← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 93

Sashe 86

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hawayen dake tsiyaya bisa kan fuskarta ta sharce, tabbas taji ƙaunar dangin mahaifiyarta ya shigeta, saidai kuma sam abun da sukayi basu kyauta ba, baikamata ace sunyi watsi dasu har haka akan wani ɗan dalili nasu ba.
Duban mahaifinnata tayi cikin sanyin Murya tace.
"Amma Baba baikamata ace donsu sunƙi nemanmu mu muƙi nemansu ba, inasonsu Baba inason naje garesu, naji gaba ɗaya naƙosa don naga ƴan uwan mahaifiyata, tabbas nasan zuwa wannan lokacin sunyi nadama, marar amfani."
Murmushi Baban nata yayi tare da kai dubansa ga Inna Ma'u wacce keta gabzan apple, duk labarinnasu da sukeyi tanajinsu, amma dake kayan kwaÉ—ayine agabanta, yasa komai da hankali garesu batayi ba, don koda ma tamai da hankali itace zataji kunya, don sam bata aikata alkhairi ba.
Girgiza kai baban yayi tare da duban Æ´artasa yace.
"Kitambayi Mijinki idan ya baki izini, sai nayi miki jagora harzuwa garin na Maiduguri!."
Murmushi kawai tayi tare dayin ƙasa da kanta.
Sam su baban nata basu wani jima sosai ba suka tafi, dama sunzone dan su dubata, haka Oummu ta haɗa Inna Ma'u da kayan tsaraba Niƙi niƙi, amma sam haka Baban Zieyaderh ya hanata amsa, haka suka kama hanya zuciyar Inna Ma'u acunkushe sam bataso hanata karɓan alkhairin da Oummu tayi mata da yayi ba, ita aganinta kawai yana mata baƙin cikine,don ita dama asontane shine yabarta ta kwana, saboda ko kaɗan bata gaji da cin kayan daɗin da aka narka musu ba,  tabbas itakam Allah Yaga zuciarta tana tsananin son kuɗi, da kayan ƙyale ƙyalen dunia, haka dai tayita surutanta ƙasa ƙasa, kana tana wurgawa Malam Garba'n harara, can ƙasan ranta tace ɗan baƙin ciki.
***
Kwata kwata jikin Pharouk yaƙi daɗi, kasancewar yasamu wani irin mummunan buguwa acikin kansa, sakamakon haɗarin da sukayi, wanda shine sanadiyar komai,  sanadin mummunan buguwan daya samu hakan yasanya koda ya farfaɗo zai dinga yawan ciwon kai  matsananci,    yanzu haka likitoti suna iyaka ƙokarinsu wajen ganin sunshawo kan matsalan nasa, tsoronsu ɗaya shine kada abun ya shafi  brain ɗinsa, inda suka dage tuƙuru wajen yi masa aiki.

Yau amatuƙar gajiye ya dawo gidan kasancewar kwana biu yatarawa kansa aiki sosai a office, sannan ga ciwonsa dake matuƙar yi masa zafi, yana ƙarasowa cikin bathroom ɗin, ya aje briefcase ɗin dake hannunsa tare da sanya hannuwansa duka biu ya kama waist ɗinsa, sosai ya ƙarewa ɗakin kallo ganin babu ita babu alamunta, ahankali yashiga rage kayan jikinsa, inda ya buɗe drawer ɗinsa tare da zaro wani sabon blue ɗin towel,   ɗaura towel ɗin yayi akan waist dinshi, tare da nufar toilet, tsayawa yayi agaban shower tare da sakarwa kansa ruwa,  saida yaji gajiyan jikinsa yaɗan soma warwarewa kafun  ya kashe shower'n,  wani ɗan ƙaramin towel ya ɗauka, yana me tsane ruwan dake kansa.
Koda yafito daga cikin toilet ɗin sama sama ya shafa body lotion ajikinsa, kallon ƙaton agogon dake saƙale  jikin bangon ɗakin yayi, 8:00 pm daidai, drawer ɗinsa ya buɗe tare da ciro wani tree quater jeans ya sanya, da body spray ɗinsa me daɗin ƙamshi ya feshe jikinsa,  wani ɗan ƙaramin set na glass wanda aka matuƙar ƙawatasa ya buɗe, wani ɗan box mai kyau ya ɗauko tare da buɗewa, wata ƴar siririyar chain ne ta bayyana cikin ɗan ƙaramin akwatin irin ta maza, sosai sarƙan keda azaban kyau, duk da cewa siririyace kuma ta maza ne amma tana da kyau sosai,  akan kakkauran wuyansa yasanya sarƙan,  inda ya ƙarasa gaban ɗan madaidaicin fridge din dake cikin ɗakin,  kwalin fresh milk ya ɗauko, tare da bootle water wanda baida sanyi sosai, tablets ɗinsa ya ɗauko tare da ɓare kowanne ya zuba acikin bakinsa, kana yabi da ruwa, ɗaukan fresh milk ɗin yayi tare da ƙarasawa gaban gadon ya zauna, tunda ya ɗaura bakin goran fresh milk ɗin abakinsa bai cire ba, har saida yashanye sa tas, cikin durstbin ya wurga kwalin tare da shigewa bathroom ya wanko bakinsa, kasancewar yayi sallan isha tun kafun shigowarsa hakan yasa kaitsaye ya nufi kan gado, kwanciya yayi luf akan gadon tare da lumshe idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa hakan yasa bacci ke fusgarsa.

Zieyaderh kuwa tun da tayi sallan magriba tatafi ɓangaren Oummu, inda acan tasamu wata ƴar aminiyar Oummun tazo, nan Oummu tasa ƴar budurwan mai suna Zainab, ta zanawa Zieyadern jan lalle ayatsunta na hannu, domin kuwa Zainab ɗin ta iya sosae.
yanzuma can cikin ɗakin Oummun take tana shirya mata kayanta acikin trolly, don Oummun tasanar da ita cewa zata koma Kaduna yayinda su kuma zasu koma gidansu, sam Zieyaderh bataji daɗin hakan ba, saboda batason rabuwa da Oummu, Oummu ce tashigo cikin ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi, duban Zieyaderh  tayi  haɗi da cewa.
"Shirya kayan ya isa hakanan ae dai ba yanzu bane tafiyan, yakamata ki É—an sarara ki huta, kuma ma naga dare yayi, ya kamata kije ki kwanta, dan inama tunanin yajima da dawowa."

Kunyane ya rufeta jin abunda Oummun ta faɗa, hakan yasa tayi ƙasa da kanta, ahankali take wasa da ƴan watsunta wanda sukasha jan lalle, cikin sanyin murya tace da Oummun "Saida safe."
Fuska ɗauke da murmushi Oummu ta sa mata tare da binta da kallo harta fice,  sosai takejin ƙaunar Zieyaderh'n acikin ranta.

Tun shigowarta cikin ƙawataccen falon tasamu tsaraban ƙamshinsa, hakanne ya tabbatar mata da cewa ya dawo, ahankali tatura ƙofar ɗakin tashiga bakinta ɗauke da sallama, dashi idanunta suka fara tozali inda yake kwance yayi irin kwanciyarnan ta rub da ciki,yayinda yasanya hannunsa ɗaya ya dafe mararsa, da dukkan alama bacci yake,  ahankali taƙaraso cikin ɗakin, idanu ta zuba masa, inda take ƙarewa naked fresh white skin ɗinsa kallo,  sosai komai nasa ya haɗu, idanunta ta sauƙe akan faffaɗan bayansa wanda keta shinning batare dako ɗigon zufa akan skin ɗin nasa ba,  ƙarasowa jikin gadon tayi tare da zuba masa ido, ganin ya kwanta akan hannunsa mai ciwo ne yasanyata ɗan rumtse idanunta,  ahankali takai hannunta daniyar taɓa sa, da sauri kuma ta janye hannunta tare da juyawa cikin sauri ta nufi hanyar   toilet, tana shiga tasoma rage kayan jikinta, wanka tayi tare da ɗauro towel ajikinta, sanin cewa yana bacci yasanya ta  fitowa da towel ɗin ɗaure ajikinta babu ko ɗar,  gaban mirror taƙarasa, kasancewar ana ɗan yanayi na zafi yasanya bata shafa mai ajikinta ba, body spray ɗinta  mai daɗin ƙamshi kawai ta fesa, kaitsaye gaban drawer ta nufa, wata ƴar ƙaraman sleeping dress tasanya, wanda take iyakanta cinya, gaba ɗaya rigan showing take, ganin dare ne yasa bata wani da muba, kwalban turaren da Hajiya Arabi ta haɗota dashi ta ɗauka takuma shafawa ajikinta, sosai ƙamshin turaren ya cika ɗakin, 
Cikin nutsuwa ta taka harzuwa kan kan gadon, zama tayi abakin gadon tare da kai dubanta garesa, zuwa yanzu ya gyara kwanciyarsa inda yake fuskantar sama,  idanu ta zuba masa tana me kallon  kyakkyawar fuskarsa haɗi da lallausan sajensa, sauƙe idanunta tayi akan golding chain ɗin dake wuyansa sosai yayi mata kyau, hakan yasa taɗan saki murmushi,  cigaba tayi da kallon kyakkyawar fuskarsa, ahankali takai hannunta kan fuskarsa, so take ta shafa lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa,  lumshe idanunta tayi alokacin da hannunta ya sauƙa akan tattausan sajen nasa, bazato ba tsammani taji yasanya hannunsa inda ya riƙe nata hannun, da sauri taɗan zaro idanunta waje, don kuwa koda wasa batai tsammanin idanunsa biyu ba,   ahankali ya buɗe lumsassun idanunsa, ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon wani irin fitinannen kallo daya jefata dashi,  lumshe idanunta tayi ahankali tare da buɗewa,  cikin nutsuwa ya jawota jikinsa inda ta faɗa kan chest ɗinsa,  cikin wani irin yanayi yake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, wani irin kallo me matuƙar kashe jiki yakeyi mata, hakan yasa sam bazata iya jure ganin cikin ƙwayar idanunsa ba, domin kuwa wani irin maganaɗisun ƙaunarsane ke fusgarta, ahankali ya ɗago hannunta, kallon yatsunta da suka sha jan lalle yayi, cikin nutsuwa ya tura ƴan yatsun nata abakinsa, lumshe idanunsa yayi yayinda yasa harshe da laɓɓansa duka biu yana tsotsansu ahankali, wani irin matsanancin daɗi ne ke ratsa jikinta, sosai ɗumin bakinsa dake sauƙa akan yatsun nata, suka sanya taji gaba ɗaya jikinta yayi weak,  cikin wani irin yanayi yasake jawota jikinsa, bakinsa ya ɗaura adaidai saitin kunnenta, cikin unique voice dinsa mai sanya bacci yace.
"I MISS YOU!."

(Kuyi haƙuri yau ina azumi shiasa bansamu nayi muku editing ba)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ!!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                 *Wattpad*
         @fatymasardauna
#romance

                  *Chapter 56*
Chapter 86 · 0% Book details