← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 93

Sashe 23

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya Shukrah tayi tare da cewa "Wai miye hakan kike dafe da goshi sai kace wanda kika bugi dutse?"

"Ai inajin da dutse da shiÉ—in basu da maraba!" Ziyada tafaÉ—i haka tana mai É—an mulmula goshinta.
Dariya su Nasmah suka sanya.  "Dole zakiji zafi mana, daganinsa ai zaki san ma'abocin yin gym" Shukrah ta faɗi haka tana mai ƙoƙarin murzawa Ziyada goshinta.  Malami ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka nutsu, tare da maida hankalinsu kansa. Kwana biyunnan duk ba atashinsu da wuri yau har 5:30 sannan aka tashesu. 
**
Tana shiga cikin ɗakinta ta soma rage kayan jikinta, banɗaki ta shiga tayo wanka.  Riga da sket ƴan kanti ta sanya sannan taɗan yafa wani ɗan ƙaramin ɗan kwali akanta.   Direct kitchine ta wuce, duk wasu ƴan ƙananan girki yanzu babu abun da bata iyaba.    Indomie ta dafa bawai don tanaso ba saidon yunwan dake damun cikinta.    Gaba ɗaya kwanukan da suka ɗan yi ƙura a kitchine ɗin ta kwashe ta kai gaban sink wankesu tayi tas, sannan tayi mopping kitchine ɗin.   Acikin kitchine ɗin ta zauna taci abincinta,  tana gamawa ta wanke plate ɗin data ɓata.    Zame ɗan kwalinta tayi ta ƙarasa gaban sink, hanu tasa ta tari ruwa ta wanke fuskarta,  tana maiƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin tanufi hanyar fita daga kitchine ɗin, harta jefe ƙafarta na hagu acikin falon, da wani irin ƙarfi taji an jawota cikin kitchine ɗin tare da sanya hanu aka rufe mata baki gam.

(Kucigaba da haƙuri kuna manage lokacin dazan ƙara yawan typing yananan zuwa.
Vote da Comment ɗinku kawai nake buƙata please karkuna bani kunya seriously ina da buƙatar vote ɗinku sosai, because tananne kaɗai zangane kuna enjoying story'n.)

   *VOTE Me On Wattpad*
        @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ !!!*

  *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 20*

Numfashinta ne yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, saboda tsabar tsananin tsoron da ta samu kanta aciki, ƙasa tayi da idanunta, tana me kallon hanun da aka rufe mata bakinta dashi, hanun namiji ta gani, wanda ke ɗauke da kwantattun gargasa da sukayi luf akan farar fatarsa,  jikinta ne ya ɗauki tsuma, wani irin tsoro mai ƙarfi ya ziyarceta,   wani ɗan corridor dake cikin kitchine ɗin ya shiga da ita,  ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi, ba tare da ya sake mata bakinta ba, ya juyo da ita suka zama suna fuskantar juna,   idanunta ta zaro waje tana me sake kallonsa.  Sake mata bakinta yayi, tare da ɗaura hanunsa akan laɓɓansa cikin ƙasa ƙasa da murya yace.
"Shiii!! kada kimin ihu, ina da baƙi a falo ki zauna anan kada ki fito"  yana gama faɗan haka ya saketa,  tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga cikin kitchine ɗin,  bakinta a wangale haka ta bisa da kallo har ya fice, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da jingina bayanta da jikin bango, har acikin zuciyarta tayi bala'in tsorata, duk atunaninta wanine daban yazo saceta,  hanunta ta ɗaura adaidai kan chest ɗinta dake ta bugawa da ƙarfi, aƙalla takusan mintuna 9 ahaka, kafun tasamu ta iya daidaita nutsuwarta, kan wani plastic chair dake cikin kitchine ɗin ta zauna,  tare da kifa kanta akan cinyoyinta. 

Shikuwa Sooraj yana barin kitchine ɗin, komawa cikin falo yayi, wajen  abokan business ɗinsa, da suka kawo masa Ziyara, yana zaunene amma gaba ɗaya hankalinsa naga ƙofar kitchine, sam  bayaso tayi gangancin fitowa,  ba tsoronsa ganinta da zasuyiba, tsoronsa shine wani irin bahagon kallo za suyi masa?  tabbas ba lallai suyi mishi kyakkyawan zato ba, shikuwa ko kaɗan bayason ayi masa irin wannan kallon.  Sunjima suna tattaunawa akan business ɗinsu, kafun daga bisani sukayi masa sallama, har bakin motarsu ya rakasu, shima daga rakiyarsu bai dawo cikin gidanba, motarsa ya shiga ya fice daga gidan gaba ɗaya.

Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan ne yasata takowa saɗaf saɗaf taɗan leƙa cikin falon, ganin ba kowa acikin falon yasa ta sauƙe ajiyar zuciya. Fitowa daga cikin kitchine ɗin tayi ta wuce ɗakinta. 

*MONDAY*

Yau yakasance ranar da zasu fara exam, 8:00 am daidai zasu shiga exam ɗin inda zasu fara da Biology.   Zaune suke akan wani bench su dukansu ukun,   kallon Shukra da Nasmah Ziyada tayi murya asanyaye tace.
"Tun safe ƙirjina yaketa bugawa, wani irin tsoro nakeji, anya zan iya zana exam ɗinnan kuwa?"

Kallonta Shukra tayi tare da É—anyin murmushi.
"Zaki iya mana, ki daure ki ƙarawa kanki confidence, amma ai babu wani wahala"   Shukra tace haka cikin son ƙarawa Ziyada ƙarfin guiwa, shiru sukayi daganan basu sake cewa komai ba. Takwas na cika dai dai suka shiga jarabawa, 1 hour suka ɗauka suna rubuta exam ɗin, cike da jin daɗi  Ziyada ta miƙa booklet ɗinta, sannan tafito daga cikin exams hall ɗin, tsayawa tayi ajikin wata bishiya tare da lumshe kyawawan idanunta, wani nishaɗi takeji acikin ranta saboda tana da yaƙinin cewa zata ci duka tambayoyin da ta amsa.  Su Nasmah ne suka fito nan suka haɗe suka ci gada da hiransu,   kasancewar yau paper biu zasuyi  ƙarfe 10 daidai suka sake shiga wata jarabawan na Islamic.  Suna kammala jarabawan  kowa ya fara haramar komawa gida, tsayawa tayi tare da dafe goshinta, gaba ɗaya ta manta batace da Kamalu driver yazo ɗaukarta da wuri ba,  gashi yanzu sun gama exam kowa na ƙoƙarin ko mawa gida.   Kai tsaye ta nufi babban ƙofar gate ɗin makarantar.   Tana fita daga cikin gate ɗin ta soma kalle kalle, batasan ya zatayi ba don bata da wata mafita, gashi su Shukra sun tafi.  Wata baƙar motace tazo ta tsaya agabanta, hakan yasa ta ɗan ja baya.   Ahankali ya sauƙe glass ɗin windo'wn motar,  kyakkyawar fuskarsa ta bayyana wacce ke ɗauke da murmushi.

Kallonshi tayi tare da sauƙe idanunta ƙasa, tabbas bazata manta shiba shine wanda ta buge kwanaki. 

Murmushi yakumayi tare da buÉ—e murfin motar ya fito, takowa yayi har zuwa inda take, murmushine akan fuskarsa wanda suka bayyana dimples É—insa. "Tsayuwa acikin rana bai kamaceki bafa Æ´an mata" yafaÉ—i haka yana me É—an É—aga kansa ya kalli sararin samaniya.
Ɗago manya manyan eyes ɗinta tayi, tare da sauƙesu akan fuskarsa.  Idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, murmushi yaƙara yi mata tare da cewa.
"Mai kikeyi anan? ba'azo É—aukarki bane?"

Samun kanta tayi ta kaɗa masa kai alamar "Eh"  

"Okay muje na sauƙeƙi agida" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin buɗe mata murfin motar, ɓangaren mai zaman banza.

Saurin kallonsa tayi tare da ɗan matsawa can gefe, sam batajin zata iya shiga motar, ita da batasan kowa ba banda MR. HANDSOME (Sooraj)  yaza ayi ta yarda ta shiga motar wani, kalan ma yaje ya sayar da ita. Abunda tafaɗa acikin ranta kenan.

Ganin alaman cewa bata yarda dashi bane yasanyashi sake ɗanyin murmushi cike da son ya gamsar da ita yace.  "Calm down dear, i will not hurt you, trust me!" 

Yanzu kam salon kallon da tayi masa, yana ɗauke ne da ma'anoni masu yawa. Horn ɗin motar da taji abayanta ne yasata waigawa, ai kuwa Kamalu driver ta hango acikin mota, da sauri ta juya ta nufeshi, buɗe murfin motar tayi ta shiga,  ƙarasowa yayi har jikin motar,  sannan yayi knocking glass ɗin window, Kamalu driver ne yayi ƙasa da glass ɗin tare da ɗan dubansa,  shikuwa idanunsa akan kyakkyawar fuskarta yake, cikin ƙasa da murya yace. "Yace kin ƙi yarda dani ko? ba damuwa ki kulamin da kanki!" yana gama faɗan haka ya juya ya nufi wajen motarsa. 

Tafiya suke amma gaba É—aya tunaninta yana ga maganan da ya gaya mata "Kikulamin da kanki!" mai hakan yake nufi kenan? tambayar da take ta yiwa kanta kenan gaba É—aya kanta ya kulle, ahaka har suka isa gida.
Chapter 23 · 0% Book details