Sashe 51
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tsaida kukannata tayi tare da buɗe jajayen idanunta, samun kanta tayi da murguɗa masa baki tare da yunƙurin zame ƙafarta daga hannunsa, murmushin daya bayyana white teeth ɗinsa yayi tare da cewa "Am sorry ai nama gama!" Kallon Oummu tayi tare da ɗan marairaice fuska, Murmushi Oummu dake tsaye tana kallonsu tun ɗazu tayi, aranta kuwa cewa tayi "Anya abun danayi kyautawa ne?"   "Idan baizama kyautawa ba to tabbas za a ƙirasa da son kai!" Wata zuciyarta ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa. "Allah shine shaidana nayi hakane don samun nutsuwa da salama azuciyar su dukan biyun, idan hakan bai yiwu ba kuwa to tabbas ko mai ya faru NI CE SANADI, sannan hakan zai zama kamar rashin adalci ne ga rayuwar ZIEYADERH!"  maganan da Almustapha ke matane ya sanyata dawowa daga tunanin da take, inda yake cewa
"Yakamata taje ta huta, daga nan zuwa da safe karta taka ƙafan muga idan babu wani matsala shikenan, idan kuma mukaga ƙafar ta kumbura sai muje hospital!" Ya ƙare maganar yana me ƙoƙarin rufe first aid box ɗin dake gabansa.
Da taimakon Oummu Zieyaderh ta iya ɗingisawa zuwa ɗaki,  adaddafe ta iya yin alwalan sallan magriba saboda zafi da ƙafan ke mata, haka ta samu tayi sallah nanma saida dabara don dazaran ta shumfuɗe tafin ƙafanta aƙasa tofa zafi zai ratsa gangar jikinta.
Yana barin falon haka yaji zuciyarsa nayi masa wani iri, yanajin yanayinsa duk ba daÉ—i, peter dake ta zaman jiransa tun É—azu a waje yana ganinsa yataso da hanzari tare da buÉ—e masa murfin motar, shiga cikin motar yayi ransa duk ajagule,  kallon agogonsa yayi yaga 5:50 am. Tsuka yaja tare da lumshe idanunsa da suka É—an nuna alamun É“acin rai acikinsu, 6 daidai jirginsu zai tashi amma gashi har yananeman yin late akan wannan stupid girl É—in, wani siririn tsuka yaja akaro na biyu, shikam ya lura kamar yanda take mashiririciya haka komanta ma yake, yayi imani haukane kaÉ—ai yake wanzar da irin tsoron da yake ganinta aciki da zaran ta ganshi. Hakanan yakejinsa cikin Æ™uncin rai, suna isowa airport ya buÉ—e murfin motar agurguje, da sauri peter ya miÆ™o masa wata Æ´ar black trolly wanda abubuwan amfaninsa ne ke É—auke aciki. Amsa yayi kana yashiga can cikin airport É—in, saida ya kammala komai kafun yataho agurguje ya shiga cikin jirgi don 5 minute kacal ya rage flight É—in ya tashi.  Yana zama akan kujera ya sauÆ™e wani irin ajiyar zuciya tare da jingina bayansa da jikin kujeran, sit belt ya É—aura kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, kamar yanda jirginsu ya tashi zuwa sararin samaniya haka arai da zuciyarsa yake fatan ace damuwarsa tayi Æ™aura daga gareshi, awannan tafiyan yanason samawa zuciyarsa nutsuwa sosai,  musamman akan sabon cutar da ta É—auko mai wanda yakasa sanin gabansa balle bayansa.Â
Kwance take luf akan gado yayinda ta baza gaba É—aya gashin kanta akan pillow, duk da cewa anÉ—au wasu mintuna dajin ciwon nata amma har yanzu tanajin zafi, wannan zafin da takeji ajikinta shine zafin daya tafi har zuwa cikin zuciyarta, ko wani bugu É—aya na zuciyarta yakan zo matane da wani sabon sauyin yanayi, akowanni daÆ™iÆ™a ji take soyayyarsa na hauhawa acikin zuciyarta, sake gyara kwanciyarta tayi tare da lumshe idanunta.  Â
         SINGAPORE
Adaidai wannan lokacin shima ya gyara kwanciyarsa tare da lumshe kyawawan idanunsa, ako wani bugun zuciyarsa ɗaya yana tafiyane da sauye sauyen tunani da yake samu daga ƙwaƙwalwarsa, hannunsa ya ɗaura adaidai saman mararsa tare da ware idanunsa, sauƙesu yayi akan haɗaɗɗen adon zanen dake kewaye saman ɗakin,  daga gefe guda kuwa ƙoyayen wutane keta aikinsu wajen bada kaloli masu ma'ana da ɗaukar hankali, domin duk bayan ko wani second kowanne daga cikinsu yake fidda wani irin diffrent colour na haske me kyau,  daddaɗan sanyin garin da kuma iskan da ake shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na sau ba adadi, burinsa bai wuce bacci ya ɗaukesa ba, don zuwa yanzu zuciarsa takai ƙololuwa wajen matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani, bayan haka kuma gashi akwai gajiya sosai atattare dashi, sauda dama yakan zurfafa tunaninsa akan rashin lafiyansa, saidai kuma yasan komai na Allah Ne sai idan yasone zai baka lafiya, saɓanin haka kuwa kowani irin magani zakasha kodako yana maganin cutar taka sai kaga baiyi maka komai ba, yana matuƙar buƙatar lafiyarsa ayanzu saboda yanaji ajikinsa cewa nan gaba kaɗan zai cire rai da rayuwa, da kuma samun ingantaccen farinciki, tabbas ƙaddaransa babbace amma zaici gaba da ɗaukanta ahaka har izuwa lokacin mutuwarsa.
Bayan tayi sallan asuba bacci tayi sosai hakan yasa ba itace ta farka ba sai after 8. aɗan zabure tatashi daga kwancen da take tare da sanya hannu ta murza idanunta, ganin hasken rana ya bayyana raɗau ta window'n ɗakinne yasanyata zuro ƙafafunta ƙasa da sauri, agurguje tayi wanka tare dayin brush, koda ta fito sama sama tashafa body lotion ɗinta, sauri sauri tasanya kayan uniform don tasan zuwa yanzu tayi latti sosai, zama tayi akan bed tare da jawo cover shoe ɗinta wanda yake na makaranta, ƙoƙarin sanyawa ta somayi, ciwon dake cikin tafin ƙafanta ne yasoma yi mata ɗan zafi sakamakon safa data sanya, shikuma ciwon baison zafi, ɗan rumtse idanunta tayi tare da soma ƙoƙarin tura kafanta cikin takalmin. Turo ƙofar ɗakin Oummu tayi bakinta ɗauke da sallama, ganin Oummu yasanyata sakin murmushi tare dayin ƙasa da kanta cikin girmamawa tace da Oummu
"Ina kwana!"
"Lafiya lau, kinsamu tashi kenan yanzu shigowana na biyu kenan, ya ƙafan naki?" Oummu ta tambaya cike da kulawa.
"Da sauÆ™i Oummu, saidai yana É—anmin zafi amma basosai ba"Â
Kallonta Oummu tayi tare da cewa
"Yanaganki cikin uniform? halan dai baki san ƙarfe nawa bane yanzun ko, kuma ma ai bazaki iya jigilan zuwa school da wannan ciwon aƙafanki ba!" Oummu tafaɗa cike da kulawa
Cikin yanayi naÉ—an sanyi ta gyaÉ—a kanta, don bata da abun cewa.
Murmushi Oummu tayi tare da dafata cike da kulawa tace "To kizauna yau ba zuwa school don mahaifiyar Almustapha da kuma wasu daga cikin ƴan uwana sun taso musamman don zuwa ganin amaryarsu!" Oummu taƙare maganar tana murmushin jin daɗi.
Faɗuwar gaba da tsinkewar zuciyane suka ziyarceta alokaci guda, amma saita ɗan daure ɗago kanta tayi ta kalli Oummu, murmushi Oummu ta mata cike da son ƙarfafa mata guiwa tace "Karki damu kanki akan komai Zieyaderh, ninan matsayin uwa nake awajenki idan kina da abun da kikeso ko abun da bakyaso duk ki sanar dani nikuma Insha Allah Zan sha re hawayenki, nasan ƴan uwana dukansu masu fahimta ne, so bakida wata matsala dasu nakuma san insha Allah Zaki samu ƙauna ta musamman daga garesu, karki damu kinji!" Oummu taƙare maganar cike da lallashi.
Kai Zieyaderh ta kaɗa mata alaman "To"
Cike da jin daÉ—i Oummu tace "Yauwa ki saki jikinki, ki cire uniform É—in zan turo akawomiki abinci, sannan kizauna cikin shiri don anjima zan turo meyin kwalliya tazo ta gyaramin ke"Â Â
Kasa cewa komai tayi har Oummu tafice daga cikin ɗakin, ɗan guntun murmushin dake kan fuskarta ne ya koma, take kuma saiga hawaye suna gangarowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hannu ta share cike da tausayin kanta, haƙiƙa tasan duk wannan abubuwan suna faruwa ne kawai saboda tarasa abu ɗaya aduniyarta wannan abun kuwa bakomai bane face UWA MAHAIFIYA haƙiƙa duk wata Uwa haskece ga rayuwar ƴarta mace matuƙar itaɗin takasance UWA ta gari, UWA itace ginshiƙi sannan kuma farinciki arayuwar ƳAƳANTA, hannu takuma kaiwa ta share hawayenta, sakamakon knocking door ɗinta da taji anayi, tana buɗewa tayi kiciɓus da Nabila hannunta ɗauke da tray ɗin abinci, Nabila ɗaya daga cikin tarin ƴan aikin gidanne amma ita tana ɓangaren kitchine ne, itace me share sharen kitchine da goge duk wani inda aka ɓata, fuskarta ɗauke da ɗan murmushi ta amshi tray ɗin, yayinda Nabila ta juya ta koma, aje tray ɗin abincin tayi tare da soma bubbuɗe plates ɗin dake saman tray ɗin, plate ɗin farko soyayyan doya ne da egg sauce agefe, plate na biyu kuwa pepper soup ne na kayan ciki, ɗayan plate ɗin kuwa shawarma ne me zafi har turiri take, duk acikin abu ukun babu cimarta, hakan yasa da ƙyar ma ta iya cin doyan, sannan ta haɗa da tea, kaɗan taci abincin ta ture gefe, bathroom tashiga ta wanke hannunta, tray ɗin ta ɗauka da niyan sauƙa ƙasa, aikuwa 3 steps kawai ta kawo sukayi kiciɓus da Oummu tare da wata ƴar budurwa dake bayanta, wacce aƙalla bazata haura 27 years ba,  murmushi Oummu tayi tare da duban budurwar cikin sakin fuska tace
"To Bilkh gama Æ´ar tawa please kiyi mata irin wanda kika jima bakiyi ba!"
Murmushi wacce aka ƙira da sunan Bilkh tayi cikin hausarta me bada wani irin sauti tace "Bakomai Hajiya Insha Allah zaki yaba da wannan aikin sosai!"
Murmushi Oummu takumayi tare da ƙwaɗawa Nabila ƙira, dama dayake tana kusa hakan yasa tataho da sauri, tray ɗin dake hannun Zieyaderh Oummu ta amsa tare da miƙawa Nabila tace takai kitchine, duban Zieyaderh tayi cike da kulawa tace "Zieyaderh wannan itace Bilkh shahararriyar me kwalliya ce, please ki bata haɗin kai, maza ki mata jagora zuwa ɗakin ki"