← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 93

Sashe 65

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin jikinta ya zame ya faɗi ƙasa,  cikin tsautsayi ƙafanta ya bugi jikin gado, suuuuu haka tatafi zata faɗi, cikin abun da baiwuce 1 second ba ya ƙaraso cikin ɗakin, da sauri yaƙarasa tare da sanya duka hannayensa biyu ya tarota, inda ya zube ƙasa kan guiwowinsa, cikin tsananin tsautsayin dake jansa ya sauƙe idanunsa akan naked pure white breast ɗinta, da sauri ya rumtse idanunsa yayinda lokaci guda yaji tamkar andoka masa guduma atsakiyar kansa,  gaba ɗaya jikinsa ne ya soma ɓari,
Ita kuwa Zieyaderh tamkar wata matacciya haka gaba ɗaya jikinta ya sandare, yayinda ta kulle idanunta ƙaƙam, cikin tsananin tsoron dake ɗawainiya da zuciyarta haɗi da fusgewar numfashi ta ɗan buɗe idanunta kaɗan, wani irin ƙara tasake sakamakon ganin fuskarsa da tayi, cikin tsananin ruɗewa haɗi da zabura ta tashi daga jikinsa,
aruɗe ta soma ƙoƙarin neman towel ɗinta daya faɗi, don suturce jikinta, irin yanayin ruɗewan da tayi yasanya takasa ganin towel ɗin, wanda kuma yashe yake agabanta,  cikin hanzari ta jawo blanket ɗin dake kan gadon na Oummu ta rufe gaba ɗaya jikinta dashi, zamewa ƙasa tayi tare da sakin wani irin marayan kuka wanda ke ɗauke da tsananin takaici da kuma haushin kanta, wata fitinanniyar kunyace gaba ɗaya ta rufeta.

Jin diran sautin kukanta da yayi acikin kunnuwansa, yasanyashi miƙewa daga durƙuson dayayi, cikin dauriya dason kawar da zazzafan ciwon kan daya kawo maza cafka lokaci guda, ya juya tare da nufan hanyar barin ɗakin.
Kasancewar har yanzu idanunsa arufe suke, hakan yasanya sam baikula da Oummu da kuma Aunty Muhibbat dake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin ba,
jin cewa yayi karo da mutum ne yasanyashi saurin buɗe idanunsa, nan ya sauƙe su akan fuskar Oummu dake tsaye tana kallonsa,  kansa ya sunkuyar ƙasa tare da raɓawa ta gefenta zai wuce, cike da mamakin yanda idanunsa sukai jajur Oummu tace.
"Kajirani a falon ƙasa".

Kansa kawai ya jinjina mata alaman. "To"
Ahankali yashiga taka matattakalan da zai sadasa da falon ƙasan. 

Oummu kuwa dubanta takai ga Aunty Muhibbat,  gane abun da Oummun ke nufi yasanya Aunty Muhibbat murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta shiga da sauri, don ta duba Zieyaderh wacce sautin kukanta ke ratsa kunnuwansu.
Oummu kuwa juyawa tayi tare da fasa shiga ɗakin, kaitsaye tanufi matattakala don sauƙa ƙasa.

Da auri Aunty Muhibbat ta ƙaraso inda Zieyaderh'n ke zaune, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya acikin blanket tana kuka.
Kallon towel ɗin dake ƙasa Aunty Muhibbat tayi tare da sakin murmushi, cikin kulawa ta zauna akan gado tare da sanya hannu ta dafa kafaɗa Zieyaderh.

"Jikinne har yanzu?"  ta tambaya tana me ƙoƙarin jawota ta zaunar da ita akan gadon Oummu.

Jin muryar Aunty Muhibbat acikin kunnuwanta, yasanyata sake ɓoye kanta acikin blanket, tare da ƙara sautin kukanta.

Still murmushi Aunty Muhibbat tayi cikin rarrashi tace.
"Kukan ya isa haka, ko so kike kanki yayi miki ciwo? maza  tashi ki sa kayanki kinji, ko SOORAJ yayi miki wani abune?" Aunty Muhibbat ta tambaya.

Cikin sheshsheƙan kuka tagirgiza kanta alaman.
"A'a"

Murmushi Aunty Muhibbat tayi tare da cewa.
"To tashi kisa kayanki, ko so kike kowa yazo yana ganinki ba kaya?"

Cikin nutsuwa Oummu ta kai dubanta garesa, murya asanyaye ta ƙira sunanshi.
Amsa mata kawai yayi batare daya É—ago kansa ya dubeta ba.

Cikin kulawa ta gyara zamanta tare da cewa.
"Duk da wannan bashine karo na farko da muka fara yi maka aure ba, amma inaso kasancewa wannan auren daban yake da sauran,  bandamu ba koda zakaji cewa hakan da mukayi rashin kyautawa ne agareka, saidai inason kasan cewa ban taɓajin ina yimaka sha'awar rayuwar aure da wata mace ba kamar Zieyaderh, 
kamar yanda kaine ka kawota kakuma riƙeta tunkan musan da ita, ayanzuma haka nakeso kacigaba da riƙeta,  kai ba ƙaramin yaro bane Sooraj,  kamar yanda na gargaɗeka abaya akan sakin aure, to awannan karon ma zan gargaɗeka, Wallahi! Wallahi!! Sooraj idan har ka saki yarinyar nan Zieyaderh kamar yanda kake sakin sauran matan da muke aura ma to tabbas saina tsinemaka!!"

Amatuƙar razane Sooraj yaɗago kansa da idanunsa wanda sukayi jajur ya kalli mahaifiyar tasa, gani yayi  sam babu alamar wasa akan fuskarta,  sake gyara zama Oummu tayi tare da cewa.

"Kada kaɗauki maganata amazaunin wasa,  idan kuma kace bahaka ba lallai zan shayar dakai ruwan mamaki"
Miƙewa tsaye tayi tare da ɗan soma tattakawa har takai  bakin steps taɗan tsaya tare da juyowa, dubansa tayi kana tace.

"Bazan baka ƴar mutane katafi da ita gidanka ba, dole anan zaku zauna, saboda haka anjima za'a kai maka amaryarka, cikin part ɗinka dake gidannan, sannan kuma Wallahi idan ka cutar da ita ban yafe maka ba!"  Tana gama faɗin haka ta juya tare da soma haura steps ɗin.

Ahankali Sooraj yaɗago idanunsa wanda suka zama tamkar garwashin wuta yabi bayan mahaifiyar tasa da kallo, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da lumshe kyawawan idanunsa,  jiki asaluɓe haka ya tashi ya bar cikin falon.

Wani irin haɗaɗɗen lace purpule colour mai taushi wanda yaji ɗinkin riga da sket ta sanya, sosai kayan ya zauna ɗas ajikinta, inda farar fatarta ta sake bayyana acikin purpule colour lace ɗin,  tsayawa ajikin madubi tayi tare da duban kanta, wani irin kunyane ya kamata sakamakon ganin yanda gaba ɗaya rabin ƙirjinta ya bayyana ta saman wuyar rigar, rumtse idanunta tayi ayayinda taji tsikar jikinta na tashi, sakamakon tunowa da yanda hannayensa suka sauƙa akan naked skin ɗinta da tayi, da sauri ta sanya hannu ta rufe fuskarta, wani irin haushi da kunyan kanta takeji,  turo ƙofar ɗakin da akayine ya sanyata shiga cikin nutsuwarta.

Aunty Muhibbat da Bilkh ne suka shigo, ganin yanda tsadadden leshin ya zauna ajikin Zieyaderh yayi mata kyau, yasanya Aunty Muhibbat sakin murmushi tare da cewa.
"Masha Allah!"

Zama tayi akan stull ɗin mirror yayinda Bilkh tashiga aikin tsantsara mata kwalliya akan kyakkyawan fuskarta, duk da  cewa bawani uban kwalliya sosai akayi mata ba, amma sosai
tayi kyau,  ɗauri mai kyau Bilkh tayi mata tare da yafa mata wani  babban mayafi ajikinta wanda yake purpule colour marar nauyi,   sosai Zieyaderh tayi kyau irin mai ɗaukar hankalin nan,  yayinda oil lipstick ɗin da aka shafa mata akan lips ɗinta keta shinning. 

Sooraj kuwa yana fita daga cikin falon na Oummu kai tsaye gaba É—aya gidan ya bari inda ya wuce night club, can yaje suka haÉ—e da Mas'oud.

Ƙarfe 8 daidai Aunty Muhibbat ta kamo hannun Zieyaderh inda ta ƙarasa da ita har gaban Oummu da ke zaune akan kujera.

Hannun Zieyaderh Oummu ta kamo cike da ƙaunar biyayya irin na yarinyar tace.
"Haƙiƙa kamar ƴata dana haifa ta cikina haka nakejinki Zieyaderh, saboda haka zanyi miki duk wani abu irin wanda uwa mahaifiya keyiwa ƴarta".

ÆŠan numfasawa Oummu tayi haÉ—e da cigaba da cewa.

"Idan akace miki zaman aure ba'ana nufin zaman wasa bane, zaman aure bayana nufin zamane da zaki zauna kiyi abun da kikeso ko kuma kiyi duk abun da kikaga dama ba, aduk sanda mace tayi aure to tana zaune ne aƙarƙashin mijinta akuma ƙasan ikonsa, haƙiƙa aure wani babban sinadarin rufin asirine ga kowacce ƴa mace, aure yana ƙarawa mace ƙima da daraja sosai,  sannan kuma idan kikaji ance miki zaman aure bawai yana nufin kullum zaman daɗi akeyi ba, kamar yanda harshe da haƙori suke saɓawa awasu lokutan haka ma mata da miji ke saɓawa, wani lokaci harma fiye da haka, saboda haka dole saikinyi haƙuri kin kuma jure daɗi da rashinsa kafun zaman aurenki yayi kyau, sannanne kuma zakici riba,  Mijinki tamkar Uba yake agareki saboda haka koda wasa karkiyi ƙoƙarin taka maganarsa, idan yace kiyi koda bakyaso kiyi matuƙar bai saɓawa addini ba, kada ki taɓa tunanin ɗaga muryarki sama akan ta mijinki, sannan kada kitaɓa sanya masa baki idan yana magana, mace tagari mai nutsuwa,hankali, da kuma ilimi bata taɓa ɗaga muryarta sama akan muryar mijinta, sannan kuma bata taɓa tanka masa idan yana magana harsai ya gama,  sannan macen da tasan kanta itace macen da ako yaushe take tausasa zuciyar mijinta, idan yana fushi ta rarrashesa, idan tayi masa laifi ta basa haƙuri, haka kuma koda shine yayi mata laifi amma idanunsa suka rufe yake ganin kamar laifinta ne takan kwantar da kanta ƙasa ta bashi haƙuri,   zanji daɗi matuƙa idan kika zamo mace tagari acikin gidan aurenki"
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da dafa kafaɗan Zieyaderh wacce ke aikin zubar da hawaye, cikin kulawa ta sake cewa.

"Nasan babu soyayya atsakaninki da Sooraj amma har acikin raina ina fata da kwaɗayin ganin ɗorewar zamanku,  kada kice don bakyasonshi zaki ƙuntata masa, haka kuma kada kice don baya sonki zaki ƙuntata masa, kada kice don bakwason juna komai ya umarceki da yi bazakiyi ba, kisani dun wani abu dazakiyi masa wanda yakasance ba daidai ba to Allah Bazai barki ba saiya kamaki da laifi, sannan mala'iku zasu rubutamiki zunubi akan duk abun da kika aikata masa wanda yake ba daidai ba, kiyi haƙuri kizauna dashi da daɗi ko babu, sannan kiriƙe muku sirrinku koda wasa kada kitaɓa barin wani yaji sirrinku, kizama mai haƙuri akullum akuma koda yaushe insha Allah Allah Zai zama gatanki ako ina!"

Kuka me ƙarfine ya ƙwacewa Zieyaderh hakan yasa ta kifa kanta ajikin Oummu tashiga rera kukanta, itama Oummu hawayene suka cika idanunta amma saita shanye tare da sakin murmushi, hannu tasanya ta ɗago Zieyaderh tare da share mata hawaye, cikin son ƙarfafa mata guiwa tace.
"Allah yamiki Albarka kema yabaki Æ´aÆ´a masu biyayya!"
Chapter 65 · 0% Book details