← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 93

Sashe 5

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaunar da ita sukayi agabansu, yayinda suka sanya ta kwaye musu cinyoyinta,  da ƙarfin gaske suka shiga durza mata ƙwaɓeɓɓen lallen ajikinta, hatta fuskarta saida suka mulke mata shi da lalle,   itadai ganin abun take awani baƙon yanayi, saboda tasan agarin nasu  idan za'awa mace aurene kawai ake yi mata haka,  suna gama shafa mata lallen sukace taje ta wanke,  wani irin daɗine yaziyarci zuciyarta, domin albarkacin wannan lallen da suka shafa mata yasa zatayi wanka, bata mantawa rabonta da wanka yau sati guda kenan, dokace mai zaman kanta Inna Ma'u takafa mata akan cewa duk randa tayi wanka, bazata sake yi ba sai bayan wani satin, ruwa takandama abaho tayi bayinsu, alokacin da tacire kayanta tasoma watsawa jikinta ruwa, saida ta sauƙe wasu lafiyayyun ajiyar zuciya harsau uku, saboda wani irin sanyin daɗi daya ratsata, dama ita tuncan haka nan Allah yayita, tanada tsananin sonyin wanka, amma kuma bata samu tanayi saboda uƙubar Inna Ma'u.  

Inna Ma'u kuwa masifa ta rufe ƙawayennata dashi wai akan mai zasu kwaɓa lalle su shafawa Ziyada.  Zulai ce tagyara zama haɗe da turo ɗaurin ɗankwalinta gaba.    "Wallahi yanzu na tabbatar baki da wayo Ma'u, kinga wannan lallen damuka shafa mata, shizai sanya jikinta yaƙara kyau, hasken fatarta yasake fitowa, kinsan yarinyar shegiya ɗanbanzan kyaune da ita, to kinga yanzu zata ƙara kyau akan nada, idan Tsoho Ɗan Dashe kuwa yaganta, saiya ƙara susucewa akanta, kinga ke kuwa kinsamu hanyar da zaki amshe masa ƴan kuɗaɗe kice kuɗin gyaran jiki, ai abirni haka akeyi kinsan nifa nayi zaman birni"

Shewa Inna Ma'u tasanya haɗe da bawa Zulai hanu suka tafa, cike dajin daɗi tace "Wallahi shiyasa nake mugun sonki Zulai, kinsan kan duniya,  aikuwa ayau yau saina karɓi wani abu daga wajensa"     sake tafawa Inna Ma'u da Zulai sukayi daidai lokacin Ziyada tafito daga wanka, zanine ɗaure aƙirjinta kanta gaba ɗaya yajiƙe yake da ruwa, tana shigewa ɗakinta, Zulai tadawo da kallonta ga Inna Ma'u cike da mamaki tace "Wai Ma'u dama haka wannan yarinyar keda diri da kyau? nikuwa anya basu haɗa iri da larabawa ba?"

Taɓe baki Inna Ma'u tayi, domin ita aduniyarta babu abun datafi tsana kamar taji anyabi Ziyada,  "To wama yasanine tsinannu, ai tunda nasamu nagama da uwarta itama yarinyar bawuya zata bani ba, wannan shegen idanun nasu masu kama dana aljanu yana ɗaya daga cikin abun dayasa na mugun tsanarsu, gashi komai na halittar uwarta ta kwashe!" Inna Ma'u tafaɗi haka cike da baƙin ciki.

"Aikuwa Ma'u kinyi farar dabara da kika haɗa auren ta da Ɗan Dashe, kinga zata ƙare rayuwarta cikin ƙasƙanci, kinsansa baya riƙe aure, duk da yagama tsofewa, amma baijirayi kansa ba,  dakin tsaya kuwa kina nan zakiga wani sarki ko senata sunzo neman aurenta"  cewar wata daga cikin ƙawayen Inna Ma'un, wato Lantana.

"Cab iye bakinki Lantana, ina darai kam ƙaryane wani mai arziki ya raɓi Ziyada, sam hakan bamai yiwuwa bane, koda kuwa zanyi yawone tsirara na gwammace nayi, dana bar jinin Maryama ta auri wani mai kuɗi, nama kashe maciji bansare kansaba kenan" Faɗar Inna Ma'u.  Dariya suka sanya sudukansu, yayinda ƙawayennata sukacigaba da fonfata....

Ziyada kuwa tsabar taji daɗin jikinta da tayi wanka tana kwanciya kawai sai bacci ɓarawo ya saceta...

Washe Gari.

*** Tun tashinta yau takejin faɗuwar gaba, babban abun daya ɗaure kanta shine, ƴan uwan mahaifinta da tagani sun cika gidan, da'alama dai kamar biki za'ayi agidannasu bata kuma san bikin waye za'ayi  ba.   Tazo wucewa zata shiga banɗaki  wata ƴar addar babanta  ke cewa "Amarya Amarya bakya laifi Amarya agidan Tsohon najadu"

Jitayi gabanta yafaɗi cike da mamaki tajuyo tana kallon Hajara wacce tafaɗi maganar, bakinta na rawa tace.   "Yaya Hajara wacece amaryan?"

Harara Hajara ta watsa mata domin dama tun can su bawani sonta suke ba.   "Wace amarya kuwa inbanda ke, ko baki da labarin cewa gobe za'a ɗaura miki aure da tsohon najadu?" Dariya Hajara tasanya haɗe dacigaba dacewa "Abun yayifa yarinya ta auri wanda yagirmi ubanta" sai takuma sake bushewa da dariya.

Jikin Ziyada ne yasoma rawa, lokaci guda taji cikinta yayi wani irin murɗawa atsorace ta ƙaraso gaban Hajara tazube aƙasa, murya na rawa tace  "Dan Allah Adda Hajara kifaɗamin gaskiya, auren waye za'ayi?"

Kallon kinma rainamin wayo Hajara tashiga yiwa Ziyada  ahasale tace..   "Bansaniba munafuka, waye baisan cewa kema son auren kikeba? dama ai kowa yasancewa ke tsohuwar hanuce, wayasanima koshima Tsohon najadun ya ɗana"  

Kuka Ziyada ta fashe dashi da gudu ta tashi tanufi É—akin Inna Ma'u, tana shiga ta zube agaban Inna Ma'u dake tsaye, cikin kuka tace.
"Dan Allah Inna Ma'u kimin rai, kifaÉ—amin cewa maganar da Adda Hajara kefaÉ—i bagaskiya bane, wai dagaske aurena za'ayi, kuma É—an dashe zan aura?"

Wata uwar tsuka Inna Ma'u taja haÉ—e da É—auko ashar ta bankawa Ziyada cike da takaici tace

"To idan bakiyi aure ba kwaɗaki zamuyi mucinye?   inbanda ƙaddarama me Ɗan Dashe zaiyi dake, shima dai dayake tsohon maye ne shiyasa, amma bacin haka banga maiyagani awannan busheshshen jikinnaki ba, da Allah nitashi kibani waje, kuma aurenki da ɗan dashe babu fashi, gobe iwar haka kinzama matarsa"  

Kuka Ziyada tashiga rerawa hadda majina tana roƙon Inna Ma'u, amma Ina Inna Ma'u haka ta murje idanunta.

Komawa cikin ɗakinta tayi hankalinta amatuƙar tashe, zama tayi daɓas aƙasa haɗe da ɗauko wani mayafin mamanta ta rungumeshi ƙam acikin ƙirjinta, kuka take tamkar zararriya...
 
"Wayyo Mamana kinga rashinki abundaya jawomin, Ya Allah kataimakeni kakawomin ɗauki!" Ziyada tafaɗi haka cikin matsanancin kuka.  Tsabar kukan da Ziyada tayi harsaida muryarta ta dashe.     Tana zaune aɗaki taji muryan Babanta, a tsakar gidan nasu, da sauri ta ɗaga labulen ɗakin tana leƙensa, sosai takejin tsananin tausayin mahaifinnata, duk da cewa tana da ƙananun shekaru amma hakan baisa takasa fahimtan cewa wasu abubuwan dayake aikatawa ba acikin hayyacinsa yakeyinsu ba,    ganin yafice daga cikin gidanne, yasa tafaki idon mutane tarufa masa baya, zaune ta iskeshi akan ɗan dakalin dake ƙofar gidannasu.  Tsugunnawa tayi agabansa  Cikin da shashshiyar muryarta da ta ƙoshi da kuka tace

"Baba!" 

É—agowa yayi ya kalleta, batare da ya amsa mata ba.

"Dan Allah Baba kataimakeni, wallahi banason ɗan dashe!"  tafaɗi haka hawaye suna mai kwaranya daga cikin idanunta.

Shiru Malam Garba yayi cike da tausayin ƴartasa, lokaci guda kuwa ya zabura kamar anjona masa shocking. 

"Uban maikikeyi anan?" yatambayeta atsawace. 

Jikintane yasoma rawa, yayinda kuka yasakecin ƙarfinta,  cikin kukan tace.  "Dan Allah Baba kaceci rayuwata, katunafa ni amana ce Allah yabaka, dan Allah Karka bari acutar da rayuwata!!"

Wata uwar tsawa yakuma doka mata, haÉ—e da rufe idanunsa yakorata gida.

Haka takoma gida tana kuka maicin rai, lallai tasake tabbatarwa da kanta cewa ita cikakkiyar marar gata ce, zama tayi akan  tabarmarta haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, lokaci guda taji zuciyarta tayi wani irin bushewa, yayinda wani tunani yaɗarsu acikin ranta...

(Menene ra'ayinku akan auren ZIYADA da Tsoho ÆŠan Dashe? Bazan cigaba ba harsai naga ruwan comment da vote É—inku, dama nace yawan comment yawan typing.)

*✅OTE ME ON WATTPAD*
           @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

       *CHAPTER 5*

Wanene SOORAJ?
Chapter 5 · 0% Book details