Sashe 26
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru Mas'oud yayi ya kasa cewa komai.  "Tabbas akwai matsala kenan" Inji cewar Alhaji Mansur.
Kai Mas'oud ya kaÉ—a alamar "Eh"
"Sooraj ne?" ya kuma tambaya.
Kai Mas'oud yasake kaÉ—awa alamar "Eh"
Hanu Alh.Mansur Mai Nasara yasanya ya dafe daidai saitin zuciyarsa, da ke É—anyi masa zafi, gaba É—aya acikin kwanakinnan haka yakejin faÉ—uwar gaba na ruskarsa, sannan gefe ga Ummu (Hajiya Sulaimiya) ta sameshi da zancen cewa tana yawan mugayen mafarkai akan É—anta Sooraj. Lallai tun da yaga Mas'oud a birkice haka, yasan matsalan babbace.  Hular kansa ya cire tare da ajeta agefe, har fargaban tambayar Mas'oud É—in yake wani hali Sooraj din ke ciki, Sooraj shi kaÉ—aine É—ansa, sannan kuma yana matuÆ™ar sonsa, sam bayason wani abu ya samu Sooraj, baisan yazaiyi ba, shi ya haifi Sooraj amma baisan Sooraj wani irin mutum bane, komai nasa aÉ“oye yake,baya bayyana duk wani sirrinsa. kullum cikin Æ™unci da damuwa zaka ganshi, ada suna tunanin rashin zama da mace shine matsalarsa, amma da sukayi masa aure, sai suka ga ashe wannan bashine matsalarsa ba.Â
"Abba akwai matsala, Sooraj yana asibitin Lagos baida lafiya, hari aka kai masa a gidansa dake Lagos!" Mas'oud ya faÉ—i haka idanunsa suna mai cikowa da Æ™walla.Â
Arazane Abba yatashi daga zaunen dayake, tare da rumtse idanunsa. Muryarsa amatuÆ™ar raunane yace. "Kada kacemin wasu sun cutarmin da Sooraj, Mas'oud, zan iya jure komai, amma banda labari mummuna akan Sooraj, sun kashemin shi ko? " idanun Alhaji Mansur tuni sun ciko da Æ™walla.Â
"Ka kwantar da hankalinka Abba, Sooraj bai mutu ba kawai dai yana da buƙatar kulawarku ne ayanzu" Mas'oud yafaɗi haka yana mai ɗan share ƙwallan daya zubo daga cikin idanunsa.
"Kayi mana booking flight Mas'oud, amma banaso Ummu ta sani, yau zamu tafi Lagos" Alh. Mansur yafaÉ—i haka cike da damuwa.Â
Gaba ɗaya Alh. Mansur baya cikin nutsuwarsa, hankalinsa atashe yake sosai, baisan awani hali zaije ya taradda tilon ɗansa ba. Babban damuwarsa ma itace Ummu, tabbas yasan idan Ummu taji to dole sai ciwonta ya tashi.
***
Yau aɗan acikin nishaɗi ta dawo gida, domin kuwa kwana biyunnan sosai Farouk ke ɗan ɗebe mata kewa, babban abun dayasanya ta shaƙu dashi, shine irin yanda yake kawar mata da damuwarta, yana sakewa da ita sosai, sannan kuma yana bata dukkan kulawansa, ako da yaushe yakan kashe ayyukansa yazo gareta, hakan yasa tayi sabo dashi.
Gobe zasu kammala jarabawansu, sannan kuma agoben za'a basu hutu.  Fitowarta awanka kenan ta sanya wata doguwar riga ja, kitchine ta wuce, tsaye tayi agaban gas tare dayin shiru, damuwarta ne ta dawo sabuwa fil. Motsinsa takeson ji acikin gidan, rashin jinsa da kuma rashin ganinsa yana damunta sosai, tanason koda Æ™amshinsa ne taji, hakanan takeji ajikinta cewa baya lafiya. Cikin rashin daÉ—in rai haka ta soya indomie taci sama sama. Tunda tayi sallah take aikin duba littafin Physics da zasuyi gobe.  Kamar kullum idan ta kwanta mafarkinsa kawai take, yauma hakance ta kasance domin kuwa gaba É—aya shitake ta gani acikin mafarkinta, yanayin halin da take ganinsa acikin mafarkin sam baya mata daÉ—i. Â
Ƙarfe goma daidai suka fito a exams, direct wajen assembly suka nufa.  Hutun 3 weeks kawai aka basu, duk da haka É—aliban sunji daÉ—i sosai.Â
Cikin sanyin jiki ta ɗago idanunta ta kalli Farouk wanda shima kallonta yake, gaba ɗaya idanunsa sunyi wasu narai narai dasu, harshensa yasanya ya ɗan lashi kan lips ɗinsa.
 "Banason wannan hutun, kwata kwata banason duk wani abu da zai nesantani da ganinki pretty na, da gaske nake inasonki har acikin zuciyata!!"    jin sauƙar kalaman nasa acikin kunnuwanta, ya sata jin tamkar aradu ce ta sauƙa, idanunta dake kan fuskarsa ne suka kawo ƙwalla, "So......na!!" tafaɗa murya asarƙe..
Kallonta shima yayi cikin wani irin yanayi, ɗan matsowa kusa da ita yayi, tare da kai hanunsa ya kama nata hanun.   "Nasan ke ƙaramar yarinyace, sannan kuma bakisan menene so ba, dan inasonki bawai yana nufin zan cutar dake bane, ban taɓa jin soyayyar wata mace azuciyata kamar yanda nakejin taki soyayyarba, Inasonki Ziyadah, dan Allah Kada ki ƙini, tun ran da naganki nakamu da Sonki, har abada kuma zan ci gaba da sonki, namiki alƙawari bazan taɓa rabuwa dake ba!!" Yaƙare maganar cikin wata murya mai sanyi, yayinda gaba ɗaya yanayin  idanunsa suka sauya.  Hawayene suka gangaro daga idanun Ziyada, karo na farko arayuwarta da wani yafurta mata kalmar SO, karo na farko arayuwarta da wani namiji ya tsaya yayi mata magana cikin kulawa har haka, saidai kuma sam bata fahimci kalamansa ba. Ganin yanda hawaye yake fita daga idanunta ne ya sanyashi, kai hanunsa fuskarta da niyyar share mata hawayen, da sauri taja da baya, tare da ƙwace hanunta dake cikin nasa.  Juyawa tayi cikin yanayi na gudu gudu sauri sauri tabar wajen, ƙiran sunanta Farouk yake amma ko waiwayosa batayi ba, balle yasa ran tsayuwarta,  ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, tare da lumshe idanunsa da suka soma sauya kala, har acikin jininsa yana jin son yarinyar, komai nata me kyau ne, kallonta, tafiyarta, nutsuwarta, sau babu adadi yakan samun kansa cikin wani irin yanayi idan yana tare da ita, da ƙyar ya iya shiga motarsa yabar cikin makarantar.
Ziyada kuwa direct inda su Nasmah ke zaune ta nufa, tana zuwa ta faÉ—a kan cinyar Shukrah, tare da rumtse idanunta.
Kallon kallo Nasmah da Shukra suka shiga yiwa juna, cike da tsantsar kulawa suka haɗa baki wajen tambaryarta. "Lafiya Ziyada? meke damunki?" duk waƴannan tambayoyin sunyi mata shine alokaci guda.
Ɗago kanta dake kan cinyar Shukrah tayi, gaba ɗaya hawaye ya ɓata mata fuska.   Ganin haka yasa suka ƙara ruɗewa.
"Kuka Ziyada, meke faruwane?" Inji cewar Shukra dake ƙoƙarin share mata hawaye.
Kanta taɗan girgiza cikin muryarta mai ɗauke da rauni tace. "Bansan me yake nufi ba Shukra, bansan menene So ba, bansan ya akeyinsa ba, gaba ɗaya ya juyarmin da tunanina, dan Allah Shukra ki faɗamin menene SO?" taƙare maganar tana mai sakin ɗan guntun hawayen dake maƙale cikin idanunta.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da ɗanyin murmushi.  "Dama nasan haka zata faru Ziyada, saboda tun randa yasake dawowa nasan ya kamu da sonki ne, So ba ƙarya bane ba Ziyada, akwaita azuciyar kowa, kuma sannan Allah Ne ke halittarta aduk inda yaso akuma lokacin da ya so, zaki gane kin kamu da son mutum ne kaɗai, ta hanyar yawan tunaninsa, yawan damuwa dashi, zai dinga faɗo miki arai aduk wani halin da kike ciki, ƙunci, ko daɗi, amma ni aganina Farouk baida aibu, domin irin Farouk ko wacce mace zataso yin soyayya dashi, gayen yayi tako ina" Shukra taƙare maganar tana sakin murmushi.
Jin kalaman Shukra yasanya jikin Ziyada yin sanyi, hakan yasa ta juyar da kanta gefe, gaba ɗaya kalaman Shukra sun ɗaure mata kai, musamman ma inda tace wai "Idan kanason mutum zakana yawan tunaninsa, sannan zaina faɗowa ranka ako da yaushe"    "Me taimako" shine sunan data fara ambata acikin rai da zuciyarta. Da sauri ta girgiza kanta, sam bazata taɓa sakewa tasoma wannan banzan wasan dashi ba, shi cikekken namiji ne, wanda haɗuwa da kyawunsa har sun wuce gaban kwatance, tayama za'ayi tasoma wannan banzan wasan akansa, kawai dai saboda ya taimaketa ne, yasa takejinsa har acikin jikinta, amma idan ba haka ba ita wacece da har tunaninsa zaina damunta? duk wuya duk daɗi bazata taɓa manta wacece ita ba, Ƙasƙantacciya, wacce bata da wani gata, wacce tataso cikin talauci da maraici. Lumshe gajiyayyun idanunta tayi, tare da sanya hanu ta tallafi ƙuncinta. Tanajin su Nasmah da Shukra suna hira, amma takasa sa musu baki, ahaka har Kamalu driver yazo ɗaukarta, cike da kewar juna tayi sallama da su Nasmah. Ko acikin mota jigum tayi gaba ɗaya damuwowi sun cika zuciyarta.
Lagos Nigeria.
Kuka sosai Alh.Mansur yayi alokacin dayaga yanda É—ansa Sooraj ya dawo, gaba É—aya ba abanbanceshi da gawa, domin kuwa har yanzu baisan inda kansa yake ba. Gaba É—aya yashiga damuwa, duk da cewa sosai likitotin suka dage wajen ganin sun bawa Sooraj É—in kulawa. Waya Alh. Mansur yayiwa babban abokinsa Dr.Mohd dake aiki ababban asibitin Abuja, Dr.Mohd Æ™wararren likitane wanda yasan aikinsa, domin kuwa aduk Abuja shine babban likita,  maganar da sukayi da Dr. Mohd ne yasanya Alh.Mansur yi musu booking flight, ƙarfe 6 na yammaci daidai jirginsu ya É—aga zuwa sararin samaniya. Â
Koda suka isa Abuja Kamar gawa haka aka shiga da Sooraj Intensive Care Unit.
Jigum haka Abba ya zauna, tare da sanya hanu ya dafe kansa. Gefensa Ummu ce wanda tabiyo flight daga Kaduna tazo, kuka take sosai, Abba yayi rarrashin duniya amma sam taƙiyin shiru.
Tafe yake yana tuƙa mota, amma gaba ɗaya hankalinsa baya tare dashi, tunani yake akan abunda zuciyarsa ke raya masa, har azahiri yana ganin hakan shine daidai.
Zaune take akan rug ta nannaɗe ƙafafunta, farcen ƙafanta take yankewa, amma azahiri hankali da tunaninta yana wani waje. Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar falonne yasa ta ɗago kanta da sauri, Dai dai lokacin Mas'oud ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ganin Mas'oud yasata tashi tsaye da sauri, murya asanyaye ta amsa sallaman nashi. Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yana mai ɗan ƙare mata kallo
Gaisheshi tayi cikin murya me sanyi, fuskarsa aɗan sake ya amsa mata, kitchine ta shiga ta ɗauko cup, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko masa ruwa, akan glass stull ɗin dake gabansa ta ajiye ruwan. Tana shirin komawa ɗaki taji yaƙira sunanta "Ziyadah!"
Tsayawa tayi cak tare da É—an juyowa takalleshi "Na'am" ta amsa masa murya asanyaye.
"Ɗauko mayafinki kizo akwai inda zamuje" Yafaɗa yana mai ɗan kurɓan ruwan da ta kawo mai.
"To" tace murya asanyaye. Sannan ta wuce ɗaki, jigum tayi tana mai tunanin ina zasu, wata zuciyarne tasoma ƙoƙarin kawo mata wani mummunan tunani, hakan yasa tayi saurin ɗaukar lufayanta tasanya, tare da ɗaukan takalmi flat shoe ta zura aƙafafunta, lokacin da tafito falon a tsaye ta sameshi yana ta kaikawo da alama yana cikin damuwa.
Yanaganinta yace "Yauwa muje ko" haka suka fito yana gaba tana biye dashi abaya, gani tayi ya tsaya yanawa me gadi magana , hakan yasa taɗan tsaya itama agefe.