Sashe 90
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Cikin matsanancin ciwon da yakeji ajikinsa ya buɗe idanunsa, sosai yakejin wani irin azababben ciwon kai, wanda har takai ga yanajin kamar kannasa zai rabe gida biyu, maida idanunsa yayi ya rufe tare da cije laɓɓansa, yayi danasani marar iyaka, yayi danasanin biyewa zuciyarsa wajen aikata abun da takeso, akokarinsa na cutar da SOORAJ sai gashi yau ya cutar da kanshi, ya kafa tarko don wani ya faɗa sai gashi reshe ya juye da mujiya, tabbas yayi asaran lokaci, tunani, dakuma damarsa, baiyi amfani da lokacinsa ba gashi har ya ƙure masa,  shigowar wasu nurses guda biyu shiya katsesa daga tunanin da yakeyi, ƙarasowa gareshi nurses din sukayi, don dama zaune yake akan wheelchair, ɗaya daga cikin nurses dinne ta zagayo ta bayansa inda ahankali tashiga tura wheelchair ɗin,
Koda suka fito zuwa compound ɗin asibitin nan suka iske ƴan uwan Pharouk ɗin tsaye ajikin mota, haka suka sanyashi acikin mota, inda kaitsaye suka nufi airport, kasancewar jikinnasa yaƙi daɗi hakan yasa ƴan uwansa suka yanke shawaran fita dashi ƙasar Germany.
***
Sam kwana biyun nan takasa gane kanta, hakanan takeyawan jin jiri na ƙoƙarin kada ita, ko jimawa tayi atsaye saitanajin kamar zata faɗi, cikin nutsuwa ta gama shirya kanta cikin wani haɗɗaɗɗen lace blue me kyau da tsada, ƴar ƙaraman hand bag ɗinta ta rataya akan shoulder ɗinta, tana tsaka da zura flat shoe aƙafanta ne aka turo ƙofar ɗakin,  sanye yake da riga da wandon jeans wanda sukayi matuƙar yi masa kyau,  tana ganinsa ta ƙaraso garesa da sauri ta kama hannunsa, cikin yanayi na tsananin sabon da tayi dashi, taɗan turo bakinta gaba ashagwaɓe tace.
"Kai fa naketa jira tun É—azu, please help me!."
Tafaɗi maganar tana me juya masa baya, gane abun da take nufi yasanyashi sakin murmushi, hannunsa yasanya akan bayanta inda ya jamata zip ɗin rigar tata dake abuɗe, juyowa tayi tare daɗan sakin murmushi, idanunta taɗan juya masa ahankali tace.
"Thank you!."
Jawota jikinsa yayi tare da tura kansa acikin wuyanta, sosai ƙamshinta keyi masa daɗi, musamman ma da ayanzun taƙara girma da wayewa, hakan yasa cikakkiyar surar jikinta sake bayyana, cikin yanayin sabo haɗi da daɗin jikin nata ya ɗago idanunsa da suka ɗan soma yin luhu luhu ya kalleta, ganin yanda idanunnasa suka sauya launi ne, yasanya ta jefesa da wani kyakkyawan murmushi, gane abun dayake buƙata yasanya taɗan shagwaɓe fuska, cikin sakalcin da ta saba yi masa tace.
"Namaka alƙawari idan nadawo, amma please karkamin irin na jiya kagafa har yanzu jikina baidaina ciwo ba!."
Murmushi yayi tare da kamo waist É—inta cikin yanayin dake bayyana zallan ajinsa yace.
"Ni yanzu nakeso!."
Idanu taɗan zaro tare da soma ɗan bubbuga ƙafafunta, cikin shagwaɓa tace.
"Please i promise zan baka da dare!."
Idanunsa ɗaya yaɗan ƙanƙance tare da ɗage mata giransa ɗaya, cikin unique voice ɗinsa yace.
"Sure?."
Da sauri ta gyaÉ—a masa kai da sauri tace.
"Yeah!"
Hannayensa yasanya ya tallafi gefen fuskarta inda ya manna mata kiss, cikin silent voice É—insa mai samar mata da nutsuwa yace.
"I will miss you my Sunshine!."
Idanunta ta lumshe ahankali itama taɗan miƙe tsawonta tare da ɗaga ƙafafunta kasancewar ya kereta tsawo, hannayenta ta ɗaura akan shoulder dinsa, cikin nutsuwa itama tayi kissing ɗinsa, take shatin lipstick ɗin bakinta yafito ya zauna raɗau akan fatarsa, cikin sanyin murya tace.
"Nima zanyi kewarka Mah Love ɗina, Inasonka sosae!." tafaɗi maganar tare dayin hugging ɗinsa tight, lumshe idanunsa yayi tare da rungumeta sosai, cikin tsananin ƙaunarta yace.
"Kiyi sauri, jirginku zai tashi ƙarfe 11:00 am yanzun ƙarfe 10 har ma da ƙarin wasu mintuna"  shiru yayi tare da lumshe idanunsa, har yanzun ba ɗabi'arsa bace yawan magana, amma saboda ita kawai yana ƙoƙari wajen ganin ya kamanta.
Murmushi tayi tare da janye jikinta daga cikin nasa, cikin kulawa tace. "Kizo muje nayi dropping ɗinku a airport, saboda a yau nakeso kudawo banaso dare ya miki awaje." Dubansa tayi kana tace. "Ko ba haka kakeson cewa ba?."
Murmushin daya bayyana fararen teeth ɗinsa yayi, tabbas hakanne acikin zuciyarsa, kana hakan kuma yakeson faɗa, saidai bazae iya ba, saboda maganan tayi masa tsawo da yawa, tabbas tafahimcesa fiye da yanda kowa ya fahimcesa, hannunta ya kamo inda ya rungumo shoulders ɗinta, haka suka nufi ƙofar fita daga cikin ɗakin, sam sun shagala da cewar sai sunwuce falon Oummu kafun su samu kansu a compound din gidan, hakan yasa kansu tsaye suka buɗe ƙofar da zata sadasu da falon na Oummu still hannuwansa nakan shoulder dinta yayinda itakuma ta ɗaura kanta akan jikinsa, kallo ɗaya zakayi musu kafahimci irin matsanancin soyayyar da sukewa juna, kana baƙaramin dacewa sukayi ba. Oummu da fitowarta daga kitchine kenan ganinsu yasa ta tsaya tare da kafesu da ido, tabbas tana cikin farinciki ako yaushe, domin kuwa cikin kaso ɗari na halayyan SOORAJ ZIEYADERH tarage masa 50 percent, haryau abun yakan bata mamaki idan taga yanda SOORAJ ɗin ke gudanar da al'muransa da Zieyaderh', musamman yanda yake sakewa da Zieyaderh'n, sannan agaban kowa baya ɓoye irin son da yake mata, duk da cewa ba faɗa yake ba amma yana bata tsananin kulawa.
Ganin Oummu afalonne yasa Zieyaderh ta fara kiciniyar ƙwace jikinta daga nasa amma sam yaƙi sakinta, hakanne yasanya tayi ƙasa da kanta, sau dayawa yakan bata kunya, don kuwa ko agaban Oummu ne idan yaso taɓa jikinta taɓawa yake babu ruwansa,  murmushi Oummu tayi tare da dubansu cikin kulawa ta miƙowa Zieyaderh'n wani babban leda, inda tace "Ga tsaraba nan takaiwa ƴan maiduguri!" ɗan rusunawa Zieyaderh tayi tare da karɓan ledan, cikin jin daɗi tayiwa Oummun godiya.
Amotarsa suka nufi airport inda Babanta dashi ke zaune agidan gaba, itakuwa agidan baya take zaune, koda sukaje airport ɗin sun samu tuni jirgin yakusa tashi, Sooraj dinne yayi musu komai, inda baibar cikin airport ɗin ba saida yaga tashin jirginsu, daga airport din kuwa kaitsaye office dinsa ya wuce, yayinda zuciyarsa ke cike da kewar matarsa wacce ayanzu tazama sanyin idanunsa.