← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 93

Sashe 28

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukansu suka ɗunguma sukabi bayan Dr.Mohd ciki kuwa harda Ziyada.   Wani waje suka nufa daganin wajen kasan na musammanne sannan kuma secret waje ne,   wani ɗan corridor suka shiga sannan suka samu kansu a gaban wani ɗaki.  Dr.Mohd ne ya tura ƙofar ɗakin ahankali, sannan suma suka rufa masa baya, Ziyada ce tayi na ƙarshen shiga.       Tana shiga ɗakin idanunta suka hasko mata shi, kwance yake akan wani gado mai ɗan faɗi, fuskarsa na kallon sama, sanye yake da dogon wando babuko riga ajikinsa, sai bandage ɗin da aka lilliƙa awajen da akayi masa aikin cire bullet.   Wata ƴar wayane aka sanya masa atacikin hancinsa,   sosai ya ƙara haske, gashin kansa kuwa sun kwanta luf,    sam batasan lokacin da hawaye suka gangaro daga cikin idanunta ba, jitayi ƙafafunta gaba ɗaya bazasu iya ɗaukarta ba. Hakan yasa ta jingina bayanta da wani dogon ƙarfe dake kusa da ita.  Ummu kuwa sai aikin share hawaye kawai take da handkerchief ɗinta, shi kansa Alh.Mansur baƙaramin dauriya yayi ba da baiyi kuka ba, musamman ma da yanzu yasan cewa ciwukan ɗan nasa sun zame masa biyu.   Mas'oud ma saida ya share ƙwallan tausayin abokinsa, domin kuwa duk wanda yaga Sooraj ahaka sai ya tausaya masa.   Hannu Ummu takai ta shafi kansa, wasu sabbin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta.  Bazata iya jurewa ba, hakanne yasanya ta juya da sauri ta fice daga cijin ɗakin,  koda ta fita waje tsayawa tayi ajikin wata rumfa tasaki kukan tausayin Sooraj, ganin Ummu tafita yasa Alh.Mansur binta saboda yasan aikin kuka zataje tai tayi, bayan kuma tana da Hawan jini,  sam bayason ciwonta ya tashi. 

Mas'oud ne ya kalli Ziyada dake ta zubar hawaye ta kafe Sooraj ɗin da kyawawan idanunta, duk abun da ke wakana ma sam ita batasan anayinsa ba, gaba ɗaya hankali da tunaninta suna ga Mr.Helper ɗinta,  har batasan sanda hawaye ke zuba daga cikin idanunta ba. 

"Ziyadah!" Mas'oud yaƙira sunanta murya asanyaye.   Sai alokacin ta dawo daga duniyar tunanin da take, bata iya amsa ƙirannasa  ba, saidai ɗago kai da tayi ta kalleshi.

"Ki share hawayenki  ba komai kuka ke magancewa ba, kiyi masa addu'a kawai, yafi buƙatar hakan agareki" Mas'oud yafaɗi haka yana mai cusa hannayensa acikin aljihun wandonsa.  

Kai kawai ta iya jinjina masa alaman "To" domin bazata iya cewa dashi komaiba ayanzu, gaba ɗaya jikinta ya mutu, zuciyarta tayi rauni, duk wani tunaninta ya tsaya cak. 

Dr.Mohd ne yace sutafi hakanan saboda ba aso hayaniya tayi yawa a inda yake.

Alh. Mansur ne ya kalli Mas'oud tare da cewa. "Mas'oud kakaisu gida, nikuma zan zauna anan"

"Banajin zan iya komawa gida Alhaji, nikam nafiso na zauna anan" Ummu tafaÉ—i haka cikin muryarta da ta soma dashewa saboda kuka.

"Zaman asibiti banaki bane Sulaimiyya kuje kawai gobe da safe sai kuzo!" Alh.Mansur ya faɗi haka  aƙagauce saboda sam bayason musu.

"Abba me zai hana kabiyomu na sauƙeku idan yaso ni sai nadawo na kwana anan ɗin"

"A'a Mas'oud baza ayi haka ba, nine nan zan kwana, kuje kawai saida safe idan Allah Ya kaimu, sannan kuma banyarda kabarsu su kaɗai agidaba, ka kwana agidan kaima" Alhaji Mansur yana gama faɗan haka ya juya ya koma cikin asibitin.   Babu yanda Ummu ta iya haka ta shiga cikin motar Mas'oud ya ɗauki hanyar Maitaima dasu inda anan gidan Abba dake Abuja yake.    Wani irin tamfatsetsen gida Ziyada taga sunshiga, gaba ɗaya ginin gidan, gidan sama ne, gida ne mai kyau da girma, komai na gidan gwanin ban sha'awa ne, ko ina dake cikin gidan awadace yake da hasken ƙwan wuta,   Mas'oud ne yasanya key ajikin ƙofar ya murza. take babban ƙofar falon ta buɗu.  haka suka kutsa kai cikin babban falon dake cike da kayan more rayuwa, kayan ƙyale ƙyale dana ado.   Komai na cikin falon tsab tsab yake, Mas'oud ne ya buɗe gaba ɗaya bedrooms ɗin dake cikin falon, acan sama bedroom ɗin Ummu yake hakan yasa ya wuce sama direct ya buɗe mata nata ɗakin.     Ɗakin dake kusa dana Ummu yace da Ziyada ta shiga, gobe zai kawo mata kaɗan daga cikin kayanta.   Saida ya tabbatar da cewa dukansu sunshiga ɗakunansu, kafun ya dawo ƙasa shima ya shiga wani ɗaki.

Aƴan kwanakinnan tasaba duk dare saitayi wanka kafun ta kwanta saboda yanayin zafi da ake ciki, amma yau hakanan tasamu kanta da rashin duk wani kuzarinta, damuwar dake kwance aranta ma bazata bari tayi wani baccin kirkiba balle har aje ga yin wanka.   Hijabin jikinta ta cire tare da ɗalewa kan gadon ta kwanta jigum, yayinda ta sanya hannayenta ta tallafe ƙuncinta.   Tunanin Mr. Helper ne ya tsaya acikin rai da zuciyarta, ganinsa da tayi acikin ciwo yau yasanya hankalinta gaba ɗaya ya tashi, wani abu takeji agame dashi, wanda takasa tantance menene amma ta ta allaƙa abun da sunan TAUSAYI,  juyin duniya tayi amma bacci yaƙi ɗaukarta, haka tayita saƙe saƙe har kusan asuba sannan tatashi ta ɗauro alwala.

Kamar yanda bacci ya guji Ziyada haka ya gujewa Ummu, haka Ummu ta kusan kwana tana sallah, sauƙi kawai take nemawa ɗanta awajen ALLAH, kuka kam tayishi, domin tun tanayinshi da iyaka ƙarfinta, har hawayen suka daina fita.  

7:30 daidai taji anayi mata knocking ƙofar ɗakin da take ciki, dama tana zaunene akusa da ƙofar hakan yasa ta miƙe taƙarasa jikin ƙofar. Koda ta buɗe Mas'oud tagani tsaye.   kafun yace wani abu tayi saurin cewa "Ina Kwana"

"Lafiya lau" ya amsa yana me miƙo mata wata leda dake hanunsa.

"Kayankine kishirya, saiki fito kiyi breakfast, anjima zamu koma asibiti"

Amsar kayan tayi tare dayi masa godiya, ta koma cikin É—aki, shima juyawa yayi ya koma wajen Ummu dake zaune afalo, tun É—azu ba abun da yake sai aikin rarrashi.

Wanka tayi sannan ta ɗauki doguwar rigan material blue wanda yakawo mata tasanya, ɗinkin rigan irin rapper gown ɗinnan ne, sannan tana da ɗan guntun hanu, kallon kanta tayi acikin madubi, tare da kallon rigan azahiri,  mamakin inda yasamo rigan take, domin kuwa tasan baya ɗaya daga cikin kayanta nacan gidan, gaba ɗaya ma kayan daya kawo mata sabbi ne, kuma duk daga ɗinkin materials sai wasu atamfa guda biyu wanda aka musu ɗinkin riga da sket.  Jihabin data gani haɗe da rigan material ɗin ta ɗauka tasanya ajikinta, kasancewar white skin gareta saigashi kayan sunyi mata kyau sosai.   Afalo ta iskesu duka suna zaune, cike da ladabi ta rusuna ta gaishe da Ummu,  amsa mata gaisuwan nata Ummu tayi tanaɗan dubanta.

Akan sofa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, Mas'oud ne ya turo mata plate ɗin soyayyen chips gabanta tare da kofin tea.

Bata wani iyacin abincin sosaiba, tea ɗinnema ta ɗansha da yawa.   Mas'oud ma sama sama yaci abincin, Ummu kam adole takecin abincin, hakan ma saboda umarnin da Alh.Mansur ya bata ne, da yace "Idan tasan bataci abinci ba karta sake tazo asibitin, idan bahaka ba kuwa zata gamu da fushinsa." banda haka babu abun dazai sanya tasanya wani abu na abinci acikinta.

Yauma dai aɗakin jiya suka zauna, gaba ɗaya zuciyoyinsu babu daɗi. Sai ƙarfe uku sannan Dr.Mohd yayi musu jagora zuwa ɗakin da Sooraj ɗin yake.

kamar jiya haka Ummu tayita aikin ƙwalla, Ziyada ma idanunta sunyi tab da hawaye, ɗan matsawa kusa dashi tayi tare da kafesa da idanunta, gani takeyi kamar zai buɗe idanunsa, gani take kamar bacci yake idan katasheshi zai tashi, gani take kamar duk abun da suke yana jinsu,  dubanta takai kan ƴan yatsun ƙafarsa, ƙurawa babbar yatsar ƙafansa ta dama idanu tayi, gani tayi kamar yatsar nasa tana motsawa, gefen hijab ɗinta ta sanya ta share ƙwallan dake cikin idanunta, wanda suka sa take ganin komai dishi dishi, sake kallon yatsar ƙafannasa tayi, sai kuma taga bata motsi, da alama gizone idanunta keyi mata. 

Kallon Alh.Mansur Dr.Mohd yayi tare da nuna Ziyada yace.

"Matarsa ce?"

"A'a ƙanwarsace" Alh.Mansur yabashi amsa shima yana mai kallon Ziyada wanda idanunta ke cike da ƙwalla. 

Kai Dr.Mohd ya jinjina tare da cewa "Inaganin ka ɗauki Hajiya ku koma gida kawai, ita sai kubarta anan, naga kamar yarinyar bata da hayaniya zamanta awajensa bazai kawo wata matsala ba, amma idan Hajiya ce zata zauna kasan dole saita ƙara ta da hankalinta"

Cike da gamtsuwa da kalaman Dr.Mohd, Alh.Mansur ya jinjina kansa.  "Tabbas maganarka haka take doctor, yanzu kuwa zamu tafi insha Allah" 

Da ƙyar da dabara Abba yasanya Ummu agaba yana rarrashinta sukabar cikin asibitin, tare da Mas'oud wanda shine ke tuƙasu. 

Ziyada ita kaɗai akabari acikin ɗakin daga ita sai SOORAJ wanda bashida maraba da gawa.  Akan kujeran dake gefen gadon ta zauna, tare da kifa kanta ajikin gadon.    Tananan zaune har aka ƙira sallan Magriba, Sallah tayi sannan ta dawo ta zauna.   Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi,  zara zaran eye lashes ɗinsa ne suka kwanta aƙasan idanunsa, sukayi luf dasu gwanin burgewa,   gani tayi gumi nata fesowa akan goshinsa, mamakine ya kamata domin kuwa sanyin AC har yaso yin yawa acikin ɗakin.   ɗan kwalinta ta ɗauka tashiga goge masa gumin.  Atunaninta ko sanyin AC'n ne yayi masa kaɗan hakan yasa taɗan ranƙwafo da kanta zuwa daidai fuskarsa, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta akan fuskarsa. hannunta takai kan nasa hanun tashiga goga masa taushin tafin hanunta akan fatar hanunsa, tanayin hakane cikin wani irin yanayi mai ɗauke da nutsuwa.  Aƙalla taɗauki kusan sama da mintuna goma tana yi masa haka. Jin ana ƙiraye ƙirayen sallan isha ne yasata miƙewa daga zaunen da take, ta juya kenan kamar amafarki haka taji ya damƙi hanunta.

*(Alhamdulillah! This is to inform all my lovely fans that this will be my last update and i will insha Allah continue after ramadan. Thank you🙏🏻.)*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *SOORAJ!!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

        *Wattpad*
   fatymasardauna

#romance

*Taƙabbalullaha Minna Wa Minkum. May Allah make us stead fast on the path of the righteous,elevate our iman, forgive our sins and bless us abundantly. Ameen Ya Rab!!!*
*🥀EID MUBARAK My Lovely Fans🥀*

         *Chapter 24*
Chapter 28 · 0% Book details