← Book details Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 47

Sashe 1

Zan Bi Zabin Umma Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAN BI ZAB'IN UMMANA*
_(Koda Zuciyata Bata So)_

*NA*
*AYSHER ANGEL*

Page 1

*Free Book Ne Daga Farko Har Karshe.*

*Littafin ZAN BI ZAB'IN UMMANA hakkin mallakata ne ban yarda a juya min shi ta kowace sigaba ba tareda izinina ba.*

WhatsApp 09169472057

A Garin Katsina,
Gida ne ginin jar kasa, irin gidajen hayar nan wanda suke dauke da dakuna da yawa amma bandaki da kitchen guda daya, mata ne zaune a tsakar gidan a karkashin iccen mangoro suna hirar duniya. A daya daga cikin dakunan, wata mata ce zaune akan tabarma yayinda wata kyakykyawar budurwa take durkushe a gabanta, matar ta dubeta fuskarta a murtuke tace,
"Hafsat baki isa ki watsa min kasa a idanu ba, nice na haifeki don haka dolenki kibi abun da nike so koda kina so koda baki so, tun wuri ki rabu da Umar, ki saurareni da kyau, ke ba Matar Talaka bace ba, ban yi wahalar nakudarki domin na aurar dake wa talaka ba, nayi kuskuren aure talaka don haka bazan bari ki maimaita wannan kuskuren ba."

Yarinyar wacce ta kira Hafsat ta d'ago da damuwa akan fuskarta tace, "Talauci da arziki duk na Allah ne. Kin ce bazan auri talaka ba, Umma idan kuma na auri mai kudi ya talauce, ko kuma talakan da na bari yayi kudi, mutum bazan tab'a tsallakewa kaddararsa ba...." Umma ta katseta da sauri kamar zata kai mata duka, "Ji min yarinya, ina magana kina maida min saboda kin rainani, magana ta karshe idan Umar yazo ki korashi ko kuma in shayar dake giyar mamaki domin k'aramin aikina ne in fita in koreshi da kaina. Tunda kin nuna baki jin maganata, gwara ki kwana da sanin cewa ba zan aurar dake wa talaka ba, sai mai kudi, mai gida da mota."

Hafsat ta d'ago da damuwa akan fuskarta tace, "Umma mun dade da Umar idan na rabu dashi nayi butulci."

Umma ta fusata ta daka mata tsawa har saida ta razana, "Haka nan auren mai kudi ba haramun bane ba, ki tashi ki bani waje, na dai fad'a maki, ko ki koreshi da kanki ko kuma in fita in korashi da kaina saidai ace ban kyauta ba tunda ba wani ya haife min ke ba, idan kuma yafi maki ni sai in gani. Tunda babu wanda ya tayani nakudarki sai in fita in korashi."

A daidai lokacin wata matashiyar budurwa ta d'aga lalube ta shiga dakin, "Salaam alaikum." A tare suka amsa sallamar da tayi.

Hafsat ta goge hawayen dake akan fuskarta tace,
"Jalila amma kikace saida rana."

Jalila tana mai karantar yanayinsu yayinda ta zauna a gefen tabarma, tace, "Na sauya shawara ne. Umma Ina kwana?"

Umma tace, "Lafiya lau."
Jalila tace, "Umma na sauya shawara sammako zamuyi."

Umma tace, "Babu komai, Allah ya bada sa'a, Allah ya sakawa kasuwancin albarka."

Jalila ta amsa da, "Amin." Tana mamakin abun da ya had'a Hafsat da Umma. Umma ta katse mata tunani, "Jalila ki rink'a fad'awa k'awarki gaskiya, gani take saurayi yafi ni a wajenta."

Hafsat ta rumtse idanu jin furucin da Umma tayi ji take kamar ta fasa ihu, Umma ce take mata wannan shaidar domin kawai tana son ta tursasata rabuwa da Umar domin ta auri mai kudi, kudin da a duniya aka samesu a nan za'a tafi a barsu, tana mata hannunka mai sanda akan mutunci yafi kudi amma da alama Umma tayi nisa bata jin kira.

Umma ta suri buta ta fice, "Sai kun dawo." Bayan fitar Umma, Jalila ta dubeta tace, "Angel baki kyautawa abun da kikeyi..." Hafsat ta katseta. Jalila tace, "Gaskiyar da baki so sai mun fad'a maki."

Hafsat tana sanye ne da atamfa dinkin riga da zani ta bud'e jikkar ghana most go da take saka kayanta a ciki ta zaro dogon hijab har kasa ta zura ta duba fuskarta a madubi tace, "Muje."

Fitowa sukayi, suka gaida matan dake zaune a tsakar gidan, santa ce wadda take dauke da gidajen mutane masu karamin karfi, gidajen dake akan santar mafi akasari kananu ne wasu ginin kasa ko shafe babu, babu kwalta a santar amma mota zata iya shigowa saidai akwai wurin da idan ta kai saidai ta tsaya, shiru santar take kasancewar yara sun tafi makarantar boko.

Wata dalleliyar mota ta tsaya a gabansu, wanda yake ciki ya kurawa Hafsat idanu yana murmurshi yace, "Barka da warhaka en mata." A ransa yana yaba kyawunta mai daukar hankali, fara, mai matsakaicin tsawo.

Ta murtuke fuska tace, "Babu ko'ina." Yayi dariya yace, "Nasan wajen muje in saukeku."

Zuciya ta kawota wuya, a fusace tace, "Tsallake titi zamuyi, kaje ga wasu can suna neman abun hawa sai ka rage masu hanya." Yace, "Muje sai in tsallakar daku." Murmurshi da yake da nacin da ya nuna ji take kamar tayi ihu, taja hannun Jalila suka bar wajen ganin yana binsu ta tsaida kekenapep suka shige.

A kasuwa bayan Jalila ta gama siyayya, suka jingina da wata expensive mota kirar Mercedes Benz suna jiran Kekenapep kasancewar dukkanin wadda zata shigo ko ta fita a cike take.

Jalila tace, "Hafsat mi kikayi wa Umma?" A lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya, tace, "Umma ta buk'aci in rabu da Omar in kawo mata mai kudi that ba zata aurar dani wa talaka ba, tace sai mai gida da mota zata aura min."

Jalila tace, "Ya zakiyi yanzu?"
Hafsat tace, "Tunda ina son farin cikinta zan rabu dashi. Ita kadai nike da a rayuwa, idan na rasata rayuwata zata tarwatse ne, kamar hakane idan nayi kuskuren zaben tumun dare akan miji aure zan hadu da kalubale, saidai ta fiye min shi a rayuwa don haka zan bi zab'inta koda zuciyata bata so."

Ta lumfasa sannan tace, "Zan rabu da Umar in samu mai kudi kamar yadda take so, Umma ta zame min gata a rayuwa, ban da ita da bansan ya rayuwata zatayi ba. Umma ta hadu da kalubale masu yawa a rayuwarta a sanadina, iyayenta basu so aurenta da mahaifina ba saboda halayensa amma soyayya ta makantar da ita ta bujure masu, wannan ya saka sukayi fushi da ita. Tun da ta aureshi take haduwa da bakin ciki da kunci, bayan haihuwata ya gudu ya barta da ni, danginta suka koreta, rayuwa tayi mata juyin waina, haka ta rink'a yawon haya, tayi wankau, tayi sirfau, tayi aikatau a gidaje domin ta inganta rayuwata, dukkanin wani burinta a kaina yake, tasha wahala ta hadu da kalubalen rayuwa domin ganin na cigaba da karatun gaba da secondary. Ta ya zan bujire mata saboda saurayi wanda da girmana ya ganni."

******

Hisham ya bude idanunsa da sauri jin sautin muryarta ta wajen motarsa, kamar mai rad'a yace, "Bilkisu." Ya zafe zuciyarshi yayinda abubuwa da yawa suke dawo mashi a kai akan muryar wacce take magana. Da sauri ya b'alle murfin motar ya zagaya inda suke ya zuba mata idanu saidai idanunta kawai yake gani kasancewar ta rufe fuskarta da niqab.

Hafsat tayi baya da sauri ganinsa tsaye a kanta, ta ware idanu ganin ya durfafo inda take, "Bilkisu."

Ta tsaya cak jin sunan da ya kirata dashi, tayi zaton wata ce a bayanta yake wa magana amma ga mamakinta yana zuwa kusa da ita, ya saka hannu tareda warware niqab dake a fuskarta yana mai furta, "Bilkisu. Ina kika tafi?" Ya ware idanu ganin ba wacce yake tunani bace ba, yayinda maganar da ya fara ta makale mashi a makoshi.

Ji tayi ranta ya b'aci ta fizge niqab dinta dake hannunsa tare da wanka mashi mari, a fusace take tana nunashi tace, "Idan kana cin kasa ka kiyaye ta suri."

Hisham ya dafe kuncinsa yana kallonta ba tareda yace komai ba, ta kai mashi duka a kafa saidai ko gizau baiyi ba, tayi mashi mugun kallo sannan taja hannun Jalila suka dauki hanyar fita daga kasuwar tana mita akan abun da yayi mata.

Jalila tace, "Angel kina da karfin hali har kika mareshi, mutumin da bugu daya zaiyi maki ki rasa inda kanki." Hafsat tayi murmurshi mai ciwo sannan tace, "Dukkanin abun da nayi mashi shine ya janyo kansa."

Jalila tayi dariya sannan tace, "Lokacin da kika mareshi saida bakin glass dake a fuskarsa ya fadi kasa." Hafsat ta tab'e baki, "Raina a b'ace yake ko kallon fuskarsa ban yi ba."
Suna fita bakin titi suka samu Kekenapep, Hafsat tana kwafa tana mita akan abubuwan da suka faru. "Daga ganin mace sai ya k'ura min idanu yana magana yana kallona kamar wanda bai tab'a ganin mace ba, shi kuma wancen har da zare min Niqab yana kirana da sunan da ba sunana ba."

Jalila da neman fad'a tace, "Ayyerh yaga bamu iya tsallake titi bane shiyasa yake so ya tsallakar damu amma kikayi mamu bakin ciki."

Hafsat tayi kwafa tace, "Ina zaune zaki dawo neman wacce zata rakaki kasuwa."

Jalila ta marairaice fuska tace, "Haba k'awata kiyi hakuri, zanyi maki wainar fulawa. Kema ya kamata ki fara sana'a, zama hakanan babu hanyar shigowar kudi babu dadi musamman wa diya mace wacce bata da dan uwa ko uba namiji a kusa da ita wanda zai tallafawa rayuwarta."

"Koda ina so, Umma ba zata bari ba, tace karatu take son inyi, bata son in raba hankalina waje biyu."

A daidai lokacin ne kekenapep ta saukesu a kofar gidansu Jalila, Jalila ta toya masu wainar fulawa suka ci sannan ta fara yanka.

Hafsat ta janyo wayarta ta kira Umar, bata tsaya doguwar gaisuwa ba tace, "Umar idan ka samu lokaci a yau ka zo Ina son ganinka." Daga daya bangaren yace, "Kinyi kewata ne." Ta bi takan maganar da yayi ba tace, "Ina son magana da kai a yau." Ta tsinke kiran ba tareda ta jira amsar da zai bayar ba.

Umar yana, "Hello. Hello. Hello." Yaji shiru yana dubawa yaga ta tsinke kiran, da mamaki yake kallon wayar saidai bai kawo komai a ransa ba, ya saka a ransa watakila network ne.

Jalila ta ajiye yankan da takeyi tace, "Angel mi kike k'ok'arin aikatawa?" Fuskarta dauke da damuwa tace, "Na kirashi yazo in fad'a mashi soyayya a tsakaninmu na k'are, ya rabu dani ya nemi wata. Ita kuma Umma inyi maka albishir da na yarda zan auri mai kudi kamar yadda take so amma akan sharadi guda daya, that zata barni in samu na gari wanda ba ya da damuwa."
Chapter 1 · 0% Book details