← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 47

Sashe 47

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A mafi yawan lokutta yana kure wanka ya murza hula dara ya sauko parlour ya hakimce ya ce ta zo ta biyashi wankan da yayi, he will like, 'Nifa koda an yaba sai an biyani kuma bani son biyan kudi, biyan soyayya nike so, a tashi kaina da salon soyayya ta yadda zanji cewa an burgeni inji cewa an faranta min'

Aliyu yana cigaba da samun sauki, abun yana dadewa bai faru ba, yana iya watanni biyu abun bai faruwa sai dai still akwai sauran jini a cikin kansa.

Daga bangaren Batuul ake kawo mashi girki safe, rana da dare, yana matuk'ar son girkin Batuul, Batuul kwararra ce akan fannin girki na gargaji da zamani, tasan hannunta saidai idan bata shiga kitchen ba, tana shiga babu jimawa kamshi mai dadi zai ziyarci falonta.

Duk da Batuul ce take kawo masu girki amma idan Hafsat ta girka mashi yana ci kuma ya yaba domin itama ba daga baya saidai kawai banbancin dake a tsakaninta da Batuul a bayyane yake, Batuul karshe ce.

Ranar suka hadu a bangaren Hafsat har dashi suka shiga kitchen suka had'a kalolin girki dadan-daban suka jera akan dinning table, Batuul ta wuce bangarenta domin tayi wanka ta shirya, Hafsat ta wuce sama, Aliyu ya rigata gama shirya ya sauko kasa yana sanye ne da dakakkiyar shadda dinkin zamani ya murza hula dara da matuk'ar mashi kyau, Batuul ta shigo tana sanye da leshe dinkin bubu ta kashe dauri, ya ware hannuwa ta fad'a jikinsa ya rungumeta tana mai shakar kamshinta ya ce, "Ranki ya dade an sha kyau."

Yayi mutuwar tsaye yana kallon Hafsat da take saukowa cike da tako na salon burgewa tana tako baki daya jikinta yana girgiza, leshe ne a jikinta dinkin straight gown wacce matseta dukkanin wani lungu, sako da tudu na jikinta ya bayyana, ta wrapping kallabi a kanta tayi dauri irin salon saka dararsa wanda yake matuk'ar burgeta.

Idanunsa akan Hafsat dake saukowa daga saman benen yace, "Ranki ya d'ad'e. MATAR ALIYU ta tashi kaina da wannan wankan, MATAR ALIYU makurar kyau ce."

Hafsat ta sakar mashi murmushi ya kama hannunta yana shakar kamshinta ya lumshe idanu ya bude ya ce, "MATAR ALIYU kinyi matuk'ar kyau, kin tashi kaina da samfurin daurin kallabinki."

Ta gyara mashi dara dake a kansa ta ce, "Ka yi kyau abunka, yadda kake daura darar nan yana tashi kaina." Ya juyawa Batuul ya ce, "Mu je ranki ya d'ad'e in kwashi garar girkinki." Suka k'arasa dinning table. Hafsat ta fara zubawa mashi sannan ta zubawa Batuul kafin ta zubawa kanta.

Aliyu yayi lomar farko ya lumshe idanu ya ce, "Ranki ya d'ad'e wannan girki ya tashi kaina, dadi akan dadi, kin iya kin huta ta wajena, ta karya maki hula." Har karya mata hular saida yayi, tayi dariya ta ce, "Na gode, aci dadi lafiya." Hafsat tayi mashi bidiyo tayi mashi tana dariya, Batuul tana tayata. "Santi yake." Batuul ta ce, "Kawo waigi mu saka mashi."

Girkin yayi dadi babu karya sai dai koda mintina biyar ba su yi da fara cin abincin ba abun ya motsa, ya toshe kunnuwa yana mai fasa k'ara, Batuul ta rabe a bango jikinta yana rawar sanyi, tsoro k'arara akan fuskarta, baki daya jikinta rawa.

Hafsat tayi baya tana mai jin tausayinsa tana son matsa kusa dashi saidai idan ta tuna gargadi da yayi mata sai ta fasa, ya jiya kansa ciwo da wuka dake akan teburin, ya watsar da komai a kasa. Yayi luu ya zube a kasa ta tallafosa hankalinta a tashe ta warware kallabinta ta nannade mashi wajen da ita.

Jiki a sanyaye Batuul ta koma parlour ta zube akan kujera tana mai sauke lumfashi yayinda tsoro k'arara ya bayyana akan fuskarta, baki daya jikinta rawa yake, ta dauki waya ta kira likita babu jima suka zo suka gyara mashi hannun tareda k'ara dubashi.

Cikin ikon Allah ya samu sauki, ya tarasu a bangarensu yayi masu nasiha tareda raba kwana kowace kwana biyu-biyu, saida suka fara rabon kwana sannan ta tabbatar da ta yi sabo da shi, saida ta yi kuka a ranar ta rasa abun da yake mata dadi.

Ranar da girkinta ya zagayo ta shiga kitchen ta zage ta girka mashi kalolin girki da ta koya a wajen Umma, tayi mashi amfani da recipe na Umma, ta gama ta jera akan dinning table, ta sha gayu ta kure karshen adaka ta kashe dauri samfurin da ta san yana matuk'ar so ta hakimce a parlour tana jiransa.

Shigowa yayi a gajiye ya ware hannuwa yana mai yaba kyawu da ta yi, "MATAR ALIYU kin kure kyau fa." Ta taka ta shige jikinsa ya rungumeta yana mai sauke ajiyar zuciya, yace, "Kamshinki yana min dadi." Ta ce, "Na gode, mu je kayi wanka mu sauko ka ci abinci na zage nayi maka girki da kaina." Ya ware idanu ya ce, "MATAR ALIYU ta kyauta, na gode, muje in gama MATAR ALIYU sannan in sauko."

Ta make kafad'a tana dure kafafu a kasa kamar karamar yarinya ta ce, "Oh-Oh ni ba za'a b'ata min kwalliya ba, na tab'a lokaci ina yi domin ka yabani." Ya ce, "Kuma na yaba." Ta make kafad'a tace, "Oh-Oh." Saida ya sumbaceta sannan ya ce, "Shikenan muje ki fadi adadin yabon da kike son inyi maki, nayi maki kafin na yab'a kwalliya akan gado, kika sani ko in balle gadon." Ta ware idanu ta ce, "A ina?" Ya nuna mata kugunsa yana juya kugunsa yana nuna mata yadda ake yi, ta juyar da kai, yayi sama da ita zuwa saman bene.

*******

Jalila duniya sabuwa ita da mijinta yawo sukeyi kasashen duniya, dukkanin inda zaije kafarta kafarshi, amma sun zama a London, a can ta haihu ta santalo D'anta namiji kyakykyawa kamar mahaifinsa, Hafsat da Aliyu sun je har London ganin babynsu. Murna a wajen Jalila ba'a magana jin Umma da Mama suna akan hanya, sukayi shagalin suna abunsu.

Hafsat tayi baby, jinsa take kamar gudan jininta, yaron Jalila yaronta ne, yaranta yaran Jalila ne, ba zata tab'a manta halarcin Jalila a gareta ba, ta rikid'a daga k'awa ta koma er uwa.

Muhammad da Little Aliyu suna London karatu tare da Abdallah, har gidan Auntynsu Hisham ta kawosu, bayan sun suna suka tsaya suka zaga gari kafin suka juyo Nigeria, duk da a wajen k'anwar mahaifiyar Hisham yaran suke karatu amma idan zamansu yana a hannun Hafsat, idan suka dawo hutu a gidanta suke sauka, Aliyu ba ya nuna banbanci a tsakaninsu da yaransa.

Hafsat ta zama er gatan Mommy da Ummi. Ummi tana ji da ita sosai, idan sukaje da Aliyu yadda Ummi take mata sai ayi tunanin ita ce diyar gidan ba Aliyu ba. Aliyu dama can na wajen Umma ne, Hafsat har mamaki Hafsat saidai hakan yana da nasaba da aiki da Umma tayi a gidansu da kuma girmamata da yake yi shiyasa take ji dashi. Umma ta zama hajiya ta ajiye fad'a da ta koya a gidan haye ta zage ibada da taimako mabukata da marassa lafiya.

Batuul ta santalo diyarta mace yarinya taci suna Hafsat amma suna kiranta da Sawwama. Murna a wajen Hafsat da Aliyu ba'a magana, anyi shagalin suna anci ansha, yayi kyautar kudade wadanda shi kanshi bai san adadinsu ba. Watanni biyar a tsakani Hafsat ta santalo D'anta namiji mai kamanni da Aliyu sak kamar kobo da kobo, murna a wajen Aliyu da Hafsat ba'a magana, yaro yaci suna Aliyu amma suna kiransa da Haidar. Shekara daya da watanni biyar ta k'ara santalo tagwaye maza wadanda suka ci suna Muhammad da Taheer, sunyi wa Abbi da Abbu (that's mahaifin Batuul) takwarori amma suna wa yaran alkunya da Imam da Shureim.

Haihuwa ta ke yi akai-akai, har en ukku tayi, ta k'ara twins maza, ta yi twins mace da namiji kafin haihuwar ta tsaya mata. Hafsat da Batuul suna zaune lafiya, Aliyu yana cikin kwanciyar hankali a kullum arzikinsa bumkasa yake yana jika matansa da yaransa da naira, babu abun da suka nema suka rasa, jin dadi na duniya yana basu saidai wannan bai saka yayi sakaci da tarbiyyarsu ba, yana matuk'ar k'ok'ari akan iliminsu na addini da na boko. Halinsa na taimako yana nan, kyauta da taimako yake da dukiyarsa kamar bai san zafin nemanta ba, arzikinsa a kullum k'ara habbaka yake.

ALHAMDULILLAH, Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya bani ikon kammala wannan littafi mai suna ZAN BI ZAB'IN UMMANA (Koda Zuciyata Bata So), Ina mika sakon godiya zuwa ga Members na ZAN BI ZAB'IN UMMANA COMMENT SECTION, sharhinku ya bada gudummuwa sosai a wajen bani karsashi na rubuta wannan labari, godiya ta Musamman zuwa ga; Writer Diamond Bhatool, Writer Maryam Annour, Writer Zouley Sabitou (Émilia), Faha'us Chambo, Zahra Graphic (Mamee), Princess Fulani, Mummy Khairat, Hajara BB, Aeesharh, Oum Hafsat, Jamila Shuaibu, Oum Gee, Asmau (Oum Ameer), Mmn Useey, Garba Fatima, Asmau Ih Usman, Hauwau Abdullahi da sauran wanda ban rubuta sunansu, MATAR ALIYU tana godiya. Ina da tabbaci akan kun shaida akan labarin nan is worth reading, thank you so much, Angel is grateful, Allah yabar zumunci, Allah ya bar kauna, Jazakallahulkhair.

Kirkirarren labari ne idan ya yi daidai da rayuwarku arashi ne, ku yi amfani da darussan da ke a ciki, ku watsar da kurakuran da su ke a ciki, wanda wannan littafi ya farantawa rai burina kenan wanda kuma ya b'atawa rai ya yi hakuri.

Sai kuma mun hadu a books da zan yi a nan gaba; *MATAR ALIYU.* (The Upside Of Down) REPOSTING, and then *SUNE SUKA JANYO MIN.* free book REPOSTING OR *ZANE A KAN RUWA.* (Mai Wahalar Gane Kamanni)

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu) marubuciyar

1. Matar Aliyu (The Upside Of Down) 600
2. Mutuwa A Maƙoshi 600
3. Su ne Su ka Janyo Min Book 1 and 2 500
4. Ban Dace Da Shi Ba 600
5. Ban Aikata Ba (Confusion Upon Confusion) 600
6. Mugun Abu Jakada (Her Rude Boss) 600
7. The Choice I Made 600
8. Y'an Mata 500
9. Ya fi Ƙarfin Kai na 600
10. Ya fi Ƙarfin Zuciya ta 600
11. Chasing My heart, A Tsakanin So 600
12. Ba ni da laifi 300
13. Zan bi zab'in Umma na (Koda Zuciyata Ba ta So) free book
14. Rumana's Diary
15. Zane a kan ruwa (mai wahalar gane kamanni)

WhatsApp 09169472057

Taku har kullum Aysher Angel (Matar Aliyu) 💖 💖
Chapter 47 · 0% Book details