← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 93

Sashe 91

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Basuwani jima suna tafiya acikin jirginba suka iso garin na Maiduguri, koda suka sauƙa a airport ɗin tuni suka samu wata mota na jiransu wanda itace zata kaisu har inda zasu, bisa kwatancen baban nata suka iso gaban wani makeken gida wanda aka ƙawata jikinsa da farin fenti, gidane me kyaun gaske yayinda wani tangamemen gate yazama shine ƙofar shiga gidan,   cikin yanayi na mamaki Zieyaderh tafito daga cikin motar, ahankali take ƙarewa gidan kallo, Baban nata ne ya ƙwanƙwasa babban gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani maigadi yaɗan buɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate din tare da ɗan leƙowa, cikin mutuntawa suka gaisa da Malam Garba, nan Malam Garba yace yayi masa iso wajen Hajiya Mama, (Hajiya mama itace mamar Maryama wato mahaifiyar Zieyaderh)
Babu wani jimawa maigadin yace su shigo, koda suka shiga cikin gidan mamakine yasake bayyana akan fuskar zieyaderh don kuwa sosai cikin gidan yayi kyau, ko ina cike yake da shuke shuken flowers masu kyau,  maigadin dakansa yayi musu jagora harzuwa cikin wani haɗaɗɗen falo, wanda da dukkan alama shine babban falon gidan.
Akan kujera suka zauna su dukansu daidai lokacin wata mata wacce aƙalla bazata wuce 30 years ba tafito daga cikin kitchine din dake cikin falon, idanu huɗu sukayi da Ziyada hakan yasa tray ɗin dake riƙe ahannunta ya suɓuce yafaɗi,  kallonta Ziyada tayi cikin yanayi naɗan mamaki, muryar wata ƴar dattijuwar mata da taji abayanta yasata juyawa ta kalli matar, wata ƴar dattijuwace wanda aƙalla bazata wuce  53 years ba, ahankali matar  ke sauƙowa daga kan steps, matar fara ce irin  sol ɗinnan, duk da cewa ta tsufa amma da ka ganta zaka gane cewa  shuwa arab ce, donko hausan dake bakinta ma wani iri ne, 
haɗuwar idanun dattijuwan dana Ziyada yasanya gaba ɗayansu sukaji ƙirjinsu ya buga,  cikin matsanancin mamaki matar wacce ake ƙira da Hajiya Mama ke kallon Malam Garba kana kuma saita dawo da kallonta ga Zieyaderh, wanda ko ba afaɗa mata ba taji ajikinta cewa matar itace kakarta wato uwa ga mahaifiyarta kenan, bazata iya jurewa ba sai kawai tatashi inda taƙarasa da gudu ta faɗa jikin Hajiya Mama, nan tasaki kuka, Aunty Ounnaisa dake tsaye bakin kitchine ganin cewa Ziyada tafaɗa jikin Hajiya Mama yasa taji hawaye sun cika a idanunta, da sauri ta ƙaraso cikin falon inda ta ɗago Ziyada daga jikin Hajiya Mama ta rungumeta, cikin muryar kuka Aunty Ounnaisa tace.
"Koda ba da mahaifinki na ganki ba, tabbas idan naganki zangane cewa kedin jininmu ce, tabbas naji hakan ajikina, naji ajikina cewa kece yarinyar da ƴar uwata ta rasu ta bari,  kece wacce mukayi watsi da rayuwarki, bisa biyewa son zuciya!."
Hawayene suka wanke fuskar Ziyada, duk da cewa batasan wacece Aunty Ounnaisa'n ba, amma taji ƙaunar kyakkyawar matar da kamar ka latsa fatarta jini ya fito tsabar fari da hutu Acikin zuciarta.
Cikin karamci Malam Garba ya gaida Hajiya Mama, inda daganan ya kora musu bayani dakuma nuna musu Ziyada, inda yasanar dasu cewa ƴar Maryama ce, daga Hajiya Mama har Aunty Ounnaisa kuka suke, sosai suke kukan danasanin abun da suka aikata na shariya dakuma halin ko inkula da suka nuna, cikin zazzafan ƙaunar Ziyadan Hajiya Mama tajawota jikinta, hakanan takeji kamar ƴarta Maryama ne agabanta,  kuka sosai Hajiya Mama tayi inda ta roƙi Ziyada akan tayafe musu watsi da ita da sukayi, haka Ziyada tayi kuka sosai, amma na tsananin farincikin ganin dangin mahaifiyarta, nanfa Hajiya Mama ta gabatar mata da Aunty Ounnaisa amatsayin ƙanwar mamanta,  daganan kuma Hajiya Mama ta ƙira dukkan familynta inda tace dasu tanason ganinsu, aikuwa cikin mintuna kaɗan gaba ɗayansu suka hallara ababban falon nata, ita da kanta tagabatar musu da Ziyada, tabbas kamannin Ziyada dana ƴar uwarsu Maryama yayi yawa sosai, kusan kowannensu saida yayi kuka musamman ma Alhaji Ahmad Rufa'e wanda yake shine babba agidan, kuma hamshaƙin mai kuɗine, sosai yayi kukan tunawa da ƴar uwarsa,   awannan rana sosai Ziyada taga gata irin wanda bata taɓa gani ba a iyaka tsawon rayuwarta, gaba ɗaya ƴan uwan mahaifiyarta ta sai nannan suke da ita, kowanne daga cikinsu burinsa shine ya nuna mata tsantsar soyayya da kulawa,  koda yamma yasomayi nan suka fara haraman tafiya don jirgin 6 zasubi sukoma Abuja, sam ƴan uwan mahaifiyar nata basu so haka ba, sunso ace takwana, amma babu yanda suka iya, don Malam Garba yace dasu mijinta bai bata izinin kwana ba, wasu irin tsaraba suka haɗota dashi  mai uban yawa, inda Alhaji Ahmad yace suma zasuzo su  Abujan Insha Allah, Nan Ziyada ta rubuta masa adreshin su,  gaba ɗaya ahalinne suka rakosu zuwa airport saida sukaga tashinsu sannan suka juyo zuwa gida.

Ƙafe 7 daidai acikin garin na Abuja yayi musu,  wata jibgegiyar mota Sooraj ya turo dan a ɗaukesu, daga airport din kaitsaye gida aka wuce dasu, duk yanda Ziyada taso babanta ya bari ya kwana ƙin amincewa yayi, haka tanaji tanagani ya shiga mota driver ya maidashi gida.

Agajiye tayi wanka, koda ta fito daga wankan, kaitsaye jakan makarantarta ta ɗauƙo, nan tashiga haɗa takardun da zata karanta don gobe zasu fara zana waec examination  inda daga ss 2 tayi tsalle zuwa ss3 don zana jarabawan waec kamar yanda Mah Love ɗinta ya buƙata.
Waya suka ɗan taɓa da Nasmah da kuma shukra don suma a ss2 din zasu zana jarabawan ta waec, daganan kuma sai suyi neco da jamb,   akasalance ta aje wayan nata tare da ɗan juyowa, jitayi tafaɗa cikin jikinsa,  idanunta taɗan zaro waje don sam bataji shigowarsa cikin ɗakin ba,  hannayensa yasanya inda ya warware tawel ɗin jikinta, take towel ɗin ya faɗi yayi ƙasa,  ganinta haka naked yasashi jan wani irin dogon numfashi tare da ɗan lumshe idanu, kana ya jawota ya mannata da jikinsa,   kullum ƙara kyau take,  yayinda yakejin skin ɗinta na ƙara laushi like cutting,   ɗan rage tsawonsa yayi tare da ɗaura kansa akan wuyanta,    cikin kasalan daya sauƙar mata lokaci guda tace.
"Mah Love am tired fa."
Saurin ɗago kansa yayi ya dubeta, tare da sakin wani murmushi, laɓɓansa ya cija kana ya riƙe waist dinsa yana kallonta, cikin muryarsa mai ɗauke da aji yace.
"Yaushe kika girma, da har kike ƙoƙarin yi min wayo?."
Dariya tayi harsaida fararen haƙwaranta suka bayyana,  ahankali taɗan karyar da wuyanta gefe cikin salonta na shagwaɓa wanda akoda yaushe ke masifar ƙara mata kyau tace.
"Please É—an kaÉ—an ko?."
Kansa yagirgiza, cikin silent voice É—insa yace.
"A'a dayawa."
Hannunsa ta kama inda ta zagayo ta bayansa, ɗan tsalle tayi tare da ɗalewa saman bayansa, kana ta  ɗaura hannuwanta akan shoulder ɗinsa, cikin jin daɗin samun kanta akan bayansa tace.
"To kaÉ—an yi yawo dani please ko zan dainajin gajiyan."
Wata t-shirt ɗinsa dake aje kan gado ya ɗauka tare da zura mata ajikinta, goyonta yayi da kyau kamar wata ƴar baby haka ya nufi ƙofar fita ɗakin da ita, luf tayi abayansa tare da lumshe idanunta, kaitsaye ƙofar dazai fitar dasu a part ɗinnasu ya buɗe ya fita, da sauri ta buɗe idanunta, ganinsu a falon Oummu yasa tasoma ƙoƙarin sauƙa daga kan bayannasa, amma ina yaƙi bata daman hakan, cikin yanayi naɗan tsoro takawo bakinta daidai saitin kunnensa inda ta ɗana masa cizo,  cikin yanayi na jin zafi yaɗanyi ƙara,  tare da saketa ta duro ƙasa, dariya tashiga yi masa sosai, idanunsa ya zuba mata Musamman ma yanda yaga tayi masifaffen kyau da tana dariyan, kanta yayo da sauri ta soma ja da baya baya hannu yasa zai kamota aguje tanufi ƙofar falonsu, hartakai bakin ƙofar ya cafko hannunta inda ya juyo da ita, azafafe ya mannata ajikinsa tare da ɗaura bakinsa akan nata.
Da sauri Oummu da tun fitowarsu take kallonsu tayi saurin juyawa takoma cikin ɗakinta, don dama tsaye take asama hakan yasa basu ganta ba,  tana shiga ɗaki ta sauƙe ajiyar zuciya, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Gobe goben nan zaku koma gidanku, bazaku ci gaba dayin iskancinku agabana ba,  bansan ma yaushe kuka zama mararsa kunya ba sam!."
Chapter 91 · 0% Book details