai yana k'are mata kallo yace, "Kin ce baki dade da dawowa daga makaranta ba."
Bata nutsu da kallon da yake mata ba, tace, "Eh dawowata kenan ka kira, wanka kawai nayi na shirya na fito."
Yace, "Na manta da na tafo maki da abinci, shinkafa da kaza. Muje restaurant sai kici abinci."
Ta girgiza kai, "A'a, naci gurasa a school." Ya dan kalleta yace, "Gurasa kuma babu eatery ne." Kanta tsaye tace, "Akwai, ban dauka da zafi bane, na tsaya a matsayina ne." Duk da haka bai hakura yace, "Ina nufin muje in siya maki ko fried rice ne da kaza, da duk abun da kike so." Tayi murmurshi tace, "Na koshi, akwai tuwo a gida idan na shiga zan ci. Kasan tuwon da ya kwana yafi wanda aka girka a ranar dadi."
Kiran tuwo da tafi ya saka yaji amai ya tafo mashi. Zatayi magana sai kuma tayi shiru ganin kekenapep ta sauke Umma a kofar gidan, shima inda take kallo ya kalla yana yatsine fuska saidai bai yarda ta lura. Tace, "Umma ta dawo na wuce ciki kada tayi fad'a." Yace, "Alright, idan kin shiga kiyi mata magana zan shigo in gaidata." A ransa yana ayyana idan kin san wata baki san wata ba.