Sashe 27
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu.  Har saida sukayi nisa da gidan kafun yaɗan rage gudun motar, kallonta yayi tare da cewa. "Inaso daga yanzu ki fara amsa sunan ƙanwata, SOORAJ baida lafiya yana asibiti yanzu haka, nasan yana da buƙatar kulawanki adaidai wannan lokacin, please Dan Allah Ziyada ki kula da Sooraj, shiɗin mai rauni ne akowani ɓangare, kulawarki kaɗai yake da buƙata"
Ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, yayinda idanunta suka cicciko da ƙwalla, damuwa ƙarara ta bayyana akan fuskarta, duk da batasan asalin sunansa ba , amma jikinta ya bata cewa SOORAJ shine me taimakonta. Har suka isa babban asibitin bata sake cewa komai ba, saidai gaba ɗaya bata da natsuwa. Haka suka shiga cikin asibitin jiki asanyaye, direct wani ɗan ɗaki suka nufa, suna shiga Mas'oud ya durƙusa tare da sake gaishe da su Abba da Umma, Abba ne kaɗai ya iya ƙarfin halin amsawa domin Ummu kam Kuka take har yanzu, cike da ladabi Ziyada ta durƙusa har ƙasa ta gaidasu,  Abba ya amsa yana me kallonta, sai alokacin Ummu dake kuka ta ɗago kanta ta kalli Ziyada.  Ganin irin kallon da Ummu keyiwa Ziyada yasa Mas'oud cewa.
 "Amm Abba dama wannan ƙanwatace ƴar Baffana ne dake Sokoto, tana karatune anan, sannan kuma suna da kyakkyawan alaƙa tsakaninta da Sooraj, shine nace mai zaihana tazo tana tayaku kula dashi tunda yanzu sunyi hutun makaranta" Yaƙare maganar yana ɗan sosa bayan kanshi, domin shi kansa yasan ya shiryota.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa "Tabbas hakan da kayi ka kyauta Mas'oud, domin dama kaga zaman Ummu'nku anan bazai yi wuba, saboda tunda tazo kuka take, nikuma banason kukannan!" Abba yafaɗi haka cike da damuwa.
Ɗan ɗagowa Ziyada tayi ta kalli wacce ake ƙira da Ummu, tsananin kaman da tagani na me taimako akan fuskar matar shiya sanya tayi tunanin ko mahaifiyarsa ce, to amma idan da yana da iyaye aida tasan bazai zauna agidansa shi kaɗai ba, dole ne zai zamana iyayensa suna tare dashi.
Kallon Ziyada Ummu tayi sosai, wani tunanine yake ɗarsuwa acikin ranta, bazatace bata yarda da maganganun da Mas'oud ya faɗa ba, amma ita ta haifi Sooraj tasan kusan gaba ɗaya halayyarsa, mutumin da bayason mu'amala dako wacce irin mace yau shine za'ace wai akwai kyakkyawar alaƙa atsakaninshi da wata?.
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
     *SOORAJ !!!*
  *Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
      *WATTPAD*
  @fatymasardauna
#romance
     *Chapter 23*
Abba da Mas'oud ne suka tashi suka fice daga cikin ɗakin, kasancewar alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba. Ummu ne tafito daga toilet ɗin dayake cikin ɗakin, fuska da hannayenta duk ruwa da'alama alwala tayi.
Kallon Ziyada dake zaune jigum tayi.  "Jekiyi alwala" Ummu tafaÉ—a tana mai Æ™oÆ™arin shimfuÉ—a darduma akan tiles. Sumu sumu haka ta wuce toilet É—in ta É—auro alwala, hanu tasanya acikin hijab É—in dake jikinta, ta zaro É—an kwalin dake kanta, shimfiÉ—awa tayi akan tiles, sannan ta hau tare da daidaita tsayuwarta, akan É—an kwalin ta gabatar da sallan Magriba, ko da ta idar da sallan, samun kanta tayi dayin shiru, tare da jingina kanta da jikin bango, gaba É—aya jin zuciyarta take babu daÉ—i, babu wani abu da takeson gani sama da Helper É—inta, sosai hankalinta yake atashe, sannan gefe guda kuma, ga kukan da taga mahaifiyar Sooraj É—in nayi yasake É—aga mata hankali.Â
Dukansu daga ita har Ummu babu wacce tatashi daga kan abun sallanta, har aka ƙira sallan isha,  baga Ummu kaɗai ba hatta Ziyada saida tasanya Sooraj cikin addu'anta.  Ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin kanta take, aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.  Alh.Mansur ne dakuma Mas'oud, Mas'oud ne ya aje basket ɗin dake hanunsa, tare da kai dubansa gareta.
"Ziyada ki zubawa Ummu abinci taci, kema ki ɗebi naki kici, zuwa anjima likitotin sun tabbatar mana da cewa zamu samu ganinsa!" Mas'oud yaƙare maganar cike da ɗan yanayi na damuwa.  Alh.Mansur kuwa kasa ma cewa komai yayi, zama kawai yayi akusa da Ummu tare dayin shiru.
Ɗaukan basket ɗin Ziyada tayi tare da zaro wasu plate, kulan dake cikin basket ɗin ta buɗe tare da sanya spoon ta zuba lafiyayyar jalop rice wacce taji bushashshen kifi acikin plate ɗin. Cike da ladabi ta ƙarasa gaban Ummu, cikin muryarta dake rawa tace. "Ummu ga abinci"
Kai Ummu tagirgiza cike da damuwa tace.
"Banajin zan iya cin abinci batare da na sanya É—ana a idanuna ba, kici kawai!" gaba É—aya muryar Ummu rauni kawai take bayyanawa.Â
Hanun Ummu Alh.Mansur ya kamo, cike da tsananin so da kuma nuna kulawa ga matartasa yace.  "Ki kwantar da hankalinki Sulaimiyya, Isha ALLAH Sooraj zai samu lafiya, addu'an mu kawai yake da buƙata bakomaiba, kibar kukannan haka kuka banaki bane."  Kallon Ziyada yayi tare da cewa.
"MiÆ™omin abincin nan na bata"   karÉ“an plate É—in abincin Abba yayi yashiga lallaÉ“a Hajiya Sulaimiyya akan taci, amma gaba É—aya ta daburce taÆ™i ci, hawayene kawai ke silalowa daga cikin idanunta, shima kanshi Abban Æ™arfin hali kawai yake amma damuwane ninke aÆ™asan ranshi.Â
Gaba É—aya itama Ziyada kasa cin abincin tayi, lomanta uku ta ture plate É—in abincin gefe, ji tayi ko kallon abincin batasonyi, hawayene suka ziraro daga cikin idanunta, da sauri tasanya gefen hijabinta ta share, tausayin halin da taga Iyayensa aciki take, musamman yanda taga hawayen mahaifiyarsa ya kasa daina zuba, jitayi gaba É—aya zuciyarta ta karye..Â
Da ƙyar Abba yasamu Ummu taci 4 spoon na abincin.  Dr.Mohd ne dakanshi turo ƙofar ɗakin ya shigo.  Cike da tausayawa ya dubi dukkaninsu, da sauri Alh.Mansur yataso daga zaunen da yake yana cewa.
"Dr.Mohd ya dai, akwai wani cigaba ko kanaga kawai gobe mu wuce Germany É—in?"Â Â Yanayin yanda Alh.Mansur yayi maganan kaÉ—ai ya isa sanya zuciyar mai sauraro karyewa, domin kuwa kallo É—aya zakayi masa kasan baya cikin wata nutsuwa, sosai rashin lafiyar Sooraj É—in ke damunshi.Â
Ajiyar Zuciya Dr.Mohd yayi tare da kama hanun Alh. Mansur suka fice daga cikin ɗakin, ganin haka yasa Ummu fashewa da kuka, domin atunaninta wani abunne ya kuma sake faruwa, Mas'oud ne yayi ƙarfin halin fara rarrashinta.
"Calm down Alh.Mansur kazauna!" Dr.Mohd yafaÉ—i haka akaro na uku kenan, domin kuwa tun É—azu yaketa yiwa Alh.Mansur É—in tayin wajen zama, amma saboda ruÉ—un da Alhajin ke ciki, sam ya kasa zama.
"Bazan iya zama ba Dr.Mohd, hankalina amatuÆ™ar tashe yake, kafaÉ—amin maiyasa ka kawoni office É—inka? Shin wani abu yasake faruwa da SOORAJ É—inne?"Â
"Na faÉ—ama ka kwantar da hankalinka Alhaji, Insha Allah Sooraj zai farfaÉ—o nan bada jimawa ba, sai dai kawai akwai wata matsalane da sai yanzu, da mukayi masa gwaji muka san da ita!"Â Dr.Mohd yafaÉ—i haka yana mai shakkan abun da zai faÉ—awa Alh.Mansur, kasancewar baisan tayaya Alhaji'n zai É—auki maganartasa ba.Â
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'n!! Doctor mai kuma yasake faruwa?" Alhaji Mansur ya tambaya cike da damuwa.
"Amm bawata matsalabace Alhaji matuÆ™ar za akula, nace dama tuncan kunsan cewa yana É—auke da ciwon zuciya ne?" Â
Ai tamkar rugugin aradu haka Alhaji Mansur yaji sauƙan kalaman Dr.Mohd acikin kunnuwansa.
Daɓas haka Alhaji Mansur ya zauna tare da sanya hanu ya dafe kansa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!" kawai yaketa ambata acikin rai da zuciyarsa. "Shikenan kuma lokacin dazai rasa ɗansa mafi soyuwa agaresa yazo, haƙiƙa wannan ƙaddaran tana da girma agaresu baki ɗaya, Allah yabasu ikon cinyeta!" yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Aƙalla yaɗauki kusan sama da 12 minute ahaka,
Idanunsa da sukai jajur dasu ya É—ago ya kalli Dr.Mohd.Â
"Idan nafahimci kalamanka Doctor kanaso kace dani Sooraj É—ana yana É—auke da ciwon zuciya ko?"
"Ƙwarai kuwa haka nake nufi Alhaji, amma ciwon batayi tsanani sosaiba, idan har ya riƙe magani da yardan Allah Zai iya warkewa ako da yaushe, kada ka tashi hankalinka Alhaji, Insha Allah komai zaizo da sauƙi!!"
Inji cewar Dr.Mohd wanda yake cike da buri da kuma fatan ƙarfafawa Alhaji Mansur ɗin guiwa.
Ajiyar zuciya Alhaji Mansur ya sauÆ™e tare da cewa.Â
"Ni musulmi ne kuma nayarda da ƙaddaran da Allah Ya aikomin mai kyau ko marar kyau, kowani cuta aduniya tana da maganinta, cutar mutuwa ce kaɗai bata da magani, haƙiƙa komai da komai na Allah Ne, samun cuta da kuma sauƙi duk waƴannan ikonsa ne, kafun ka tsara naka shi yajima da tsara nashi, idan Allah Ya ƙadarta maka ƙaddara mummuna babu wani mahaluƙi daya isa sauya maka ita, haka idan ya nufeka da kyakkyawa babu wanda ya isa sauya maka ita, babu wani abu aduniya da yafi ƙarfin ikon Allah da kuma Addu'a, zamuyita addu'a Insha Allah komai zai zamo tarihi watarana!!" handkerchief ɗin dake cikin aljihunsa ya ciro tare da sanyawa yaɗan share ƙwallan da suka cika idanunsa.
Murmushi Dr.Mohd yayi tare da cewa "Haƙiƙa duk wani musulmin ƙwarai irinka akeso yakasance Alhaji Mansur, Allah yayi mana jagora"
Da "Ameen" kawai Alhj Mansur ya iya amsawa, sannan suka tashi suka fice daga cikin office É—in.
Direct É—akin da su Ummu suke suka nufa.Â
"Hajiya zaku iya ganinsa yanzu" faÉ—ar Dr.Mohd.Â