Sashe 4
Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umar ne." Tace a takaice. Umma ta murtuke fuska, "Saboda mi yake damunki bayan anyi walkiya kin ganshi ganin idonki..." da sauri ta katseta sanin matan gidan sun kasa kunne suji abun yadawa a gulma. "Na kashe wayar ne baki daya."
Umma ta ware idanu tace, "Akan miye zaki kashe wayarki." Ta fizgo wayar ta kunna kafin ta mik'a mata tace, "Amsa ki sakashi a wannan abun wanda koda mutum ya kiraka ba zai samu ba." Ta gane blacklist take nufi, tace, tace, "Umma Blacklist."
Umma tace, "Eh shi, makashi a can, ke dashi saidai hange daga nesa, nan gani nan bari sadakin bazawara ai koda na budurwa ne yafi karfin wasu."
Wani kiran ne ya shigo ta tsinke tareda saka numbobinsa a blacklist.
"Kin saka." Umma ta tambaya. Hafsat ta gyad'a kai tace, "Na saka."
"Yauwa er albarka, idan ya kuma kiranki da wata numbar kina jin muryarshi itama ki sakata a can."
Ta gyad'a kai. Umma tace, "Haka nike son ji." Ta lumfasa sannan tace, "Angel iya zama da mutane yayi a rayuwa, bikin da za'ayi a gidan da nike aiki amaren da kansu muke cewa dani za'aje kaisu, daya za'a kaita Abuja daga nan su wuce Italy inda mijin yake zaune, daya kuma Kano."
"Amma Umma ina zakije a ciki?" Hafsat ta tambaya.
Umma tace, "Abuja kai yayar, idan zamu dawo zamu biya ta gidan k'anwar a Kano. Ki tattara kayanki goben ki wuce gidansu Jalila har in dawo, bani san zamanki a gidan nan ke daya, mugu ba ya da kama, ga gulmar matan gidan nan ke kuma ba iya fitina kikayi ba, idan kin gama min kunshin kema ki cike kumbarki, ina so ki auri mai kudi amma kina yawo da hannuwa da kafa kamar na kato, kina gyara kanki kina abu irin na mata, sai kiga cikin sauki kinyi wuff da wani attajirin mai kudi."
Murmurshi ne ya sub'uce mata tace, "Umma zan yi."
"Allah yayi maki albarka."
"Amin."
Washegari Umma ta wuce wajen biki yayinda Hafsat ta tattara kayanta ta koma gidansu Jalila, ta yada zango a dakin Jalila.
Washegari da marece suna zaune a tsakar gida, Jalila tana chat na cinikin wasu Hijabi da ta dinka, ta d'ago tace, "Umar fa?" Hafsat tace, "Umar mi?" Jalila was like, "Ikon Allah kina amsa min tambaya da tambaya." Hafsat tace, "Ki fito ki fadi abun da yake ranki."
"Ya sameni ne da maganarki."
Hafsat ta rumtse idanu ta bud'e fuskarta dauke da b'acin rai tace,
"Ban fad'a maki abun da yayi min bane saboda ina cikin b'acin rai makura, idan na sanar dake raina ne zai k'ara b'aci idan na tuna, bayan da na sanar dashi yadda mu ka yi da Umma na fad'a mashi ya rabu da ni, shine yayi min gori ya kirani da er mace sannan ya aibata mahaifina." Ta kwashe abun da ya faru a tsakaninsu ta sanar da ita, ta dora cewa, "Shiyasa na godewa Allah da ban bijirewa Umma a kanshi ba."
Jalila ta jingina kai, "Umar bai kyauta ba, ya bani mamaki, ban tab'a tunanin zaiyi haka ba amma duk da haka Angel kiyi hakuri ki ganshi saboda..." ta katseta, "A wanne dalili zan ganshi?" Jalila ta dafata, "Please kiyi min alfarma nayi mashi alkawari, yanzu haka yana akan hanya, da nasan abun da ya faru bazan yi mashi alkawari ba."
Hafsat tayi shiru cike da takaici, Jalila tace, "Kiyi hakuri ban san abun da ya faru bane ba, babu dadi yazo baki fita ba amma duk da haka bazan maki dole ba idan kina ganin akwai damuwa idan yazo sai in fita in bashi hakuri."
Ta daureta da jijiyoyinta, Jalila tana da matsayi mai girma, tayi mata halarci, sau da yawa tayi abubuwan da bata so saboda ita. Ta lumfasa sannan tace,
"Idan yazo zan fita."
Jalila tace, "Na gode."
Hafsat ta rufe idanu yayinda ta lula a duniyar tunani.
Bayan Rabin Hour
Umar ya kira Jalila akan yana a kofar gida, fahimtar shine ya kira tun kafin tayi mata magana ta mike ta fita, bata fatan k'ara haduwa dashi a rayuwarta, yayi mata gori, ya aibata Umma, ya aibata mahaifinta, wanda bai mutunta iyayenta ba mijin aurenta bane ba koda kuwa shine autan maza, koda kuwa shine wanda yafi kowa arziki, bata tab'a sanin mahaifinta ba, ya watsar dasu, bai waiwayesu amma a zuciyarta tana mashi uzuri domin Uba uba ne.
Jalila ta zura dogon hijab akan kayan da suke a jikinta, ta biyo bayanta, tace, "Umar ga Angel nan, na barku lafiya." Umar yace, "Na gode." Ta juya ta koma cikin gida.
Umar ya dubi Hafsat wacce ta murtuke fuska, yace,
"Angel ina mai baki hakuri akan abun da ya faru a waccen ranar, nayi nadama matuk'a akan abun da nayi maki, ban yi da nufi ba, raina ne ya b'aci shine nayi sub'utar baki."
Ta rasa bakin magana, tun da suke tare dashi bata tab'a tabbatar da bai iya magana ba sai a wannan ranar, ya dubeta yace sub'utar baki, lallai Umma tayi gaskiya akan cewa da tayi Umar bai dace da ita ba. Da ace ta bujure mata ta aureshi tana mashi laifi kadan zai fara mata gorin iyaye yana zaginta. Tayi murmushi mai ciwo sannan tace, "Ba sai ka bani hakuri domin naji matuk'ar dadin wannan sub'utar bakin da kayi saboda ya saka anyi walkiya naga ainihin waye kai, na gode Allah da ban bijirewa Ummana a kanka ba, na gode Allah da ya kubutar dani daga aurenka domin na tabbata da ace na aureka, gorin da zaka rink'a min kenan bayan aurenmu."
Kamar zaiyi kuka yace, "Angel..." ta katseshi, "Eh Angel sunana ne, mi aka yi? Mi kake son kace? Ka fad'a ta cikinka domin ina da abun yi." Ya marairaice fuska yace, "Hafsat ina so ne ince maki kiyi hakuri hakan ba zai sake faruwa ba, nayi nadama sosai akan maganar da nayi maki." Ta d'aga mashi hannu tana mai girgiza kai, "Umar nadamar da kayi ba shi da amfani domin bakin alkalami ya riga ya bushe, umar ka b'ata rawarka da tsalle, kaje ka nemi wata, bazan tab'a aurenka, bazan tab'a auren wanda bai san dajarar iyayena."
Ji yayi ranshi ya b'aci, yana bata hakuri tana abu kamar diyar gold, bayan yasan komai a kanta, bayan taimaka mata zaiyi ya aureta, kyawunta ne kawai take dashi amma bata da asali. Ya rumtse idanu ya bud'e yayinda suka sauya kala zuwa launin ja, ya daka mata tsawa, "Ke! Mi kika dauki kanki ne? Ina baki hakuri kina b'audewa, naga dai abun da na fad'a gaskiya ne, ba k'arya nayi ba." Ji tayi hawaye sun zubo mata bata tab'a tunanin rana zata zo da umar zaiyi mata gori, bata tab'a tunanin wannan abun daga gareshi, a tunaninta idan aka yi mata gori shine mutum na farko da zai bi mata hakkinta yaji dadi amma sai ya bige da yi mata da kanshi. Tana mai zubar da hawaye tace, "Shiyasa hausa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, ina mai baka hakuri akan bata maka lokaci da nayi kayi soyayya da marar asali irina tunda yanzu idanunka sun bude ka gane gaskiya."
Yace, "Na san komai kuma na zab'eki saboda ina matuk'ar sonki."
Ta rasa bakin magana, yana tukfa yana warwarewa, mamaki yake bata, tace, "Umar kaje ka nemi daidai kai, domin nafi karfinka."
A fusace ya taso mata, "K'arya kike, tunfa har nike sonki dole sai na sameki, daga ke har kwadayayyar mahaifiyarki baku isa kuyi min wasa da zuciya ba, ina ce kudi ne matsalarku, torh zan shiga duniya inyi kudi ta kowace hanya sannan in dawo in aureki, ke tawa ce."
Hafsat tayi mashi mugun kallo, akan idanunta yake kiran Ummarta da kwadayya, ji take kamar tayi ball dashi, tace,
"Angel da kake gani nafi karfinka, koda kudinka ba rabonka bace, bazan tab'a aurenka ba Ban san *BURIN ABBANA* ba amma _BURIN UMMANA_ shine in auri mai kudi, ni kuma burina shine in auri miji na gari don haka zan had'a burikanmu a waje guda in auri mai kudi sannan kuma miji na gari, domin a tsakanin masu kudi da talakawa ana samun na gari da mugaye."
Umar ya daka mata tsawa, "Hafsat dolenki ki aureni saboda ina sonki." Tayi murmushi na takaici sannan tace, "Umar nayi nadamar b'ata lokacina da nayi a wajen soyayya da kai, ina so ka saka a ranka cewa baka tab'a soyayya da ni ba, ka manta da ni, ka saka a ranka cewa ka tab'a soyayya ne da wacce take shigen KAMANNI da ni. Zan jure komai amma ban da wulakanta mahaifana..." ya katseta, "Wulakanci ko kuma gaskiya. Angel Idan ke kince baki sona, ita ummar taki idan naje nayi kudin ina dawowa na watsa mata su a fuska, kwadayin kudinta ya tashi, zata bani aurenki koda kina so koda baki so, burinta shine kudi, torh zanyi kudi. Ki cire wa ranki cewa zaki iya rabuwa dani domin nine kadai hope dinki, ka fad'awa kanki gaskiya koda talaka bazai auri mace marar asali ba ballanatana kuma mai kudi, ke da kyau ne kawai kike taqama, saidai kinyi rashin sa'a domin akwai mata masu kyawu da yawa a gari wadanda suke da asali da nasaba."
Ta fashe da kuka tana mai jin tsanarsa a ranta, "Umar na tsaneka, nayi nadamar soyayya da nayi da kai." Ta juya da gudu ta shige ciki ta tsaya a soro ta fashe da kuka, saida tayi mai isarta sannan ta goge fuskarta ta shiga ciki ta wuce dakin Jalila, ta kwanta tayi lamo tana hawaye.
Jalila ta biyo bayanta tana mai tambayarta abun da ya faru. Tana mai cigaba da kukan tace,
"Ina kuka ne saboda bakaken maganganun da yayi shiyasa ban so fita ba."
Jalila ta ware idanu tace, "Kina nufin bakaken maganganu ya fad'a maki. Ashe ba ya da mutunci, dama saka na fitar dake ne domin ya b'ata maki rai, lallai kuwa zai san ya raina min hankali, ni zai mayar mutuniyar banza." Sanin halin Jalila da daukar zafi, idan ta fita ba zaiyi kyau ba, tace, "Ki barshi kawai, rayuwa ce, wata rana sai labari."