← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 47

Sashe 43

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta murtuke fuska tace, "A yaushe?" Yace, "A lokacin da zanyi magana kika ce hakuri ne kin hakura." Ta k'arasa gaban closet tana duba kaya tace, "Sai kuma aka ce don nace haka kayo shiru kada ka bada hakurin." Yace, "Ikon Allah amma kin ce kin hakura." Haushi ya bata ta juyo tace, "To na janye hakuri."

Sati biyu ya daukesu yana binta tana ja mashi aji, idan ya yi magana ta ce a wajenshi ta koya, dakyar ya samu ta hakura suka dinke soyayya suke zubawa babu kama hannun yaro. (Ni kuwa na ce soyayya sai idan Aliyu ya farka tukunna 😅 🤣 😂 saidai suje a basu course).

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu).🥰😘🥰

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 19

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*
*Daga Marubuciyar:*

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)
9. Y'an Mata 500
10. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
11. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
12. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
13. Ba ni da laifi 300
14. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) Free
15. Rumana's Diary

WhatsApp 09169472057

Hafsat tana zaune a ward din tana goge mashi jiki, ta dauki Alk'ur'ani mai girma tana rerawa a cikin kira'arta mai sanyi, Batuul ta shigo dauke da kwandon abinci, bayan Hafsat ta kai aya ta fad'ad'a fuskarta da murmurshi ta ce, "Sannu da zuwa Aunty." Batuul ta ce, "Yauwa, kiyi hakuri fa na barki ke daya, na biya ta gida ne na kai yaran." Daga nan ba ta sake magana ba taja kujera ta zauna.

Ta dubeta ganin ba ta da niyyar zuba abincin kamar ba za ta yi magana sai kuma ta ce, "Ki zuba abincin ki ci mana." Hafsat ta gyad'a kai ta ce, "Zan zuba." Batuul ta d'ago daga danna waya da ta ke yi ta zubawa Aliyu idanu sai kuma ta maida dubanta akan Hafsat kafin ta ce, "Hafsat ba ni kishi da ke, idan ta ni ce zamu zauna lafiya babu fad'a babu hayaniya, duk da a lokacin da na ajiye abincin ban ce maki komai ba amma kin san naki ne sai ki dauka ki zuba. Ke kishiyata ce wannan suna ne wanda bazan sauya ba, ba'a sauya wa tuwo suna, ina da kishin miji na sai dai wannan ba zai saka inyi kishin hauka da ke ba, kishin da na yarda da shi shine wacce ta iya allonta ta wanke, kishi na kyautatawa miji. Hadin kai na kishiyoyi kamar k'awaye wannan ba zan iya ba, sannan ba zan iya kishin hauka da makirci da asiri ba, idan kina min kallon muguwa ne ki bari, ba ni da damuwa idan har ba'a tab'oni ba."

Hafsat ta ce, "Allah ya bamu zaman lafiya." Batuul ta amsa da, "Amin." Mikewa Hafsat tayi ta janyo kwandon ta zuba abincin wanda ya kasance shinkafa da taliya da miya wacce ta ji naman kaza (ka da ku ga na cika cewa shinkafa da taliya with stew, kawai a kwanakin nan ita nike sha'awa kuma na kasa girkawa 🤣 😂 har mamakin kaina nike da kaina 🤣 😂) ta koma ta zauna ta dubi Batuul ta ce, "Bismilllah mu ci." Batuul ta d'ago tana kallonta da mamaki kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, ta girgiza kai ta ce, "Ikon Allah kamar ba yanzu na gama wannan maganar ba, na fad'a maki baki da damuwa da ni amma maganar cewa kishiyoyi suna abu kamar k'awaye ko en uwan jini wannan ba zan iya ba domin na san k'arya nike koda nace zan iya, and ban iya fuska biyu ko pretending ba, Allah ya sani babu mugunta ko cutarwa a zuciyata, ba ni damuwa da aurenki da yayi, kowa da halinta za ta zauna, ina sonshi shima kuma nasan yana sona, na sani dole akwai wacce ya fi so a tsakaninmu wannan kuma abu ne wanda ba zan iya sauyawa ba sai dai zan iya k'ara sona a zuciyarshi. Kishiyoyi suna cin abinci a kwano daya I suppose abu ne mai kyau sai dai ba zan iya ba gaskiya bugu da kari sai da na ci sannan na fito, idan ina son in ci na san inda abincin ya ke."

Hafsat ta gyad'a kai tana mai tsakurar abincin ya yi dadi ba kadan ba, Batuul makura ce a fagen girki koda a wancen lokacin ta sani tunda yana yawan fad'a mata matarshi karshe a fagen girki, akwai aiki sosai a gabanta domin banbancin da ke tsakanin girkinta da girkin Batuul banbancin a bayyane ya ke, dama tana kankaro mutunci ne da girkin Umma.

Memaah k'annansa ne suka shigo, "Aunty Fatima har kin dawo kenan." Batuul ta gyad'a kai ta ce, "Ban jima da dawowa ba." Rumana ta ce, "Sannu Aunty Hafsat kina k'ok'ari tunda ki ka zo asibitin nan ba ki fita, ya kamata ki je gida ki huta." Hafsat ta girgiza kai sanin ba za ta iya ba, "Rumana ba na iya motsawa daga kusa da shi gani nike komai zai iya faruwa, ina tsoron rasashi." Batuul ta dubeta sai dai ba ta ce komai ba har sai da suka fita. Ta ce, "Hafsat ban san abun da yake a zuciyarki ba amma abun da ki ke yi sai yana saka mutane suna min kallon ba na kyautawa, koda ba kiyi da nufi ba, sai suna ganin kamar ban damu da shi ba ne, kije gida ki huta gobe ki dawo sai mu fara raba ayyukan a tsakaninmu." Hafsat ta zaro idanu ta ce, "Na'am." Batuul ta ce, "Ina nufin mu raba kwanakin, idan na tsaya kwana biyu ina wuni dashi ki je ki yi girki ki dawo, nima in yi girki na kwana biyu." Hafsat ta ce, "Amma bazan iya motsawa daga kusa dashi ba..." Batuul ta katseta ta ce, "Kuma idan hakan ya cigaba da faruwa mutane za su yi ta kananun magana a kai don haka yadda na ce haka za'ayi."

Hafsat ta rasa abun da ya ke mata dadi bata matsawa daga kusa dashi but maganar Batuul tana akan hanya, ta gyad'a kai ta ce, "Babu damuwa, ina mai hakuri idan hakan ya b'ata maki rai ban yi da nufi ba." Batuul ta gyad'a kai kawai. Hafsat ta mike ta fita ba domin ranta yaso ba sai bayan ta fita ta nuna babu mota a wajenta ta kira Umma ta turo direba ya daukota ta jira a receptionist har ya zo suka wuce, ba ta jima da tafiya Hajiya Zainab ta zo da mamaki take tambayar Batuul inda Hafsat take. "Na turata gida ta huta, ba bu dadi a barta da aiki ita daya, ya kamata nima na rink'a tsayawa." Ummi tayi murmurshinsu na manya kafin ta ce, "Idan ban da abunki kema kina wahala, ga kula da yara, ga girki, a hakan wuni kike a wajensa, ni babu abun da zan ce maku sai dai Allah ya saka maku da alheri." Batuul ta amsa da, "Amin."

*****

Umma ta yi mamakin dawowar Hafsat duba da tasha ta yi mata magana akan ta dawo gida ta huta amma amsar daya ne that ba za ta isa nisa da shi ba. Hafsat ta gane ma'anar kallon ta zauna akan kujera tana mai cewa, "Aunty Fatima ce ta nemi da in dawo in huta idan ya so sai mu rink'a raba kwana, daya ta zauna da shi, dayar tayi masu girki." Umma ta gyad'a kai ta ce, "Hakan ya yi, ki tashi ki ci abincin ki kwanta ki samu kiyi barci kallo daya mutum zaiyi wa idanunki ya fahimci ba ki samun barcin kirki."

"Yaran fa?" Ta tambaya. Umma ta ce, "Suna gidanku." Ta gane gidan Abba take nufi.

Kadan ta tsakuri abincin ta wuce dakinta tayi wanka ta kure Ac ta kwanta bacci ne ya yi awon gaba da ita, abunka da wacce ta ke da bashin bacci sosai.

Da dare ta kasa barci tunaninsa ya addabi zuciyarta bugu da kari barci da ta yi da rana, dakyar ta samu ta yi barci wajajen karfe biyu na dare.

Washegari tun da safe ta dauki breakfast da Umma ta yi masu, ta wuce da yaran daga nan ta saukesu a makaranta, Batuul kawai ta tarar ta gaishe da ita, "Ina kwana Aunty Fatima?" Batuul ta ce, "Lafiya lau."

Muhammad ya ce, "Ina kwana?" Tace, "Lafiya lau babana."

"Ya mai jiki?"

"Da sauki."

"Allah ya k'ara sauki."

"Amin."

Aliyu ya ce, "Ina kwana?" Ta ce, "Lafiya lau mai gidana." Ta fi sanin Little Aliyu kasancewar Aliyu yana zuwa dashi gidan a wasu lokuttan.

Hafsat ta ajiye breakfast da suka zo dashi, "Ga breakfast Aunty." Batuul ta ce, "Okay, na gode, sannu da k'ok'ari."

Ba su dade ba suka wuce, Batuul ta kalli breakfast din ta janyo wayarta ta kira gidansu ta yi jim sannan tace, "A tafo min da breakfast da alkubus." Ummi ta zo tare da Na'ima, bayan sun gaisa da tambayar mai jiki. "Hafsat fa?" Umma ta tambaya.

Batuul ta ce, "Ba ta jima da zuwa ba, ta kawo breakfast."

Ummi ta gyad'a kai kawai ta ce, "Ki ci." Batuul ta girgiza kai ta ce, "A'a na kira za'a tafo min da alkubus na tashi da kwadayinsa ne." Ummi ta ce, "Okay."

********

Bayan ta sauke yaran ta kaisu class ta juyo ta hadu da Bilkisu kasancewar shima Suleiman a makarantar ya ke, suka gaisa, "Ya wajensu Abdallah mutunen London?" Bilkisu ta ce, "Suna nan lafiya lau. Ya wajen mai jiki?"

"Da sauki."

"Allah ya k'ara sauki."

"Amin."
Chapter 43 · 0% Book details